← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 95

Sashe 82

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Farida yayanta take nemowa aure Haka ta dage tana kamun kafa wajen Raheela har gidan su Raheela take zuwa,Raheela tana sonsa sosai Tace ta Amince,Farida tace kiyi Hakuri da halin Yaya Nan gaba Zaki ji Dadi kin San shi Shuru Shuru ne,kunya ce da shi kiyi Hakuri Zaki ga kamar Yana da girman Kai Nan gaba zai daina,Raheela sabo da ta rigada ta fada sai ta yarda ai ba girman Kai ne da shi ba Hayaniya ce Bai so sai kunya Dake Damunsa,Farida Kiran Yazed tayi tare da sanar masa,murna ta kamashi kamar yayi hauka yace kice da gaske nakeyi idan ta Amince a kawo kudi,Baki Farida ta Bude tace Yaya Haka akeyi? Sai fa kazo zance sosai kowa ya sanka an San asalinka sai ka nema a baka dama a Kai kudi,Yazed yace to ba ta Sanni ba Mene Kuma zanje zuwa Daya biyu shike nan,ke da kika auri Belloti ai Bamu sanshi ba,Kai Yaya ai Ni kaddara ce tazo min a haka,Nima tawa hakan zata Zo,Farida tace to shike Nan yanzu Mene next? Kije ki mata siyayyar abinda ya Dace ki Kai Mata kice inji Ni,Okay to Zan Kai,Zan Miki transfer,Ina da kudi fa Cewar Farida,bana son naki nafi so na turo da kaina yanda za a fi siya Mata me tsada,bana son karamar harka kin San bana son raini Harkar girma Kawai,Dariya Farida tayi Tace ba damuwa.
Haka Kuwa ya tura kudi Farida taje ta Mata shopping abubuwa na kayan Mata Wanda tasan zata birgeta ta kai,Raheela Ana ta murna ta turawa Yazed da text na godiya.

Reply ya Mata da Baki ga komai ba sai Allah yasa na aureki Zaki San kin auri Miji,Zan shagwaba ki,wannan ba Wani Abu bane.
Raheela kwana tayi tana murna yau akan Kawai ya nuna ya Dan damu da ita ya nuna zai kula da ita ,a hankali ya dawo idan ya Kira ta sau Daya sai ya Dade Bai kirata ba,itama Haka take Masa Haka text ma basa zafafawa gashi kowa Yana kaunar kowa Kamar hauka,Raheela ta matsu yazo shima Haka,Ranar Friday yace zaizo Sunday ta shirya,Raheela duk ta wani gigice ta rasa inda zata saka kanta sabo da Murna,Kannenta suna Palo suna kallon wakoki sai gani Suka Yi ta fito tana ta chashewa Kamar ta zare ,Mamansu ce ta fito ta ganta tana ta rawa Tace ke Kuma lafiya Dan abin kunya a Gaban kannenki ke da ba a ko Ina kike rawa ba? Raheela Tace Mama Nayi goshi,Dariya sukayi gabadaya tace Nayi goshi fa,Mama Tace ke kika sani Suka barta,a ranar yini tayi tana nishadi ko magana kadan akayi sai ta washe baki,Dariya ba yankewa,Ranar Kuwa da zaizo gani akayi tana ta girke girke kala kala,ba Wanda ta gayawa ba Kuma Wanda ya tambayeta,har ta Gama ta fesa wanka,Sabon dinkinta data karbo wata atamfa dark milk and brown Riga da skert ta zuba kyau Dinkin Yan gayu,Mayafi,takalmi dark milk ta zauna tana jiransa.

Yazed Kuwa Kayan da zai saka sai a jaka yazo da abinsa Kano duk da cewa a Jirgi yazo amma Dan Kar su lalace Raheela Bata gani ba Bai saka su ba,Belloti ne ya dakko shi a Airport zuwa gidansa,Yana zuwa Farida sai murna takeyi,shima Yazed baiyi zaton gidan Belloti ya Kai Haka haduwa ba,Bai San irin wahalar da Suka Sha ba a baya.
Abincin Farida ya fara ci ya kalli Farida yace dama Haka kika iya girki? Dariya tayi yace me yasa mu bakya Mana a gida? Belloti yace ai Ina Jin Dadi a kasar Nan,Yana Nuna Farida da Baki yace wannan Yarinyar Indai kudina sun Kai Zan iya siya Mata jirgin sama ma,Yazed ya dinga Dariyar Belloti,Belloti yace tsakanina da ku sai Addua kunyi Rawar gani da kuka iya bani Yarinyar Nan ba tare da tararrabi ba,Yazed Yana dariya yace dole kayi kiba wannan irin girki Haka,Belloti ya Miko hannunsa tare da furta kalli yanda fa skin Dina ta wani Yi balance,amma kafin Na aureta sai kace bayan Bishiya skin Dina a takure ,Anya Kuwa ba home management ta karanta ba? Dariya ta Kama Yazed yace ai Bata Dade da Gama secondary ba ka aureta,Baki Bude Belloti ya furta amma ta iya abin duniya Haka? ai tare zamu shiga University verysoon,so nake kudina su Dan Kara yawa sai na Nema Mana private me sauki mu shige Home management zata karanta tazo taci gaba da kula da gida Kawai girki kala kala masu Kara lafiya,Yazed ya dinga dariya ya Mike yace Bari na shirya kar ku kasheni da dariya,Farida Tace ai ya iya cefane Yaya ka godewa Allah kanwarka tayi Dace.

Yazed wani room Farida ta kaishi harda sake sabon wanka Wai ya Sha Kura a Hanya,Wata Gezna ya Sha Ita ba golden ba ita ba milk ba,hularsa hadaddiya Kalar kayan ya tsirata a Gaban goshi yanda samari ke Yi,takalmin ma iri Daya,cover din wayarsa ma Haka,Sumar Nan Tasha gyara da yawanta gata Nan ta Bayan hula baka wuluk,Yana zuba kamshi ya fito palo,Belloti yace Wow Kamar kasan kano sai da hula....Farida Tace ai dole yau ta kasa bacci,Belloti harda Karin gishiri wane mutum taga wannan tayi bacci ai karya ne Ina bazai yuwu ba ai yau yanda taga Rana Haka zata ga dare,wani ita tayi bacci yau,Yazed irin babban Yayan Nan Harda basarwa Wai baya Wasa da su Kar su Raina shi mutumin da Bellotin ma ya girme shi da kadan,Belloti ne ke Driving suna tafiya cikin nutsuwa Yana satar Kallon Yazed yanda yake ta kallon Kansa a mudubi Kamar mace,Dariya ta Kama Belloti a ransa ya furta yaro Dan ma baka tsoma Cucumber a gidanta na gaskiya ba ai da ka haukace da hujja.

Har Gidan Su Raheela Belloti yayi parking motarsa,Yazed yaga irin tsaruwar gidan da kyawunsa a ransa yace lallai masu kudi ne,Direct Belloti ya Masa iso har cikin palon Mama Bayan ya aiki me Gadi ya sanar mata,Bayan sun Shiga Mama ta fito da fara'a da mutuntuwa suka gaisa sosai,Belloti ba ruwansa yace Yayan matata ne Farida sunansa Yazed,yazo ne nace ya kamata yazo ku gaisa,Mama Tace mashaallah ai ya kyauta mun gode Abban Yara gaf yake da shigowa Inshaallah kafin ku tafi sai ku gaisa,Yazed yace Allah ya kaimu,Belloti yace Bari na kaishi palon Baki a turo Raheela mu gaisa ai ya santa sosai Sanda taje can.

Sai lokacin Mama ta gano dalilin Raheela da take ta faman murna tayi girki yanzu Kuma ta sheka gayu Ashe da dalili,Mama ta yaba da nutsuwar Yazed yayi Mata har ranta wani sabuwar girmamawa ta sake musu ta daban,suna barin palon Belloti yace ka samu shiga shike Nan,Yazed yace Hmmm Kawai Yana wani Taku dai dai,Belloti ya kaishi palon bakin Dake shi ya Zama Dan gida tuni,Zan wuce Yaya Yazed idan ka Gama ka kirani, Alright ya furta Yana latsa waya,Bellotiba ransa yace zaka daina wannan girman Kan Bari tukun kaji karar Inji.

Bayan ya tafi Raheela an kashe uban dauri aka fito, kallon kwaf ya Shiga Mata ba tare da ya shirya ba,duk yanda ya Kai ga son kin kallonta abin ya gagara Haka ya kafeta da kallo itama Haka wankan ya tafi da Imaninta,ya Gama da ita Sallama tayi Masa ya amsa a hankali sannan ta karaso tare da Zama a kujerar Dake facing juna da shi,salon yace Raheela Mai ladabi ce tunda ta fuskanci Yana da son girma harda wani rusunawa tare da cewa Barka da Rana,Ina yini,Ya hanya? Fatan kazo lafiya,Yazed a ransa yace Iyye harda rusuna min Kai lallai Yarinyar akwai tarbiyya a matan Nan na zamani mace ta rusunawa saurayi ai ko mijinta ba kowa ba,sai yaji wani ta sake birge shi,da sakin fuska ya amsa daga Haka Bai sake magana ba,Raheela ta gaji da shurun Tace ya su Manal da Malam?su Afrah fa hope kowa lafiya? Yazed yace kowa lfy Alhmdllh ya sake Shuru ya rasa me zai ce to,sai can Yana latsa waya ba tare da ya kalleta ba yace kinyi kyau,taji sanyin Dadi Tace kaima Haka,Hannu ya Mika Mata Wai ta dawo kujerarsa,tasowa tayi ta zauna a gefensa yaji wani tsigar jikinsa na tashi,Cassava ta fara harbawa ba shiri yace koma kujerar ki Wasa nake,haushi taji tace Wai ko baka damu Dani bane? Sai kana Abu kamar dole Ni fa Ina da samari na masu kaunata sai na zabi Daya ciki idan wahalar Dani zakayi gwara Kar Abu yayi nisa.

Yazed harda nuna Kansa da yatsa da kike? Ni kike fadawa kina da wani?a ransa sai bakin kishi yake Yana tsoro Kar ta guje shi,yace me kike so na Miki? Tana shagwaba Tace ba caring ba komai,babu su I love you,I miss you,Kira,text duk babu,to ai Ni ban taba soyayya ba shi yasa Amma tunda Haka ne karki damu sai kin gaji da jinsu,a Haka dai suka danyi Hira sannan Ya Kira Belloti zasu tafi ya Bata kudi Taki karba,Belloti Yana tsaye a gefe ya basu waje Amma Yana Jin me suke cewa kasa kasa,Yazed yace ki karba bana son musu,Raheela Tace Nifa bazan karba ba,Ki karba tun kafin na cusa Miki su a cikin Bra karbi,Dariya tayi a kunyace dama ya iya irin Haka shima,Belloti Yana ji yace Kowa dai shegen Kansa ne a Haka Kamar na Allah yanzu Kuma Muna barin Nan sai aga ya dakko carbi,Karba tayi tana godiya Suka tafi.
Chapter 82 · 0% Book details