Sashe 22
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Suka cika cikinsu tare da samun nutsuwa da dare Suka shiga motocinsu tare da komawa gida,Mai Martaba yaji Dadi da dawowar Dan nasa lafiya sai yaga yayi Yar kiba,Ameer Yana kasa a zaune Gaban Mai martaba amma Fuzail a kujera ya zauna shima ba ruwansa,Sarki yayi Murmushi tare da furta Fuzail Naga Kamar kiba ma kayi? Tunowa yayi da Abar kaunarsa Manal ya saki murmushi tare da furta ganin masoyiyata kullum ne ya jawo,Ido sarki Ya zaro tare da tambaya Masoyiya Kuma? Fuzail yace Yeah Dad na samu macen da nake so wacce Zan aura,Farin ciki ya Kama sarki yace da gaske? Sosai ma Dad Yar sila ce karama Allah ya hada mu sabo da haka zan kawota Nan gaba ta gaishe ka,Sarki yace Kai Mashaallah Amma nayi Murna wannan abin murna ne,Allah ya kaimu tazo,Jakadiya tana gefe,Sarki ya furta Jakadiya a sanar Matar da Fuzail zai Aura zata Zo gaisar da mu Nan kusa Inshaallah,Allah ya Kara yawan Rai magana Kamar ta Isa kunnen kowa cewar Jakadiya.
Fuzail mikewa yayi ya fita,Ameer ma ya wuce gidansu,11pm Fuzail yayi Shirin bacci cikin kayan baccinsa masu Dan Karen tsada silk purple Bayan ya kwanta wayarsa me azabar tsada ya jawo tare da Danna Number layin Dake Wayar da ya bawa Manal ta rike.
Manal tana kwance ita Daya ta kasa bacci in Banda tunanin Fuzail dinta ba abinda take yi,a fili ta Furta ko yanzu suna Ina oho,Addua ta Shiga Yi Allah ka tsare su,Allah ka Kai su gida Lafiya,Wayar ce ta dauki ruri sai da ta Bata tsoro sabo da Rashin sabo,Kawai dagawa tayi Dake ya koya Mata,Sallama tayi a nutse,Ido ya lumshe tare da yin Juyi a saman makeken bed dinsa,Naira darin data taba ajiyewa cikin Bra ta zaro zata bawa Me Napep Fuzail ya kwace ita ya dakko a cikin aljihunsa Yana Kare Mata kallo Yana magana a waya da Manal.
Masu Sharhi Ina Matukar godiya wallah Kuna birgeni.
AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭
IS DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP.
26-30
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Ummu Shahidah
Ikeen Mama
Hajjora investment
Jamila sule
Minerh
Yar Albarka
Maman Ashraf
Zainab Abdullahi
Rukeey a Bako
Ummu Abba
Alhamdulillah
Salihu Ubaidat Haruna
Zakiyya Bello
Rukayley
Muryarsa Manal taji da sauri ta Zabura tare da mikewa zaune, Farin ciki ya mamaye Mata zuciya sabo da Bata Yi zaton da gaske zai nemeta ba a tsorace take da mutanen duniya,Saita kanta tayi Kar ya Gane ta haukace a Kansa a nutse Tace Ina yini? Kunje gida Lafiya? Alhmdllh ya furta a wani yangance Kamar bazai magana ba,Manal a ranta Tace Izza ta motsa ko Kuma gajiya ce oho,tunaninta ya katse Mata ya Family naki hope Basu Miki komai ba?dama ai Kaine basa kauna tunda ka tafi Kuma ai Basu da damuwa Dani kayi Hakuri da abinda Suka maka,ba damuwa tunda ba kece kika min ba,murmushi tayi Tace yaya Ameer? Yana Nan yayi bacci kin ganshi kusa Dani,Hmmm Ina Dan Uwan naku da matarsa fatan dai sun karbe ku ba matsala,Fuzail yace bamu da matsala an Bamu masauki me kyau dakinmu harda Tiles da komai,Manal Taji Dadi ta tambaya da katifa? Katuwa ma harda katon Bargo ya Bata amsa,Yayi kyau,Yaushe zanzo zance to? Manal sabo da Murna Harda dunkulewa a saman katifarta Tace Saturday ko Sunday,Murmushi yayi Wanda sai da taji sautin har kwanyarta sannan ya furta is too far yayi nisa,to zaba da kanka,Wednesday zanzo Kinga yau saturday remain 4days,Allah ya kaimu.
Bacci zan tafi yace,Allah tashe mu lafiya cewarta,Yace baki missing Dina ba? Missing.....Missing ta shiga tambayar kanta,yace bana koya Miki ba ko kin manta tuno Ma'anar tayi Tace oh na tuna Ina Yi Mana,to kice kina missing dina,Manal da shagwaba Tace to Wai Ni kullum kullum sai na dinga ta Fadin abu Ni Allah Kai zaka fada yau,Hausawa kanku Kato ne Wai Baku so namiji ya Gane Kuna sonsa da yawa,Ni fa ba Dan kasar Nan bane ya kamata ki sani Halina daban Ni duk irin wannan zurfi can ciki ban Saba shi ba,so kike wata ta fa'a min?
Idan Baki fa'a wace zata fa'a? Manal ta fara dariyar Hausar tashi ba shiri tare da ce Masa to Bari na Fa'a, Nima ukku Nika hwadi makka aradun Allah gobe Jibi bani Sake Hwaddi makka,Fuzail yace ke Ameer yace Yar Fullo ce Hausar ma Baki iya ba sai ta daji,Manal a ranta Tace kaji Ameer Munafuki Ina ganinsa na Allah harda fadawa Farooq ta daji nakeyi Nima Zan dage na koyi ta birni wallahi na daina Zama Ana Bari na a baya ana min Dariya daga yau ta karfi Zan canja.
Ina jinki Bacci,Manal Tace Ina missing naka to,Say You love me,I love you,Love you too ya Furta yace karki Bari na sake tambayar wannan sai na roka Zaki fa'a,Shuru tayi ya datse wayarsa Addua yayi tare da kwanciya bacci,itama Haka.
Rugar Su Manal Majalisar su Belloti ta cika makil da matasa Yan Fulani suna ta shaye shayen Sigari,wasu Kuma suna cin Gyada suna Hira da ihu da dariya,gaba dayansu sun Tara Uwar Suma sun San Relaxer tayi wani yalo yalo kowanne da Kalar askinsa na iya shege,gashi kowanne da sandarsa a hannunsa ta kiwon shanu,Belloti ne ya fito sanye cikin wata koriyar Shadda rigar iya gwiya ta dameshi sosai Kam Kam a jikinsa Haka wandon ma Sai zip aka sa Masa a kafar wandon Shaddar shi a Dole gaye, gashinsa gaba Daya an kwalkwale ko Ina an bar wata Yar toliyar gashi a tsakiyar Kansa sai kace Shedan shi a Dole gayu yayi,Duk garin ba Wanda ya Kai Belloti wayewa da daukan wanka,Yana wulwula Sanda Yana fito da bakinsa ga wani katon karensa Baki wuluk Yana binsa a baya.
Belloti Yana zuwa Suka tafa Daya bayan Daya sannan ya zauna shima a saman wani benchi kato,Belloti yasa aka yanko musu rake kowanne na Naira ashirin suna ta garza.
Wani abokinsu lawi shima yazo ba ko Sallama yace Yaya Belloti wannan wankan fa Haka sai kace Manal tana gari,Belloti Yana gabzar rake ya cika bakinsa yace Ina cikin fadamar rake Bari tukun,sai da ya Gama sha Lawi ya sake cewa Belloti yanzu idan Manal ta samu Miji a birni tayi aure fa? Belloti yace Alqur'an duk uban Wanda ya aurar min Mata sai ya Gane kurensa, suna dariya wani Yahaya yace to idan me kudi ne fa? Belloti yace sai na jira Nima idan nayi kudi na kaishi Kara kotu na fadawa alkali ya aurar min mata ya sakar min ita ko uban waye komai kudinsa wallahi sai munyi Sharia da shi a kotu ko uban waye.
Ja'e ne ya taho shima da wata addarsa ga Sanda Yana wulwulata Yana zuwa wajen matasan yace Wahala tazo fa,Wahala ce ta saka Riga da wando take yawo da kafafunta tana Tafiya,Wahala? Matasan suka Furta sun San Indai akace Wahala ta saka Riga da wando to akwai matsala,Ja'e yace Belloti Kawai ka Kara Hakuri,Belloti yace Kai Malam lafiya? Ja'e ya zauna a gefen Belloti ya fara tausarsa Yana Masa nasiha wacce Basu San dalilin wannan Nasihar ba,Ja'e Bai kulasu ba duk Kuwa da tambayoyin da suke Masa ko lafiya?
Kafadun Belloti ya sake dafawa ya Furta shi lamarin Allah Haka yake idan Abu ba rabonka bane to fa baza ka samu ba Matukar Allah baiyi ba,ya Zama Dole ka yarda da kaddara Belloti, Ja'e Dan rainin hankali sai Hakuri yake bawa Belloti karshe yace kayi Hakuri kabar Maganar Neman aurenka na Manal ka canja Budurwa kawai.
Jiya Baffa na matsa Masa sai ya min Istahara a kanka da Manal to dai cikin ikon Allah yace yanzu ma Haka wani ne a ranta ba Kai ba Kuma kasan Istiharar Baffa babu karya,Gaban Belloti ya yanke ya Fadi,tsaye ya Mike tare da Furta yau Istiharar Baffa tayi karya,tsafi dama yakeyi ai ba malamin Allah bane,ka taba gani Istiharar gaskiya anga Abu kururu? Ka fadawa Baffan naka karya yakeyi matsafi,Uban ma waye yace a duba min?nace a ayi min duba Dan Uwarku? Karma ku dauki wannan zance wahala data saka Riga da Wando wannan ita ta jiyo idan taga Dama wahalar ta saka Wando Jeans ma Ni ba ruwana Kuma wallahi ko waye sai munyi rikici da shi akan Manal, Amma yanzu bazan zauna jiranta ba na gano wata cika a kasuwa Ranar Juma'a Ina so farkon watan sabuwar Shekara Januware (January)ake cewa ko ta a watan Kuna ganina ku kirani da Masoyi sai watan Zan fara soyayya karshen shekarar a daura min aure na samu wacce Zan dinga kankamewa cikin dare kafin nayi kudi na dawo da Manal wajena,Dariya Suka dinga yi,Lawi yace to Belloti yanzu fa me zai Hana ka bi Manal can birni? Ina fama da ciki na da kyar nake iya ci da kaina Ina Ni Ina birni ai yanzu Budurwa tafi karfi na.
Kasan mu sai Dole muke cin tuwo a kauyen Nan da kyar nake samun kudin shayi ma bare har nake rike wata,auren gata idan an maka sai dai fa a tukunyar cikin gida kuyi ta cin tuwo,matar tawa Zan dinga bawa tuwo ta lalace Ni da nake so ma Nan gaba na bar shanun Nan na koma birni,idan nayi kudi yarana kullum su Sha miyar dage dage da Mai Amma Nan Kauye sai dai a cika musu ciki da tuwo cikin yara duk ya kumbura kaga Yara Malam ciki Kamar Tulu ga jarabar Shan Madarar shanu cutar da shanu suke Yi wallahi itace take Kama yaran Fulani sabo da direct muke Shan Madara ba tare da an dafa ba,Ni Nan da Dan wani lokaci wallahi fecewa zanyi in tafi Neman arziki birni.