← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 95

Sashe 48

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida sababbin kawaye ta samu Yan wanka,Gaba dayansu su Uku zuwa suke Ana musu Allura me da fari da kiba,Walida ita ce Suka fi shiri da Farida,Walida itace ta koyawa Farida yawace yawace yanzu basa Zama kullum suna gantali a gari a Haka zasu samo mazajen aure masu kudi,Cikin lokaci kadan Farida ta fara komawa wata baturiya itama ta Sha Allura,Malam gajiya yayi ya Kira Farida yace ke Dan Ubanki kema Kwailin din kika shiga Yi? Kalli Fatarki duk kin kankareta da mayamayan banza,wallahi ki shiga hankalinki Baki da Aiki sai yawo da shigar banza,ga kanwarki can tana zamanta a dakin mijinta asirinta a rufe ke kince sai me kudi wallahi ki fito da Miji ko wallahi na zabo Miki da kaina,Farida da fitsara Tace to Ni me nayi Kawai dai ka tsaneni,Ni duk anbi an tsaneni a gidan nan,babu me kaunata sai Uwata dama na sani ai,Mutum baza a Bari ya samu Mijin kirki ba me Dan abin hannunsa Ni wallahi sai na zaba na darje.

Takaici ne ya Kama Malam yace ai shike Nan Mu zuba Ni da ke sai na gani idan kece kika haife Ni Dan ubanki, laifin Uwarki ne ita ta lalataki,da sauri Hajiya ta Fado dakin tana nuna Malam da yatsa karka sake ambatar sunana,naji dama kana wani Zaginta ta Zama Fara tayi waye da waye ai Kai dama baka waye ba kolo ne,dama wani kolo ne zaiyi abin Kirki,Sanda kaci zamaninka ai gwara Farida da Kai,Mene baka Yi ba? Wacce tafka tafka ce baka Tafka ba eyeeee sai yanzu zaka Zo kana wani wanwanawanawan......'yata ce a kyale min abata yawwa ehe dama mu mun Dade da sanin ba kaunarmu kake ba,Kuma Dan bakin ciki sai dai ya mutu abinda ba a so mu samu sai mun samu.....Malam har kwalla yayi sabo da takaici gashi baida bakin magana shima yasan ya sheka tsiya,tuba ya sake Yi a ransa yace Ina muku Nasiha kuji tsoron Allah ko Dan guzurin gobe alkiyama,Kai guzurin kayi? Wanne guzuri kayi na tafiya lahira har kana da bakin magana,wallahi ka sake Walakiri sai ya dilliki gadon bayanka ma tun a Nan duniya cewar Hajiya.
Hannun Farida ta ja Suka wuce abinsu.

Ummi na fita Fuzail ya fisgo Manal zuwa jikinsa,ta kankame shi suna dariya,Tsinin Hancinta ya taba da Yatsansa tare da furta Yar Kuyanga ta? Manal tana Dariya a jikinsa tana sake makale shi ta furta Ambaby na,Lips dinsa ya turo gaba ta Masa kiss mmmuhmmahh,Sake Yi sukayi har sau Uku a saman Lips,zata Mike yace More Baby ya tallafo fuskarta ya hade bakinsu a hankali yake tsotsa Yana Mata wani irin kiss me zafi.

Tsayawa yayi kadan yace tsaya a kwashe abincin Nan dama Ummi ce ta damu sai naci ko akwai abinda Zaki ci a ciki? Manal ta dauki wani Naman rago yanka daya,Fuzail yace ajiiye Indai shi Zaki ci akwai na Amarya na musamman,Nan take ya Kira a waya wata baiwa tazo ta kwashe lokacin Manal ta buya a kitchen.

Kitchen din ya shiga wajenta inda yace dafa min Indomie kin iya dafa Indomie ya furta tare da Hugging dinta ta baya ya daura habarsa a saman kafadarta Yana saka hannunsa ta cikin Hijab dinta tare da lalaubar Albarkatun kirjinta masu tafiya da Imaninsa.
Girkin ta daura sannan ta juyo ya jawota jikinsa a Haka ta sarkafo hannayenta ta wuyansa suna kissing juna tana shafa Masa gashinsa me laushi da kamshi.
Manal ya kalla yace ki zauna a Haka ban yarda da Ummi ba zata iya dawowa,ai Kuwa sai ga Muryar Ummi tana cewa Fuzail kana Ina na fasa fita ance Goslow yau akeyi a hanya,Fito ka karbi wannan zanje na kwanta bacci nakeji,Ta kitchen taga ya fito Tace me kakeyi a kitchen? Yace Indomie Zan dafa abincin na kasa cinsa,tunda nake ban taba ganin ka Shiga kitchen ba Son,Murmushi yayi yace ai na koyi dafa Indomie Ummi zauna na Gama dafawa kici kiji Dadi,Ummi Zama tayi ta canja Chanel din Larabawa anci sa'a a kujerar dazu ta zauna wacce idan ka zauna ka bawa kitchen baya.

Manal sabo da iya shege duk ta cire Hijab da Nikaf din ma Sai kayanta na Kuyangi silk yard,lallabowa tayi Fuzail Yana kusa da Kofar kitchen din ta rungumeshi ta baya suna dariya marar Sauti,Yana cewa ai Ummi Film din Nan yayi,Ummi ba tare da ta juyo ba ta zubawa TV Ido tace shi yasa bana gajiya da shi Indai ana haskawa sai na kalla.
Samun waje yasa Fuzail ya jawo Manal ta dawo gabansa ya Mata kiss a kumatu,Cikinsa ta mintsina da sauri yace ahh Dadi ai Dadi ne da Film din nan,Ummi Kai dai Bari Son,Manal sai ta shige kitchen sai ya bita suka Gama Murje murjen juna sai ya dawo Kofar kitchen ya tsaya Yana ta yiwa Ummi rainin Hankali.

A Haka Manal take girkin,a spoon ta ebo Indomie din tazo har bakin Kofar ta zuba Masa a baki,yace Delicious lokacin a film din Ummi an hasko Ana cin abinci,Ummi tace ka koyi kwadayi Kaima ko? Daga kallon abinci a film, Manal ta koma kitchen tana ta dariya kasa kasa,Fuzail ya fada kitchen din shima Yana dariya yace Zan daga Hannaye kina zuwa Kawai ki dinga Hugging Dina,Manal Tace an gama,Ya koma Bakin kofa tare da daga hannaye sama Yana karkada waya yana furta Ummi Kasar Nan ba Network,Ummi Tace ka fiye surutu kasan dai halin kasar taku ka kyaleni nayi kallo na kafin na tashi na tafi,Manal tazo ta Masa zazzafar runguma, ya lumshe Ido ta baya Suka fada kitchen ya dauki Manal cak ya jujjuyata a ciki,Tana Gama dafa Indomie din ya goyata a bayansa Kamar Baby, ya zubawa Ummi Indomie a plate tare da sa fork ya fito da Manal a bayansa har kusa da kujerar Ummi sannan ta sauka ta koma kitchen da sauri ta boye,Sai lokacin Ummi ta juyo baya ta kalli Fuzail tace har ka gama? Tace bani na tafi da ita part Dina bacci nake ji,Ta Mike da plate a Hannunta tace Allah ya maka Albarka kana kula Dani ga yanda kake bin Umarni na kana birgeni.
Tana gaba Yana binta a baya harda dagowa Manal Hannu Wai ta fito su Raka Ummi,Sadaf Sadaf da kasada ta bi bayansu,Ummi tana saka kafafunta a waje ko Gama fita Bata Yi ba Fuzail yace H U G Wai Hug,Manal kuwa tayi hugging dinsa Yana ta yiwa Ummi sai da safe Ummi ta Yi Gaba ko juyowa Bata Yi ba da ta kure Fuzail amma Ina.

Ajiyar zuciya Fuzail ya sauke sannan ya kashe duk wani abin wuta tare da kulle ko Ina Gam inda ba Wanda zai iya ko ganin alamar haske a part dinsa bare, Indomie dinsa Manal ta dauka tace Kafafu na sun gaji ga bacci Ina ji,Fuzail a ransa yace Zaki ga Bacci yarinya yau.
Harda shigewa dakinsa Direct tare da fadawa Toilet ita a Dole zata Yi wanka tayi bacci.
Ummi Kuwa tuni taci Indomie dinta tana Santi a ranta harda cewa ai ban San ya iya girki Haka ba gobe nace ya sake dafa min Wata,Wanka tayi ta kwanta kafin ma tayi Addua bacci me karfi yayi gaba da Ummi ko motsi Bata Yi sai bacci.

Fuzail Kuwa ya Gama matsuwa a hargitse yake baya hayyacinsa shi yasa dazu shi da Manal ya sata Suka dinga Iskanci a bayan Ummi,bazai iya Jiranta ta fito daga wankan Bama,Indomie dinsa ya manta da ita har ta bushe yayi tafiyarsa Daya room din yayi wanka,Alwalar ma da kyar ya iya yinta,Turaruka ya shafa daga shi sai Boxers Manal taga ya shigo Wai har yayi Shirin baccinsa shi,tana Daure da Towel ya jefa Mata hijab dinta da kayan Bayi yace pls sa muyi nafila Akan Allah ya tausasa zuciyar Ummi ta dinga kaunarki,Manal ta washe Baki tare da sakawa Tace to muyi, Jallabiya Fara ya zura tare da janzu Sallah Adduar ma kadan yayi nutsuwa babu ita a jikinsa,Kayan Manal ta cire tare da adanasu yanda ko Ummi ta shigo baza ta gansu ba,Daure take da Towel shi Kam ya cire Jallabiyar sai Dan guntun Wandonsa,Hajiya Babba ta cika fam ta batse kadan take jira,Manal da kuruciya duk ita Bata kula ba Kuma Bata Ankara ba Tace Bari na dakko kayan bacci na,Hannunta ya rike yace no Ni bana so,mu kwanta Haka,Kafafu ta fara dokawa a kasa da shagwaba Ni....Ni....Allah ...ban Saba bacci Haka ba,Ni a gida ba Haka nake kwanciya ba Watarana ma harda Hijab nake kwanciya,Fuzail yace Nan gida ne to? To Wai.....a daji muke Dan Allah kaji ka da wani magana Nan gida ne mana,.

Tana Masa shagwabar Nan wani Kara hargitsa Masa lissafi takeyi,tana Kara tunzura shi yana Jin wani sabuwar sha'awarta,tunawa tayi taga ya saka key a dakin ga abubuwan ci Nan a ledojin take away iri iri Amma Fuzail ya manta ma da su ba tasu yake ba,Manal ce ta lura Tace laaa da Ice cream a ciki? Sai lokacin ya kalli Ledar yace babu,Naman da kace fa na Amarya? Da sauri yace shima babu duk ba kayan ci bane,ganin zata Bata masa lokaci ya kashe light tare da fisge Towel din dake jikinta,Manal ta saki Salati la'ilahaillahu wannan wanne Abu ne Haka? Wacce irin lalata ce wannan sabo da Allah?tana maganar tana fadawa saman bed tare da janwo bargo ta lullube jikinta,Gefenta ta bubbuga da tafin hannunta tare da cewa Zo ka kwanta a wajenka ga iya tsaginka nan,a haukace Manal taga yayo kanta Bata taba ganinsa Haka ba,tsorata tayi tayi tsalle gefe tana wayyo Allah na shiga Uku,Kuka take kokarin Yi zata gudu ba dama,Manal ta Mike tsaye a saman bed ga Bargo ta jawo jikinta Tace dama kana da Aljanu? Kuyi Hakuri dama rashin ji ne ya kawo Ni dakin ku,Ummi tana hanani kulashi Ashe gata take min ban sani b.....Fuzail ne ya cafkota lokaci Guda Manal ta fara wutsil wutsil tana wayyo na shiga Uku na lalace,Aljanu Ga indomin ku can kuje kuc.....
Chapter 48 · 0% Book details