← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 95

Sashe 57

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

5pm Farida tana kwance a tsakar gidansu tana latsa waya suna chat da samarinta, yaro ya kwada Sallama Wai Farida tazo inji Wani a waje,da sauri Hajiya Tace a me yazo? a machine ko a kafa ko a mota? Yaron yace a mota yazo,Hajiya tace to tashi wala'allah Mijin naki ne ya karaso,Farida da sauri ta Mike ta shige daki taci kwalliya sharp sharp,kafin ta fito Hajiya ta leka Kofar gida ta hango wata zundumemiyar mota Wata Benz Baka,Da sauri ta shigo da Murna tace Jeki sauri shine ma Naga Alama,Farida tana tafiya cikin yanga ta Isa inda motar take a Kofar gidansu,Wani Matashi ne ya fito wankan Tarwada zai Kai Mate din su Fuzail Yana kamshi ya fadada murmushinsa tare da cewa Barka da isowa Gimbiya,Farida tayi wani Fari da idanuwa Tana yanga tana tauna chewgum Tace yawwa ya kake? Tana wani yatsina ita a Dole babbar yarinya,Matashin yace lafiya Alhmdllh,yace Nasan Baki Sanni ba Sunana Fahad Ibrahim,Unguwar da nake bani da nisa da ku,Farida Ni Doctor ne bazan boye Miki ba na taba aure matata wajen Haihuwa Allah ya Mata Rasuwa Ina da yaro Daya Wanda ta Haifa ta mutu ta Bari Yana Hannun Mahaifiyata na Dade Ina sonki Allah ne baiyi nazo ba sai yanzu,Farida ba ko Allah yaji Kan Rai a ranta sai murna take itama maikudin Nan ta samu a daina Mata yanga,Nan take Tace ba komai na Amince Allah yasa albarka amma Yaron ba nice zan rike maka shi ba ko? Dan Ni bazan iya rainon dan wata katuwa ba gaskiya,ka barshi a inda yafi wayo wajen Mahaifiyarka yawwa shine amma Ni akan na rike Dan wata gwara na fasa auren,Baki Fahad ya Bude yace Ni Kuwa Kinga dalilin Yaron ma zanyi aure,Kuma Mene Dan kin rike Dan wata?ai da na kowa ne,Kuma yaro Ina ruwansa? Farida Tace Dan kishiyar Zan rike? Lallai baka San wace Farida ba,Fahad ya jinjina Kai yace to gaskiya Naga baza mu shirya Dake ba,Bai ma dace na aureki ba magana ta Allah,yo dama Ni Nace kazo raino zaka aureni nayi maka wallahi bada Ni ba ta juya tayi tafiyarta.

Har ga Allah Fahad Bai taba aure ba ya ganta Yana Sonta yazo ya gwadata Dan yaji irin hankalinta gashi tayiwa kanta,Fahad kwata kwata baya rayuwa a kasar a can Dubai yake Aiki Likita ne a Dubai yake Neman Matar Aure,Har ya shiga Mota sai ga Ruma kawar Farida,Ruma kyakyawa ce chocolate me haske,Sai Yaga tafi Farida komai ma,Magana ya Mata cike da Nutsuwa ta je inda yake tare da Masa gaisuwa ta mutunci daga Nan ya Dan jata da Hira sama Sama da barkwanci daga Nan ya shigar da soyayyarsa wajen Rumaisa,Rumaisa ta gani ta kyasa ya tafi da ita,Yanda yacewa Farida Yana da Mata da yaro Haka yayiwa Ruma bayani,Ruma tace Allah yaji kanta da Rahma,Allah sarki naji tausayin Yaron wlh Inshaallah Me zai Hana a rikeshi,ai Indai kana son mutum baza ka kyamaci Dansa ba,duk Wanda kaga Bai son jinin Dan mutum to baya son Iyayen ma,da ai na kowa ne, Rumaisa ta dinga tsari Fahad yaji hankali da sanin ya kamata Nan take ya karbi contact din Ruma daga wannan ranar Suka Fara soyayya,sai da ya tabbatar me hankali ce sannan ya fada Mata gaskiyarsa,Itama Ruma ta sanadiyar Farida ta tsinci dami a kala,Kanwa da Babbar kawa sunyi mazaje na nunawa sarki duk a silar Farida tana ta tsallake rabonta.

Ko sati biyu ba ayi ba da zuwan Fahad sai ga wani yazo wajen Farida,Farida Idan Baku manta ba Allah ya Bata farin jini ita ba kyau ba amma sai ayi ta sonta tana samun samari na kirki Kuma masu abin Hannunsu amma halinta yasa ta kasa amfana,Wani Babban Custum ne yazo,Babban mutum ne ga kudi yazo Mata a mota Golf,Babba ne Amma kyakyawa ne fari zai Kai 45yrs Yana da mace Daya da yaransa uku,Tunda Farida taga Golf ta fito ta Masa wulakanci na gaske harda Shopping ya Mata idan sun dai daita zai Bata kayan amma Farida ta wulakantashi Takaicin hakan yasa ya Fisgi motarsa cikin bacin Rai Irin da matsayinsa aka Masa wulakanci haka,Baya hayyacinsa Haka yake tuka motar Yana zuwa Titi Shukrah ta tsallaka zata je Shagon Su Yazed ta gaisar da su amma Custum Alhajin Umar ya maketa da mota,Allah yasa Bata ji rauni da yawa ba,a gigice ya fito har ta Mike ma tana dingishi Ana Mata Sannu,Ya fito Yana sannu Dan Allah kiyi Hakuri wallahi Ina cikin bacin Rai ne, muje Asibiti Shukrah tace ba inda yake min ciwo ma wlh na gode,To in ba damuwa muje na ajiyeki a gida,Badan ta so ba Haka ta shiga Gaban motar ya kaita har gida,Suna Isa zata fita kayan Shopping din masu tsadar gaske da ya siyo zai bawa Farida su ya dauka gaba Daya ya bawa Shukrah ledojin,ko Number dinta Bai karba ba ya Kara Mata dubu Hamsim yayi gaba abinsa.

Shukrah tunda ta shiga gida ta Bude Kaya ta kasa rufe Baki,Takalma masu tsadar gaske kala biyar kowanne da jakarsa,sai atampopi masu tsada da lace kala Uku,ga Shadda kala biyu Yan gaske,Sai wata sarka ta Gold me shegen kyau,Shukrah Bata yarda Gold bane sai da taje wajen masu siyar da Gold aka auna Mata taji kudin sarkar wajen dubu dari biyu,ta dinga mamaki ,Shukrah akwai son me kyau tunda ta ganshi fari me kyau shike Nan ta koma tunaninsa sai Yazed ya samu lafiya da nacin Shukrah,ta fada son me Gold,Manal ta bugawa Waya tana ta Bata labari,Manal Tace to Yayan Nawa fa? Ke rabu da wannan Yaron ba aure ne a gabansa ba mayen Boko Kawai,sai yangan jaraba yake min Dan yaga Yana da kyau Nima yanzu nabi inda yake da dahir ki tayani Addua Allah yasa ya dawo,Wallahi ya hadu so Gentle gashi kyakyawa,tunda na ganshi naji ya min yasan me yake ba irin Yayanki ba yaro sai kuruciyar masifa,Manal Tace Zan Miki rashin mutunci Wallahi Shukrah Yaya Yazed Din? Ae shi din fa wani girmata yayi abinda sa'a nane,Manal tace kinci abinci,yaushe Zaki zo? Shukrah Tace wannan gidan naku marasa mutunci inzo suna min kallon banza,Manal Tace akwai labari pls idan naje school Zan biyo na daukeki,sannan zamuje gidan Matar Nan na siyo kayan aiki Fuzail akwai kwarzaba dole sai Ana kara gyarawa,Dariya Shukrah ta dinga Yi tace a Ina kuke haduwa kika ce min ke Ummi ta Hana komai,Ina ruwanki nace kizo zanzo na dauke ki Kawai,Okay Allah ya kaimu Hajiya Princess ta Prince Fuzail an Zama babbar yarinya.

Bayan Kwanaki Tanko ya Gama shirinsa shi da Fuzail,Duk wani Kaya an dinkawa Tanko kyauta,tun kafin Ranar Tanko ya koma me tsafta Yana gyara ya siyo sabulunsa na maza me kyau Yana wanka da shi yayi wani fresh,yau Saturday zasu je, wanka ya fesa,yasha wata Shadda Silver me tsada, Sani abokinsa Suka nada Masa rawani na girma,Billen Dake gefen fuskar Tanko kusa da kunnuwansa Yan biyu biyu rawani ya rufe shi,Tanko ya dawo wani kyakyawan matashi Kamar ba shi ba,Takalminsa Half cover na sarauta me kyau da tsada,Wata sabuwar Motar Fuzail Fara ya shiga,Sani shine Driver, mota Daya Kuma na takewa Tanko baya,suna tafiya a hankali cikin nutsuwa,Babu me Gane Tanko sabo da rawani ya canja Masa kamanni duk an rufe inda za a Gane shine,a Kofar gidan Su Farida sukayi parking a Kofar gidan su Farida,Lokacin da Yamma su Falaqi sun dawo daga school da gudu Suka shiga gidan suna cewa motoci sunzo,Hajiya tace sai me Farin jini wallahi maza tashi Jeki shine ma Dama ance da motoci zai zo ba mota ba.

Farida dama ta dau wanka zata fita gantali sai ta fasa ta fito wajen Masu mota ko Bari Bata Yi an Kira ta ba,sai tayi Kamar Unguwa dama zata tafi ta fara tafiya,Sani ne ya fito da sauri dama da sauri yace Farida da Allah Dan tsaya Abokin Yarima Fuzail ne yazo wajenki,tun wajen Daurin auren Fuzail ya ganki yaji Yana sonki Dan Nuhu Tanko ne wani Hamshakin me kudi a Adamawa Kuma Nuhu Tanko Kanin Sarkin Adamawa ne jinin sarauta ne,yanzu Haka Shi wannan Hakimi ne ma Kuma shine Dan Majen Adamawa,yanzu ma Ziyara yazowa sarki shine Yace zaizo wajenki,Farida ji take Kamar tayi ihu sabo da Murna,harda cewa Sani Ina wannan Garan Abokin naka Tanko? Sani yace ke rabu da gara Yana can bakin gate,Muje ga saurayi kinyi na kece raini wallahi karki sake ki tsallake rabonki daga sama,Karki ki Amincewa sunansa Hakimi Iliyasu Nuhu Tanko,Kowa yasan waye Nuhu Tanko a kasar Nan idan Baki sani ba ki tambaya kiji.

Kin San sunayen masu kudin Nan ba Dadi ne da su ba amma idan da kudi sai aji sunan yayi Dadi,Yanzu ki duba Dangote Mene Dangote Dan Allah Ina sunan yake da Dadi Amma dake akwai kudi ya kika ji idan aka ce Dangote? Farida Tace wallahi Dadi Kawai kudin kake hangowa,Yace mu tafi cikin Birnin Kano kiji Isyaka Rabiu,yanzu ce nine Ake ce min Isyaka ya kika ji? Farida Tace sai ka koma Wani Gara,Yace Buhari Dan Allah Ina Dadi Buhari fa,Yanzu kalli talaka ace sunansa Buhari,Ko Dadi babu cewar Farida,Yace Attahiru Bafarawa,Mene Wani Bafarawa,Yanzu Kamar Tanko Ace Bafarawa,Dariya Farida ta fara tace cab Dakiki Tanko,Yace kawo min Sunusi Lamido Sunusi Dan Allah Dake kudi ne ba sai yayi Dadi ba?Amma Talaka ace Sunusi ya kika hango Sunusi me kayan Miya? Mirgayi Ado bayero,yanzu ace Ado nine yanda nake Talaka akace Ado ya zakiji Amma Dake masu kudi ne sai yayi Dadi cakwai abin ya bada citta,to Ga Baban Iliyasu ya kika Ji Nuhu Tanko,Farida Tace idan na tuno Tanko abokinka sai naji ba Dadi Amma tun daga Motocin wannan me kudin naji sunan yayi Onga,Sani yace shi yasa kike birgeni muje Dan Allah Nima ki kankaro min girma ko na rabauta da kyauta me tsoka,Angama cewar Farida Suka karasa.
Chapter 57 · 0% Book details