← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 95

Sashe 85

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai wurin 2pm ta dawo Yana Zaune yaga ta shigo jikinta a sanyaye suna hada Ido ta fashe da kuka,gabansa ne ya Fadi yace lafiya?rudewa yayi ya rungumeta tsam a jikinsa taci gaba da kukanta,mayafin ya zare Mata ya kaita Bedroom tare da zaunar da ita a saman cinyarsa Yana tambayarta lafiya? Result ta Mika Masa ya duba yaga ance tana da hawan jini an Rubuta Mata magunguna,hankalinsa ya Dan kwanta sabo da yayi zaton wani Babban Abu ne,Mene ne to Dan kina da hawan jini na masu ciki ne dama wasu suna Samunsa idan suna da ciki kina Haihuwa Zaki warke ko Likita Bai Miki bayani ba? Manal tace da gaske yake? Sosai ma Inshaallah Zaki warke,Dan ya kwantar Mata da hankali yace ai Nima na taba Yi gashi na warke,Sanda kana Brazil? Fuzail yace Sosai,Sanyi taji a ranta ya Shiga kwantar Mata da hankali har ta manta ma tana Fushi da shi,sunyi missing juna suka fada saman bed suna nunawa juna kauna Kamar zasu cinye kansu Manal da katon cikinta ya girma sosai,sai da yayi nisa gab da zai fada wata duniyar ta zare jikinta,lafiya? na gaji ni Allah bacci zanyi bani da lafiya,Hankalin Fuzail tashi yayi ya kankame Manal,Tace wayyo cikina da sauri ya saketa Yana lallashinta,har yanzu Baki huce ba? na huce Mana,Baki yafe min ba ko? Shine Zaki min wannan hukuncin? Manal Tace a'a ba Wani hukunci,Rirriketa yayi yace please ki bani Sunshine Dan Allah nace,bazan iya sake kwana Haka ba,Sanda ka tafi ka barni ka tuna Ni Zan iya nemanka ko bukatarka ce Kawai bukata,na dinga hadaka da Allah kaki saurarona,na yarda nayi laifi na fada Miki Zan fada Miki Kuma me ya kaini Abuja akan komawarmu can naje Naga tsarin komai ba Wani Abu ba,nafi so sai na Gama komai idan kin Haihu sai mu koma,Manal tace Alright it's okay Amma Allah Indai ka sake min Haka Ni bazan iya hakura ba,bazan sake ba nace ko please ya Furta,Manal sai lokacin tace a bani Cassava na shanye abata to....shi yasa kike birgeni,gashi Nan kin Gama zauta ni Bana iya komai idan bakya kusa,Manal harda yanga daga Nan suka fada sabuwar duniya,sai da Manal ta nemi afwa sannan ya Dan rage zafinsa.

Sai da suka samu nutsuwa ya rungumeta sosai Yana shafa gashinta cikin rada yace I'm Sorry My Sunshine Nasha wahala Dana tafi babu Ke kusa ba shiri na dawo gida,naji jiki shi yasa na dawo gida ba shiri bazan iya rayuwa babu ke ba,Manal tace hmm Kawai,Karki sake na sake abu kisa damuwa a ranki gashi kin jawo Mana Hawan jini,ai Kaine kasan Ni bana son damuwarka bana so na Bata maka Rai shine kayi Fushi Ni Kuma Ina da sa abu a Raina shi yasa dama Doctor Tace jini na ya kusa Hawa na kiyaye Kuma ka tafi na Shiga damuwa ai gashi Nan ya hau sai kaji dadi.

Zai warke Inshaallah kinji,Allah yasa ta furta tana sake shigewa jikinsa yace nayi missing da yawa second round Baby,Manal tana Jan aji Tace sai 5:30am,da Asuba fa kenan kike nufi? Baka ga bani da lafiya ba,Dan Allah kiyi Hakuri ki taimaki Dan Ummi nayi missing dinki da yawa bazan iya kaiwa 5am ba,Manal Tace bacci idan ka shirya ka tashe Ni,bafa Haka kike min ba Sunshine ko har yanzu Haushi na kike ji?haushin me Zan ji,ko 30mnt ba ayi ba Fuzail ya damu Manal sai da ya sake,a Haka kafin safiya yayi sau Uku,bayan Sallar Asuba ya sake Yi.

Ameer kuwa dadin da yaji da Manal ta bawa Matarsa alawa yasa ya Kira Fuzail Duk da Badi'at taji wahala yace daga yau na Zama Abokin Belloti nima,Fuzail ya dinga dariya yace Dan Allah ku Nemo inda ake siyar da ita ko kwali Guda na siya wacce zata Mana shekaru,Suna ta dariya,Ameer yace ku bani number din Belloti shegen Gari, Haka aka bashi number Belloti.
Rumaisa tana can da Fahad dinta a kasar waje Yayin da Shukrah ke GRA katafaren gidanta ita Daya tal.

Ameer ne ya Kira Belloti Suka gaisa yace Ameer ne Abokin Fuzail Belloti yace ah guy ya garin ne ya ake ciki ya amarya? Ameer dama Nan yake so a tabo,yace Dan Allah Alawar daka siya nake so wata wacce.....ba sai ka fada ba na ganeta ai kala wajen biyar ne alawoyin kowacce da aikinta akwai ta Mata akwai ta maza akwai wacce ake Sha mace da namjin,Ameer yace kana birgeni kasan Kan gari Belloti yace ai ba a Zama Haka matan yanzu sai Namiji ya hada da tsumi shima sabo da kullum a cikin Shan Kayan aiki suke idan ka zauna sai a zaune ka,Ameer ya dinga dariya Belloti sai kace wata mace,yace akwai wasu tsumi ma na karfin maza zaka Dade kana Aiki ba tare da Injinka yayi sanyi ba,Ameer yace a sa Mana a mota a kawo Mana sai mu karba a Tasha,Belloti yace angama,ai Ni sabo da a Kauye abokaina da yawa suna da Aure sannan wannan Alawar Uche ne ya bani as a gift na aure na.,Ameer yace shege Uche,Haka suka Gama iya shegensu sannan Suka Yi Sallama.

Kwanci tashi ba wuya komai Yana tafiya dai dai cikin so da kaunar juna,cikin Manal ya Gama Isa Haihuwa ya cika wata Tara cif Yayin da bikin Yazed Saura kwana Uku rak duk wani shirye sun gama.
Manal tana Jan cikinta Haka take lallabawa sai da Fuzail ya kyaleta dole ta tafi gidansu zata kwana,Farida sunzo Belloti Yana can sai an daura Aure zasu taho da amarya gaba Daya,a Haka Kuma Belloti yace Faridansa a jirgi zata je ba Hawa mota, ya dage ya Siya Mata ticket. Dangin Malam Dana Annatu sun cika gidan Malam,Hajiya da kishiyarta Karimatu Suma nasu Dangin sunzo,Hajiya wannan lokacin ta nutsu duk wannan bakin cikin babu da ita ake komai itace Akan komai ma ka rantse ita ta Haifi Yazed,Haka Amaryar Malam ma mace me Hakuri ba ruwanta ango yayi gayyata ta gaske,Ana shagali Amarya tsoro ne a ranta sabo da Yazeed ba Wani Daukanta yake da muhimmanci ba,hakan yasa Tace baza tayi komai ba a daura Aure Kawai ya Isa.

Manal tunda tazo gidan Bata tashi ba,Sallah ma a zaune takeyi,Fuzail sai aikin bugo uban waya ba ji ba gani,washe Gari da safe Ango,Fuzail,Ameer,su Malam harda Maimartaba da tawagarsa da wasu abokan Ango jirgi Fuzail ya biya musu Suka tafi masu zuwa Kuma wasu Suka wuce a Motoci lafiyayyu, 11am dot aka Daura Auren Yazed da Raheela,Ango yasha farar Shadda irin kyan da ya zuba ba'a magana,Bangaren gidan Maimartaba Hajiya Babba da Amarya tare da wasu Yaran Mata biyu sunzo gidan su Manal sunyi Allah Sanya Alkhairi,Farida ansha Lace,Manal Kuwa Shadda tasa doguwar Riga katuwa sabo da cikinta,Farida ce akan komai tare da Kannenta,Yazed ko pics dinma Bai tsaya anyi ba Suka taho gida,bayan sun dawo prince direct cikin gidan ya shigo sabo da ya Gaida su Annatu sannan ya duba lafiyar Manal,tana bedroom a kwance tayi turus,Bayan ya gaisar da su Annatu ya Shiga wajenta.

Zama yayi a gefenta tare da duka Kansa a saitin kunnenta Yana tambaya ya jikin? Kalau kike Kuwa? Manal ta fashe da kuka tace Dan Allah ka kaini asibiti a janyo min nakuda ta karfi wallahi na gaji,Edd dinki fa ya cika tun last week kiyi Hakuri kin kusa,tunda ma an samu hawan jinin babu ai da sauki,lallashinta yayi kafin Maimartaba ya Kira shi a waya ya tafi,Yana zuwa Kiran Maimartaba yace aikenka zanyi Lagos zaka Kai Sako,yace Manal fa ta kusa Haihuwa Taya Zan dinga nisa da ita,yau zaka je ka dawo Inshaallah minti Nawa ne a flight,Fuzail badan yaso ba Haka ya Kira Manal a waya ya sanar Mata Tace a dawo lafiya lokacin Kuma ta fara Nakuda tun safe take Jin ciwon kasa kasa Bata San nakuda bace sai da taji abin ya gagareta sannan ta Kira Farida,Tace Farida ku kaini asibiti Ina Jin mutuwa zanyi,Farida tana Jin Haka ta bazama ta sanarwa su Annatu da Hajiya Sharifa a sirri sabo da mutane a gidan da yawa.

Kafin a Kira Yazed yazo a kaita asibiti Manal ta fara kuka duk ta tonawa kanta asiri,Yazed yazo aka tafi da ita Asibitin da take ganin likita,anji matar prince da wuri aka karbeta Ana lallabawa dama abinka da private,Manal duk kukanta ya ishi mutane,Hajiya Sharifa tace ke Dan Allah karki ja Mana abin kunya mace da kukan Haihuwa,duk macen da tayi kukan Haihuwa sau Daya to har ta Gama haihuwarta sai tayi kuka abin kunya ne wlh,Yazed yace Dan Allah ki kyaleta tayi abinta haba kin takura Mata,Kafin masu dubuta su Zo Manal ta zaci Yazed ai shine prince rigarsa ta rike Tace ka cuceni Fuzail ka cuceni.....ta fisgi rigar Yazed Kamar zata yagata....waje aka Yi da Yazed Manal tana Allah ya Isa Fuzail ai dole ka fita ka Gama Dani,gaf da zata Haihu Hajiya Sharifa Tace Addua akeyi,Manal ta fara Summassabila yassara ......Summassabila yassara Allah ka yassare min......Kan Jariri ya fito ta sume sai da taimakon likitoci ta karasa Haihuwa mace ta Haifa wata firit da ita Bata da wani girma sai wahalar masifa,Hajiya Sharifa Tace sai kace bakya cin kayan Vitamins Yar nan, Kina gidan me kudi komai gahi Nan abailability (available)wannan yarinya Kamar Yar gidan masu fama da cutar yunwa akanta kike wannan kukan he kace Ana gididdibaki Kai wallahi Kin bada Mata kinji kunya Manal,Manal ta Haihu lafiya ta Gama abin kunyarta na uban kuka da fadar maganganu da zagin Miji,sai tayi tsuru tsuru,Hajiya Sharifa tace hegen Ido Kamar me Jin bacci kin Gama abin kunyar a cikin gidan biki kika dinga tsala ihu wallahi Bari Fuzail ya dawo sai na fada Masa,har kina zaginsa Dan Ubanki Sanda kike manne masa wa yaji kanki sai yanzu,Manal dariya tayi Tace wallahi kinji kuma sai naji na warke garau,Kyace Haka Mana tunda ke Baki da juriya.
Chapter 85 · 0% Book details