← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 95

Sashe 16

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna bakin Titi Tace to sai mun tsallaka Titi,yace cross titi? Okay Tsalka na Gane,Dariya Manal tayi Tace Niger ta cuceka wallah Wai tsalka,muje ba mota Hannunta ya rike sosai Yana kallon Titi Suka tsallaka,Napep ta tare suka shiga duk Bai iya Hawa ba Amma Haka ya daure ya nuna ya Saba ai,Har cikin Hospital ya kaisu sannan Manal Tace me Nape Nawa? Fuzail yayi Dariya yace Napep not Nape Haka Ana ce a Nigeria,Manal Tace to anji Dan gwani nace Napep,Me Napep kallon Farooq yayi Wanda Fuzail kenan Jin yanda yayi Hausar,Itama Manal gaba Daya harshenta na Yar Fulani sai kace fulatanci take Yi,Me Napep yace dari biyu Manal tace aradu baka Isha ba,dari nika baka aggarin mahaukata mukkai,Fuzail yace how much? Me Napep yace two Hundred Naira,Fuzail ya daura hannu a Kai Wai yayi tsada da yawa yace ba mafiya muke Yi ba fa?Manal sabo da dariya harda rike ciki Farooq yaji hausa harda dogon sentence,Me Napep yace ku kawo dari na tafi Kuna Bata min lokaci,Manal yanda Suka Saba a Kauye ajiye kudi a cikin Bra,Hannu ta zura ta zaro wata dukunkunanniyar naira dari,Fuzail ya zaro Ido da mamaki,me Napep ta mikawa Naira darin kafin ya karba Fuzail ya kwace kudin ya ja Manal gefe yace akwai cuta jikin kudi ....no....no...fasa turancin yayi yace ba'a sawa a bra noooo....really bad,Manal tace na daina naji Farooq bashi kudin mu tafi,Fuzail yace no....ya taba nono naki,Me Napep zai taba laushin a jikin kudin,Manal tayi Dariya tace laushin ba makalewa zaiyi ba a jiki ka bashi mu tafi,Fuzail fafur yaki bada Naira dari yace me Napep yazo su shiga hospital ya karbi wani kudin wajen Ameer,Me Napep da masifa yace Amma wannan Mijin naki ya cika kishin bala'i in Banda hauka a jikin kudin kirjin zai makale da zai Hana kudin aikin banza,shi kadai ne me Mata,ya kalli Fuzail yace har Mata biyu gareni banza Dan akan wannan Yar kauyen ma ance maka Dan Iska ne ni? na yafe muku wallahi kuje Ni baza ku Bata min lokaci ba,Manal ta dinga Murna Tace da gaske ka yafe? Yace ae wallahi Yaja Napep yayi gaba,Farooq ya boye kudin a aljihunsa.

Suna shiga Suka Iske Yaron Ameer Yana kula da shi Amma Manal Bata sani ba,ita dai ance a Asibitin yake taimako yakeyi Kawai,Manal tace Wai ku Kira danginku Mana ko a waya ne ganin wata karamar kwakurar waya Vivo a Hannun Ameer,Shi Kuma Fuzail Wanda ta sani da Farooq tasa Wayar Tecno ce pop 3 ta talaka dai dai gwargwado sabo da matasa yanzu suna kokarin rike Yar babbar waya,Ameer Yana kwance Fuzail ya kyafta Masa Ido,Ameer yace ai kin San duk Dangin namu mun fada Miki suna kauyen Niger,mu Nan zuwa Mukayi Neman wajen Zama kafin mu samu sana'a akwai Wanda yake Dan garin namu anan Baya Nan sai Nan da sati biyu zai dawo shi zai mana komai,Manal Tace Haka Farooq ya fada min Allah sarki Allah ya baka lafiya Sannu, Inshaallah kana warkewa zaku samu gidan zama.

Allah yasa Kinga bawan Allah din Nan ma Yana kawo min abinci Sadaka Ina ci gashi Yana kula dani cewar Ameer ,Manal tana murna Tace da mutumin mun gode Allah ya saka da Alkhairi,mutumin yace Ameen ai yiwa Kaine ko ba komai Zan samu lada sabo da Allah nayi,Manal Tace kai Ameer gashi Kana Jin hausa sosai ya akayi Farooq shi Bai Jin hausa? Ameer yace ai ni kusan a Kano state Muka Yi karatu shi yasa muka ji hausa sosai,shi Kuma a kauyenmu yayi primary da secondary school,sannan University ma wata yayi wacce a Kauye take ma Kuma ba a hausa a yankin,Manal Tace ayya shi yasa ashe to shike nan.

Ameer yace yanzu matsalarmu kayan sawa Amma wannan bawan Allah yace zai siyo Mana kayan gwanjo kala biyu Sadaka sabo da Allah,Manal tana murna Tace har Ina tunani wanne Aiki zanyi na samo kudin da Zan siyo muku ko gwanjo ne ku samu amma bawan Allah mun gode,Fuzail dai Manal yake ta kallo da tsananin mamaki sai murna takeyi kamar wasu Yan uwanta.
Ameer Yana kallon irin kallon da Fuzail kewa Manal Yana mamaki mutumin da Mata ma hadaddu Basu isheshi kallo ba sai wannan ga kauyenci ga talauci duk da yasan karyar mutum ya kalli Manal Bai sake kallonta ba sai dai hassada amma Manal abar kallo ce,Manal tace Farooq ka zauna a Nan Bari naje gida nayi Mana abinci sai nazo na tafi da Kai gida,bani naira darin Nan sai na hau Napep da ita ta furta tana Mika Masa Hannu,Fuzail ya kyaftawa mutumin Dake kula da Ameer ido Nan take yace kanwata kema ga Sadakar dubu Daya kiyi amfani da ita,Manal ta Bude Baki Tace Malam kudin sunyi yawa ka bani duka Sadaka Haka? Yace karbi Allah ya bamu Lada kema ai kin taimaka.

Manal har kasa ta durkusa tare da sa Hannu biyu ta karbi kudin tana uban godiya da Addua sabo da Bata da ko sisi dama so take taje ta nemi aikin wanke wanke da shara a gidan masu Saida abinci tayi ko na yini Daya ne a biyata ta samu ta dafa musu abinci da kudin sai gashi ta samu Amma duk da Haka tasan a tsadar abin duniya a yau dubu zata Kare gwara ta nemi kudin tun yau gobe ta samu su Kara kawai.

Da murna ta kalli Farooq tare da cewa Zan wuce sai nazo daukanka,Murmushi yayi ta tsira Masa Ido yanda yake da mugun kyau duk da shigar Daya canja tare da kasumba da uban gashi Bai Hana kyawunsa bayyana ba musamman idan yayi Murmushi kyawawan hakoransa suka bayyana ga wani lips dinsa red masu kyau,Hancinsa kadai ya Isa a kalli Farooq,ga kirar surar jikinsa musamman skin dinsa abin Yana birge Manal ita Kam ta Gama ganin kyau wajen Farooq inama zaiyi Aski da yafi Haka kyau ta furta a ranta,tana gama tunaninta tace na tafi ta juya tana waigowa tana kallon Farooq,Hannu ya daga mata har ta bar asibitin.

Tana tafiya wajen wata me siyar da Abinci a Tasha ta tsaya,suna mutunci da Dattijuwar Manal tasan Yaya Yazed ya hanata irin wannan Neman kudin Amma Dan kudin Daya bar Mata su Farooq sun cinye su Dole ta nemi wasu,Ladidi Tace Manal yau ko aikin kika Zo Yi ne? Da sauri Manal Tace ae Ladidi,okay Zo dama ga wanke wanke ya taru bana so customers su fara yawa ba a wanke ba,ai Kuwa Manal ta shiga wanke plates da spoons tana ta faman Yi ana siyen abinci Ana cinyewa za a kwaso wasu a kawo ta wanke,tunda ta fara aikin Hannunta Bai huta ba har 3pm tun safe,lokacin ta tuna da bakinta da suke wuyanta, Nan take tace tafiya zata Yi ta Gama aikin yau,Ladidi taji Dadi sabo da Manal ta Iya Aiki sai tace Manal akwai shinkafa da Miya,fried rice,sakwara da miyar Egusi,ga tuwo ma ki zaba a ciki me Zaki iya ci na zuba Miki ki tafi da shi gida ai kin Sha aiki,Farin ciki ya Kama Manal ba sai tayi girki ba da dare sai ta dafa musu Indomie kawai.
Manal Tace Frit race (Fried rice) za a bani da sakwara,Ladidi da yaranta suka dinga dariya tare da cewa Fried rice ake cewa sai da Manal ta iya fada sannan Ladidi ta Mata take away harda nama yanka biyu a kowanne girki,Ledoji biyu Manal ta karba tana godiya sannan Ladidi ta Bata dari uku.

Ameer Kuwa take away aka musu lafiyayye amma ga mamakinsa sai Fuzail yaki ci,juyin duniya yace na gidan mu zanci,Dariya Ameer yayi yace au har gidansu ma ya Zama gidanku? na talaucin? Kuma wannan Yarinyar in Banda jagwalgwalo me zata yi,Fuzail Cikin Harshen turanci yace yarinyar data taimaki rayuwarka kake fadawa Haka?Yarinyar data kawoka Hospital da kudinta,Yarinyar da zata iya aikin kaskanci ta ciyar da wani,yarinya karama with Good heart,wannan Yarinyar tana da wasu Good Qualities da ba ko wacce mace ke da irinsu ba,Ameer kallon Abokin Nasa Kawai yake Yi da mamaki wannan Yar Yarinyar Yar Kauye yasan tana da Hali me kyau,Ameer yace yanzu prince baza kaci Abinci me kyau ba na waccen yarinyar zaka ci? Idan cuta ta Kamaka fa? Fuzail Baki ya tabe sannan ya bawa Ameer Labarin gidan su Manal da abinda Yan uwanta su Farida suka Masa,Ameer ya dinga dariya yace wlh sunyi dai dai,Fuzail Dan hauka ka shiga dakin yarinya idan da sun Tara maka mutane fa? Yarinya Haka ku kwana tare mahaukaci ne kai? Ban San tayi bacci bafa,Hmm Ni Dadi ma naji tun ranar da yarinyar Nan ta rike Hannuna na Gane Ni Namiji ne Fuzail ya furta Yana murmushin Jin Dadi, Ameer ko magana baiyi ba Likita ya shugo tare da wanke Masa rauninsa yana canja plasta Manal ta shigo da fara'a tayi Sallama,Ameer ta kalla ta Iske Yana cin abinci tace jiki yayi kyau Sannu,karka damu kaji an kusa sallamarka ta furta tana lallashinsa,ta Bawa Ameer Dariya yarinya karama sai iya tattali Amma tana birge shi murmushi yayi tare da furta me kika kawo Mana,Yana magana amma surar Fuzail take kallo yanda ya tube rigarsa taga Namiji iya Namiji ga skin me kyau sai sheki yake yi,surarsa take karewa kallo,Ameer yace Ina magana Yan mata,Firgit ta saki murmushi tace ahm...Uhmm....Fried rice da sakwara.

Ameer yace ashe abin Dadi ne Yar Fulani an iya turanci Ashe,da sauri Manal ta zauna a gefensa tare da furta kaji tsiya wata ce Tace sai na koya yanda ake fada da turanci sai Dana kwashe Rabin awa ban iya fada ba sai da kyar kasan kaina kindirmo ne a ciki ya daskare,Dariya Ameer ya dinga Yi yace Baki da dama,Manal tana Dariya Tace wlh Ni wata Kindirmo ce ka ganni to ya za muyi talauci ne ya jaja mana,Da ace da kudi yaushe zaka ganni haka yanda nazo birni ai da tuni na dauki Hanyar wayewa dodar.
Chapter 16 · 0% Book details