Sashe 46
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har wajen kakannin Sarki da Tsofaffin gidan an kaisu sunga juna an gaisa karshe aka rakasu part din Manal,Sai kallon Manal sukeyi yanda ta tsula kyau,Annatu tace yo Manal ai sai kika saje da su,kema har kin Zama Yar burrrrrni,Annatu ta Furta da hausar fillanci,Ita kuma Sharifa Tace Yar banza har ta Zama irinsu Tama fisu kyau,He ta koma itace Kalar Gidan Saurautar, Manal sawa tayi aka cika musu gabansu da kayan Alatu,Yan Fulani Yan garin su Annatu Suka ki ci sabo da kunya,Annatu Tace yo sabo da Allah ma ki(ci) abinci gidan surrrukaiiii ai abin kunya ne,Dahara Tace aradu yanzu ma kunya Nika ji Kamar a bonne Ni a Rami na huta,Bangaren su Sharifa Suka ce wallahi ci zamuyi wannan Dadi Haka ga kaji ga su Hinkafa, kalli yau mun hige su harda Hinkafa me ruwan rawaya rawaya, Hajiya Sharifa Tace Alqur'an ku Bude ciki mu Danni abinci mota fa zamu Higa akwai nisa garinmu.
Annatu part din Manal Suka gani suna ta Santi Suka Mata Nasiha sannan Suka ce zasu tafi,Manal Wai sai ta fara kuka Kuma tana rike rigar Annatu,Fuzail ne yayiwa Ummi wayo yace zaije su gaisa Kar su gano Dan yaci mutuncin yarsu ya aureta,Sai gashi ya shigo ya Iske Manal ta kankame Annatu Wai sai ta bisu,Hannunta ya fisge Yana cewa mene haka? Manal ta saki Kuka me karfi,Annatu sai kunyar surukinta takeji ta kasa sukuni tuni sukayi waje,Fuzail ya fita har mota ya rakasu da Ameer,kudi ya Basu me yawa abincin da Suka ki ci yasa aka zuba musu kajin da yawa a Leda da wasu Naman daban,lemuka da ruwan Roba caton da yawa aka zuba musu a mota,Har kauyensu yasa a kaisu Wai bazai bari surukansa su hau motar haya ba,sai Albarka suke sa masa suna Manal tayi Dace,Annatu tafi kowa murna.
Yana dawowa daukan Manal yayi cak tana kuka ya shige Bedroom da ita tare da sa key a Kofar.
Godiya ta musamman gereku
Ummi Deejat
Auta
Bestynbeelat
Mrs Om@r
Hajiya Khausar
Ummu Lateepha
Khadija A Dandume
Diyar Katibi
Fancy Honey
Maman Samha
Sweety Bella
Rahmatu Kunde
Mmn Ummee
Mom Aneesah
Hafsat A bako Maibeza
Ummu Amaturrahman
Sa'adatu Tijjani
Rukyaly
Innallaha maassabirin
Mifeedah
Ummin Sadeeq
Ina godiya da sharhinku Ina yinku.
AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭
DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP
56-60
Official
By
AsmaBaffa
Page Naku ne
Real Maman Waleeda
~50
Maman Amal
Maman Khadi
Name
Meeramu
Mom Abdallah
Safeeyat
Ummu Shafa'at
Maman Yasir
Ummi Tandama
Niimatullah
Ummu Abdulmajeed
Rabi Mukhtar (Mmn Hubba)
Daukan Manal yayi cak zuwa Bedroom dinta bayan ya kulle dakin da key ya ajiyeta gefen bakin bed shima ya zauna sai Rusa kuka take yi,hankalinsa ne ya tashi ransa ya jagule,me ya faru? Ya tambayeta Yana Wasa da yatsunta yace ko wani abun ya faru? Bata kulashi ba tana kukanta,fada min wa ya taba min ke? Ya furta Yana shafa bayanta da sigar lallashi,sai lallashinta yake Amma Taki yin Shuru ganin hankalinsa ya tashi sai ta Dan rage kuka tana hawaaye tasa Yatsanta na tsakiya a Baki tana cin farcen da babu,zanen lallen Hannunta ya Shiga kallo yayi kyau abinka da fara,Hannun ya shafa tare da cewa wow lallen yayi min kyau,Manal da tabara tace Kaine ka mareni ba,Kuma Ni bana son gidan Nan ka canja min gida,Kallonta Kawai yakeyi Kamar tsohon maye shi kukan nata ma birgeshi yayi yaji wani sha'awarta sabuwa ce ta kamashi,Hannunsa yasa tare da tallafo fuskarta da tafukan hannayensa Guda biyu tana faman Hawaye Fuzail yace Ina ma kukan Nan Zaki Adana min shi sai anjima idan kinzo ai da kin bani Ginger, bata Yi Niyyar magana ba tace me zaka min idan nazo? Ya wayance Mata da idan kinzo ki min kukan a can yanda zanfi lallashinki,Kafada ta makale ta Dora daga inda ta tsaya da kukanta.
Fuzail jikinsa ya jawo ta tare da kwantar da ita saman cinyarsa ya zame siririn mayafin nata Yana shafa gashinta me Matukar santsi da tsayi,Bayanta yake shafawa Yana lallashinta amma Taki yin Shuru ya rasa ma me zaice mata sai yace Oh Yanzu nasan Su Hajiya Herifatu an kusa karasawa,Shima Fuzail a wajen su Na'ima yaji suna Dariya suna ta nanata sunan Wai Hajiya Sharifatu itace tace sunanta Herifatu,Manal ba shiri ta saki Dariya tace wannan gidan naku Allah munafukai suna da yawa waye ya fada maka?,Hawayen nata ya goge Mata da hannayensa Yana cewa I love you,Wasa ta shiga Yi da botin din Gaban rigarsa, ya furta Kawai Dan Kinga su Annatu sai ki fara yiwa mutane kuka,Manal Tace Hmm Kai dai Bari Saniyata ce Annatu tace tana can ranga ranga Bata da lafiya Saura kadan ta mutu Kuma Dan Busuru na ya kasa an siyar da shi,Fuzail Kansa ya nuna tare da furta ai ga wani Bunsuru kin samu sabo dal,Baki Manal ta Bude tana sheka Dariya tace ka zagi kanka ba ruwana,kanta ya kifa a cinyarsa Yana kallon shashin wuyanta ta baya zuwa kafadunta yanda gashi ya kwanto a keyarta yala yala,iya ta bayan keyar Manal idan ka kalla kasan me gashi ce ,Shafawa ya dinga Yi a hankali Yana yawo da Yatsunsa a saman keyarta zuwa wuyanta,kamar Wasa sai tayi bacci Kawai Bata sani ba,Bai tashi ba ya zauna a Haka tana cinyarsa ya gyara Mata kwanciya Kawai taci gaba da baccinta me dadi,Shi Kam sai Yan tabe tabensa yake a jikinta,Ganin baccin nata yayi nisa sai ya kwantar da ita a tsakiyar bed sabo da Kar Ummi ta fara sintiri,Sanyin ac ya rage Mata tare da lulluba Mata blanket sannan ya lallaba tare da barin sashen nata gaba Daya.
Wani Driver daban ya dauka ya kaishi Guess House a can yayi baccinsa shima sai Magriba ya dawo gidan Bayan yayi Sallar Magriba,Manal kuwa Sallar la'asar ce ta tasheta tayi Sallah ta sake cin abinci sannan ta jawo Littafan Boko dinta ta karanta abinda ta Gane Wanda Bata Gane ba ta Kira Yaya Yazed ya Mata bayani,Tana Gama na Boko ta Koma Karatun Qur'ani abinta har Magriba sannan tayi Sallar Magriba ta shiga wanka.
Fuzail Kuwa Yana dawowa Ummi ya samu a palonsa na kasa tana kallo,a ransa yace na shiga dubu ma ba Tara ba,Zama yayi a gefenta bayan ta amsa sallamarsa ta kalle shi tare da furta daga Ina? Naje part din wannan Yarinyar dazu Naga tana bacci,Wai Bata da Aiki sai bacci ne? Fuzail Baki ya tabe tare da furta Ina Zan sani matar da ko part dinta ban San kalarsa ba Taya Zan San tana bacci,ke kika damu da ita shi yasa kika San tana da bacci ma,Yayanta ma ya kirani a waya Wai yau da dare zata tafi gida acan zata kwana sabo da gobe suna da Exam Fuzail ya shiryo karya,Ummi Tace ban Gane daga kawo Amarya ta tafi gida ba akan exam ko da safe baza a kaita ba,wa zai kaita? ta Isa na kaita Ina ruwana idan zata tafi taje ke Ummi Nifa ba kauna ce tasa na auro ta ba Dan Allah ki daina min zancenta.
Ummi taji wani Dadi harda sakin murmushi tace day school za a tafi kwana gida? Fuzail yace tayi kwana dari ma ba damuwata ba,Ummi tana ta Jin Dadi tana sani take zancen dan taji yanda Fuzail ke nuna tsanarta karara a fili.
Ta sake cewa da kasa Driver na ya kaita,God for bid over my Dead Body Ace Driver din Uwata Guda shi zai dauki wannan kucakar da nayi asara a duniya,Ummi ta kurbi Lemon Jin Dadi taci gaba da kallon Film dinta suna Hira Sama sama,kafin kace Me Ummi duk ta bawa Cid dinta Umarni idan Manal ta tafi su bar part din kawai,Ana Yin Sallar Isha Manal ta shirya cikin Black Abaya ta shirya sosai Kamar gaske da katuwar Jakar ta wacce maza da Mata suna iya Daukanta ta rataya abarta zata Yi tafiya,Sallama sukayi da Masu kula da part dinta sai Nan da 3days zata dawo idan sun Gama Exam.
Direct Part din su Ameer ta nufa Allah yasa ba kowa bangaren Maman Ameer ta wuce sabo da Bata Nan ta tafi Abuja wajen yaranta da suke karatu a can,sabo da Manal ba Yar wani bace ba Wanda ke wani Bata tsaro, shi yasa take walawa a gidan, Ameer Yana jiranta ya nuna Mata bedroom a part din Mamansa ya fice abinsa.
A ciki Manal taga kayan kuyangi wata barmemiyar rigar yadi Silk green da zani red,Kayan jikinta ta cire ta maida cikin Jakarta irin ta matafiya Wanda zata ci kaya kala Uku zuwa biyu ta zamani,Sosai ta shirya tsaf cikin kayan,Wata bakar safa ta saka a kafafunta da Hannayenta,ta saka Hijab Green sai ta sa Nikaf Baki Wanda Idonta Kawai ake gani,idon ma Bata barshi ba sai da ta sa farin glass karami, ta fito tsaf ba Wanda ya Isa ya Gane Manal,Ameer tuni ya karbi jakar ya tafi part din Fuzail Direct ya Shiga ya gansu tare da Ummi suna Hira,Ummi ta kalli Ameer tana murmushi ta furta abokan juna,abotarku tana birgeni Ina zuwa Haka da wannan jakar katuwa? Ameer murmushi ya saki tare da cewa wasu dinkuna ne nawa na karbo bana so a taba min su shi yasa na kawo Nan Zan ajiye Yana furta Haka ya haura sama tare da shiga bedroom din da aka tanadarwa Manal Wanda Ummi Hankalinta bazai Kai Kansa ba bare ta shiga,Bata taba shiga dakin ba,jakar ya boye ya fita yayi tafiyarsa a she ta Kofar kitchen ta can baya ya budewa Manal yanda zata shigo ta kitchen tunda kofa biyu ce.