← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 95

Sashe 40

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watan Maulidi ne yazo wani ya hada gagarumin Maulidi Belloti yaji Ana ta gayyatar Maulidi yace ah yau fa akwai chasu,shi da Abokansa Suka tafi wajen Maulidi da kwalaben giya,Ana Maulidi su Belloti giya suke bulbula,Wani Sheikh ya gansu da Idonsa yasa Yan Sanda suka kamasu Ashe Belloti akwai giya a aljihunsa ya tafi da ita,Sheikh yace wlh kotu Za'a kaisu Direct,aka tafi Dasu kotu Kuwa,Alkali Yana sauraren Kara Belloti ya zaro giya kwalaba Guda a Gaban Alkali ya daga abarsa tiltiltiltil Yana tiltilawa cikinsa,Alkali ransa ya baci Nan take ya yanke musu hukuncin Bulala tamanin tamanin,Haka aka Zane su Belloti tsaf sannan aka sake su.

Manal Kuwa Bayan ta raka Fuzail da wani irin farin ciki ta dawo cikin gida tana shigowa tana rawa ta shigo ta kalli su Farida tace Me Laya ki yayi me zamani,Idan da Laya kuke takama Ni da zamani nake takama,nice nake zamani,Kai Allah na gode maka Ina zamani Ina lokaci wallahi,Ni ake yayi yanzu , Manal tana lokaci,Waka ta Mai da abin tana irin Rawar Kauye a jefa Kafa gaba ana dawo da ita baya tana waka Manal tana lokaci ganjiganjigaganjiganjiga tana girgiza da juyi har Gaban Hajiya ta girgiza Mata kafada tare da cewa ehhhh sawa,Kudin da Fuzail ya Bata Yan dubu dubu sababbi Kar da yawa ta zaro tare irgo Guda biyar ta mikawa Farida karbi Yar kurkura mu gobe ma wasu za a kawo min,ko nayi waya yanzu kiga an aiko Tanko Yana gudu Yana faduwa ya kawo min wasu yanzu,Haushi yasa Farida duk son kudinsu suka ki karba,Manal Tace ba komai gobe zaku ci shinkafa da kudin,shinkafa Zan siyo duk bala'inku sai na taimakeku wlh ya zakuyi da me lokaci yarinya daga ruga ta zama 'yar yayi Manal me zamani,kudin gaba Daya ta mikawa Farida tace ki karba ma duka ko albarkacin Mafarkin da kika dinga Yi min kullum ai a Baki Lada wallahi wannan irin mafarki Haka Sannu Aunty Ni wallahi bazan ajiyeki a Cameron ba Original kasar waje Zaki je ki kalli turawa-turawa ma su kalleki,Kuma ko ba komai Zaki dinga zuwa gidana Abuja Inshaallah kusa da Villa,idan Kuma Lagos dince a cikin mafarkinki Makwafta nake da Davido da Wizkid ko pics prince Charming ya hadaku ki dauka ki samu na status,kizo gidana insa kuyanga ta goge Miki kaushin kafarki fes.

Farida sai Hawaye ita yanzu da gaske ma ba kudin Fuzail take so ba Fuzail din take so Bilhakki da gaskiya batun wani kudinsa ya Kare a wajen Farida,Farida kuka ya kwace Mata me karfi Wanda ya jawo Manal tayi Shuru tana kallon ikon Allah,Farida durkusawa tayi har kasa a Gaban Manal ta fara rokonta tana kuka Dan Allah Manal Dan girman Allah Kinga ke Yar uwata ce kanwata uba Daya ba Wasa ba,Dan Allah Ina neman Alfarmarki, wallahi na Shaku da Fuzail a mafarki,mun Shaku da juna da shi a mafarki,wallahi Ni yanzu tunda na ganshi ranar da aka Daura muku Aure ranar na fada sonsa na gaskiya,duk son da nake Masa na mafarki son kudi ne,amma yanzu Dana ganshi wallahi ji nake Kamar Zan mutu sabo da sonsa da nake ji,Dan Allah Yar uwata ki bar min Fuzail kice ya sake ki ya aureni Dan Allah.

Majina Farida ta ja tana kuka Tace Dan Allah Manal ki bar min Fuzail Ni Kuma na Miki Alkawarin wallahi ko Nawa ne idan ya aureni Zan baki,Manal tayi Shuru ta kalli Farida tace Farida kina da hankali Anya? Haukar Manal tunaninta me Chemist ma Likita ne,dama tana da number me Chemist na unguwarsu a daren ta Kira Salisu a waya tace da Allah kayi sauri kazo Salisu da kayan aikinka ka taho da komai na aikin gwaje gwajenka zaka auna min Wata,Farida tana ta rokon Manal har Salisu yazo da ledarsa Viva,yawwa Salisu dakko kayan aikin ka gwada min kwakwalwar Aunty wallahi wajen shekara biyar kenan da samun tabin hankalinta,tun abin nata tana Yi a mafarki har yanzu ya taazzara ya fito fili Ina me tabbatar maka gaf take da Fara tsincetsince a bola ko ta fara duka.

Salisu yace Eyya ai mu ba likitoci bane Kawai idan Likita ya rubuta magani mu ake kawowa a siyi maganin,sai shishiginmu da katsalandan na Yan Nigeria Me Chemist sai azo a fada Masa matsala Kuma ba gwaji ba komai shi ba Doctor ba ya dauki magani ya ba mutum Wanda sai an samu akasi Kuma a komawa asibiti da jangwangwama musamman a kauyuka wasu ma Basu Yi karatu ba Kawai koya sukayi da ka,Yanzu Nima a shishigi na Ina yiwa Mata awon ciki,da awon Hawan jini,malaria,da sauran kana Nan abubuwa Kuma duk wannan ba Aiki na bane,yanzu ai asibiti Zaki kaita a Mata gwaje gwajen Daya kamata su rubuta Mata magani idan an Rubuta sai kizo ki siya a wajena,Manal Tace Kai Allah wadaran Yan Birni da karya,Salisu jeka Harkar Taku duk karya ce.

Salisu Yana Tafiya Farida taci gaba da rokon Manal tana cewa Kinga dai irin abinda na yiwa Fuzail bazai surareni ba Ni kaina bazan iya tunkararsa ba bani da bakin magana tunda Yana Jin maganarki Dan Allah tunda nasan ba abinda ya shiga tsakaninku na aure ki bar min shi,Wata Shewa Manal tayi tana tafa Hannu tare da cewa duk wata dama Allah ya Baki ita akan Fuzail wulakancinki da Rashin tarbiyya ya ja Miki,Duk abinda Hakuri Bai baka ba rashinsa bazai baka ba,rashin kunya ba inda zasu kaiki,Kuma Nufinki da zai saurareki sai kije kice kina sonsa? Farida Tace da gudu ma kuwa Nifa idan Ina son Abu ba abinda bazan Yi ba.

Girgiza Kai Manal tayi tace Naga Alama ke wata Dusa ce a cushe kanki yake har abada baza ki samu abinda kike Nema ba,Hajiya Haushin Farida ya Gama kasheta Wai ta durkusa tana rokon Manal ta bar Mata Fuzail su da suke so su kwace shi ta karfi su nunawa Manal ita ba kowa bace Amma ta zauna tana rokonta,ai Nan take Hajiya Haushin Farida yasa ta Dinga durmawa Farida duka karshe ma ta rufeta da duka tana cewa Ashe Baki da zuciya Baki gaje Ni ba? Ni zuciya ce Dani wallahi wani Bai Isa Dan Ina son Abu na roke shi ba,Yar Iska mahaukaciya,Manal ta dinga dariya tace Kara Mata Hajiya Yi Mata Kutufo wallahi,Nan Manal ta barsu Farida tana ta kuka.

Hajiya ta ja ta daki Tace Yar Iska ke da nake so tunda Munga Fuzail din bazai samu ba kema ki canja salo ki samo wani Alhajin me kudin gaske ki aure abinki yanda zamufi karfin Allah sarki,idan kema kika auri me kudi waye zai daga Miki Kai,gidan sarauta ne Kawai masu kudi? Ga alhazawa Yan siyasa da Yan kasuwa ki samo Daya ciki,ki hakura Amma wallahi Manal ko mun hakura mun daura gaba ta har abada da Manal,babu mu ba su cewar Farida,Hajiya Tace har abada tsakinmu da su Manal sai Sharri Bamu ba su, kyaleta da Fuzail bala'in gidan sarauta ma ya isheta,Kuma wallahi Har Fuzail da Yan Uwansa Matukar zasu Zo gidan Nan ba mutunci cewar Hajiya,Farida Tace Hajiya wallahi kaunar Fuzail nakeyi da gaske yanzu ba kudinsa nake so ba,ko bashi da kwandala Zan aure shi da Zan samu,Hajiya tana lallaba Farida tace na sani...na sani Farida ta kiyi Hakuri shi so danne shi akeyi har ya bar zuciyarka.
Gaki kina da kyanki ba laifi Kawai fa sai dai akan Manal ace Miki Mummuna amma kyakyawa ce Kuma kin iya wanka.

Mazan yanzu ai duk kyalkyal banza suke biyewa su dai suga Yar wanka Yar gayu tana kamshi,su ganta da shape,duwaiwaka mashaallah,aga kirji tullukwikwi to ko ciko tayi sai kiga an aureta da wuri da gaggawa,Yanzu kitson Attach Zaki koma ko yaushe,ga Mai me kyau ki dau haske,wannan Duwawun na ciko da ya shigo Wanda Zaki ga Dan wando ne Amma an Masa soso da ciko mata shi suke sawa a ciki su daura skert a Kai Malam kiga duwawu Kamar zai Fado maza Ana kallo Ana yaye baki duk karya ce daga masu Shan kwaya sai masu sa wandon ciki,Farida Tace ga Manal Nan nata ita Haka yake Kato,Ke banza irinsu Basu da yawa a duniya a gari daya baifi ki samu mace Daya ko biyu ba masu na Allah da Annabi a birni Kuwa kaf layi duk girmansa ba afi a samu Mata goma ba idan ma sun kai,su dama maza Yanzu sun lalace da sai fara,Fara ko na Mai ne sai kiga Namiji zai hada babban hatsari a kwalta sabo da kallon Budurwa.

Hajiya Dan ta kwantarwa da Farida hankali ta tsaro karya tana cewa Rannan ma wata taci Mai Ni ko birgeni ma Bata Yi ba duk ta karce fatarta ta tashi daga aiki Dole sai ta koma baturiya tana tsaye a gefen titi me Hannu Daya wasu Trailer Guda biyu sun taho Daya daga can Hannu Daya daga wancen Hannun duk garin kallon Yarinyar Nan me Mai Suka hadu Suka Yi Karo da Karo Munga tashin hankali ranar,kana Nan motoci su biyar suka zo suka shige cikin Trailers din Nan wayyo akan yarinya Wanda farin nata ma bana Allah bane aka Yi asarar rayuwa haka,sabo da Haka duk munin mace Bata rasa miji yanzu babin daukan wanka zamu bude Kawai duk layin Nan sai dai a kalli sabon yayi a jikinki a kwaikwaya.
Farida tace to Allah na tuba da Sanda Muna Talauci ma Mukayi bare yanzu da muke da harka,shege Tela na ma na daina bashi dinki na yanzu ya Zama tsohon yayi,Hajiya Tace ai sabon Yayi za a dinga kaiwa,sun Dade suna tsare tsarensu,Manal tana can ta dukufa akan Littafanta da su Masatura suna ta koya Mata abubuwa.

Washe Gari ma Fuzail shi ya Kai Manal school Tanko ne Driver,Yanda ya Kai Manal har class Haka ya sake kaita Kuma ya dakkota,Islamiyya Kuma Tanko ne ya kaita shi daya,zuwa dakkota aka dakkota da Fuzail suna bayan Mota sai rike riken Hannu suke suna wasanni da hannayen juna,Tanko Yana satar kallonsu yace Ana soyayya a Nan Nima da waccen me gashi kamar Isgar arnan zata tallafa min ai da na more Amma tunda yanzu taga ba auren Prince zata Yi ba babu mutunci tsakaninmu,Tanko ya Saba ganin gashin Farida sabo tana Dan yin dauri Wanda zai fito Tum tum daga baya.
Chapter 40 · 0% Book details