← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 95

Sashe 19

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manalll...ya sake furtawa Karo na Uku Manal harda rufe Fuska da hijab sabo da Murna da dadin sunan fuskarta boye a hijab tace Allah wallahi Yaya Yazed ya iya sa min suna Ashe Yana da Dadi Haka yau naji matsayin Yaya Yazed ya karu a zuciyata,Fuzail yana ta murmushi yace rigar jikina susar min ciwo takeyi,to cire Mana,Bai dace ka zauna da Abu ya dameka ba,rigar ya cire Manal taga Kira iya Kira Tace huuu tare da rufe idonta da sauri Wai kunya, Juya muga ciwon ko ya fara warkewa Tace Idonta a rufe sai da ya juya Mata baya sannan ta Bude idonta ta kafe bayan da kallo ko ta ciwon ma Bata Yi sai da ta Dade a Haka har ya gaji zai juyo tace tsaya na gani sosai kamar wani waje zai kwabe,Tsayawa yayi ya juya Mata baya Manal a ranta tace Wannan Allah ya bashi sura da fata me kyau,Sai da ta Gama tunaninta sannan tace Alhmdllh kallon Musulunci nayiwa bayanka wikil nayi da Ido na shike nan ya kusa warkewa sannan ya juyo.

Manal ta zuba Masa Ido kamar me yace lafiya? Tace tsaya a Haka inyi ta kallonka ka hadu inji Yan Birni Suka ce ka haduwa,Dariya yayi ta sake cewa bature yace Handsome,kaji haukar Bature Hand fa Hannu kenan to some din ta mene chab hauka,Sanda Yaya Ya fara koya min turanci tunda Muka zo kalmar Nan na tsani turanci gaba Daya sai da na daina kula Yayana nayi gaba ta tawon kwana Uku da Yaya na akan Handsome din Nan,sai gashi ashe tana da Rana Kaine ma kalmar Handsome din gaba Daya Kai bature ya kalla ya kirkiro Handsome,Fuzail Yana ta kyalkyala dariyar da Bai ma taba yin irinta ba,Kuma sai Dadi yake ji Manal tana ta yabonsa shi Kam yau ya Gama Jin dadinsa duk yabon da ake Masa Bai taba murna ba sai akan na Manal.

Manal ce ta dauki wayarsa tare da Kara haske Fuskarsa ta karewa hancinsa kallo Nan take ta furta Chab Surayya sunan wata,Dariya ta kwacewa Fuzail sosai yace Hanci na Surayya ne?Manal tana Dariya tace Sorry karka ce na Raina ka,kasan Allah muje kayi Aski gobe sai kafi Haka kyau,Dan Allah kayi Aski gashin yayi yawa kalli tudun gashi ga gemu dogo da kasumba Haka ai Dole su rage maka kyau Amma daga hancinka bakinka zuwa idonka an San Handsome ne Kai kawai kallonka ne ba ayi,Fuzail ji yake kamar ya tashi sama Sabo da farin ciki.

A hankali yace gashi Ni talaka ne Amma na tambayeki? Manal Tace Ina jinka,yace Zaki iya aurena a Haka idan na samo Mana ko gidan haya ne Zan fara sana'a ko dako ne a kasuwa Ina ciyar dake da sauke duk hakkinki na matata dai dai talauci na kafin Allah ya Buda min? Idan na samu kudi Zan saki a makaranta kuma kema ki Zama Yar Birni yanda kike da kyau nasan sai an kalleki Nan gaba,Manal sabo da Murna ta rufe Ido tare da dauke wuta tayi duf,yace ko bakya so na? Manal ta girgiza kai,shi Bai San wata kunya ba,yace talk yanda Zan gane,Manal a kunyace tace Allah sai Naja Aji Haka Kawai na Fadi gaskiya da wuri,Shuru yayi Yana dariya a ransa,sai da tayi minti Uku sannan Wai har ta Gama Jan ajin ta furta Ina sonka Nima sannan Ni ba kudinka Zan aura ba Kai Zan aura ba ruwana da talaucinka,Kuma Inshaallah baza kayi dako a kasuwa ba,Idan Yaya ya dawo wallahi Zan fada Masa Dole sai ya min aure idan ka samo Mana gidan haya ka dinga siyo Mana Dan waken mu gongoni biyu Ina Yi Mana faten wake,Allah na tuba Ni Dana Saba rayuwa ma a daji rugar Fulani ko a daji ne Zan bika mu zauna Matukar kana cikin dajin Zan zauna tare da Kai iya wuya Rai da ajali.

Kuma ai sai mu dinga wata sana'r a gidanmu kaga sai mu dinga samun kudin da zamu rufawa kanmu asiri,muna samu wata sana'ar sai kaga Sanadiyarta Allah ya rufa Mana asiri mu haifi Yarmu Shafa'atu,Fuzail yace Shafa'atu? Yana dariya yace no ba a Kan 'yata ba ,Manal ita a Dole Yar gayu tace Kai Shafah za Ana ce mata,Fuzail yace no...no....

kallon Manal Kawai yakeyi da mamaki matan yanzu taji wannan talaucin Amma tace zata aure shi Haka tana ganin yanda ko Naira dari baya iya Fitowa da ita itace ma ke dawainiya da shi Amma ta yarda,a ransa yace irin matar Dana ke so ce with Good heart,matar rufin asiri matar da zata so ka ta zauna tare da kai a cikin ko wanne yanayi na rayuwa ba wacce zata so ka Dan kudi ko Dan wani sura naka ba.

Manal kunya ta dameta Yana ta kallonta ta Mike zata koma shimfidarta ta kwanta da sauri ya sa Hannunsa me Matukar taushi ya rike Hannunta yace kwanciya zakiyi? Manal tana boye Fuska ta daga Kai Wai ae yace Good Night tare da sakar Mata hannu.

Dukkansu kwanciya sukayi kowa yayi Shuru Yana Jin wani farin ciki marar misaltuwa a ransa,Ga wani shauki Yana fisgarsu,a hankali Yana daga kwance ya Dan matso jikinsa,Manal ma da wayo tayi step Daya daga kwance zuwa inda yake,Ya sake matsowa a hankali,itama ta matso again suna Haka har suka zo gaf da juna,ga wani shaukin juna Yana fisgarsu,tunawa yayi da sauri ya matsa can baya tare da Furta Devil Shaitan,Manal ta matsa itama da sauri tare da cewa marar mutunci zai sa na a sukurkutani kafin biki a tsotse min madarata Dan ance idan aka kebe mutum biyu na Uku Shedan ne shine yazo to mun Gane,Yana jinta Bai San ma nufinta ba Wai da Shedan take ya koma inda yake a Haka bacci ya kwashe su kowa can nesa gefe.

Washe gari Farooq yayi Sallah da Azkhar dinsa sannan yayi wanka tare da canja Kaya cikin na gwanjonsa,Manal Kuwa Dama Bata Sallah wanka tayi ta canja wata Yar jemammiyar Atamfarta koriya wacce Farida ce ta Bata kwancenta,zata bayar a makota Manal ta dinga rokonta da kyar ta bar Mata rigar Dake dinkin birni ne sai tayi kyau a ciki.
Farooq Bai San ma ta Bude gidan ta fita ba, Manal Shago taje ta siya Indomie biyu da kwai danye hudu,sai ruwa Pure water na Hamsim,ta siya musu Omo da Sabulun wanki,ta dafa musu Indomie harda kwai kowanne Guda biyu dafaffe a gidan Baba me kayan Miya tayi girkin da kanta ta zubo a flask,Lokacin Fuzail Yana ta Neman Manal har ya bude kofa ya fito hankalinsa a tashe sai ya hangota da Kaya Niki niki,farin ciki da tausayinta ya kamashi yanda take dawainiya da shi,da sauri ya karasa tare da karbo wasu kayan na Hannunta ya rage Mata nauyi Yana cewa baza ki fada min ba na taimaka Miki sai ki tafi ban sani ba kin San hankalina ya tashi.

Murmushi Manal tayi tace ka yarda Dani ba inda Zan tafi na barka Suka Shiga gidan nasu tana cewa Kamar yau ko gobe naji Likita yace za a sallami Dan uwanka,Fuzail Wanda ta sani da Farooq yace sai jibi ma naji Likita yace,Allah ya kaimu karka damu Inshaallah zai warke,Farooq yace Yeah,Abincin ta zuba Masa a plate wannan Indomie ya santa Yana ci sosai Kuma ta Masa Dadi cikin kwanciyar hankali yaci ya koshi abinsa ya Sha ruwa,sai da suka Gama ta wanke komai ta mayar gidan Baba,sai yaga ta dawo da wani botiki,kayansu da Suka cire ta eba zata wanke,karbe wankin yayi yace Ina Nan kiyi wanki kawo na wanke,Bata Yi musu ba Tace to wanke kawo naje na Kai maka wayarka wajen caji,Wayar ya Bata ta tafi ta Kai wajen me cajin kusa da su,kafin ta dawo ma ya wanke kayan Dake ba Dirty,lokacin data shigo Yana daurayewa ta kwasa ta samu Kan wasu katako a tsakar Gidan ta Shanya musu kayan sannan ta dakko wata tsohuwar bra dinta wacce ta Gama tattalewa zata wanke da kanta sai babboyewa takeyi sabo da Kar ya gani Amma ya gani ma.

Ya fisge Bra din ya Shiga kallo Yana ta dariya yace wannan trash ne fa,ya duba Size Amma tsabar Jin jiki size din ya goge babu, tambayar Manal yayi yace Kuma wannan Yana Kama chest naki? Manal ta Harare shi ban sani ba ta ce,da Kansa ya wanke ta fes Yana ta dariya Wai mutum ke sa wannan lalatacciyar abar,pink ce ya wanke ta Kuwa fes ta kwace ta Shanya a barta Hannayensa da yayi wanki yake kallo shi Bai taba yin wanki da Kansa ba gaba Daya Dan wankin da yayi Yatsunsa sun farfashe suna Jini,Manal ta zaro Ido tace baka wanki ne muga hannunka ta fisgo hannayensa tana kallo,Idonta ya ciko da kwalla Tace me yasa baka fada min ba baka wanki kalli hannunka muje asibiti,duk ta rude.

Hannayensa ya kwace Yana cewa wani ciwo ne Dani shi yasa Idan nayi wanki suke Haka ai dama tun Ina yaro Haka sukeyi zasu warke in two days,Manal tace ka tabbata? Yace ae tace to,tayata yayi Suka gyara gidan fes harda wanke toilet Kal abinsu.
Da Rana Kuwa Jullof din taliya ta karbo musu a gidan Baba,Da dare Kuma Waina ce da Miya,tare Suka karbo wayarsa daga wajen chaji ta cika full.

A saman shimfidar zanin ya kwanta Yana latsa wayarsa,Manal ta shigo dakin Tace Farooq Kunna Mana kallo kafin na tafi gida yau a gida Zan kwana Kar a kala min wani sabon sharrin,baida film din hausa sai American film,Yace American film ne Dani,Manal ta Bata Rai Tace Ni hausa nake so Gaskiya yaren da Zan Gane,Bari na duba ko Ameer ya tura wani,a Haka ya Mata wayo Nan take yayi Mata Download ing hausa Film latest sababbi kala Uku ko wanne complt 1&2.

Yace kinyi sa'a ga wasu Ashe Ameer ya bari,Manal ta washe baki,ya dakko flask ya jingina Wayar a jiki Suka zauna kamar tv Haka Suka sa waya a gaba suna kallon hausa Film.
Chapter 19 · 0% Book details