Sashe 64
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna ta faman Yi Manal tana jinsu tace surukinku ne dai,Wlh Kuwa cewar Dahara,Kida ne ya fara tashi Yan Solo tuni sun Fara taka rawa ta fitsara Ana ta Shan kallo Mata da maza Yara da maza gasu Nan Yan solo sun ja Hankalin kartai,sai liki ake Ana zuba kudin ka rantse dama an shiryi abin,Amarya tana Shan liki,Yahaya tsohon abokinta shima suna wajen da abokansa suna ta cashewa da su ake iskancin Rawar,Yan matasa da su sunyi kicin kicin duk mutanen Farida ne,Hajiya ce ta dakko wanka cikin Shadda wata sea Blue dinkin manyan mata ,idan kunga Hajiya ba Wanda zai Gane ta,ta zuba Uban kyau ta Sha make up ta gaske harda Eyelashes aka sa Mata Kamar Budurwa Haka ta dawo dama Hajiya Yan Birni,Takalminta Kalar zaren dinkin dark pink da mayafinta har Jakarta me tsada dama sabo da bikin ta dinka,Malam can Yana Sallamar Baki yaga Hajiya ta zuba kyau Hajiya ba karya Yar birni ce ba a barinta a baya musamman a biki,Malam ya hadiyii yawu tare da sharewa Kamar Bai ganta ba,Su Walida Suka Yanyame Hajiya suna tafi suna ai sai Hajiya wallahi kinyi Kyau,Hajiya tana murmushi Tace Ina ta godiya ba adadi,Rumaisa tace Hajiya kinyi wlh, Hajiya Tace na gode ta wajena,dalilin Farida duk suna Dan Wasa da Hajiya kadan kadan,Hajiya Kamar kawarsu Haka suke Abu da ita,Walida ta rike Hannun Hajiya tace Hajiya shiga mu zuba liki,ciki aka shigar da Hajiya Ana ragargazar uban kida, Suka saka Hajiya a tsakiya Suka zagayeta suna zagawa suna cashewa ana liki Hajiya tana musu suna Mata itama,Hajiya tace ku fita na kwaso Shoki Nima yau sai na Rama wallahi,Manal Bata San ramuwa za ayi ba ta taho da sauri da kudinta Yan dari biyu biyu zata Yi liki,lokacin an tsaya da kida, Hajiya ita kadai a fili ta kalli Dj da karfi Tace Music......sai aka saki kida Hajiya nata Shokin ma har kasa ta tsuguna ta kwarfo shi itama dai dai Manal ta fara Mata liki tana Dariya Hajiya tana Ebowa ta juyewa Manal a tsakiyar kanta har da dangwara tafin Hannunta sosai a tsakiyar Kan Manal sai da Daurin dan kwalin Manal ya ware kadan Amma ba cire ba,Hajiya ta Kama bakin mayafinta ta sake kwaso Shokin da shi ta watsawa Manal,aka saki Ihu da dariya,Manal ta Gane Wato Hajiya ita a Mayafi ma zata kwaso me yawa,Manal taci gaba da zubawa Hajiya Naira tana Dariya sabo da Hajiya Shokin ta sake Ebowa da Hannu biyu ta watsawa Manal wannan karon Hajiya harda gwalo ta hadawa Manal,Su Annatu da suke kallo ma duk ta kwaso ta watsa musu,Farida ta shigo Itama kusa da Hajiya Suka Fara kwasowa tare suna watsawa Manal Shoki,Harda sa musu wakar Shoki ahh Shoki,Su Sharifa Suka ce Ana zuba bariki a wajen nan, su
Yahaya da Basu San ramuwa ake Yi ba suka ce Hajiya Haka akeyi Bari ki gani Suka shige Suka dinga cashewa suna girgiza da Murguda Kugu Kamar Mata,Hajiya Tace Uwaku ba rawa nazo Yi ba.
Fuzail da kishinsa ya koma gida,Ummi tana kallonsa duk ya kasa sukuni,Tace akan Allah baiyi Tanko ya auri Farida ba ko wa take? Sai ka zauna ka damu kanka akan me,tunda ka shigo kake kunci an rasa me aka maka,Yarinyar Nan ce ta min fitsara Dan taga naje gidansu Ina ruwana da safgarsu da har zata gaya min magana,Dariya Ummi tayi tace tukunnama Indai matsiyaci ne,wa yace kaje,kace ba kulata kake ba me ya kaika? Baza ki Gane ba Ummi,Ummi tace Ni dama wallahi Ina son magana da Kai naji a gidan Nan Ana gulma kana bibiyar Kuyanga yanzu Fuzail abinda zaka min kenan akan kayi lalata da Kuyanga wallahi gwara ka kula matarka Ummi ta fashe da kuka,Fuzail yace Ni karya ake min me zanyi da wata Kuyanga,wallahi idan ta tabbata ko kayiwa wata Kuyanga ciki a gidan nan ba Ni ba Kai Kuma kasan Maimartaba sai ya daureka wallahi Dan Allah karka ja min abin kunya,Fuzail yace tukunna ma Sai Manal tayi ciki kunji ance Kuyanga ce kwayi bayani,a fili yace Allah Yana bayan me gaskiya,Allah ya tona asirina Indai Ina kula kuyanga,kwafa Ummi ta ja tace ai Allah Yana gani ta fice a fusace.
Fuzail ta matarsa yake,kasa nutsuwa yayi 2pm ya ci abinci lafiyayye ya sheka wanka ya fito cikin wata jallabiya Fara tas Kamar wani Balarabe Yana kamshi,bayan yaje Sallar la'asar yace Tanko yazo ya kaishi gidan su Manal,Tanko ne yayi Driving dinsa, har can lokacin Ana ta cashewa,Manal ya hango tana ta zirga zirga gyalenma babu ta ajiyeshi Haka suke yawonsu dukkan su matan,daga nesa yasa Tanko yayi parking Yana ta kallon Manal ransa ya Kara baci ya hasala sosai sai zirga zirga sukeyi tare da Yan Mata su Shukrah,duk ta fisu yarinta,Tanko Yana satar Kallon Fuzail Yana dariya a ransa yace jaraba sai kace shi kadai ne me Mata duk ga Mata Nan wajen ma da matane mazan Basu da yawa duk ya damu Kansa,Tsaki Kuwa Fuzail ya ja yafi kwando Guda,Ya Kira Wayarta Kuma a kashe Bai San ta kasheta ba ta bawa Annatu Ajiya Kar me Dan Hali ta sace mata.
Tanko Yana sani yace Ranka ya Dade Kira maka ita za ayi ne? Da bala'i ya kalli Tanko Yace a Haka zaka je wajenta ka ganta,yo gani na nawa Kuma Tanko ya furta a ransa,Gajiya Fuzail yayi Akan ya barta a Haka gwara Tanko ya Kira Masa ita, Tanko kira ta kace tazo Tafiya gida zamuyi kace tazo mu tafi ka fada a Gaban Annatu dole zata Koro min ita,Tanko yasha yadinsa milk duk cikin kayan da Fuzail ya dinka Masa yayi kyau harda hularsa ka rantse ma Abokin Prince din ne,Yana tafiya sai ga Islaha da Dan farin Hijab dinta da Leda a Hannunta ta auno Madara ta yin Alawar Madara,tana kallonsa ta Gane Tanko da karfi Tace laaaaa Iliyas ? Tanko ya tsaya da dariya yace lallai kinyi kokari da kika Gane Ni Haba taya bazan ganeka ba tab Sannu Ina yini?Tanko yace lafiya Alhmdllh,Fuzail sai masifa yake a ransa ganin Tanko ya ma manta da aikensa ya Kama Hira da wata yarinya.
Ina kika je Haka? Madara na siyo ta gobe,kaga wayata tana ta aikinta gaskiya me kyau ce kaji idan na Kira Goggota muryarta a cikin rangadadau, Tanko yace ba karamin Aiki na bane In Baki babbarta Islaha ta fara Masa fada wai Kai wallahi ka kiyayi wannan kyautar taka Yan Mata yanzu kulaka zasu dinga Yi su maidaka gara,ai Ni me kaunata nake Bawa abina,Ni kaina kana birgeni da ka bani Wayar Kuma sai naji wani tausayinka naji ka sake birgeni,Ai kyauta Dadi gareta cewar Tanko,ai Kuwa dai Nima naji,da Kamar Kar na karba,da tuni kin cuci kanki Tanko yace Yana kallon fuskar Islaha kyakyawa da ita me haske, yace kina da kyau duk masu suna da L masu kyau ne,Islaha tace uhm ai ni Zan fada maka Haka Ni da nake ganinsu a makarantar safe,Hmm Ni dai Zan tafi gida,Tanko tuni yace muje na rakaki a Ina kike ko a Nan Unguwar kike? Fuzail Yana Shan mamakin rainin Hankalin Tanko yanda yabi Budurwa ma ya manta da shi sun tafi suna ta Hira suna dariya,Islaha tace Allah ya kiyaye min zama a wannan Unguwar lalatacciya,Fuzail a fusace ya Kira wayar Tanko,Tanko ko duba Wayar baiyi ba Islaha ta tafi da shi tuni sun bar layin ma.
Yana kallon Amarya da Yan Mata suna ta nishadi,Fuzail yayi Dariya shi kadai yace Allah ya tsare Allah ya jishe mu Alkhairi,Yana Haka sai ga Ango da wasu Yan matasa irinsa Wanda a garin zuwansa Suka Saba a wata majalisa,Motarsa ya kotse tare da parking Suka fito da kudaden liki Suka yiwa Amarya Liki Wanda abokan nasa ma Belloti ne ya Basu kudin likin sabo da su rufa Masa baya,Amarya ta Shiga,Belloti har zai taka rawa sai ya fasa Kar a ganoshi Dan Tasha ne,ya nuna nutsuwa da da'a sosai Farida ma Bata nuna zakewa ba ta nuna itace Amarya,Manal ta fito da wani kudin zata Yi liki tana cewa Ango ya shiga? suka Kama Fulatanci da Belloti lokacin data shiga tana Masa liki ta Gama ta fito,Belloti Bayan ya fito yaje wajen Manal Yana fada Mata su Lawi sunce a gaisheta suna Dan tuna gida suna Dan magana abinka da Yan gari Daya an taso tare gashi Kauye kowa yasan kowa dole a gaisa ayi Hira,shi Fuzail Bai San wannan ba,ransa yayi tsananin baci Kamar ya fashe Haka yake ji,zuciyarsa kamar ta fito sabo da kishin bala'i ne da Fuzail matuka.
Nan take Idonsa ya canja yayi wani ja,farcensa yasa a Baki Yana kwankwasa hakorinsa da shi,Yana kallo gab da Magriba Manal suka shige gida sai gata sun fito da Mayafi sun Mike layinsu sun Kara gaba ko Ina zasu oho,dama Haka Mata ke biki wasu Indai Suka fito biki to fa shike Nan ba ruwansu ko Ina zasu iya zuwa Kuma a layin Haka da masu aure da marasa aure Haka basa yafa ko mayafi baza ka Gane matar aure ba.
Basu Dade ba yaga sun dawo a Napep da ledoji a Hannunsu alamar wani abin Suka siyo ma.