← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 95

Sashe 20

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana satar kallon Manal yanda gaba Daya kamar ta shige cikin Wayar Yana ta dariya a ransa,Manal tace wallahi Ina son waccen efto din Ni ko a kauyenmu film Indai bana sa bane bana bin su Khaltum zuwa kallo,a duniya Yana birgeni Ina sonsa wallahi ya hadu,ga iya soyayya ga tsara Yan mata ga iya rawa,Nan take Farooq ya hade uban Rai Idonsa ya canja,Ransa yayi masifar baci sai da Manal ta tsorata ta ja baya daga kusa da shi,karfin Hali yayi yace waye shi? Manal da tsoro ta nuna Masa Adam A Zango tace gashi sunansa Adamu Usher,Farooq yace wow then ba a wayata za a kalle shi ba,sai kije Wajensa tunda sonsa kike Yi,wayarsa ya dauke tare da kashe kallon yace dama ba so na kike Yi ba? Manal tace baka da Hausa Farooq ba irin so na aure ba so na film nake nufi ba,okay karki sake cewa kina son wani da Namiji a gaba na Kawai kice kina son Film dinsa,to naji Zan kiyaye kayi Hakuri kunna min,Yace bani kunnawa sai kince kina so na,Manal taji kunya ta Shiga yarfe Hannu tana boye Fuska,Kallonta Kawai yakeyi tana birge shi kunyar Nan tata tana birge shi a duniya,Manal tace Ina sonka sai ta kife kanta a cikin cinyoyinta,gyara zamansa yayi sosai Yana ta Jin Dadi yace I love you too,Manal tana ta Jin dadi kunya tasa ta fice da gudu ta bar gidan gaba Daya zuwa gidansu.

Haka suka ci gaba da Zama tare Amma suna kiyaye duk wani Abu Wanda Shedan zai shiga ciki suna tunatar da kansu,Farooq ya fara koyawa Manal turanci sannan Yana Kara gogewa da hausa sabo ita Bata Jin turanci Dole sai Hausar yake Mata ta karfi hakan yasa kullum Jin hausarsa da iyawarsa karuwa sukeyi,irin Hausar Yan Fulani duk ya koya wajen Manal,Manal ma tana ta koyon turanci a Wajensa Yan kana Nan kalmomi Wanda ya sansu da hausa su yake koya Mata,komai ta fada ko ya furta sai ya koya Mata da turanci,hakan yasa Suka wani mugun shakuwa da juna ka rantse gida Daya Suka taso,Komai tare sukeyi Yana ta Dan Wayar da Kan Manal,hakan yasa ta siyo littafi tunda ta fara primary ta dinga koyon Rubutu da karatu,Fuzail ya dinga koya mata a nutse yanda zata gane.

Yau sati Guda kenan da Haduwar Manal da Fuzail Wanda ta sani da Farooq,sun shaku matuka Kamar kullum yauma da yamma suna zaune ya rike Hannunta Wanda take rike da biro Yana koya Mata rubutu,Haka ake rike biro,Hannunsa Daya hade da nata yasa taji wani Yama-Yama a cikin jininta wani Abu na Mata yawo har kwakwalwarta,shima wani Shock yake ji a jininsa duk Sanda fatarsa ta Gogi fatar Manal,tsoron Allah yasa ya janye hannunsa da sauri,Suna Haka Ameer ya Kira Fuzail yace an sallame shi.

Manal ta Mike zumbur tace muje mu taho da shi Alhmdllh dama bana son kebewarmu mu kadai sabo da shedan,Fuzail yace Me too ya rike Hannunta Suka fito,suna Fitowa ta Zame hannunta Tace ba kyau fa,Yayi Murmushi yace sai yaushe zai koma da kyau? Manal ta kalle shi tace idan ka biya Sadaki Mana an daura Aure,Murmushi ya saki tare da cewa Talaushi akwe babu dadi,Dariya tayi taji Hausar sai a slow itama Suka shiga Napep zuwa Hospital Suka taho da Ameer.

Ameer da kayansa shima na gwanjo mamakin shakuwar Manal da Fuzail yakeyi,Fuzail da yake baida fara'a baya Shiga safgar kowa,ba irin matan da basu kawo kansu gare shi ba Amma ko kallo Basu ishe shi ba sai Manal,a Napep Yana kallonsu sai kus kus sukeyi suna dariya Kuma yasa Manal a gefensa shi Yana gefen Ameer sabo da kar Ameer ya taba jikinta.

Ameer mamaki yakeyi yanda yaga gidan da Manal ta Nemo suka zauna,suna cikin gidan Manal ta tafi karbo musu abinci,Ameer ya samu dama Bata Nan yace Prince wallahi Mai martaba Yana ta kirana akan lallai mu dawo gida sati ya cika,Fuzail yace Ina sane ai zamu tafi,Kuma dazu naji Kamar kana cewa you love her is tht true? Fuzail yayi kayataccen murmushi yace Yeah I do really love her, Ina so Aurenta verysoon,Ameer yace ta cancanta gaskiya Amma Kuma Umminka fa kasan warning dinta fa sannan gidan sarauta za a maka Dariya ba lallai su Amince ba,Fuzail yace wallahi Dole kowa ya yarda ko na bar kasar Nan Zan iya Aurenta a boye ma so is better for them su Amince ma shine samun lafiya,Ameer yace nafi Jin Umminka Fuzail, please Ameer bana son zancen Nan Na fada maka babu Wanda zai hanani abinda nake so Ina komawa Zan sanarwa sarki,Shuru Ameer yayi Yana hango irin rigimar da za a kwasa,shi Kuwa Fuzail sauri yayi ya Kira Umminsa suka gaisa,ya Kira Mai martaba yace gobe zai dawo,sarki yaji Dadi sosai da baya karya dokarsa.

Suna ta Hira Kasa kasa Manal ta dawo Riki Riki da Abinci Shuru sukayi sai Sannu da Fuzail yace mata,ta Ajiye a daki ta dawo tsakar gida inda Suka zauna suna hira,Fuzail Yana ta latsa waya baya saurarar Hirar Manal da Ameer,ba zato yaji an kwace wayar,Manal ya gani tana cewa sai naga mene a wayar,ai da sauri ya bita zai kwace ta zille da gudu,Bai so taga sirrinsa shi yasa ya dage sai ya kwace wayarsa,tsakar Gidan Suka shiga zagawa suna Dariya,ganin Haka Ameer ya saita wayarsa ya shiga Daukansu video,suna ta guje guje daga Nan ya cafke Manal ta cikwikwiye shi sosai tana jikinsa Ameer Yana ta dauka,sai da ya kwace wayarsa sannan yace Yi Mana pics Ameer,Manal ba ko gyarawa ta dinga yin tsaiwa iri iri sai ta matsa nesa da shi sosai sai tayi style a dauka Kawai haukar tsaiwarta takeyi ta Kauye,Ameer Dariya Kamar ta kashe shi.

Yace gyara Manal ki koma kusa da shi,Manal tana komawa ta sunkuya tayi ruku'u sosai Tace da Fuzail nayi Salona Farooq dafa ni,Farooq dai shima Dariya yake Yi ya daura kirjinsa da Fuskarsa a gadon Bayanta Suka kalli Ameer ai Kuwa ya dinga dauka kyas kyas,ta Mike tsaye ta Mika hannaye sama tayi Handsup shima Fuzail yayi Haka tare da manna jikinsa a Bayanta aka dauka Nan ma,Hannayenta ya rike suna kallon juna aka dauka,a gabansa ta tsaya tare da tale kafafu ta daura Yatsanta a karshen gemunsa Wai style tayi ai Kuwa Ameer Yana ta kyas kyas Yana uban Dariya sai da Fuzail ya Harare shi sannan ya rage dariyar.

Manal ta tsaya a gabansa tare da rike Kugu Tace Ameer dauke mu Ina Yi Masa masifa da bala'i,Ameer yace to an Gama har Video zanyi ya fara dauka,sannan yace Zan fara Video ki fara Masa Masifar kinji?

To Manal ta furta tare da rike Kugu ta zarowa Fuzail Ido tare da Furta sunan wata Yayata kenan Farida sai ta fara yiwa Fuzail Fari farrr.....farrrrrrr tana jujjuya ido tana yin tafi ya kasa rike dariyarsa,Manal Dan taji sunan Namiji Man da turanci Tace Hey Mans tana nuna su duka su biyun Tace Ba Singular nake nufi ba Plural Ameer yana ta uban dariya Kuma Bai fasa daukan Video din ba,yace nasan wallahi Farooq ne ya koya miki,Manal tayi Dariya tare da Furta Confirmed past tense nake nufi Kai Ameer, Suka sake shekewa da dariya Fuzail yace Haka Ana ce plural na Man? tunani tayi can sai ta kwaikwayi Muryar Fuzail yanda yake irin na turawa Oh My Gosh Men,Ameer Yana dariya yace kina da Basira Manal Kin Iya yanda yake magana wlh.

Fuzail Cikin Farin ciki ya Riko Manal Yana dariya yace ci gaba da Masifar Yana dauka fa,Manal taci gaba Wai masifa take yiwa Fuzail Tace Your Nose is like Biro like pencil,Ameer yace Iyyee Yana dauka,kasan me? Kai wani market ne wlh,wani ShopRite da Kai,Ameer wata Mahaukaciyar Dariya yake ta yi,Manal tace Finished Wasa ya watse an gama, tana shigo kaima Ameer ya shiga ya dinga haukar tsaiwa shima Yana biyewa Manal Yana ta musu Selfie sai da Suka gaji sannan ta zubawa Ameer Jullof din shinkafa da nama Guda Daya tal,Tasu da Farooq Kuma a flask din itama Mama Daya tal.

Tunda Manal ta samowa su Fuzail gidan Zama Farida kullum sai taje gidan Sarki taji ko masoyinta ya dawo daga tafiya Amma sai ace Bai dawo ba,Yau ma tana zuwa Tanko ya washe Baki,Farida tace Tanko Babban Bafade Ina labari? Tanko ya washe Baki tare da furta sai mun kebe akwai labari na kirki.

Farin ciki ya Kama Farida Tace Muje,Tanko ya jata inda Suka Saba kebewa Tanko ya furta fara Yi min Service da garanbawul Ina bukatar ayi min Juye,notika na sunyi tsatsa ya kamata a goge min su,Farida ranta Bai so ba ta zumburo Masa Baki tare da tsayawa kerere,Tanko ya shafa Hannunta yace wow Fatarki santsi wanne Mai kike shafawa? Farida ranta ya sake baci Yana Bata Mata lokaci da masifa tace Snow White,Ya furta wow ki dinga hadawa da Glycerin da man kadanya Zaki fi Haka laushi,Farida Tsaki taja tare da furta Dan Allah Malam sauri nake Yi ana Harkar arziki kana ta tsiya Mene wani man kadanya in Banda wari me zanyi.

Tanko yace yarinya ki dinga bin duniya a Sannu sai na siyo Miki man kadai din da Glycerin me kyau me tsadar ma ya Kai dari biyar,Takaici ya Kama Farida Tace wallahi badan Kai bane yau da Babarka ma Sai taji zagin da Zan maka daga kabari.

Indai iya ji ne Dan tana kabari taji kin zagi danta Tanko sai me? Ai ji Kawai ba matsala Hajiya Farida Yana magana Yana kashe Mata Ido daya sai da ya Gama wahalar da ita tana jiransa sannan ya wani cakumeta ya mutsitsikata,Farida cikin haushi Tace Wai mene Haka kamar ka samu kayan wanki? Tanko Yana washe Baki yana wani karewa kirjinta kallo yace Allah yasa wannan Abincin 'ya'ya nane.
Chapter 20 · 0% Book details