← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 95

Sashe 4

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Belt ya zaro yana cewa yau sai na kafa Miki tarihi a rayuwarki,Ina so na shiga record yau,ya dinga tafkar Farida tana ihu ganin ita ake jibga ba Wanda yayi magana ko ya Hana sai ma farin ciki da mutane Suka ji dama ta damu kowa a layin,ai Kuwa Dan kwaya Bai kyaleta ba sai da ya farfasa Mata jiki ya Mata ligif ya barta Nan,Almajiri Mai rike kayan Miya ya jefar da kayan Miya a gabanta ya fece da gudu da ragowar canjin Dari Uku na Farida data bashi ya rike Mata.

Sai kannenta su Alhaqatu da Falaqi sune Suka zo tare da tallafa Mata Suka jata gida,Yazed Yana gidan yaji duk abinda ke akwai Dariya ya dinga Murna Yana godewa Wanda ya Zane Farida yau,Yana Kallo Hajiya Kamar tayi hauka tana Bala'i da masifa za a kashe Mata Yarta,ta haukace a tsakar Gidan tana Bala'i Tace wannan ai hassada ce da bakin ciki sabo da kar Dan sarki yazo yaga Farida fes shine aka Yi makarkashiya aka turo Dan Daba ya tsokaneta tayi magana ya farfasa Mata jiki to wallahi Bari Allah ya kawo mijinta yazo zamu ga uban Wanda zai Hana mu warwasawa.

Malam Wanda ke Kan Wheelchair dinsa a tsakar gida Yana Jin radio ya kalle su Kawai Yace kunyi asara mahaukatan banza Ina kika taba ganin Ana yarda da mafarki abinda Baku da Tabbas,Farida tana kwance saman Tabarma ta harari Mahaifin nata tace wallahi da gaske ne munje anyi Mana duba,Kuma ko jiya sai da na Kara yin mafarkinsa yazo da motoci sunfi biyar yace min Sunansa FUZAIL Yana nufin Generous Dan Kai baka Yi boko bane baza ma ka Gane ma'anar turancinba Ni Kuma bazan Bata lokacina wajen fassara maka ba sabo da a yanzu na kusa Zama gimbiya,Ni Tarihinsa ma kusan na sani.

Sunansa FUZAIL Dan Sarkin Garin Nan ne Wato Sarki Usman Manu Lamido, Hajiya Babba Wato Balkisu tana da Yara biyar,Salman,Aliyu Saima,Naja'atu,Hassan da Hussain ,Sai Mata ta biyu itace Ayusha Yar asalin Algeria ce Sarki ya ganta a kasar Brazil ya aureta ya kawota Nigeria Bayan shekara Biyu ta Haifo Danta Kato kyakyawan gaske Fari Fari Haka yake Kuma shi ba Chocolate ba Kuma shi baza ace Fari Kal Kal ba,wani irin skin ne da shi Unique duk Wanda ya kalle shi yasan ya Gama kaiwa karshe,aka sa Masa Suna Fuzail.

Tunda ta haifeshi sauran matan Suka Mata caa da bakin ciki da hassada irin na gidan sarauta ganin za a kassara Mata rayuwa da danta sai ta tattara nata ya nata tare da danta ta koma Brazil inda suke rayuwa da iyayenta,Sarki ransa ya baci sabo da ba yanda baiyi ba akan ta zauna Amma Taki yarda,jinin Larabawan Algeria ce Bata kaunar talauci ita shi yasa ma ta iya auren sarki Usman sabo da tasan akwai kudi,rashin Hakuri yasa ta gudu da danta itama kanta Ayusha ba matar arziki bace,a can Fuzail ya girma Wanda shi Kansa sarki baifi sau Biyar ba ya taba ganinsa a duniya ba,Yana bin Dansa da Addua Kuma Yana Burin dawo da shi gabansa sabo da addininsa Yana tsoro Kar Dansa ya fada halaka.

Shi Kuma Fuzail Adduar Mahaifinsa ta bashi duk da baida wani ilimin Islama da yawan gaske amma yasan me yake halaye ne da shi masu kyau sai dai baza ka Gane Haka ba sai ka zauna da shi,Sarki Yana so ya dawo da Dansa ya zauna da shi a Nigeria shi da kasar waje sai dai da yawo,Kuma magana tazo karshe tunda Mahaifiyar Fuzail ta Amince Danta ya dawo Kasar Mahaifinsa amma Kar ya sake ya auro Mata wacce ba jininta na Larabawa ba Ko kuma Yar me kudi shine sharadin Ayusha,Kuma Fuzail ya Amince.

Salman a Yaran sarki shine Babba Kuma shine magajin sarki domin mutumin kirki ne Komai na sarauta Yana gaba,Yana da tarbiyya mutane suna kaunarsa,sai Mahmood,Ishaq sannan Fuzail sune manyan. Hajiya Raheena Ana Mata lakabi da me kallon Gabas, tana da Yara Biyar itama Na'ima,Fatima,Haisam,Rumaisa,sai Auta gaba Daya Ammar.

Sarki Usman Yana da kanne biyu Hajiya Zainabu sai Alhaji Ishaq Wanda shi sarauta har kala Uku yake rike da ita a Nan garin Nasarawa,Yana da Mata biyu da yaransa Mata da maza sun Kai goma,Hajiya Zainabu tana auren Sarkin Katsina yaranta Uku kacal duk Yan Mata ne sabo da Allah bai Bata Haihuwa da wuri ba,sai sauran Yan Uwa Wanda duk jinin sarauta ne duk sarauta ce da su,Haka Yaran sarki kaf maza duk hakimai ne da Karin wasu sarautun a kansu,Anyi anyi Fuzail yace Bai so shi,a rayuwa ya tsani Harkar Sarautar da akeyi a Nan kasar ayi ta wani girmama mutum Kamar za a bauta Masa shi baya so abin Bai birge shi.

Sabo da Haka Sarki ya kyaleshi yace ko ya dawo baza a takura Masa ba da Harkar sarauta duk abinda yake so shi zaiyi za a bashi Freedom sabo da duk Ana so ya zauna Kar ya gudu ya koma,yace part dinsa Kar yaga fadawa a ciki me Aiki maza biyu mace Daya tal yake so,Mace Kuma ta kasance Babba,sannan shi zai zaba wacce tayi masa,sai maza biyu Nan ma shi zai zaba,sarki yace ya Amince Masa sannan yace a dauke shi a Airport next week Kuma zai Shiga makarantar addini ya Kara Ilimi akan nasa,Fuzail Yana Jin Hausa amma shi Bai iya maida Hausar ba sosai hakan ma sabo da Ameer Dan Kanin Babansa Waziri Ishaq tare Suka Yi karatu a London har masters a wajen Ameer ya koyi hausa da Ilimin Addini.

Fuzail Bai Shan komai,baya Neman Mata Bai taba yin ko Budurwa ba,Yana da hankalinsa dai dai gwargwado .
Fuzail kyakyawa ne na bugawa a jarida duk inda kuke Neman kyau da kyan sura to Fuzail karshe ne,Kuma Malam wallahi nice matarsa Ni zai Aura Ni Farida na fada maka na sake rantsewa Ni matar Dan sarki ce,har bikinmu da yanda za a gudanar da shi duk na rigada na sani a mafarki,Kuma Nan da 5days zai bayyana a gidan Nan zaku ce na fada muku Kuma,Ni Farida matar manya ce,Kwana Nan zaku ganni da Hajiya a private jet,Muna Hawa motoci na Alfarma,muna shiga da fita a cikin Gezna,tunda Malam Kai ka haifeni Zan sa ya kaika kasar waje ko za a Dace ka warke duk da nasan kaima ba sona kake ba,Zan Gina maka gida me kyau kaci albarkaci.

Tunda Farida ta fara labarin mafarkinta a Kan Fuzail Malam da Yazed suke Jin tatsuniya,Malam yace shashasha daga Jin sunan kasan na Aljanu ne Wai Fuzail to Aljani ne babu wannan sunan a Jibsin mutum,Kina mafarkin Aljani kina rantsuwa da gaske ne,Farida Tace zaku gani Kuma wallahi ba karya bane,Amma ko Kai Malam ai sunan Aljanun kake sa mana,ka sa Wa'qia,Falaqi,Masatura,Saiha,Amma Farida,Manal,Yazed mune kadai Allah ya taimakemu Iyayenmu Mata suka dage sai da aka canja Mana suna me Dadi,Amma ai gashi Nan ka sake maidawa a Kan kannenmu amma Fuzail ne zaka ce sunan Aljani....wata Tsawa Yazed ya daka Mata bafa Sa'anki bane Malam,Shi fa ya haife ki,kisan me Zaki fada a gabansa,Idan ma mafarkin naki gaskiya ne mu Ina ruwanmu ki auri Dan Sarkin Makkah ma,Hajiya caraf Tace Dan bakin ciki sabo da ba Kanwarka bace Manal Inshaallah aikin wanke wanke da shara zata tayi masu har gidan Sarauta Hassada aniyarku ta biku.

Sharhi fans pls

AsmaBaffa
[1/1, 10:23 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭

BANA KUDI BANE

WANNAN NOVEL SADAUKARWA NE GA YAN GROUP DINA

DUNIYATA AAMNA FNS GP.

4-6

LITTAFAN DANA RUBUTA SUNE

GASKIYA CE
MA'AIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMAR SU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
ME MAGANI
TUBABBIYA
HADIN KAI
RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA
DANGIN RABI
DUNIYA TA AAMNA
MAFARKIN FARIDA....

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

AISHA
KHADIJA DANDAWAKI
MAMAN MURTALAH
YAHAJJA KAMSHI
BESTYN BEELAT
BASMAM GLAM

Yazed tashi yayi tare da tura Malam zuwa dakinsa Suka koma suna Hira abinsu,Suna Shiga Malam ya kalli Yazed Hawaye ya zubo Masa sabo da irin bacin ran da Hajiya ke cusa Masa tare da yaranta,Yazed ya rigada ya sani lallashinsa ya shiga Yi yace Dan Allah Malam ka kyale su ba su kadai Allah ya baka ba,gamu Manal ma jibi zata Zo ta tayani kula da Kai ka daina damuwa Dan Allah Malam, Malam ya jinjina Kai yace Hakika a baya na tafka kuskure gashi Ina girbar abinda na shuka Allah ka yafe min,Yazed yace haba Malam Kamar baka San kaddara ba kayi Hakuri,Malam ya kalli Yazed Dake goge Masa Hawaye yace abinda ya dameni shine Yan gonakina na Kauye da Suka rage Mana nake Dan tabuka wani abin da kudin noman nasu Wai Gomnati ta kwace su da wasu na mutane wajenta ne Wai yanzu wata University zata gina a wajen Kuma babu ko diyya da zasu biya mu,Salati Yazed Ya saki yace Malam waye ya fada? Tun sati biyu da suka wuce Kawunku ya bugo waya Suma harda wasu nasu ciki,Ni dama kasan layi biyu Suka rage min a can duk cuta ta cinye komai Nawa to yanzu gashi Dan abinda muke dogara da shi ya kare gashi Bamu da geron Koko,Gashi kaima Allah Bai baka wata sana'a ba ta kirki,Yazed ga Karatunka ga na sauran Yara,Yazed cikin karfin Hali yace karka damu Malam Allah zai rufa asiri,ai dama Allah keyi ba dabarar mu ba,yanzu ma shi zai mana mu dage da Addua,Malam yace Hakane Allah ka dafa Mana Dan girmanka ya Allah cewar Malam shima,Su Hajiya duk Basu San me ake ciki ba ta Shirin tarbar bakinsu sukeyi Dan Sarki Fuzail na cikin mafarki.
Chapter 4 · 0% Book details