← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 95

Sashe 6

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal ta fara karewa gidan kallo tare da furta chab Ashe Birnin duk karyar banza ce,gadar sama da haske shine Kawai abin birgewa amma Ashe ta Gina Bata Shiga bane.
Farida ta San Manal Amma sai ta Mike ta ruga daki da gudu Wai tayi gamo sabo da wulakanci,Hajiya ma tana lekowa taga Manal ta ganeta Amma sai ta kwala Ihu ta banke Kofar ta suna lekowa ta window,ita Manal ma Bata iya Gane su ba sabo da rabonta da su tun tana Yar 7yrs da Annatu ta kawota Hutu.

Yazed ransa ya baci matuka sai kace sunga dodo Haka ya shiga da Manal wajen Malam,Malam ya dinga Murna yace Manal Haka kika girma? Ai kinfi Farida ma girma kamar kece yayarta,Manal ta durkusa tare da gaisar da shi tana tausaya Masa yanda baya iya tashi,Tace Malam ai Farida ita jirani wada ce,Tayi gajeriya da yawa Saura kadan ta Zama wada,Haka ake cewa Irinsu Jirani wada Ina zuwa, Madarar Shanu ce take Aiki a jikina shi yasa na girma Haka,Dariya Malam yayi yace to Alhmdllh ka nuna Mata Daya dakin da ba kowa sabo da ko ka kaita dakin su Farida zata fuskancin matsala gwara tunda da daki daban ka sata ciki,Yazed dama ya gyara dakin har ya sa Mata Yar karamar katifa a ciki da Ledar tsakar daki,Manal ta Ajiye kayanta,Yazed ya kawo Mata sabuwar Ghana must go yace ki shirya kayan sawarki a nan,ki fito kiyi wanka sai na kawo Miki abinci,to Manal Tace tare da aikata abinda yace sannan tayi wanka ta canja wata Yar tsangalalliyar doguwar rigar wani yadi Wanda ya ji jiki green.

Yazed Shinkafa da Miya yaje ya siyo Mata harda Nama yanka Uku,Duk gidan ba Wanda yaci komai ba a Dora girki ba sabo da babu kudi,shima Dan ragowar dari biyu ce Dan kar ya barta da yunwa ta fara rigima shi yasa ya dauke ya siyo Mata abincin har da Pure water Guda uku,Zama tayi ta ci ta koshi tare da rufe ragowar sai zuwa Yamma zata karashe abarta.
Ba ko dankwali a kanta gashin Nan yalala abinka da Yar Fulani har gadon baya,da rigarta me Hannun vest ta fito zata fita waje a Haka Yazed ya daka Mata Tsawa Baki da hankali ne? Nan fa ba Kauye bane,Sai lokacin su Hajiya da su Farida Suka Fito,Hajiya tana tabe Baki tace au Manal ce dama? Farida da su Sa'iha suka kwashe da dariya Kamar mahaukata Wai dama Manal ce Amma Kamar aljana? Farida ta Furta tana dariyar rainin hankali,Ran Manal ya baci gata duk ta fisu girma ma ai Kuwa Masatura tace Allah Kamar wata arandoni ...kafin ta rufe Baki Manal ta daure ta da Mari tare da furta Uwarki ce arandoni ba Ni ba,Dan Uwarki sa'arki ce Ni ko Baku Sanni ba? Duk da cewar na Dade ban Zo ba ai nasan Kun sannni Sarai,Farida ta zuciya an Mari kanwarta ta cakumi Manal zasu Yi kokawa,Manal girman Kauye ce ba yanga,gata yarinya Danya me ji da wauta ai Kuwa Kawai surar Farida tayi Kamar ta dauki tsinke ta bugata da kasa ta zaune a kanta ta shiga dukanta ta ko ina,Hajiya Ihu ta saki da kururuwa.

Tana za a kashe min 'yata,shike Nan Fuzail za a maka asara,wallahi Baki Isa ba mun kusa shiga daula baza ki Rusa Mana mafarki ba,Matar Dan Sarkin kike duka? To Dan sarki zata aura kwana Nan wallahi sai an koreki daga garin Nan idan ta Zama matarsa muguwa,Cak Manal ta tsaya tare da tashi daga Kan Farida tana murmushi ta tambaya Allah da gaske Dan sarki zata aura? Hajiya da Gadara Tace kwarai Kuwa ki daina Raina ta kwana Nan zaizo Zaki gani da idonki,Manal harda ihu tace ai aradun Allah ban sani ba,Sannu Gimbiya ta rike Hannun Farida,Farida ta kwace Hannunta tare da galla Mata harara Baki da hankali Ni Zan hada jiki da ke ki shafa min warin Kauye Salon Yarima yazo yaji Ina tashi,Manal duk ta dauka a gaske ne zata auri Fuzail tace ba komai girmanki ne Allah ya samu a danshinki,Na tayaki murna Yar Uwata,Hajiya ta washe Baki Tace to daga yau ba raini Kuma wallahi kika sake taba ta sai ta sa an koreki daga garin nan,Manal Tace ikon Allah yaushe zai zo zance?Hajiya Tace ya kusa zuwa Kinga ko Aiki sai ki dinga zuwa kina Yi a gidan Surakan Farida,Manal ta rike Baki Tace cab Ni Kuma bauta zanyi? Ina Yar uwarta Ina laifin ma a talauce ta siya min mota ta milliyan goma Haka,Baki Suka Bude Farida tace Baki Isa ba wallahi yarinya ai ko keke tunda Baki da mutunci,Manal Tace Dan Allah Yaya Farida kiyi Hakuri ance da ac a gidan ko iya ac ki lamince min in Dan Sha ko ta kwana biyu ce ko ma ta yini Daya ce.

Yazed da Malam suna jinsu suna ta dariyar Haukar Su har Manal da Bata San duk a mafarki bane,Farida tace sai dai idan daga yau Zaki dinga wanke min kayana kina gyara Mana gidan Nan sannan duk wani Aiki ke Zaki Yi q gidan Nan to idan ya aureni har Makkah Zan sa ya kaiki, bana so a dinga Bina gidan sarauta Ana kunyata Ni,Kun San gidan sarauta basa son Hayaniya kudi Ne da mulki dankare a gidan,Manal tafi tayi tace Allah ya yarda na Yar Uwa shike Nan Dan aikin gidan Nan ai karki damu Matukar ac da nake Jin labarinta naurar sanyi zata fifita Ni ba abinda bazanyi Miki ba.

Karki sake Fatarki ta lalace Yaya Farida,Farida Tace ke dalla Yar Kauye Aunty ake cewa Aunty Farida karki sake ce min Yaya Haka Kawai salon Fuzail yazo yaji kauyancinki,Manal tace gaskiya Anty Ina yinki irin wannan soyayya Haka,Farida tace Yau zamu Fara shirye shiryen ya auren Nan nawa zai kasance,littafi ma Zan siyo zamu rubuta komai,Manal tace ai Yasin hakan yayi ayi sauri a tsara komai sabo da idan lokaci yazo komai an tsara yafi.

Farida kallon Manal tayi Tace ranta min Naira Hamsim idan Fuzail yazo Zan biyaki abarki ba kyauta nace a bani ba,Farida da sauri ta fada dakinta tana murna harda Waka ta dakko Hamsim cikin kayanta ta bawa Farida,Hajiya Tace Masatura karbi maza kuje kanti ke da Falaqi ku Siyo littafin ku dawo,karba suka Yi suka tafi siyo littafin,Manal tana kallo Suka dawo aka dakko Tabarma tare da shimfidawa a gindin bishiyar Dake tsakar gidan har Hajiya,Farida ta rike Biro tace ranar Thursday za a fara bikin Haka na gani a mafarki,Hajiya tace Party ne ranar a Raais Guess palace kin San Nan sai manyan mutane maza rubuta,Farida ta rubuta tare da cewa sai Friday ranar Bridal Shower 8pm,Masatura Tace kamata yayi a Juji palace Kin ga sai Gomnoni ne ke shiga wajen sabo da tsada,Farida Tace haka za ayi,Sunday Kuma daurin Aure da Kai Amarya sabo da kar a ja bikin gwara na hau karagar mulki na Zama Gimbiya cikin gaggawa,a mafarkin Nan Naga ba Delay a Harkar bikin cikin gaggawa aka daura.

Hajiya Tace to yanzu Kinga Muna da munafukai da mahassada a Unguwar nan, mutane suna gulmar mu suna zagina cewar Ina fasa Miki,Ina lalata ki,Baki da tarbiyya,to Dan ubansu rubuta duk Wanda muka sani makiyanmu a Unguwar Nan,Yana aurenki zamu sa aci ubansu,Farida Tace Fire for Fire wallahi duk sai mun Rama zasu ci ubansu.

Masatura Tace Haka Maman Haneef ma ta dinga Mana Dariya Wai Ina Mijin mafarki yake,Da Sauri Hajiya Tace munafuka sai anyi auren su lallabo suce zasu kulla alaka Dan a taimaka musu to karya sukeyi Basu Isa ba,Farida tace waye ya Isa ma yazo Gidan sarautata yace zai dinga nuna min yanda Zan gudanar da zamana a masarauta,Hajiya Tace rubuta Maman Haneef itace a farko cikin Bracket kisa Uwar Gulma sai mun sa an kore su daga garin Nan gaba Daya mun siye gidan nasu na gado da suke takama da shi,Haka Farida ta rubuta Kuwa,Hajiya Tace ta Biyu Hajiya Abu Naga tana min gani gani kwana Nan rubuta ta Dole ta ci ubanta Nan gaba,Nan ma aka rubuta,Hajiya Tace saka Sunan Malam Zikirilla Rannan harda Yi min wa'azi Wai na dinga kula da tarbiyyyarki kaji munafuki yarsa na lalata da zai dameni Dan bakin ciki,Farida ta rubuta Malam Zikirillah prison na shekara goma a gidan yari,Rada Hajiya tayiwa Farida Tace rubuta Manal a ciki tsinanniya na tsaneta so nake Ana auren a dauketa Aiki a gidan,ko Kuma kafin a aureki mu kaita can aikin Bauta,Manal Bata iya karatu da Rubutu ba a gabanta aka rubuta sunanta da duk irin azabar da za a gana mata ba tare da ta Gane ba,ita dai tana mamaki akan za a auri me kudi Dan sarki sai a wulakanta mutane Kuma tun ba ayi Auren ba,Yazed ne ya fito cikin kodaddiyar shaddarsa peach zai fita yace Manal tashi bana son ki shiga wannan haukar wannan Mijin da ake lissafi duk a mafarki ake ganinsa,Manal Tace ban Gane ba? a takaice ya Bata labarin a Gaban Kuma su Hajiya,Manal sabo da dariya harda faduwa a kasa tana kwalla tace Wai dama a mafarki ne? Hajiya ce ta Bata Rai matuka taji haushi Manal Shuru tayi ganin Rai zai baci Tace fatan Alheri nake Miki Anty Farida Allah ya tabbatar.

Yazed Hannunta ya rike tare da janta gefe yace bana son fada,karki Shiga harkarsu bare kuzo Kuna tayarwa Malam Hankali idan aiki ne ko mene idan Basu Yi ba kiyi,gidan Nan kazamai ne idan Baki gyara ba babu me Yi kiyi Hakuri da rayuwa kiyiwa Hajiya Biyayya,itama Faridan ta girmeki ki Mata biyayya,nasan halinki da Shiga abinda ba ruwanki wallahi naji anyi fada dake sai na Miki dukan tsiya a gidan Nan,ba ruwanki,duk abinda zasu Yi ba ruwanki kinji na fada miki,ki jira zanyi kokari na sakaki a makarantar Boko da Islamiyya ko ta Gomnati ce sannan Zan dinga koya Miki karatu da kaina a gida,Manal tana murna Tace to Yaya Inshaallah,Fita Yayi Ita Kuma ta koma dakinta.
Chapter 6 · 0% Book details