← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 95

Sashe 37

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Belloti yace itama fa maryam din Yan rainin hankali ce kasan ba Wani zumunci sukeyi da ku ba sabo a Kauye kuke bare wani ta so ni,Lawi ya damu Belloti shi sai ya hada shi da Maryam,ai Kuwa ya bashi Number Maryam,a ranar ya fara waya da Maryam, Farar Daya yace Yana Sonta itama ba Bata lokaci Tace ta yarda tana sonsa, Kullum sai Belloti ya tura Mata da katin waya na dari biyar har accnt number take tura Masa Yana zuwa Birnin Bauchi ya sa Mata kudi,Maryam tana ta wanke gara,Watarana Tace za ayi bikin kawarta,Belloti yace zaije Mata har Kano bikin shima Tace to.

ai kuwa ya shirya tare da daukan wanka ya canja sosai yayi kyau Ya samu ya kashewa jikinsa kudi shaddarsa Yar Dubu takwas,ga agogo na dubu biyu,takalmi ma Dan dubu hudu,yayi wankan Nan na fita sosai, shi kansa yasan yayi kyau har da aske tozon gashinsa na tsakiyar Kai duk sabo da zaije Birni wajen Yar birni,ya siyar da Ragonsa ya ebi kudinsa dubu ashirin a ciki sabo da idan yaje Zai bawa Maryam su kyauta tayi biki lafiya zai Mata alheri,yaje Kuwa har can, ta sauke shi aka kawo masa ruwa da lemo ga abinci yasha nama,yaci ya koshi Ashe wai Sam ba bikin kawarta akeyi ba bikinta akeyi ita kanta Maryam din,Ashe ita ce Amaryar.

Belloti yana dakin da aka sauke shi Bayan ta kawo Masa abinci sun fita ya fara Irga kudin da zai ba Maryam kyauta kenan yaji ita da kawarta sun tsaya a bakin kofa suna Dariya suna tafawa,Maryam tace kyale gara Bai san bikina akeyi ba ai na wanki gara wallahi yaje, Basu San Belloti Yana daga daki yaji komai ba, suna Shawara kawar tace ki fada Masa gaskiya Dan Allah wallahi hakan da Mata sukeyi yanzu babu kyau,kasan ba son mutum kakeyi ba ka yaudare shi karshe maimakon ayi rabuwar mutunci sai wulakanci ya biyo baya.

Wannan abinda Yan matan yanzu ke Yi hakkin samari da yawa wallahi shi yake bibiyarsu gidan miji,kaga idan sunyi aure Sam babu zaman lafiya sai dai wahala da wulakancin Namiji ya biyo baya karshe ma hakkin wani yasa a sake ta da wuri ta dawo bazarawa to ta zalunci maza da yawa Wanda ita a lokacin ta manta,Ana mantawa da Allah baya mantuwa shi,wasu ma Sai mutum yace zaizo wajensu Rumi Rumi su sa ya Sha wahala a garin suyi ta bashi wrong Address Yana ta bulayi a garin karshe sai dai ya Sha wahalar banza ya koma gida,babu ruwansu daga nisan duniyar da yazo,da kudin da ya kashe a Hanya da sauransu ya taso yazo Dan Yana son mace amma ta wahalar da shi a banza,gashi kema Maryam kinyi Masa sai Kun cinyewa mutum kudi karshe sai dai ya tsinci labari anyi bikin mace wannan wacce yaudara ce? Wacce hauka ce da Jahilci da hauka irin ta mu ta hausawa? Wallahi wannan ba wayewa bace rashin Ilmi ne da Rashin sanin darajar Dan Adam da so,mutum yace Yana sonka Maryam ai arziki ne,idan yace fa ya tsaneki ko labari kika ji baza kiji Dadi ba,Amma kin San ya tura miki kudi ki karbe,har bank yake zuwa birni ya tura miki ta bank,Haba Maryam kiyi Aiki da hankali wannan aikin Wanda Basu San me suke Yi bane,duk masu cewa Sun wanki Gara kaza kaza hauka ne fa,mutum ya dauki kudi ya baka kayi amfani da su ka kashe matsalarka ai taimakonka yayi wallahi.

Abin haushin duk cin kudin matan yanzu da sukewa samari babu Wanda Suka taba karya Masa tattalin arziki sai dai ita macen nata data Yi yaudara ta samo su Kare a banza, wa kika gani sanadiyar cin kudin Budurwa ya rasa kudi ko kudinsa sun Kare? Sai dai me Neman Mata wallahi shine kadai bazai ajiye abin duniya ba. Maryam tace ke Rahila Adana wa'azinki bazan iya ba gaskiya Kawai tunda Dan Iska ne Kamar Ni zai ce yana so na, Kinga Ni na Riga na auri Mahmood Dina zabin Raina,Kuma duk samari na ba Wanda ya sani sai dai suji a gari,shi yasa ban gayyaci mutane ba ma,Bari na Masa sharri nace ga Dan Kidnapping yazo shege a daure shi ya Sha wahala a prison Nan gaba bazai Kara cewa ya sanni ba a rayuwarsa.

Basu San belloti Yana ji ba,Yana Jin alamar sun tafi ya fito daga gidan gaba Daya da Niyyar guduwa Maryam ta hango shi ta kurma Ihu a Kofar gida ga mutane maza da Mata Yan biki tana cewa Barawo ne ga Dan Kidnapping,Belloti kafin ya gudu ma mutane ta ko Ina sun Kama shi,Rahila Kawar Maryam itace ta dinga cewa wallahi karya take Masa karku taba shi sharri ta Masa wallahi ba ruwansa bawan Allah,Allah sarki Belloti an ganshi Dan Fulani an Masa sharri mutane Suka ki yarda,Rahila tayi ihu da rantsuwa tafi cikin container amma anci sa'a yayi amfani kadan Belloti ya Sha duka,kafin kace me an fasa Masa kai Rahila Dake an santa sosai a wajen sun Dan saurareta tana ta Basu labarin gaskiyar al'amari,Amma mutane wasu tuni sunci gaba da jibgar Belloti an Masa budu budu tare da fasa Masa jiki,Suma yayi a wajen Lokacin Kuma manya da suke wajen Suka dakatar da mutane daga dukansa aka tsaya sauraron Rahila,duk bayanin Rahila mutane sunji karshe Rahila Tace Kuma wallahi Dan asalin kauyen su Maryam din ne,Abokin ma Dan uwanta ne a Ruga,duk da Haka mutane sai da suka Kira Police aka damka Belloti a Hannunsu aje ayi Bincike,sabo da halin da ake ciki a kasar Nan yanzu ba a saurarawa.
Maryam ko a jikinta,Rahila sanadiyar Haka ta zazzagi Maryam Suka Yi kaca kaca ta bi Bayan yan Sanda inda aka tafi da Belloti ita lallai sai an kwatowa Belloti Hakkinsa.

Washe gari Ummi taga Fuzail ya dau wanka da niyyarsa ya Kai Manal School Kamar jiya ranar zuwanta na farko,a jikinta taji wajen matarsa zai je,sanye take cikin kayansu na Larabawa Arabian Gown,tana zuwa ta kalleshi tare da hade Rai Tace Ina zaka je? Ba tare da ya kalleta ba yace Unguwa,baza kaje ba Kawai ta furta,yace why? Na hanaka fita yau,a ranar yau ba inda zaka fita,Fuzail yace ai iya yau kika ce ko? Ummi tace ae,yace fine ya koma saman makeken bed dinsa ya kwanta abinsa Bai kulata ba yaci gaba da latsa wayarsa,Text ya turawa Tanko yayi sauri yaje ya Kai Manal School,Manal tana ta murna zataga Fuzail dinta yau ma sabo da jiya taji dadi ai sai taga Tanko shi Daya ne ya kaita school,tana sa ran ko da Fuzail za a zo Daukanta taga Nan ma Tanko ne kawai.
Manal Tace ai dama Bai damu Dani ba na sani ta shige gida cikin Fushi,Ba Wanda ta kula tayi wanka tare da Sallah Islamiyyar ma kin zuwa tayi Wai sai yazo ya Kai ta idan ba Haka ba baza taje makarantar ba har Bokon ma gobe baza ta je ba Indai babu shi.

Manal ta dafa Indomie tana ci a tsakar gidansu zaune saman Tabarma,Farida tana zaune tana duba littafin soyayya a waya itama a tsakar gida saman kujera,Hajiya tana wanke wanke,Yazed da Malam basa Nan sun koma kauye wajen me magani sai gobe zasu dawo,Yara Kuma duk sun tafi Islamiyya,Babu ko Sallama Suka ji an banko kofa an shigo,Balarabiya Suka gani ta Sha Arniyar farar gown ta Larabawa ta zuba kyau,Ana ganinta anga kudi,a waje Kuma ita kadai ce tazo sai Driver da ya kawota Wato Tanko,a Wajensa ta samu Address din gidan su Manal,Ana ganinta ba sai an fada ba an San Maman Fuzail ce suna Kama.
Hajiya taji Dadi a ranta damarsu tazo ta kalli Farida tare da kyafta Mata Ido,Tanko shi Bai San me za ayi ba Tace idan yasan gidan matar Fuzail ya kaita,shi Kuwa ya kawota.

Farida da sauri ta fara soshe soshe tana Jin kunya tana rufe Fuska ita a Dole itace Manal Amarya me kunya,Ummi ganin Manal yarinya karama Kuma kallonta tayi Kiri Kiri Bata ji kunya ba,sai taga Farida da Alama itace Babba Kuma itace take nuna kunya sai ta tabbatar Farida ce matar Fuzail dama maybe Fuzail ya nuna Mata pics dinta ta Santa shi yasa ta fara kunya lokacin data ganta.
Ummi Tsoron Dan nata Fuzail ya kamata bayan talaucin ma Wannan Mummunar ya auro Kuma a Haka yake sonta,Tsaki Ummi taja tace Amma Fuzail yayi asara wallahi Bai min Adalci ba ya rasa wacce zai so sai wannan abin,Hajiya Target dinsu ya hau sai ta tabe Baki Tace ai ba 'yata bace Yar tsohuwar matar me gidana ce,sai ta Nuna Manal tace Ni Kinga 'yata can sunanta Farida,matar Dan Iskan dan naki gata can sunanta Manal ta nuna Farida da Yatsa,Manal ta bude Baki ,da sauri ta Mike tazo Gaban Ummi Tace Ina yini Ummi Sannu da zuwa Bamu Baki wajen Zama ba.

Wata Uwar Harara da Tsawa Ummi ta bugawa Manal tace karki sake kirana da Ummi aikin banza mayu Kun mannewa Dana aikin banza to wallahi Dana yafi karfinku,Hajiya Dan Munafunci sai itama ta Mike tare da cin danmara da dankwalinta tace ke dakata tsohuwar banza ga matar danki Nan karki sake zagin 'yata wallahi sai nayi kasa kasa dake a gidan Nan duk kudinki ai ba matar Sarkin bace ce ba abinda kika Isa ki Mana,shegiya kodaddiyar banza,bakuwar haure Kun hauro kasar mu Kun bi Kun kankane Mana masu kudin kasar sai auresu kukeyi Kuna Tara arziki,gantalalliya tsohuwar banza karuwar tsohuwa,ai da ganin irin wankan da kike dauka an San karuwa ce ke dama ai an fada karuwanci kike a Brazil amma Malam ya Baku yarsa banza a banza.
Chapter 37 · 0% Book details