← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 95

Sashe 59

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tanko cikin Shaddojinsa masu tsada ya zabo Wata grey ya dau wanka yau shi kadai ya tafi kowa yaga Tanko yasan yayi kyau,Napep ya shigo hannunsa rike da Handkerchief wata Yar Budurwa ya Iske a Napep din Fara tsaleliyar gaske sai dai da gani talakawa ne,Alawar Madara ta dakko a wani Farin bokiti Tanko ya kalleta ya sake kallonta yace Kaiiiii Allah Mai baiwa,Wato ko Ango ne a wajen Bikin nasa zai ga wacce tafi Amaryar tasa,Ke ya sunanki? Yarinyar da Bata fi Manal ba ta washe Baki jerarrun hakoranta Suka bayyana tace Sunana Islaha,Iyye Wannan sunan ya Dace Dake Islaha me Alawar Madara,Tanko Nan take jikinsa Yana rawa yace juye min ita a Leda na siyeta gaba daya,Islaha ta Bude Baki yace ko Dan kyanki ai a siya,Islaha tace ai ba leda,Tanko Yace Siyen Zuma Zan Mata na siyeta har Botikin,Islaha ta kalli Tanko ita sai taji Tanko ya birgeta,Dai dai din wani a karkacen wani.

Islaha ta bashi du Ya biya kudi gaba Daya,Tace Kai me kudi ne gaskiya,Tanko Yace Allah sarki Mission na fito Yi wallahi ba karya wani Aiki zanyi Amma da kike ganina Me Gadi ne a gidan Sarki,Islaha murna ta kamata tace wayyo Dan Allah a gidan Sarki kake Aiki?Tanko Yace Uhm Bayi ba mu a bauta Muka taso,Islaha Tace cab wallahi ai Kai ba bawa bane,ai yanzu an daina bauta tun zamanin Jahiliyya aka Yi wannan,Ya sunanka Kai? Tanko Yace Iliyas harda gyara suna Iliyas Ana ce min Tanko,Wannan Kaka ta cuceka wallahi ka canja suna gaka kyakyawa Ana ce ma Tanko Kawai ka koma tk,Tanko Yace No T&K ko? Islaha tace da yafi kasan Ni Ina son Inga mutum Dan wanka,sai ka birgeni,Tanko Yace lallai darajata ta karu,Nan take yace kina da waya? Islaha Tace Rannan ta Fadi,Tanko ya karkace ya zaro wata karamar wayarsa Tekno Yar Dubu Hudu ya zare Layinsa yace gashi Islaha Sarkin kyau na Baki kyautarta ki sa layinki,Islaha tace bazan karba ba Haka Kawai sai kace Yar Iska,Nifa Malam ba karuwa bace Ni,Baki Tanko Ya bude yace nayi Miki kala da Karuwiii Ni?Dariya Islaha tayi Tace Karuwii wai? Tanko ya nace Sai da Islaha ta karbi waya,yace Kai Me Napep bani aron Biro da takarda,Me Napep ya bashi ya rubutawa Islaha Number dinsa sannan ya sauka dauke da Botikin Alawar madararsa.

A ransa Allah Allah yake yaga Farida ji yake kamar Ana ruru Masa wutar kaunarta a zuciyarsa duk ya rasa dalili sai tunaninta yake ko wanne time,Haka ya karasa Kofar gidansu tare da Bawa Me kanti Ajiyar Alawar Madararsa,Farida ko kwalliya Bata Yi ba ta fito fit sanye da Hijab me Hannu,tana zuwa Tace Algungumi cire Takunkumin face mask da ka saka da wannan munafukin rawanin daga nada Wato Ashe Tanko ne ai Allah ya Toni asirinka,Tanko Ga Kaunar Farida ta Masa yawa gashi an kure shi,Haka ya tsaya sololo Farida ta Gama ci Masa mutunci sannan Tace bani ba Kai,Malam ne ya dawo yaji irin maganganun da Farida take watsawa Tanko,Malam yace ai Baki Isa ba Tanko sai kin aure shi ba abinda zai hanani daura muku Aure ko Zaki mutu Ni Iliyasu Ina kaunarsa yayi min,Malam ya kalli Tanko Yace ka turo Magabatanka,Tanko Yana ta murna da godiya ya kalli Farida ya zaro Mata harshe Wai gwalo sai ya tsaya a Gaban Malam yace Ni talaka ne har ga Allah Tanko ne me aikin su Fuzail,Malam ya washe Baki yace Ni kayi min Tanko karka damu ka turo manyanka.

Tanko Alawar Madarar ya karbo ya mikawa Farida yace gashi a rabawa su Falaqi da su Alhaqatu idan Kuna da su Aliflamin ma ki raba musu su sha yanzu karya ta Kare Tanko Kiri Kiri kina gani shi Zaki aura,Farida ta fashe da kuka tare da yin ball da Botikin Alawar Madara Tace wallahi bana sonka ta shige gida da kuka,Hajiya da gudu ta fito tana lafiya? Farida sai lokacin ta kwashe komai ta sanarwa Hajiya,Hannu Hajiya ta Dora a Kai Tace wayyo na shiga Uku na lalace gashi Malam Dan Haru yayi aiki,Farida ta sake rushewa da kuka tace Hajiya kin cuce Ni kinyi Gaggawa da kika tafi wajen Malam Dan Haru gashi wallahi tsafi yake Yi,Hajiya tace ai shine yasa ma Malam yace sai ya Baki Tanko dole,Yanzu ya zanyi? Farida Tace mu koma a karya asirin me zanci da Tanko.

Wajen Malam Suka koma suna zuwa Farida sai Rusa kuka take Tace Malam kayi min Rai wallahi Dan karya ne ba Mai kudin bane,Tanko ne me gadin gidan Sarki Fuzail,Wallahi Dan karya ne Bawa ne,Shi Kansa Malam Dariya ce ta kwace Masa ya shiga kyakyata Dariya ba ji ba gani,Haushin hakan yasa Hajiya ta daga hannu ta zuba Masa Rankwashi sun Kai biyar da bala'i Tace wallahi idan baka karya ba sai na Kira maka Yan Sanda sun Kamaka na tona maka asiri,Malam yace wallahi bazan karya ba sabo da Ni ba Allah bane da za ace komai Zan gani,Dan haske ne aka haska Mana muke ganin wani abin sauran mu fassara da kanmu,Kuma mu Aljanu ke Mana hidima muma Muna musu,tunda Baki da mutunci da girmana Zaki rankwashe Ni wallahi bazan karya ba,duk abinda zakiyi kiyi,Hajiya ta shiga bashi Hakuri tana wlh saurin Hannu ne dani ko yarana Haka nake dukansu kayi Mana Rai Dan Allah ka karya asirin Nan,Malam Dan Haru yace dama ai duk me Hali irin namu karshemu nadama,Ni dama nasan sai sa'ar gaske Zan tuba,sabo da Haka wallahi bazan karya ba,sai mun hadu a wutar Jahannama Ranar da Shedan zai taramu ya Mana General Assembly ya karanta Mana Wala ta lumuni wa lumu anfusakum,Ma'ana karku zargeni ku zargi kayukanku,ku tashi ku bani waje Malam ya daka musu Tsawa,ba shiri suka fito Farida sai kuka Hajiya tana Bata hakuri.

Malam dagewa Yayi lallai Tanko ya turo,Wanda hakan yasa Hankalin Farida yafi na San Huda tashi,Gaba Daya ta rasa sukuni ta daina komai sai Kuka za a Mata auren dole,ga Tanko ya dage kusan kullum sai yazo zance duk Kuwa da irin wulakancin da take Masa ,Tanko ya fadawa Babarsa ya samu matar aure shi Kam,tsohuwa ta dinga Murna ta samu Yan Uwan Mahaifin Tanko tare da sanar musu suje a Kai kudin aure,Ai Kuwa Dubu dari Suka kawo kudin auren Farida Ranar Farida tayi kuka ta godewa Allah,ta rasa sukuni ta rasa Wanda zata samu ya taimaka Mata,Hajiya duk kokarinta tayi akan Malam Kar ya Amince da Auren Amma Malam yaki yarda,Hakan yasa Farida tayi wanka ta shirya tace Wajen Manal Zan je ta taimaka min ta hadani da mijinta ya sa baki wallahi bana son Tanko gwara ko waye a bani akan na auri Tanko,Yazed Yana ji yayi Dariya yace Amaryar Tanko dama Manal zasu Miki Rana? Fuzail yanzu Baki ji kunya ba zuwa Neman Alfarmarsa? Ko gidan Manal Baki taba zuwa ba sabo da Hassada da bakin ciki yanzu Kuma Zaki tafi sabo da bukatarki?Ko kinje Malam bazai fasa ba sai idan Tanko ne yace ya fasa da kansa.

Farida Bata kula Yazed ba ta dauki Hijab harda sa Hijab sabo da aji tausayinta ta fice tana zuwa gate din farko Sani yace kin daki gurbi sahibin naki ya fita yanzu ya tafi kasuwa zai Fara rage kayan lefenki jiya ma Akwati biyu manya aka siyo suna Nan,Farida ta Harari Sani tare da wucewa ciki,Tunda ta shiga iyakarta gate din farko ba a Bari ta Shiga gate na biyu ba bare ma ta Isa ga Wajen Iyalan sarki,ta Dade a tsaye sai lokacin ta tuna ta Kira Manal,Wayar ma tana Hannun Fuzail Yana Bude Mata Wasu Media,Aunty Farrrrrrr....yaga an sa tana kwance a saman kujerar da yake ta Mike kafafunta a saman cinyoyinsa tana kallo,Wayar ya daga tare da karawa Manal a kunne,Manal ta Mike zumbur Aunty Farida lafiya mutuwa akayi? Tsaki Farida ta ja tare da furta malama Ina gate din farko an hanani shigowa wajen ki,Manal Tace Bawa masu gate waya,suna karba Manal da Iyayi wai Tace Princess Manal ce sai da Fuzail ya kalleta Yana dariya,Me kula da gate na biyu yace wa? Ta sake cewa Mrs Fuzail da masifa,Sai lokacin Dogarin ya fara kirari Yana bada Hakuri,Farida tana kallo tana Ina ma ace nice,Nan take aka Bata izini taje har bangaren Maimartaba Nan ma Sai da Manal tayi magana sannan Farida ta samu ta Shiga,Saude Manal ta turo Direct part dinta aka wuce da Farida,Farida ta Zama wata Yar kwaya,gaba Daya ta chake sabo da kyau da Haduwar da take gani,mamaki ya isheta Wai Manal ce a cikin Nan.

Tana zaune a palon kasa taji takun Manal da sauri ta kalli sama inda taji motsi Fuzail ta gani yasha wankan wani danyen Yard blueblack Kamar zai je party,ya zuba kyau ya Kara kyau,kiba da haske,Manal tana bayansa ya goyota ta matse cikin kana Nan Kaya wani matsiyacin Bumshort fari ,ya kamata Gam ya Mata kyau matuka,sai Yar t-shirt wata maroon,gashinta ya Sha gyara suna zuba kamshi,Farida jikinta sai yayi sanyi gaba Daya sai ta shiga tausayawa kanta,Manal tana wani mahaukacin kamshi tazo tare da Rungume Farida Aunty Farida oyoyo,Farida tayi wani saraaaaa sannan tayi karfin Hali tace ya gida ya Jin dadi? Manal ta koma ta zauna tare da Furta Alhmdllh tana murmushi,Tace ya su Hajiya su Malam,sati biyu kenan har yanzu ban samu na shigo ba makaranta ce tayi zafi,ga Kuma Prince idan nace zanje sai yace na fiye zuwa gida,sannan na Kira Hajiya nayi nayi a kawo min su Falaqi Hutu Taki wlh,Ko kwana biyu da sun min,Farida wani bakin ciki taji da ba ita bace Manal ce a wannan gida,da wannan Mijin nata hadadden gaske.
Chapter 59 · 0% Book details