← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 95

Sashe 77

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha gidansu Yan Izala ne ba Wani party da za ayi Walima zata Yi Kawai,Bangaren Amaryar Ameer Kuwa a can Abuja zasu Yi abinsu a kawo masa Amarya,Manal kullum sai ta Kira Farida akan lallai tazo musu biki ita da Belloti,Yanzu Farida Basu da kunyar kowa tace ai Inshaallah zasu zo har anko tayi na bangaren su Ameer Dana su Islaha.
Belloti mutunci ya kullu sosai tsakaninsa da Alhaji Kasim,gidan Mai har biyu Belloti ke kula Masa da su,gashi Belloti Yana shirye shiryen shiga private University Nan gaba tunda ya duba Waec dinsa tayi kyau,Alhaji Kasim cikin motocinsa ya bawa Belloti kyautar 406 ruwan toka,Ranar Farida sai murna Kamar me,Lokacin Alhaji Kasim ya hada Belloti da danginsa dake Kano yace suje su gaisar da Yayansa Wanda Uwarsu Daya ubansu daya da Alhaji Kasim,Alhaji Al'amin shima me kudi ne sosai Yana da matarsa da yaransa shida Mata hudu maza biyu.

Ranar Saturday ba Aiki da Yamma Farida ta Sha Shadda Wata sea blue me adon Silver,irin kyan da tayi ba a magana,Belloti kuwa Shadda yasha me kyau Silver color,sunyi kyau sun birge Yan gayu a motarsa suka je gidan dake sun San da zuwansu aka sauke su gaskiya gidan ya hadu na masu kudi ne.

Alhaji Al'amin da Alhaji Kasim suna zaune a palon Su Belloti Suka kwashi gaisuwa,Matar Alahji Al'amin ta fito da fara'a cikin shiga ta Alfarma ta zauna Suka gaisa sosai,Yan Aiki Suka cika musu gabansu da Abinci iri iri,Hajiya Karima tace Bari a Kira Yaran ku gaisa ai ya kamata a San juna,Kiran Yaran tayi Suka fito Mazan Yara ne matan ma Basu da girma mace Daya ce Babba zata Kai sa'ar Manal,Belloti da sauri yace Rahila.... dama Nan ne gidanku? Rahila tace ikon Allah Kamar Belloti Dan fillo Wanda kaje bikin Maryam ta maka sharri ko?
Yace nine Mana ai da badan kayi magana ba bazan ganeka ba,Address din da kika bani faduwa yayi wallahi naso na kawo Miki Ziyara Allah baiyi ba.

Lokacin Belloti ya kalli Farida tare da furta Kinga wacce nake Baki labari ta taimakeni a wajen Yan Sanda,Rahila tayi Dariya tana bawa su Abbansu labarin abinda ya faru da Maryam ta Masa sharri,Alhaji Kasim yace wasu matan Basu da hankali wallahi ai gashi Nan Maryam din ko shekara Bata Yi ba ance Mijin ya sake ta tana gida tana Zawarci,Allah ya kyauta Farida ta furta tana karewa Rahila kallo wata kyakyawa da ita me hasken fata amma ba haske can ba,dariya Rahila idan tayi sai ta birgeka sabo da Kyawun murmushinta,gata Yar Duma Duma da ita ba ramammiya ba kuma za ace me kiba can ba.
Farida ta Riga tasan Mijinta Yana Sonta Sai ta saki jiki Suka Fara Yar hira,Rahila ta janyeta zuwa dakinta,Kafin wani lokaci sun Zama kawaye,sai da Yamma zasu tafi Rahila ta kalli Kanin Babansu tace Abba Karami yaushe zamu tafi Nasarawa din mun fa Gama Waec,Ni daga Nan Ghana Zan tafi gaskiya,Farida tace mu jibi zamu tafi can biki idan ta shirya ba sai mu tafi da ita ba,Yawwa shike Nan na huta cewar Alhaji Kasim.

Duk wani Shirin biki an Gama shi Saura kwana biyu biki Belloti ya dora mataimakinsa akan komai na aikinsa sannan Farida,Rahila da Belloti Suka dauki Hanyar Nasarawa,Belloti Yana Driving Farida tana gaba sai murna takeyi zata ga Yan Uwa,Rahila tana Bayan mota suna ta Hira abinsu har Allah ya kaisu lafiya,Rahila gidan Alhaji Kasim ta gwada musu suka sauketa a gidan tace sai munyi waya Farida,Farida tace kizo fa muje bikin Nan dake na Harkar masu Walosi ne,Mene Kuma Walosi? Masu Hannu da shuni Mana,Dariya sukayi Tace sai nazo ta shige gida da katuwar Jakarta.

Belloti gidan Su Farida suka nufa tun kafin suje Farida tace Fara kaini gidan Yayan Hajiya Kawu Sani na fara ganin lafiyar Uwata,Belloti ya kaita Kuwa Farida ta shige gidan da sallama ta Iske Hajiya tana wanke wanke ,Salati Farida ta saki ganin Yanda Hajiya duk kibarta ta rame ta fikale,Farida tausayin mahaifiyarta ya kamata ta fara kuka tana tambaya Hajiya cuka kikayi me ya sameki? Itama Hajiyan Idonta ne ya ciko da kwalla Tace Rayuwa Farida,ya zanyi duniya ta juya min baya,na cuci kaina dama mutum shi yake wa Kansa yace an Masa,Kawunku tunda Suka tafi ko a waya Basu sake nemana ba,idan na kirasu ma basa dagawa,Dan abinda kike tura min shi nake cancanawa ga Matsalar Malam irin wulakancin da yake min,saukinta ma Yazed Yana tallafa min da Yan kudi,Nayi nadama Farida ki yafe min duk Ni na cuceki ban Muku tarbiyya ba,Dan Allah ki bawa Babanku Hakuri ko zai dawo Dani da wuri,na kusa Gama Idda fa,Farida tace Hajiya Nima da kika ganni yanzu ne Allah ya rufa Mana asiri Farida ta kwashe labarin tun tafiyarta da Belloti har zaman Kauye da komai ta fadawa Hajiya.

Hajiya Baki bude tace Sannu Farida Munga Iftila'in rayuwa, mu Muka jawa kanmu sai mu tuba ga Allah karki fadawa kowa zancen Nan bare ayi Mana Dariya,ai bazan fada ba,dama wannan ai sai ayi min dariya cewar Farida,Bari na tafi gidan can,Hajiya tace amma a Nan ma Zaki kwanan mun kafin ku koma ko? Farida tace ae ai Zan zauna ayi bikin su Shukrah tunda tsiransu sati Daya Idan anyi sai na tafi shi dai Ana daura auren Su Tanko Zai tafi sabo da yanayin aikinsa,Allah ya nuna Mana cewar Hajiya,Belloti ya shigo ya gaisa da Hajiya harda Hira Hajiya sai sa Masa Albarka takeyi tana godiya.

Farida ana gobe daurin aure ta tafi gidan Maimartaba wajen Manal,Belloti kuwa Yana cikin abokan Ango su Tanko shi a layin su Tanko yake ba ruwansa,Ranar da Farida tazo kwata kwata Manal ko a waya Bata saurari Fuzail ba,shima baya Nan suna Busy,sai dare ya dawo ya samu Bata bangarensa,Waya ya Mata kina Ina ne? tace kayi baccinka Aunty Farida tazo tare zamu kwana, ban Gane ba ke bana son shirme,Farida tace ke tashi ki tafi wajen mayen mijinki karki jawo min Ni waya dama zanyi da Baby,Manal tace Hirar zumunci mukeyi fa,mu ta kiyayya zamuyi ai ya kashe wayarsa,Sai da yayi Shirin bacci ya kwanta ma ransa na suya jira yake Kawai idan Bata Zo ba gobe ta Gane kurenta sai gata ta shigo,Hijab dinta ta cire kayan baccinta pink Suka bayyana,ya kashe light dama saman bed din ta Haye tare da kwanciya a gabansa ta matsa sosai tare da shigewa jikinsa ta makaleshi Tace gani cinyeni....sai ka sideni ka lashe ni....Yar Uwar mutum tazo baza ayi min afwa ba,ba tare da ya Bude Ido ba ko yayi maganaba yayi guntun murmushi Kawai.

Washe gari daurin auren Tanko ranar Rahila gidan su Farida taje Wanda ta Bata Address tana shiga da Sallama ta Sha wani lace purple and peach ta zuba kyau,Yazed ne kadai a gidan Yana Zaune a saman wata kujera yasha Shadda Yana jiran Malam zasu tafi daurin auren suma Yana latsa wayarsa ya dago ya kalli Rahila zuciyarsa ce ta Buga, Rahila ma Haka ta kalleshi taga Haduwar Dan saurayi sai taji kunya ya Mata wani kwarjini,Kanta ta Sadda kasa Duk ta rasa inda zata sa kanta da kyar tace Farida nake Nema? Yazed uban Yan Isa fuskar Nan tamau yace Bata nan yaci gaba da latsa wayarsa.
Rahila tace ko ta tafi gidan bikin? Yace ae Kawai,Tace Dan Allah inane? Tsaki Yaja yace ki kirata a waya Mana Ni Ina Zan sani,Rahila ta matsa inda yake tace to bani kujerar taka na zauna sai na kirata kafin Nan na sameta a Wayar,Yazed yace Baki da hankali Amma ko? Rahila da shagwaba tace pleaseeeee ........Yazed yaji wani yarrrrrr a jikinsa,Bai kulata ta ba ta jijjiga kujerar ka bani ko na zauna a cinyarka ta tsokane shi da sauri ya Mike ya bar Mata kujerar ganin Yar duniya ce Haka,dakinsa ya koma ya bar Rahila a zaune,Tunda Yazed ya Shiga dakinsa ba Zama yayi ba labewa yayi ya leko ta window Yana kallon Rahila,a ransa yace har saje ne da ita,kalli gashi har Gaban goshi me santsi,Kansa yayiwa fada Ina ruwanka Yazed Wai,komawa yayi ya zauna a saman bed sai ya kasa yaji Bai son daina kallonta ya sake lekowa ta window,a zuciyarsa yace gata da kirji...bakinsa ya rufe da sauri a fili yace nooo...Dan jikinta irin na Manal Dina ce shi yasa na damu da ita,Bari na kalleta sosai sai nacewa Manal Naga me yanayinta yaci gaba da karewa Rahila kallo Bata sani ba,sai da tayi 5mnt sannan Wayar Farida ta Shiga,da sauri ta fice ta bar gidan,Yazed Yana wayyo ta tafi ban Gama ganin ko irin kafafinsu Daya da Manal ba.

A hakan tana tafiya ya Kira Manal,ta daga tace Yayana yace Ni ba gaisuwa nazo ba yanzu me irin yanayin jikinki ta bar gidan Nan,Kuna yanayi Baki ganta ba gashinta ma Yama fi naki baki Kamar me, Hancinta shigen naki,naso ma na gani ko irin kafarku Daya sai ta tafi,Manal tana ta dariya a ranta a fili tace Yaya wajen wa tazo? Farida take Nema gidan bikinku zata Zo Zaki ganta ne,Manal ta kyalkyale da dariya tace wallahi Yaya ka fada,Kauna ce ba Wani me Kama Dani sonta kakeyi Bari tazo na fada Mata Muna ciki wallahi,Bana son hauka Ina wasa Dake Ni Nace Miki Ina sonta ne?Kawai Yaja tsaki tare da kashe wayarsa.....

AsmaBaffa.
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭

DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP

96-100

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne

GIMBIYA DIYAR KATIBI

Manal murmushi yayi kawai,ta Ajiye Wayarta gefe Ana musu makeup,Yan Abuja gaba Daya danginsu suna Nasarawa sabo da Haka sai Suka saukaka Kawai a daura a Nan tare Dana Tanko ba sai anje har Abuja ba,Ango Iliyas Tanko an Sha wanka yayi wani kyau dake baiyi wahalar komai na aure ba sai kiba da yayi ya wani hade gashi dogo sosai,Ya Sha farar Shadda taji Aiki babbar Riga,Ameer Kuwa Water Arsh yasa shima Babbar Riga 11am aka fara daura auren Tanko da Islaha Kan Sadaki dubu saba'in,Maimartaba da Kansa ya daura,Sai Ameer da Amaryarsa Badi'at shima Kan Sadaki dubu Saba'in gaba Daya sarki ne ya biya musu,Algaita da Maroka suna ta fama ana hada hada an kashe pics.
Chapter 77 · 0% Book details