← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 95

Sashe 3

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya a nutse tace Malam ka Dan bani dama nayi ihun murna yace na Baki dama, ta dage tare da kurma Ihu sau Daya sannan ta cukule ta furta Muna jinka Malam, Malam yace kije ki shirya Amma karki Bari damar Nan ta wuce ki,duk abinda yake so kiyi Masa,zaizo da Neman taimako wajenki ki kiyaye,Bazan bada matsala ba Malam ko Mene zanyi,Ku tashi kuje ku jira Nan da wasu satikai,to Malam ba Dan wani dafa'i da za a Bata sabo da mahassada da Kuma wani na farin jini Wanda idan yazo zai Kara sonta? Hajiya ta tambaya,Malam yace akwai Mana Nan take yayi wani Rubutu a Allo ya wanke ya Basu yace gashi idan kun koma gida ta Sha ta shafe jikinta,Wani turare ya Bata wannan Kuma kullum Bayan Sallar Magriba kafin Sallar Isha zata dinga wannan turaren Kar a Bari Isha tazo ba ayi turaren ba,Kuma Kar tayi da ko pant a jikinta sai ta tube zigidir sannan ta tsuguna a Kan Hayakin,Malam ya Kara da cewa Ki turare kirjinki sosai,sannan kasanki ma Haka Malam ya furta Yana murmushi,Dubu Biyar Hajiya ta Ajiye Masa suka fito suna murna Kamar me.

Ko da suka fito daga gidan Malam Farida tana wani yanga a Hanya Hajiya tana zugata tana Mata wani kirarari har suka dawo gida Ana kallon su,Bata Dade da dawowa ba Wani Alhaji Hamisu babban mutum ne Yana da mace Daya da yaransa biyar, zai Kai 47yrs yasa a Kira Masa Farida sabo da Yana mugun sonta da Aure gidajensa biyu ya Gina Yana Burin Kara aure yasa Daya matar a sabon gidansa.

Farida sanye ta fito da English wear Riga da skert Suma na gwanjo ne sunji jiki,Da Gadara ta fito tana yatsina ga Uwar Izza tana ji,Alhaji Hamisu ya kalle ta tare da zuba murmushinsa yasha farar Shadda me kyau Yana kamshi yace tunda ba gaisuwa malama Farida Ina yini? Da kyar ta iya Furta lafiya tana Jin kanta wata princess,Murmushi ya sake Yi yace dama ba Wani Abu ne ya kawo Ni wajenki ba Kuma ba Wasa nazo Yi ba ko yaudara Farida na Dade Ina kaunarki,Kuma da gaske nake Yi aurenki zany.....kafin ya rufe Baki duk shekarunsa Farida babu Bata lokaci tayi tsalle tare da kwashe shi da mahaukacin Marin da yasa Alhaji Hamisu yayi mutuwar tsare tare da dafe kumatunsa.

Da yatsa Farida ta nuna shi cikin zallan bala'i tace baka da hankali? Kana hauka ne? Kasan Kuwa matar waye Ni? Idan baka sani ba ka sani da princess kake magana,Ni nafi karfin talaka irinka,Nawa ka Tara just Dan kana da Ordinary two Houses kana da one old car har ka Isa na aureka,ka kalleni unique color,real Chocolate cute girl like me kalleka Wanda ka kusa fara Tara katon tumbi ka kusa mutuwa lokacinka ya kare,kamarka kamata yayi ka tare a masallaci fadar ma'aiki ka Mika lamuranka ga Allah amma look at your fucking stupid life kana so na Ni kamata,Ni Farida nafi karfin kowa a garin Nan babu sa'an aure na a garin Nan ka hau Bishiya kasa speaker ka sanar Farida sai Birnin Tarayya Abuja Near National Assembly ko Opposite Villa House,idan ba Nan ba na tabbata my Charming Prince to Lagos zai zaba can kusa da gidan Wizkid ko Davido,Ko Kuma nayi makwaftaka da Naira merly ko Burna Boy Muna tare Ni da arna Amana ce,Duk wata Kuma Muna London,Paris, Turkysh etc Ni da turawa Amana ce,Sabo da Haka ka ja jikinka ka bar Mana Kofar gida ko wallahi nayi maka Atile da kasa,je kaja wannan gongonin da kake Kira da mota ka bar Mana gida Idiotic idiot ta juya ta shige gida abinta,Alhaji Hamisu ya rike Baki Yana maimata Idiotic idiot tab.

Tana komawa ta hau bawa Mahaifiyarta labarin irin duk abinda tayiwa Alhaji Hamisu suna ta dariya har da tafawa ita da Hajiya tana cewa kin min dai dai ai babu sa'an aurenki a Nasarawa state kaf gaba Daya,Shi Kuwa Alhaji Hamisu yau tunda Uwarsa ta kawo shi duniya Bai taba bacin Rai irin wannan ba,ya rasa mahaifiyarsa da Mahaifinsa Amma Bai taba Jin bacin Rai irin wannan ba,Kansa ya daga sama Idonsa yayi jajir ya furta abinda Yarinyar Nan tayi min Allah ka gani Allah ka saka min Yaja motarsa ya Kara gaba.
Bayan Kwana Uku tsakani Farida kaf unguwarsu an San yanda ta sake canjawa wajen yanga da iyayi sannan Bata kula kowa duk Kawayenta ta daina kulasu sai Guda Daya Rumasa'u,sabo da Ruma tare Suka taso da Farida Amma Ruma ita mutuniyar kirki ce tana da tarbiyya Kuma daidai gwargwado tana bawa Farida shawara sai dai Farida Bata dauka,Dan ma ba yanda zata Yi ne sun Shaku da Ruma Amma da tuni ta daina kula Ruma,Kuma Ruma ita Iyayenta suna da rufin asiri sosai ba karamin taimakawa Farida takeyi ba da kudi da kwancen sutura harda kayan abinci Mahaifin Ruma Yana Aiko musu musamman azumi da sauran Lokuta,haka zakka ma Yana Basu shi yasa ba yanda zata Yi da Ruma.

Yau da Yamma sun dawo daga Islamiyya ita da Ruma suna tafiya a hankali Farida tana ta yanga tana karairaya,Farida Allah ya Bata farin jini ba Wani kyau ne da ita ba Amma tana da masifar farin jini daga Allah,baka ce Amma tana siyen Mai me kyau shi yasa ta dole ta koma chocolate Kuma Dake ta iya shafa man Kuma me tsada ita da Hajiyanta suke take Tara kudi a siyawa Farida sabo da zata Zama matar Dan sarki kwana Nan ya kamata ta Kara kyau sosai,ai Kuwa Farida tunda ta Kara haske da kyau farin jininta ya karu,tauraruwarta tana haskawa tana Kan sharafinta.

Suna tafiya wasu matasa Yan gayu baza su wuce 27yrs ba Suka tare su Ruma,dama sun Dade suna son su furta musu suna son su,Daya Usman Yana son Farida Daya Kuma Abdulhakeem Yana son Ruma,wata Uwar Harara Farida ta balla musu tare da Jan Tsaki,tsayawa tayi tana kallonsu tana yatsina,Cikin karfin Hali Usman yace Malama ya sunanki Dan Allah ya furta Yana kallon Farida,Fari Farrrrrrrrrrrrr Farida tayi da idanu tana juyasu yanda taga Dama sannan tayi Dan tafi Tace Kara da DA,duk Basu Gane me take nufi ba,Suka ce me kike nufi Munga kinyi Fari da idanuwa kince mu Kara da DA me kenan,Ya sunan abinda nayi da idanuna? Abdulhakeem yace Fari Mana to idan ka hada da DA me kenan? Suka tuntsire da dariya Usman yace FARIDA kenan ko? Farida ba mutunci ta wani Bata Rai Tace Yeah sai akayi Yaya? Nan Usman ya furta abinda ke ransa Yana son Farida,Dariya Farida ta dinga kyalkyalawa ta maida su mahaukata karshe ta kalle su shekeke tace kunga nayi Kama da matar Yara irinku? Yan chatting ba Uwar da kuka sani sai Chatting da waya sabo da Rashin aikinyi talakawa,Baku da ko sisi sai son kula Mata ku batawa Yar mutane lokaci,ku lalata Yar wani,me kuka iya irinku in Banda kunzo zance ku laguda Yar mutane,jikina jikin prince ne,da Princess kuke magana,Hannun talauci baya taba jikin Farida.

Baka da kudin da zaka iya aure na bare ka dauki nauyi na,iya body lotion Dina kadai kudin cefanen gidanku ne na sati biyu,Ido ta zarowa Usman tace karka sake Ina tafiya a Hanya ka sake tareni wallahi wallahi sai na kunyataka Watarana,sai na tozartaka a idon al'umma,Ni ba class dinku bace,in Banda Kun rainani ma Kuna yawo a kafa ko keke Baku da shi har Kuna iya tare mace a zamanin Nan? Wannan ai karambani ne in ba Haka ba Ina ku Ina fara Neman aure dalla ku tafi kuci gaba da karatu ku nemi kudi,yanzu Abinda ya kamace ku kenan kuyi karatu ku nemi kudi matasa irinku sabo da tsaurin Ido ku kalleni ku tareni ga Ruma nan maybe ita zata iya da ku Ni Bari nayi Nan,Farida ta tafiyarta tana yanga da Izza tana tuna hadadden prince dinta na mafarkinta,Ruma Hakuri ta dinga Basu,Usman yace kyaleta ba komai Rayuwa ce gata ga duniyar Nan,Ruma ta tsaya ta saurare su ta Basu Address din gidansu sabo da taga suna da nutsuwa ba laifi.

Bayan Kwana Daya tsakani Farida ta siyo salat da kayan Miya Amma sabo da tana Jin kanta ita fa matar Dan sarki ce sai Almajiri ta samu ta bashi naira Ishirin ya daukar Mata Yan kayan miyar a Yar Leda baka Yana binta a baya da shi Yana take Mata baya,tana hanyar komawa tana yanga da Izzarta wani matashi da gani kasan Dan Tasha ne zai Kai 33yrs ya tare Farida da gani yayi shaye shaye sosai,Yace ke ya Ana Miki magana kina share mutane? Yana ciccije Baki yace Naga kina wani Izza ne ko kece Izzatu ai Kya salalawa ranki har Ana Miki magana kina wani Shan kamshi kamar Kinga Kashi na rantse da Allah sai na mammake ki,Dan ma anganki Ana so shine Zaki Raina min hankali Dan Kan Uwarki,Farida babu ko tsoro sabo da karfin gwiwar prince dinta fa ya kusa zuwa ma ya dauketa gaba Daya Tace Kai dalla Rufewa mutane baki,idan kana Jin Kai Dan Tasha ne to wallahi Ni nafi karfinka,Kai ai baka cika Dan Iska ba tunda har yanzu idan dare yayi gidan uwarka kake kwana,idan dare yayi a bayan uwarka kake kwana duk dare baka kwana a bariki ai Kuwa baka je ko Ina a Iskanci ba tunda har dare zaiyi ka koma gida wajen Iyayenka,da Abu ya faru sai gida zaka koma ai Kai banza ne,a Yan Tashan ma baka ma San Yan kwaya ba kai ko kashin kadangare kake Sha Haka zaka ganni ka kyaleni Ni ba kalarka bace Kuma wallahi ka tabani idan har Prince yazo sai an kulleka an jefa mukullin a katon teku,Kai da Fitowa har abada,Shi dai Dan kwaya ma Dariya Kawai ta bashi da tunaninsa me hankali ce Amma yanzu ya gano Sam Bata da hankali ma ko kadan Bai ma dace a saurareta ba Kawai ya juya zai tafi sai Farida taja Tsaki,ai Kuwa ya juyo a fusace ya dinga kwada Mata Mari Kamar Allah ya Aiko shi sai da ya kumbura Mata kumatu duka biyun,Yace Dan Uwarki wallahi sai na kashe ki na kashe banza,ba irinmu akeyiwa Haka ba,sai na bar Miki tarihi yau.
Chapter 3 · 0% Book details