Sashe 13
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
A Haka Matan sarki da Yan Uwan Fuzail sai tallan mata suke kawowa Fuzail amma Sam Bai zaba ba yace duk Basu Yi ba,har an gaji an kyale shi,Yau Sarki ya matsa Masa sai yaje ya zauna a fada yaga yanda ake mulki,kayan sarauta aka sashi ya saka Dole yaje,Yana zuwa ya Iske masu busa Algaita suna ta busawa sarki sabo da Dole ne kullum sai anyi ta a Gaban sarki da safe,ai Kuwa Fuzail yaji kida yaki karewa gashi Yana tausayawa masu Algaita yanda suke kunburo kumatunsu,tun Yana kallo Yana danne zuciyarsa har ya kasa ya daka musu Tsawa tare da mikewa tsaye Yana masifa a Fadar yace Wai sai Kun cire kumatunku? Nawa za a baku please ku bari Nan,ba ruwansa ya kunyata Sarki a Gaban manyan masu sarauta,Ba shiri Me matarba yace yaje inda zai je ba sai ya zauna ya ga wani yanda ake mulki ba.
Kuma shi Fuzail ba ruwansa da wasu Fadawa Bayi da kuyangi duk Fadawan Nan maza Hannu yake mika musu suna gaisawa,matan Kuma Hannu yake daga musu,an Masa fada yace shi bazai iya ba Ana gaisar da shi Yana share mutane sannan musulunci yace ayi musabiha da Sallama Dole aka barshi Nan ma.
Akwai abokinsa Guda Daya Dan gidan Kanin Mai martaba Kuma wazirin sarki Ameer,Ameer Dan Waziri ne tare Kuma sukayi University da Fuzail sabo da Haka a Nan Baida Abokin da ya wuce Ameer,Shima Ameer Yana da sarauta,shi Kuwa Fuzail yace Bai so shi Business man ne ko a can Yana da Company shi Karan Kansa me kudi ne Bai dogara da kudin Iyayensa ba,akwai shi da son Neman na kansa tun Yana yaro Hajiya Ayusha Umminsa ta dorashi a Harkar Business dinta har ya girma Kuma ta bashi jari me yawan gaske Haka Sarki ya Kara Masa shine yake Harkoki da dama na Business masu kawo kudi,Yana da shares a wani katafaren Mall Dake Korea Republic,sannan Yana da shares a wani Company na kera motoci,Haka Yana shares a hukumar kwallon kafa ta wani team dake Brazil,ko ta Ina kudi shigo Masa sukeyi dama sai da kudi ake Neman kudi,sai kaga Kamar baya neman kudi Kuma a Haka millionaire ne na gaske duk yafi Yaran Sarki kudi sosai sabo da a waje akwai Harkoki na samun kudi idan kana da jari.
Ameer ne zaune a palon Fuzail,Cikin Harshen turanci Fuzail yace Ina son Inga rayuwar talakawa,tunda na taso rayuwa kala daya nayi ta masu kudi,ban San Daya bangaren talakawa me suke ciki ba,Ina so Naga irin rayuwarsu,Ameer yace ya kamata Kuwa amma Kai Mene damuwarka Allah ya baka kudi Ina ruwanka da su,idan taimako zakayi kayi Kawai amma ta ya zaka ga wani rayuwarsu.
Na fa tambayi Me martaba zanyi tafiya nace Masa Zan je yawon Bude Ido a Nan Nigeria Zan Shiga kauyuka zanyi Kamar 1 to 2 weeks sannan yace indai ba tare da Kai zamu tafi ba bazai barni ba,Amma Indai dakai zanje ya Amince ko gobe zamu iya tafiya.
Dariya Ameer ya dinga Yi yace Shikenan Prince ban Isa na kasa bin umarninka ba yaushe zamu tafi? Fuzail yace gobe amma fa kasan baza muje a Haka ba,ka samo Mana kayan talakawa mu saka sannan Ni gaskiya sai na canja ma fuskata Zan saka hular gashi ta maza me uban yawa sannan na Kara da gemun karya kaga idan mun Shiga mutane babu me ganewa su waye ko ya kace? sannan Suma talakawan baza su gujemu ba tunda munyi iri Daya da su cewar Ameer tafawa Suka yi suna ta shirye shiryensu.
Washe gari da zasu Yi tafiyar cikin shigarsu ta Alfarma sukayi Sallama da kowa Suka fita,suna barin gidan Sarki Wani Guess House Suka shiga me kyau anan Ameer ya saka wani dogon wando jean Wanda yaronsa ya tura layin Yan gwanjo ya siyo musu kayan aka wanke su tas,Ameer Dogon wando ya saka jean black duk ya Dan kode da ka gani kasan na talaka ne,t-shirt dinsa wata Grey me karamin Hannu shi Bai rufe Fuskarsa ba.
Fuzail Kuwa Wandonsa blue jean ne 3qutr da t-shirt me dogon Hannu wata me zanen layi layi red and Black,Wani hular gashi me uban yawa na maza ya saka a Kansa sai kace a Kansa aka halicceta,babu Wanda zai Gane sawa yayi yayi wani kyau abinka da me kyau,Gemu dogo ya Kara a kasan nasa da saje duk Fuskarsa ta Kara Rufewa da gashi duk Wanda yasan Fuzail to ba shakka bazai taba Gane shi ba duk da yayi kyau,skin dinsa ce Kawai ta nuna Hutu,suna kallon kansu a mudubi suna ta dariya,Ameer wankan Tarwada ne shi,Bai Kai Fuzail tsayi ba amma shima ba baya ba ya hadu.
Fitowa sukayi Suka jawo wani tsohon machine da Ameer ya siyo a wajen wani bakaniken machine,Dariya ce ta kamasu Suka dinga yiwa kansu Dariya Musamman Fuzail Bai taba Dariya ba irin ta yau ba Ameer har mamakinsa yakeyi yanda yake nishadi,Ameer ne zai tuka machine din Fuzail ya hau bayansa Yana dariya ya daki kafadar Ameer yace let's go man.
Ameer Yaja machine cike da kwarewa,Fuzail Cikin turancinsa yace a fara zuwa unguwannin Talakawa sai mu shiga kauyuka baza mu koma gida ba har Jigawa state sai munje,Ameer yaci gaba da tafiya Yana bin unguwannin Talakawa na garin suna kallo wani abin ya Basu tsusayi wani ya Basu Dariya da sha'awa,Wani abin ya Basu haushi,Har Yamma suna yawo gaba Daya yunwa ta kamasu,lokacin Kuma Farida taci Uwar kwalliya cikin wani lace dinta Dan dubu goma fari tas ta tafi gidan Sarki yau ta rantse sai taga masoyinta Fuzail.
Tana tafiya a layinsu tana yanga,Manal Kuwa tana gida yau ma tayi Awara da yawa gashi ba Wanda yazo ya Siya har Yamma tayi ganin zata sake tafka asara sai Kawai tayi wanka ta Sanya doguwar rigar atamfarta Leda wata maroon and milk tayi kyau dake me kyau ce Manal fara tas ga kyan sura ko Bata Yi kwalliya ba kyau takeyi,gashi Yazed da Malam Basa Nan ya tafi kauyen su Malam za ayiwa Malam maganin Hausa ko za a dace sai sun kwashe sati biyu kafin su dawo.
Dole ta dauki katon botikinta na Awara ta fito da Niyyar ta zaga ko zata samu masu siye,tana tafiya a layinsu Kamar zata Yi kuka ba mutane ko mutum Daya a layin Kamar ba kowa a layin nasu Haka take tafiya ita daya.
Farida Kuwa juyowa tayi ta hango Manal da bokitin Awara ta dinga dariya ko kallon hanya Bata Yi tana faman yiwa Manal Dariya,Kawai Su Fuzail Suka yanko kwana sai ganin mace sukayi a gabansu,Fuzail ya saki Kara,Ameer ya firgita garin zai kaucewa Farida Kawai ya daki jikin katanga da machine din Suka Fadi gaba daya,Farida tsorata Kawai tasa ta Fadi a kasa Amma ba abinda ya sameta ta Mike da sauri tana Tsaki tana goge jikinta tsayawa tayi akan Su Fuzail Wanda basa ma Hayyacinsu Amma ta dinga zunduma musu ashar ta uwa ta uba,tana shegu matsiyata talakawan banza,Kun jawo min yanzu sai na koma gida na canja kaya sannan zanje ganin masoyi na.
Allah ya Isa tsinanannu talakawa matsiyatan banza Yan Iska Shegu,Juyawa tayi zata koma gida ta kalli Ameer Ido cikin Ido Tace sai kunci Uwarku yayan mayu ta tafi abinta,Fuzail Yana numfashi sama sama yace kaga wannan Bata taimakemu ba sai fada takeyi,Kamar naji zagi take Yi? Ameer yace ban taba ganin marar tarbiyya irin wannan ba kaji Kuwa zagin da take Mana,Fuzail yace na Gane ai,yau Fuzail ya koyi zagi da hausa a wajen Farida Kamar karatu ya rike a Kansa dama Bai iya Zagi ba, sosai duk zagin data musu ya koya,Ya kalli Ameer yace Matsiyata let's go,kasa tashi sukayi sunji rauni,Manal ta hango abinda ya faru tana nesa sosai Amma Haka ta shararo da uban gudu Kamar zata tashi sama,Botikin awarar ma gaba Daya sakinsa tayi ya tarwatse a wajen tana karasowa wajen su Fuzail ta daura hannaye a Kai ta fara yaren fulatanci itama Hausar Bata ishetaba, karshe tace Hodijam taga Ameer yafi Jin ciwo sai Kawai ta tafi zata cakume shi Fuzail yasa hannunsa da kyar ya ture ta gefe,Manal tunaninta zallan bahaushe ne taga yaki magana tayi zaton rauni ne yai rauni tace Sannu bawan Allah Sannu kaji me tubu tubun gashi Allah gashinka kamar dakin Girkin Annatuna Allah sai an maka Aski sai kace dakin bukkar rigar mu,Bawan Allah idan kayi Aski ai sai kaji dadin kanka.
Me Napep ta tare da sauri ya fito Kuwa ya taimaka Mata aka saka su a ciki ta tafi da su asibiti,ta manta ma Bata da ko sisi.
Amma Haka tasa aka kaisu asubitin Gomnati, Likita Yana dubasu yace babu matsala Yar buguwa ce Amma Ameer sai ya zauna a Hospital na sati Daya shi Kuma Fuzail yau za a sallame shi,Manal Tace Alhmdllh dama Bata da kudin da zata biya,ta rasa yanda zata Yi gashi an Rubuta allaura da magani,Suna kwance a gadon asibiti ta kallesu duk bacci sukeyi ta fita da gudu,Fuzail shi ba bacci yakeyi ba yaga Sanda ta fita a baya ya bita a hankali har wajen Asibitin ya hangota tana bara Manal tana a taimaka min bayin Allah ga Kati marasa lafiya ne Dani Bamu da halin daukan nauyinsu,Haka yaga tana bin mutane tana bin duk wata mota da tayi parking,mamaki ya kashe Fuzail dama akwai mutane irin Haka tayi bara Dan ta taimaki wani,to me yasa ma ta nace sai ta taimake su,Wani me kudi ne ya karbi katin Guda biyu a Hannunta Yana kallo Suka tafi Chemist na Asibitin aka siyo Mata magungunan,Fuzail Kuwa ya koma ya nannade a Gadonsa,sai gata ta dawo da sauri tana murna Tace Alhmdllh na samo kudin maganin gashi an siyo komai har kudin cin abinci ya bamu Allah ya biya,.