← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 95

Sashe 33

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sukayi yace karki damu my Manal,Kallonta ya shiga Yi tayi ta Masa kyau a lace din maroon Wanda shima cikin kayan Shukrah ne,Fitted gown aka Mata tayi zam zam tare da yafa Dan mayafinta,Gemunsa ya shafa da Sajensa Yana kallonta kamar maye wani nishadi yake ji,Manal Fuska ta shagwabe Masa tace Kamar fa kallo na kake Yi Ni Allah kunya kake bani,kyawawan idanuwansa ya lumshe Manal tayi awon gaba da Imaninsa da wannan shagwabar tata,Manal din tasa ta fara chasa gayu itama,Kunya tasa ta Mike daga saman Tabarmar Tace bari na kawo maka ruwa ta fara cat walk dinta dagwas-dagwas,Fuzail yace Uhm kaga tafiya me kyau ya fara Irga Mata Yana cewa Left-Right....left-Right,juyowa Manal tayi tana Dariya da wata matsananciyar kunya ta shige gida da gudu abinta.
Ruwa da lemo ta kawo Masa tare da Zama a gefensa da mificinta suna Hira tana Masa fifita sabo da yanda yake Jada jufa abinka da sabo da ac.

Fuzail ya Kira ta da Yan matana? Tace Na'am Dan samarina tana gyara pink lips dinta Kamar wata me tsotsar Alawa,lips din ya kurawa Ido tare da furta na hango shi cikin Nawa Malam ba'a magana,Manal ta fara Dariya Tace Allah ka manta surukinka ne fa Malam din shine ka Kira sunansa wannan ai cin mutunci ne,shi sai yanzu ma ya tuna a ransa yace Kai Manal da yarinta take sai kace sunansa na gaskiya ya fada,a fili yace ai ba Malam namu nake nufi ba,ayyoooo na gane tace tana kokarin Bude Masa ruwan amma sai ta kasa sai shine yace kawo marar karfi ya bude da Kansa.

Farida ta saka jaraba a ranta na tunanin Fuzail zaiyi aure sai ramewa takeyi tana karmashewa,Biki Yana matsowa Saura kwana biyu biki Annatu tazo da sauran Yan uwanta Mata da maza lokacin Saura kadan a Gama Gina gidan Malam,kowa ya kalli gidan dagwas sai yayi sha'awa ya sha tiles ko ina,Hajiya tunda Baki Suka Fara sauka take ta Fushi tana bakin ciki,Bata da Aiki sai habaici da takewa su Annatu.

Su Annatu da kayan abincinsu da komai na abinci Suka zo sabo da sun San halin Hajiya,ai Kuwa ko cokalinta Suka dauka sai tayi zage zage a gidan,wani yaro tsautsayi yasa ya shiga toilet din Hajiya sabuwa taji Tiles tare da fatattaka zawo a kasa,Hajiya Katsam ta ganshi gashi Yaron Kauye cikinsa katon gaske,Hajiya Takaici yasa ta finciki hannunsa Kamar ta dauki tsinke ta hantsila Kansa kasa tayi Masa butar Malam tare da zaro tsintsiyar kwakwa ta Zane Masa gadon baya,yaro jikinsa duk Kashi Yana tsala ihu,Uwarsa Yar Fulani ta fito da gudu tana gwarancin hausarta Minena(Mene ne) Hajiya? Hajiya Tace Uwarki ce Minena Shegun yaranku ciki duk tuwo sunzo suna Bata Mana gida,aikin banza anyi Mana sabon gida za a Bata Mana akan bikin banza bikin wofi sai kace wacce zata auri Dan Gomn, Annatu ce tazo Tace Harira muje ki kyaleta Mene duniya Hajiya,Biki na lokaci daya wallahi Kowa yayi Fushi da bako zaiji kunya.

Hajiya lebenta na sama Yana tashi tace Indai kunyar bako irinku ne Allah ya sawwake min Yan Iska arnan daji,wa zai kalleku yace mutanene ku aikin banza kafa duk kaushi,Annatu tace Li'ilafi kurayshin aniyarki ta biki Suka juya Suka tafi dakin da Manal take.
Hajiya danginta ko Daya Bata gayyata ba,Yazed duk wani cefane na abinci yayi Wanda Baki zasu ci su Sha.
Manal sai murna takeyi taga su Annatu da su Khairan,harda Kiran Fuzail lallai yazo yaga Yan biyu kannenta Bata San har kauyen yaje ba wajen Anna,Haka yazo Suka gaisa da Dangi daban daban.

Gidan Sarki Kuwa ba Wanda ke murnar auren,Kowa ya shiga harkarsa,Hassan da Hussain ne Kawai ke kula abin su dai suna son Manal Haka duk da Basu taba ganinta ba,auren a katafaren masallacin idi na unguwar su Manal za a daura,tunda Memartaba yaji Sunan Unguwar su Manal yasan sai mutum ya shahara a Talauci yake Zama a Unguwar, Takaici ne ya Kama shi Yace Uhm uhm hum, Ko a radio Maimartaba Bai bada sanarwa ba,Ranar auren ranar Mai martaba ya sanarwa Ummin Fuzail,Fuzail yasan zata Neme shi sai ya sa wayoyinsa a flymode gaba Daya,Yau wankan na daban ne.

Gidan Su Manal kuwa Yan Fulani sai hada Hadar girki akeyi ana shewa da Murna,Hajiya da Farida sai kunci suke yi,Hajiya ganin irin uban Naman da aka kawo za ayi Miya da shi ai Kurar sai ta shige cikin Yan girki tana tayasu sabo da ta samu dama ta saci Nama ta Kai dakinta,Sai shishigi take musu,Kuma Tace lallai sai abinda Tace shi za ayi a girkin,Hajiya tana juya Miya da ludayi ta dandana Tace ba curry Ina Uwar 'ya a bayar da kudi a sa Mana Curry zata fi shiga, Annatu ta bayar da kudi aka siyo,Dan mugunta ta sake cewa an saka Mr Chef Kuwa? Annatu Tace Mene Haka Kuma? Hajiya tana goge Gumi Tace Kauye Bata Yi ba wallahi Maggi ne shima,Annatu ta sake bada kudi dubu Daya,Hajiya Tace Saura Onga da Curry me tafarnuwa,Annatu Tace ya Isa Haka Hajiya asha miyar Nan Tasono Kawai Kawai na gaji.

Hajiya Tace ban Gane a shata Tasono ba? Anna Tace ai Haka ake cewa idan Miya Bata ji Hadi ba ko ba nama a ciki sai ace ayi ta Tasono,Hajiya tace magana sai Kauye Yan Kauye anji jiki, burunku tuwo ko? ku dai aci tuwo Kawai mashaallah Amma tasono ai mahadin majina ne a Hanci ku komai sai Kun hada da kazanta,Harira Hajiya tayiwa Habaici tace shi yasa Muka ga gidanku ga shi Nan fes da shi ko Ina Kal,Karki zageni dai,Baza kizo har gidana ki fada min magana ba,Shuru suka mata duk ta hanasu sakewa.

Fuzail da Ameer sun fita iya fita,Ango yasha Farar Shadda me tsadar gaske,da wata hula ta musamman Kalar dinkin babbar rigar, takalmi,Wayar ma fara,Haka motarsa ma,kowa ya kalli Fuzail bazai so ya dauke Idonsa ba, har Maimartaba kallon Dan Nasa yakeyi kawai yanda yayi kyau sai nishadi yake Yi,duk danginsa sun Sha wankan ganske,Ameer kuwa Shaddarsa silver ya saka shima da babbar Riga da hula sun wani cokota gaba yanda matasa Yan gayu ke Yi, Manal kuwa musamman aka kawo Mata kayan da zata saka kala biyar masu tsadar masifa,Mamaki takeyi a Ina ya samu kudin,Haka Shukrah ta zabar Mata Lace fari and Golden,wurin make Suka je aka tsara Amarya,ciwonta ya kusa warkewa dama,dauri aka tsara Mata da Golden Head sannan Suka dawo gida,Farida ma sunyi dinkuna sosai duk sunsha gayu Amma Bata da sukuni sabo da bakin cikin Manal data ga Angon ya kawo mata Kaya masu tsada,Shukrah Tace Saura Lefe bayan daurin aure za a kawo shi, musamman takalma da jakankuna da mayafai kyau da tsadarsu ya Isa,ga Kuma yau Fuzail din nata shima ance zai angwance.

Suna zaune Speaker din Farida na tashi su Masatura sun kunna da kawayensu sai rawa suke Tika,Su Falaqi da abokansa Suka shigo da gudu gida suna cewa Wallahi an daura Sadaki million Daya da mota sabuwa,Manal ta dinga dariya tare da furta mahaukata ku wuce a wanke muku rigunanku Kun lalata su da Miya,Sa'iha ce itama da kwalliyarta ta gaske ba karya sunyi kyau Tace wallahi sarakuna ne a wajen na rantse Aunty Manal,Sadaki Million Daya da mota,Hajiya kirji ta dafe tace bana son karya,wallahi Allah da gaske cewar Alhaqatu data shigo har wajen Muka je,Muka ji Ana sanarwa an daura auren Manal Rabiu da Fuzail,Farida Tace Fuuu me? Fuzail, Farooq ake cewa Yan Mata Manal ta Furta.

Taron daurin aurem Ana ta yiwa Fuzail Murna,Duk Yan Uwan Fuzail tuni sun watse sai Hassan da Hussain da Ameer tare da wasu abokan Ameer na jiki su Biyar da su aka tafi gidan Amarya.
Fuzail ya kalli Ameer yace to yanzu duk abinda za ayi sai ayi,Dariya sukayi,Ameer yace yau fa Dole a nunawa Su Farida zahiri,Sured cewar Fuzail,Motoci na gagara sunfi goma Sha biyar harda jiniya Securities sojoji da Dogarai a saman dawakai Kamar ana hawan sarki suna take musu baya,Jin Jiniya motoci suna ta tsayawa a Kofar gidan ai Farida da Hajiya sun Riga kowa fitowa Sannan auran Yan biki har Shukrah a Amarya Wanda sun Sha gayu,Dogarai suke faman Kirari suna Wasa Fuzail ana Masa Algaita ka rantse shine Sarkin,Manal, Hajiya,Farida,Shukrah da sauran mutane makwafta Yan Uwa da abokan arziki duk suna wajen an cika makil Ana kallon kudi,Fuzail aka Budewa murfin motar da yake ciki rantsatsiya,Wata Sanda Fara tas kwagirin kudi Wato Sandar girma kenan ita ya fara zurowa waje sannan kafafunsa masu dauke da takalmin sarauta na ubansu,Fitowa yayi Kamar daga inji aka fito da shi,yasha uban kyau,Binsa akayi da kallo yuuuuuuu,Ameer Yana Fitowa Manal ta Bude Baki ta Zama gunki,Farida Kuwa Hannunta na rawa ta duba hotunan Fuzail da suke Wayarta ta tabbatar shine ai Hajiya ce ta fara rike katanga Gam sabo da Kar ta Fadi,ita Kuma Farida ta kankame Hajiya Hawaye ya fara zariya a Idonta,Manal ita taga ya Mata Kama da Farooq Amma Bata Gane shi ba,Gabanta ya tako da Gadara Yana Izza yace afwan My wife,Sunana Prince Fuzail Usman Manu Lamido,Bako Wanda yazo gidanku kuka sanshi da Farooq Kuma angonki a yanzu,Karki damu duk abinda nayi banyi Dan wata manufa ba sai don Alkhairi da so da kauna,Manal tayi mutuwar tsaye Hassan da Hussain Sai gulma sukeyi Auntynsu me kyau ce,Jan Hannun Manal yayi Kawai Suka tsaya a gefe ta kasa magana,shi Kuwa Ameer ya musu pics kala kala har su Hussain tare da Amarya Bata magana sai yanda akayi da ita.

Suna gamawa suka shiga motocinsu zasu tafi kenan Farida ta sulale kasa Sumammiya su Kuwa Suka ja motoci suka Kara gaba Basu San dalilin sumanta ba,Hajiya ta rude tana a Miko ruwa,Shukrah itama ba bakin magana Haka taja Manal ciki,Anna Dariya tayi Kawai tayi tana murna,Yazed da Malam ko a jikinsu Abin ya Bawa Manal mamaki,Manal tana yin magana Tace ai Kuwa bazan so wannan ba Ni waccen Farooq Dina nake so wallahi kuka ta saki tana wallahi baza a kaini gidansa ba,sai Kuma ta tuna wani Abu ta goge hawayenta Suka Yi ciki.
Chapter 33 · 0% Book details