← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 95

Sashe 10

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai rabu Dani da Bokon Nan marar amfani Yaya gwara sana'a,naji tashi ki fita tunda ke ba a Hirar Ilimi da ke,Yo Yaya Allah na tuba Ilimi ba kudi ba ko sisi da me za a ji,fita tayi tana Dariya shi dai Yazed a duniya ayi karatu, Bayan Kwana biyu sai ga Yazed ya siyo Mata Gyada,Manal ta dinga Murna su Farida sai kyalkyala Mata Dariya sukeyi,Farida tana faman kwalliya tana kallon Mudubi tare da Furta Hajiya Body Lotion din Nan Yana Aiki Kinga yanda nake Glowing Dole na birge Fuzail,Hajiya rangada shewa tayi tare da Furta ai Malam Dan Haru yace Saura kwanaki kadan yazo Nan gidan,Ihun Murna Farida keyi tare da Kannenta Sa'iha da Masatura,Alhaqatu,Falaqi Kuwa Yana Jin Dadi yace Aunty nasan ma a London zanyi First Degree na ko? Farida tace tab sosai ma ai dama Falaqi Kai kana London,Masatura Kuma tana Dubai,Sa'iha tana Russia abinta Sai Alhaqatu ita a can Madagascar zata Yi nata.

Manal tana jinsu ta kasa daurewa Tace Amma Dan girman Allah Dan Allah Sa'iha Kinga ance Rasha Basu da tarbiya Dan Allah Banda Shan giya da wiwi,Idan kika ga Barasa to kiyi arewa ita tayi kudu,ba ruwanki da shaye shaye kinji Sa'iha,Farida tana fari da Ido Tace woo Ni Ina ta yin sunan Nawa fari kana Kara DA ya koma FARIDA,ya kike da suna ma Manal ko?Hajiya Manal ki fito fili kice kina maula ko Chadi ko Cameroon a kaiki kema,Dariya Manal tayi tace ai wallahi gwara ki barni a Nigeria yafiye min Wata Chadi,Hajiya Tace to munafuka da kika samu ma za a kaiki banza Yar Kauye har abada baza ki waye ba,kalli kayan jikinki ko kunya bakya ji uban waye zai ganki a Haka ya so ki banza akuya,Manal taji haushi tace naji dama ai Ni bance a so ni Dan kyau ko Dan wani abin jikina ba.

Wata Dariya Suka kwashewa Manal da ita Hajiya tace Manal kike suna ko Dadi babu Dan Iyayin Yayanki harda wani canja Miki suna akan yaga na canjawa Farida shine kema ya canja Miki ai wallahi gwara sunanki na asali Waqi'a yafi Dadi ma Amma Mene wani Manal,tun daga Jin sunanki saurayinki zai gudu,Farida tana Dariya Tace Kuma Hajiya Wai Bata so a so ta Dan kyau wani Abu na jikinta to ki daina batawa kanki lokaci mazan yanzu sun daina soyayyar gaskiya Jerusalem naki ne Kawai burinsu gwara ma ki Bude idonki,Manal Tace ku kuka San wani Jerusalami ta ci gaba da Shirin soya gyadarta,tana aikin gyadar Tace ga me siyen Gyada marau marau me gishiri yau Zan fara duk kulli Naira Ishirin naira hamsim babu bashi bare kyauta,Farida tayi wata shewa tare da Furta wa zaici gyada? Allah kiyaye kuraje su fito min a Fuska tun Fuzail Bai zo ba,Hajiya Tace kwantai ma zata Yi mu Nan ba Kauye bane basa cin wata Gyada kayan wahala,Manal tana aikinta ko kulasu batayi ba.

Tunda Manal ta fara Gyada sai ta samu kasuwa sabo da yanda take soyata me Dadi,riba take samu sosai,idan ta soya ko kwana Bata Yi take karewa,ganin Haka yasa Yaya Yazed ya samo kudi ya Kara Mata kwano Daya take soya ta kwano biyu kullum duk da ya hanata talla a gida ake sintirin zuwa siya maza da Mata,a cikin ribar Kuma da ita yawanci ake cefane Ana ciyar da gidan,Ganin Haka sai Yazed ya auno Mata waken suya ta fara awarar siyarwa shi ya koya Mata yanda ake soyata da kwai sannan a yanka Mata su Albasa da kayan Miya harda cabbage,Manal sai kasuwar Awara ta Bude sosai ko Basu samu sunyi girki ba to awarar Nan ake ci kowa ya Sha ruwa,idan jari ya karye Yazed ya Dora jarin,Haka Malam masifar Jin dadin sana'ar Manal yakeyi,Kuma kullum itace take kula da shi idan Yazed Baya Nan,Haka ita da Yazed suke hada kayan Malam Dana Manal Dana Yazed su wanke abinsu tas su goge kullum cikin tsafta suke,Zuwan Manal gidan ya cire kazantar gidan komai ita take gyarawa shi yasa sai kaga ko Ina Kal Kal,jikinta ma fes matsalar Kawai rashin sutura,Sabanin su Farida da Hajiya tana da Yan uwa masu Dan Hali suna tallafa musu da kudi da sutura,idan Suka samu kudin Kuma a jikin Farida suke karewa wajen gyarawa Fuzail jiki sabo da ya sota sosai.

Bayan Kwana biyu tsakani Sai ga Farida tana Hawaye jiki a sanyaye ta shigo gidansu,takalminta Dan dubu bakwai me tsini ta cire a hannunta,English Gown dinta Yar dubu Tara ta dageta sama a Haka ta karaso wajen Hajiya dake goge Mata kayan sawarta da dutsen guga sabo da ta Hana Farida daukan ko tsinke a gidan sabo da kar skin dinta ta lalace,a tsorace Hajiya tace Farida lafiya kike Hawaye? Dan Sarkin ne ya wulakantaki?Farida ta girgiza Kai tana share hawayenta ta furta mafarki na ne wani a ciki ya Zama karya,Gaban Hajiya ne ya yanke ya Fadi tace yau na Shiga Uku ba dai auren ne bazai yuwu ba? Farida Tace a'a dama Hajiya Ni mafarki na ban taba ganinsa ba Ashe na taba ganinsa sau biyu ma,sannan a mafarki na Bai taba zuwa kasar nan ba Ashe ya taba zuwa har sau biyar ma,Kuma Yana Jin Yar hausarsa Yana Yi Kuma Amma ba can ba sabanin mafarki na, Lokacin Dana taba ganinsa a wani kazamin goslow ne da aka taba yi,Ina taxi ya fito da escort dinsa a wasu mahaukatan Motoci,sannan na sake ganinsa Yana rabawa talakawa tallafi a kusa da makarantar mu Muka wuce shi da kawayen mu,Kinga yau na ganshi Dana je gidan Sarkin Muna tare da Bafaden gidan ya fito zai fita Allah yasa zai Shiga mota na saita wayata na dinga Masa hotuna,sannan Kinga Bafaden ya tura min wasu hotunan Fuzail sunfi ashirin,zanje gidan Hoto a wanke min su nazo na lika su a dakina..
Ashe na taba ganinsa rashin ganiya ce irin tawa Amma Allah a fili yafi kyau ma Sau dubu fiye da mafarki na,wayyo Allah na more da Mijin aure,Ni Kam na taka sa'a shike Nan Ni Hajiya Farida ta furta tana Juyi da murna da Ihu gaba Daya

Hajiya ta sauke Ajiyar zuciya tace akan wannan kike kuka nayi tunanin ma wani Abu ne Babba nuna min hotunan nasa,Farida ta kamo Hotunan Fuzail masu shegen kyau wasu ma duk a kasar waje ne,duk inda kake neman me kyau Fuzail ya Gama cika sharadan,ai sai murna ta Kama Hajiya tana bin hotunan da kallo Daya bayan Daya tana Inyeeee....Carkwadi,ke Kam Farida kin Dace kalli fatarsa dinsa wani irin haske me wani dum dum...wow Kai kalle shi a dusar kankara wannan Bai Saba da zafi ba Dole mu Nemo ac mu saka ko a Rubabben dakin ki ne tunda Nan gaba zai dinga zuwa zance,Farida tana murna tace wallahi har hotunan Zan na yiwa fifita kafin a sa ac.

Manal tana ji tayi Dariya tace Haba Ni nasan Yasin kin sanshi kin taba ganinsa Amma sai kace wata waliyya ace ka dinga mafarkin mutum baka taba ganinsa ba Kuma ya Zama gaske Haba Anty yanda kike da bakin Hali yaushe ma zaki ga mutum a mafarki baki sanshi ba,Uwarki Hadiza nace cewar Hajiya,muguwa Yar bakin ciki,yarinya Zo kiga saurayi hadadde me kudi,Manal taje ta leka Wayar gabanta ne ya yanke ya Fadi ganin irin wannan mutumin me Arnen Kyawun da Bata taba gani ba tsawon rayuwarta,ga kudi ga Hutu,wasu pics din ta gani tace chab Allah ya samu a danshinki,Farida tana murna tace ya kika hango Ni a gidan sarauta na Sha alkyabba? Manal Tace ta bature yace wow...Dariya sukayi gaba daya Hajiya tana murna Tace jibi Zan karbo dinkuna na sababbi sabo da tarbar bakin gidan Sarki.

Tunda Manal take Sana'a tana samun ciniki hakan Yana konawa su Farida da Hajiya Rai,Hajiya tace wannan Yarinyar fa Muna zaune sai wani juya kudi takeyi Kuma ace Wai itace ma take yawan yin cefane a gidan Nan,Farida tace ai wallahi gwara ma mu dinga yini da yunwa akan ace wannan tatsitsiyar Yar kauyen ce zata dinga wani bada kudin cefane,Hajiya Tace kyaleta gidan Malam Dan Haru zamu je a toshe Mata hanyar samun,gaba Daya ta daina ciniki a daina siya ta koma yin kwantai Kinga Dole ta daina sana'ar, ai kuwa dare Nayi Hajiya sai gidan Malam.

Malam yace Hajiya meke tafe dake? Hajiya Tace bukatata na kawo Malam,Gani Malam ka taimaka Manal Yarinyar kishiyata bayan mun koreta na fada maka ta dawo asirin ya karye da wuri,yanzu ba bukatata a kore ta ba,tana Nan ta Kama sana'ar Gyada da Awara Malam Yarinyar ciniki takeyi sosai yanzu ma ita ke cefane a gidan Muna zaune,Ina bakin ciki Naga maza da Mata Ana sintiri a gidan Nan domin siyen kayanta,yini akeyi siyayya,tun tana soya gyadar kwano Daya yanzu kwano Uku take soyawa,Haka Awara yanzu ta kwano Uku tas take karewa Kuma abin haushin ko talla Bata fita a gida take zuba Uban ciniki Haka wallahi Rannan a ganmu ta irga dubu biyar ribar data hada ta damkawa Dan Uwanta Yazed ya siyo taliya da macaroni wallahi ranar kwana nayi banyi bacci ba,Ni Malam akan ace sune zasu dinga ci damu wallahi gwara mu dinga kwana da yunwa.

Malam Dariya yayi yace sana'ar da takeyi Awara da Gyada ko? Hajiya tace tabbas,yace indai Awara ce da Gyada daga yau an daina siye ko mutum Daya bazai Zo ba,Hajiya tana murna Tace duk abinda tasa Hannu akai Malam ya lalace Kar a Bari ta ci gaba,Malam yace ba lallai akan ko me ta taba zai lalace Amma duk abinda ta fara kika ga bakwa so kuzo ku sanar min a dakatar da abin,Hajiya tace dama yaushe Muna kallo zata Zo daga Kauye ta wuce mu ai bazai yuwu ba.
Chapter 10 · 0% Book details