← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 95

Sashe 71

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da Yamma likis su Belloti Suka dauki wankan sugar Farida sabuwar atamfa ta saka ta lefe dinkin Riga da skert tayi mugun kyau Pink and blue,Farida hips din Nan gashi nan Kamar me,ta zuba kyau ta kafa daurinta,Belloti harda Saka sabuwar shaddarsa wata Blue ya dinka su Kala hudu Bai taba sakawa ba Kawai ya ajiye masu kyau,Dinkin matasa,Belloti akwai Kyawun sura duk kayan da yasa kyau yake masa,Sumar Nan taci kudi Farida tana taje Masa tace Kar a aske min Sumar Nan Ina sonta da yawa,Belloti Yana waya da Babarsa Yana cewa gobe zasu Zo a gyara musu dakinsa Yana Jin Me Farida take furtawa yace an Gama,Tace da gemun ma da sajen duk a bar min shi,Belloti Yana wani daura agogo a dole Babban yaro Yana Mata magana da Ido Wai yaji za ayi hakan,Yana Gama Wayar ya dauki wayarsa da key din room din tare da rike Hannun Farida Suka fita ya rufe dakin Farida takalminta me tsini da hand bag duka pink,ta Sha Daurin Zahra Buhari,Farida tayi kyau sosai,Belloti yace kullum kyau kike karawa Farcy Beb,Farida Sarkin Fari tayi wani walwal da idanuwa tare da Furta kullum fa Fresh cucumber nake ci ba Dole na canja ba,Belloti yace hakane,Napep Suka shiga Farida tana mamakin kanta Wai ita me son mota yau itace ta Kare a Miji ko Keke baida shi,Kanta ta bawa laifi tasan ita ta jawowa kanta amma shege So Farida Son Belloti yasa Haka take gani yanzu gwara Haka akan a Bata duniya da abinda take ciki gwara a barta da Bellotinta,Hajiya ce ta Kira Farida suka gaisa,Farida tace Hajiya ya gida?

Ke dai Bari gida Yana wajen Masu shi,Ni da nake Dan rabawa Ina Naga wani gida, kin ganni matar yayan ma abinci sai taga Dama take bani Farida,ga aikin gidan Nan kaf yanzu Ni nakeyinsa sai kace yarinya,da girmana ai Ko darajar girmana Yaya ya kalleni ya tausaya min sai ma zagina da masifa da yakeyi Wai laifina nane,Dangina yanzu bani da Iko na shiga cikinsu sai a dinga jefar min da babaken maganganu Ni wannan zaman ya isheni nasan Nan gaba ma Yayana Korata zaiyi daga gidansa....Hajiya ta karasa da kuka Tace Farida yanzu naira Hamsim gagarata takeyi ga yunwa ba a bani abinci akan lokaci duk na rame,Yan Yaran ma da suke zuwa wajena Ina kallonsu Ina Jin Dadi Malam ya hanasu zuwa,Yau ma Farida tun safe ba abinda na samu na saka a cikina,Yaya da matarsa sunyi Tafiyarsu Lagos Wai sai Nan da sati biyu zasu dawo Kuma wallahi sisi bani da shi,ko kwallon shinkafa Basu bar min ba,tasa key ta kulle store dinta Wai idan Ina da kudi na siyo da kaina ga kitchen Nan na dafa,Kuma Yayan ya biye mata Suka kwashe har yaransu Suka tafi abinsu,Ina Jin Farida yunwa ce ajali na,kowa na tambaya a dangi babu me taimaka min sai suce ba ruwansu Wai Ni na kashe aure na,yanzu bani da kowa Farida Sai ku yarana tunda mijinki Yana da Dan arziki Kuma kince Kuna zamanku lafiya sai abinda kika ce Dan Allah Farida ki turo min ko dubu biyu ce a accnt Dina na samu naci wani Abu,Allah ya kyauta kiyi Hakuri Hajiya Inshaallah Zan San yanda za ayi,Hajiya da sauri ta dinga godiya.

Bayan Farida ta kashe wayar suna Napep da Belloti yaga ta fada tunani da damuwa sosai a fuskarta tana Neman yin kuka sabo da Farida Bata da ko kwandala Sadakinta ma Fridge aka siya Mata da shi anyi zaton za a Mata jere,Kuma kayan gaba Daya suna gidan Yayan Hajiya,Kiran Hajiya ta sake yi ta daga tare da cewa Farida kin tura? Farida tace Hajiya Ina kayan kitchen da muka Dan siya wasu abubuwan ki dauki wani abin me tsada ki siyar da su kiyi amfani da kudin,Hajiya Tace tab yo ai tunda na dauki Blender a ciki na siyar Yaya ya boye kayan a wani Empty house yasa key ya garkame Kuma yace idan na taba wallahi sai ya ci mutunci na,Farida Kawai ki bani ko dari biyar ce ma ki turo min abin kunya ne na Bude sirrina naje na tambayi wani kudi ke kin San me Mukayi wallahi Dariya za a min.
Okay Farida ta furta ta sake kashe waya ranta a jagule Idonta ya ciko da kwalla zata Yi kuka,Belloti ya fahimci matsalar kudi ce,yace Lafiya Baby? Farida tana goge hawayen da ya zubo Mata tare da furta ba komai,Ya Zaki ce ba komai ki fada min idan Bai fi karfi na ba Zan Miki,Farida Taki fada sabo da boye sirrinta Su Farida ba a son Raini,Belloti ya matsa sai ya ji dole ta hakura Tace Hajiya ce take son Kudi ko 1k ne Wai amfani da zata Yi da shi Bata ce yunwa bace Kar ya Raina su,Belloti yace Akan wannan kike Kuka har baza ki fada min ba,ke Nifa bana son irin wannan, waye Bai San rayuwa ba yanzu,kune komai sai kunyi karya ta Yan Birni da kin fada min da tuni ba a tura Mata ba Zan rasa kudin Bata ne kika ji? To ko abokina na sa yanzu zai tura Mata bani accnt number.

Farida Lokacin farin ciki ya kamata taji wani sabon son Belloti ya kamata Haka ta bashi account Number Nan take yayiwa Hajiya transfer na 5k, yace ki tambayeta idan ta gani sai ga Kiran Hajiya Tace naga 5k da accnt din mijinki 5k Bello Muhammad Tukur ko? Farida Tace ae,Hajiya godiya ta shiga zubawa harda sa Albarka Tace bani shi nayi Masa godiya,Farida tace My Hero ga Hajiya zata maka godiya Belloti yace Akan 5k Mene 5k gaskiya bazan iya amsa ba kunya ma nake ji 5k kacal a kanta za a gode min Fafur Belloti yaki karbar waya Wai kunyar Kansa yake Yi ma a hakan.

Farida a ranta tace Allah me iko a baya 20k ma mutum ya bamu Bai Isa mu gode Masa ba bare 5k wa zai saurare shi ma duk talaucin mu,Wani Shawarma Joint Suka Shiga kida na tashi iri iri ya musu order na Shawarma da fruits salat Sai ice cream,Belloti harda Bawa Farida a Baki sai da Suka ci suka koshi suna hirarsu cike da nishadi da kaunar juna.
Bayan Nan Shopping Mall ya kaita yace to karki karar Mana da Dan kudin tafiyar mu kauye yanzu Abu me ma'ana zamu siya,Wanne Body Lotion ne ya karbe ki? So nake a samu me kyau kiyi haske me kyau Normal bana son wannan hasken dau da kikayi kafin aurenki, gwara kiyi me kyau,Farida tace lokacin fa wata Allura ake min,Yace Kar a sake ba a gidana ba,Dan cream din ma me kyau Bai Isa ba sai anyi wani haukar haske tunda Allah yayo mutum Baki Ina laifi ma da Allah ya Bawa bature ikon Kirkiro body Cream a shafa ayi kyau duk haka ba a gode ba sai an Zama baturiya, siyi Cream me kyau me Dan tsada Wanda zai gyara skin ko hasken ne ayi me kyau na hankali na wayewa,Farida tace ai tunda nayi Allurar sau biyu na daina gashi duk na fara dishewa,Belloti yace yawwa kinfi kyau haka daga Cream na dubu Uku zuwa hudu Zan iya siya Miki dai dai karfi na.

Sai da suka Gama shawarwarin me zasu siya na tafiya Kauye Wanda ko sunje bazai Kare da wuri ba zasu Dade sannan Suka shiga ciki,Farida ya Siya Mata body Lotion Kalar data zaba Dan 4k Guda biyu,sai na face dinsa,su shampoo Kuwa duk ya Siya Mata duk da cewa tana da wasu a lefe,Turare zai siya Tace Ina da Humra fa da yawa ga Kuma na lefe it's okay,Belloti shima ya siyawa kansa abinda zai iya,Har su kayan shayi cornflakes sai da ya Siya musu Kar ma suje Kauye a samu matsala tunda yasan Farida bata Saba da cima ba ta kauye ba,Sai da suka Gama suka dawo wurin 12am a daren suka shirya komai nasu har tsarabar da zasu Kai sun siya,Belloti gaba Daya Dan abinda ya Tara ya kwashe harda siyawa Iyayensa Buhun shinkafa,taliya,macaroni,Mai,su Indomie da su sabulan wanka da wanki.

Washe gari 8am ya Kira wani Me Golf da ya dauka Drop zai kaisu har kauyen suka shirya kayansu tsaf sannan Belloti ya shiga bedroom din Uche ya bashi Hannu Suka tafa yace Zan wuce,Uche sai Kuma yaji ba Dadi gaba Daya yasan Bai kyauta ba,Nan take yace na hakura Bello ku zauna,mu zauna tare I'm so sorry for what I have done to you,Belloti yayi murmushi yace ai ba Haushinka naji ba Kawai Allah yayi tashi na ne ka barni na tafi Zan dawo verysoon Zan na zuwa Muna gaisawa,Uche Yace Alright Be a good Man ya ciro 10k ya bawa Farida yace ajiya gashi asha ruwa,Farida ta karba tayi godiya ta ci gayu cikin lace dinta peach doguwar Riga me kwala dinkin manyan Mata,Shi Kuwa Belloti wata Shadda ya saka ruwan toka an Masa gyaran gashi yayi kyau sosai da gani kasan ya waye ba Kalar Kauye bane.
Chapter 71 · 0% Book details