Sashe 24
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana Fitowa ta kalli Shukrah Yar gayu tasan ma me zatayi da Manal ko a kawa, Farida ta kyalkyale da dariyar Mugunta tace Hala sata tayi muku? Nasan tunda nake ganin kudi a Hannunta sai dai sata ta koma,Shukrah ta dinga mamaki Yan Uwa suna Haka a junansu,dama Ameer yace ta kula da su,Shukrah Tace Dan Allah tana ina? Farida da sauri sabo da mugunta Tace muje na rakaki dakinta,Manal tana kwance ta fara bacci Ma taji Muryar Farida tace tashi Dan Ubanki anzo kureki,Manal ta Mike zaune a tsorace Idonta ya zazzaro ita tasan Bata da kawa a garin Nan bare wannan Yar gayu Haka ai Dole ma laifi tayi,Murmushi Shukrah tayi ta wani Yi acting kamar gaske Tace yanzu Manal Baki Gane Ni ba? Gaskiya kin bani haushi,Nurse ce fa Shukrah wacce kika taba Kai wasu marasa lafiya maza samari su biyu kin tuna? Manal ta tuna Sanda ta Kai su Ameer asibiti da sukayi hatsari Amma ita Bata Gane Nurse din ba,Dama Shukrah karya tayi a private Hospital take Aiki ba wata Manal data sani.
Manal Tace ban iya ganeki ba,Farida dake tsaye tana Jin gulma Jin ance maza da sukayi hatsari an kaisu asibiti Nan tasan su Farooq ne da suka cuceta ai sai taja Tsaki sabo da tsanar da take yiwa Farooq tayi gaba abinta Bata son Jin ko sunansu,Manal Kawai murmushi tayi Tace wallahi na kasa tuna ki kiyi Hakuri,Shukrah tayi Dariya Tace ba komai dama Kawai kin birgeni ne ganin yanda kike da tausayi gaki da hankali yarinya karama Dake kuma shi yasa nace Inshaallah sai na nemi gidanku,Rannan Katsam kin fito siyen Abu Ni kuma Zan wuce ta layin Nan Naga kin shiga gidan Nan shi yasa nazo yau na tambaya Ashe ma Nan ne gidanku,Manal Tace Amma na gode lallai kina kaunata,da fatan Zaki Zama kawata? Shukrah ta tambaya.
Manal da sauri Tace ba matsala na gode Dama bani da kawa ko Daya na samu abokiyar Hira,a wacce Unguwa kike? Shukrah ta fadawa Manal inda gidansu yake tare da cewa ta Nan layin nake wucewa idan zanje wajen Aiki Zaki dinga ganina akan lokaci,Manal tana murna tace to na gode Bari in kawo Miki ruwa.
Manal tana fita Shukrah ta zare dubu Uku ta daga pillow din Manal ta Ajiye Mata dubu ukun ta zauna jiranta,Manal tana shigowa da pure water Guda biyu a leda Shukrah ta Mike Tace sauri nakeyi Kawata bani na Sha na tafi, Shukrah ta Sha ruwan da sauri sannan Manal ta rakata har bakin Titi ta dawo gida tana tunanin me zasu ci da dare dubu biyun da Ameer ya bata sun Kare a abincin Rana da kudin makarantar su Falaqi,Zama tayi tana tunani gobe da me zasu karya ga Yara kanana,da ace ma iya su manya ne da sauki Amma yaro karami Yan makaranta a barsu da yunwa ga yunwar makaranta,gajiya tayi ta Mike ta fito ta Iske sun Kuma Bata gidan da Yamma ta share ta gyara.
Hajiya duk kudin da suke samu sai su Hana cikinsu su kaiwa Malam ko su siyawa Farida kayan kwalliya da gyaran jiki.
Suna zaune Yara suna Islamiyya Manal tana Jin hirarsu da Hajiya suna gani Basu da abin da zasu ci Amma Hira sukeyi Farida tana cewa ya kamata Hajiya na fara gyara jikina irin na amare sabo da Kar yazo yace bikin Nan a kusa yake sonsa maganin Sanyi da Wanda zai Dan karawa mace lafiyar jiki ya kamata ace Ina amfani da su kafin yazo,Hajiya Tace af ya akayi basirar mu ta Kare ai ya kamata yanzu tunda ba kudi zanje wajen Yaya Sani ya bani ko dubu biyu ce a Nemo Miki maganin Sanyi ko kala biyu ne masu kyau ki fara Sha yanda da yazo ko gobe ne a shirye muke,Manal ta kallesu tayi Dariya Tace wallahi Allah ya kamata a kaiku gidan masu tabin kwakwalwa,asibiti ya Dace a kaiku a auna hankalinku.
A duniya idan da a Film naji Ana Haka wallahi Zan zagi me film din ne zance karya ne,wani abin idan kaji a duniya sai ka rantse bazai taba faruwa a gaske ba,Amma sai kaga abinda yafi Haka ma yana faruwa a gaske mutane Kamar Basu da hankali idan suna wani abin,akan son zuciya da son kudi,son kudi duk ya haukata ku na tabbata yariman Nan da kuke so da ace talaka ne duk kyansa baza ku so shi ba,Amma sabo da kudi duk Kun maida kanku wasu zararru,Unguwar Nan sai gulmarku akeyi dangi da mutanen arziki ba Wanda Bai fada muku gaskiya ba kunki yarda,Mafarki har abin dogaro ne?,ke ba wata Waliyya ba bare ace wata Aya za a saukar a kanki,Dan Allah ku rungumi talaucinku mu dawo gaskiya mu nemi sana'ar Yi wacce zamu dogara da kanmu mu rufawa kanmu asiri mu hada kanmu, shirmen Nan mu daina mu zauna mu nemawa kanmu mafita Dan Allah Hajiya kece Babba ki daina wannan abin ke fa ya kamata ace kina Yi Mana fada kina Dora mu akan hanyar gaskiya,kece me Bamu tarbiyya Amma kin zauna Farida ta Gama lalacewa duk wata hira da kalaman Banza fada takeyi a gabanki Kuna Hira Kuna Dariya Kuna tafawa Dan Kawai kina da ya Budurwa,a kanki aka taba haifar yarinya budurwa,na tabbata abinda Farida keyi a gabanki ko da kawarta Ruma basa haka.
Yarki ce fa,kowa Yana so yaga Dansa ya Zama na gari duk da nasan yanzu Haka matasan Iyaye ke Yi gani suke wayewa ce da birgewa ka haifi yarinya budurwa sai su maida ta kawarsu,duk Maganar da Uwa taga Dama fada take a Gaban yarta,suyi Hira su tafa duk inda zata je su tafi tare tana nunawa duniya Yarta ta girma tayi Kai Daya da ita,shigar banza da kayan shafe shafe duk ita ke Dora Yarta akai ko yaranta Mata,tana Alfahari da su,a Gaban Yara Uwa zata ci mutuncin mijinta Kuma ubansu,wasu su tayata kishi harda masu gaba da Iyayensu maza akan anwa Uwarsu kishiya,su hadu da Uwar a gallazawa kishiya da yayan kishiya azaba,su Hana ubansu kwanciyar hankali,shi yasa yarinya sai kaga tafi karfin Iyayenta yanda taga Dama Haka zata fadawa uwarta magana son ranta,karshe Kuma Uwar data lalata su itace zasu gagareta ta rasa inda zatayi da su karshe ita kanta sai dai ta Kai kararsu wajen Iyayenta kakanni idan suna Raye ko wajen danginta ko Dangin Ubansu ma ayi musu fada basa Jin maganarta sun gallabeta Bayan ita ta jawa kanta.
Wallahi Hajiya kika sake abinda Farida sukewa Baba Yasin sai sun Miki ai gashi Nan kina gani ke Bata Miki wanki ba kin moreta a matsayin ke kika haifeta sai kece ma kike Mata wanki da guga da sauran ayyuka idan Baki Yi ba baza suyi ba Kinga kin maida su kazamai kuma laifinki ne,sannan duk abinda Tace shi Zaki Mata,ga Yara su Sa'iha duk basa Jin maganarki Nan gaba Zaki ga wulakanci kuwa wallahi kafin kowa yayi kuka ke Zaki fara yi mu Yan jaje ne,Iyaye Yara Suki yin Aiki idan anyi magana Tace idan sunje gidan mijinsu ai zasu Yi dole,Basu Saba ba ta Ina zasuyi Dole? yanda yanzu aka daina biyayyar aure,yanzu ke Farida ko kin auri Prince din Haka Zaki Masa kazanta? Nufinki akwai Bayi su zasu Miki komai? Ko shafe shafen naki zai kalla Kawai? Hajiya tunda Manal ta fara magana ta saki baki har wajen minti talatin Manal tana zazzaga musu fada, kowa yaji fadan Manal yasan gaskiya ta fada Amma Hajiya ta fashe da kururuwa Tace Manal ta zazzageta, Farida Tace sai ta Mata duk ta dakko tabarya,ganin da gaske sukeyi ta fece dakinta Farida tace ai Zaki fito ne wallahi ko Zaki shekara a daki Indai kika fito sai na fasa Miki Kai,Manal Taki Fitowa Haka suka kwana da yunwa rashin fitowar Manal sun San da Manal ta fito ko a shago sai ta ci bashi ta siyowa su Falaqi ko garin kwakwi ne da sugar,Su Falaqi sun Sha haushi yau rashin fitowar Manal.
Da Sassafe Kuwa zasu tafi makaranta Manal tana daki a kulle ta hau gyara dakinta yunwa na cinta sai ko ta tsinci dubu Uku a kasan pillow sababbi dal dal,ko Bincike batayi ba Manal Tace baiwa daga Allah wallahi Allah ne ya ciyar dani,tana cikin murna su Falaqi Suka hau dukan Kofar Manal suna Manal zamu tafi makaranta ki fito,Manal tace ku tafi Mana Haka Kawai Anty Farida ta nakasa Ni da tabarya,Alhaqatu tace Bamu karya ba Anty yunwa wallahi zata kashe mu jiya Falaqi Kwana yayi Yana kuka,Manal Taji tausayinsu,Sa'iha Tace ki fito Manal tunda kina da karfi ki dauki Anty Farida ki nunawa Allah ki bugata da kasa,Dariya Suka bawa Manal Shegu Yara sunji wuya cewar Manal ta furta tare da Bude kofar.
Ihu suka fara yeeeeeeee
eeeeewwwwww Suka cika gidan,Hajiya ta leko da kanta tsakar gidan Tare da tambaya Nepa aka kawo ne? Falaqi yace Aunty Manal ce ta fito yanzu zamu ci mu koshi Yeewwwwwwww suka Kama Rawa da tsalle,Manal tana sani ta kalli Hajiya ta daga dubu Uku sama ta karkada su a Iska,Hajiya ta zaro Ido Tace bakya sana'a wallahi Sata kike Yi barauniya an koma satar kudin mutane.
Falaqi ya shiga Kare Manal yace Hajiya Sana'a take fita Yi a kasuwa,inji Ubanka kullum Muna tare da ita a Ina taje Neman kudin? ka koyi karya shegen Kai Kamar randar kauye,Falaqi yace to tunda kullum Muna tare da ita a Ina zata sato kudin mutane tunda Bata fita ko Ina kince,Allah ne ya Bata mudai muje Anty Manal ki siya Mana dafaffe a gidan Maman Aisha, Manal tace yawwa muje a siyo Kawai ku tafi da abinku school sabo da karku makara,Falaqi da gudu ya kwaso kulolinsu na Yan makaranta suka fita gaba Daya,Gidan Maman Aisha babu abinda Bata dafawa na abincin siyarwa ko me kake so komai dare komai safiya zaka samu,Manal tace kowa ya zabi abinda zai ci,Suka zaba aka cikawa kowa Cooler dinsa sannan ta Basu Naira talatin kowa kudin Break Suka tafi school da murna.