← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 95

Sashe 84

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda Yazed ya tafi Kuwa Kamar su Farida sun sani da kyar Raheela ta samu da Asuba tayi bacci tana ta tunanin sahibinta shima Haka,a ranar wurin Magriba yabi jirgi ya koma,zuwan Yazed Uku Zance aka Kai kudin aure tare da sa Rana Nan da wata Uku,Manal tana ta Jin haushi lokacin cikinta ya tsufa ko kyau baza tayi ba.
Fuzail Kuwa tunda ya tafi ya kasa sukuni ji yake me yasa ma Bai taho da Manal ba,anya Kuwa zai iya bacci,a wani katafaren hotel Bayan yaci ya koshi ya kalli dakin yace komai yaji Amma ba Sunshine a kusa Mene Haka kenan?,Kamar yasa ta taho amma idan ya tuna gwara ya Dan hora ta sai ya fasa a Haka ya kwana Daya da kyar,in Banda tunaninta ba abinda yakeyi,shi kadai ya dinga dariya,abinda ya kaishi ma kasa yinsa yayi ga Cassava Taki kwanciya tunda ya bar gida.

Manal Kuwa ranar ganin da gaske tafiya yayi sai kuka kwana tayi tana kuka,da Sassafe Ummi ta Kira a waya,Lokacin Ummi tana gidan Dan uwanta suna shirye shiryen za a maida Aurenta ita da Mai martaba,ta karkashin kasa suke komai ita da Sarki ba Wanda ya sani,zuwanta gidan yayi sandin tasar da tsohuwar soyayyarta ita da Sarki,Yana ta ganinta tana chasa gayu yaji bazai iya ba Itama Ummi Haka tunda ta dawo taji sha'awar komawa dakin mijinta,daga Nan suke komai a boye sai komai ya tabbata sannan mutane zasu ji,Manal tana kuka,Ummi tace lafiya? Manal tace Prince yazo Nan ne? Sai kace mace yayi yaji Ana tambaya ko yaje can,Ummi tace Bai zo ba lafiya? Manal tace ba komai Kawai yace zai zo ne wajenki ya taho Kuma na kasa Samunsa,Fuzail din ne zaizo Bai fada min ba Anya Kuwa lafiya? Naji kamar kina kuka Mene ne? Manal tace dama Wai akan mun Dan samu sabani shine Yace yayi yaji ya hada kayansa,Dariya Ummi tayi tace Bai so ya Miki fada ne fa Manal akan ya Miki fada yaga gwara ya bar gidan kawai, zai dawo ne,karki damu,Manal Tace Ummi yace bazai dawo ba Dan Allah ki Nemo inda yake sai naje bikonsa,Ummi tace zai Nene ki ne, wayarsa ko na Kira baya dagawa sai ya turo min text yace Kar na sake kiransa yanzu Ummi Haka ya dace Dan Allah?Ummi Tace Bai Dace ba Sam kyale Ni da shi,ya makarantar? Alhmdllh munyi hutun sati biyu ma,Okay to karki damu kici ki koshi kiyi banza da shi idan Ana damuwa da maza yanga sukewa Mata ki nuna Baki damu ba,Manal tace ai Ni nayi Masa laifi idan nayi Haka ban kyauta ba,Ummi Tace Haka zakiyi yanda nace shine Kawai,Ni dai zuciyata baza iya ba Manal ya furta,Ummi Tace to sai ya dawo Zaki ganshi.

Ummi tana kashe waya ta Kira Fuzail ta hau shi da fada lallai ya koma gida,Dan Iskanci yarinya tana da ciki dama Haka kuke sai Kun Gama da yarinya Kuma ku tsiri Iskanci wlh idan baka koma ba sai na Saba maka,Ummi ita.....bana son ji Kawai ka koma yarinya tana ta uban kuka sai cikinta ya samu matsala ko? Haka kake so cikin nata ya samu matsala kana sa Mata bacin Rai.
Kiyi Hakuri Zan koma gidan Nan nake so Naga yanda aka hada shi,to shike Nan amma fa ya kamata kazo Brazil ka duba abubuwanka na gaji da kular maka da Business,Ina bibiyar komai Nawa fa Ummi nafi so Manal ta Haihu sai muje ko Ina Naga komai kin San Michiel idan Yana Kan komai har ya fini kula da alamuran ma,na sani ai Allah ya kaimu ta Haihu ai dole Ni Zan ci gaba da komai kafin ta haihu nafi so ka zauna ka kula da ita kafin ta haihu zanzo ai Inshaallah,Allah ya kaimu yace Kinga tunda Maimartaba ya barni na zauna inda nake so Nan gaba Kawai zamu koma Brazil ko London da Manal sai mu dinga zuwa ganin gida akan lokaci Kawai,idan ya barka shike Nan nasan yanzu bazai hanaka komawa ko wacce kasa ba tunda ka auri bahaushiya Yar uwarsa dama Haka yake so,murmushi Fuzail yayi Suka Dan taba Hira Kan harkokinsu.

Bangaren Yazed Kuwa shirye shiryen biki sukeyi bangarensa da bangaren Raheela sai dai ango da Amaryar basa wani soyayya sai dai suna Dan kula juna sama sama,duk yanda Raheela taso ya nuna Mata so da kauna yaki dole itama ta bishi a yanda yake so,hakan yasa take jimamin aurensa tasan zai wahalar da ita ,ita ta kasa Gane masa,ba waya ba komai sai yaga dama gashi an rigada an Gama komai shi yasa ta mikawa Allah alamuranta Bata wani murnar auren jikinta a mace yake gaba daya Kamar auren kiyayya,sai Farida ce ma ke Dan Kara Mata karfin gwiwa tana kwantar Mata da hankali.

Bangaren Prince Kuwa kwanansa biyu kacal ya tattara ya taho gida ya kasa Zama yayi kwanakin da yake so,Manal tana bedroom da katon cikinta kafafunta sun kumbura da jikinta Bata San dalili ba tana shafa musu magani tana faman Hawaye sai kace famfo taji kamshin mutum a kanta da sauri ta dago kanta da Hawaye a fuskarta.

Maman Samha Ina gaisuwa.

AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭

DEDICATED TO DUNIYATA AAMNA FANS GP

111-115

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

Jamil 50
Sadiya Muhammad Bala
Sadiya Aliyusafiya89
Bilkisu Aminu Ibrahim
Safiya Bature
Mom Aneesa
Hajjaju
Khadija
Maman Dr

Ina miko gaisuwa Mai yawa

Bestynbeelat
Maryam T Baliya
Maman Murtala

Ido suka hada da prince ta wani Kara kwabe Fuska tare da amsa sallamarsa Alkslm, ganin ya dawo sanyi taji a ranta a fili kuma Bata Yi murna ba,sai ma hawayenta data goge,Kafatar ya Dan latsa da yatsa Yana tambaya lafiya? Shuru ta Masa yace Ina tambayarki tashi mu tafi asibiti Manal Nan ma tayi Masa banza,Ni kike sharewa Sunshine? Ya Furta tare da Zama a gefenta kafadarsu tana gugan juna,Maganar duniya yayi amma Manal Taki kulashi,hakan yasa ma ta kwanta tare da juya Masa baya,Okay naji nayi Miki laifi I'm sorry...so sorry Baby kin San kin Bata min rai taya Zaki Bawa Amarya magani Wanda zai iya cutar da ita,da ace wani Abin ya sameta fa ya zamuyi? Na Miki fada Amma bakya Jin maganata idan nace a kyale abu baza a daina ba,ban Isa da ke ba,ban Isa da gidana ba haba My wife,Karka dameni Dan Allah ka koma inda ka fito Ni bana son hayaniya sai da ka tafi yawon duniyarka zaka dawo ka dameni dama can kayi Niyyar tafiya wajen Budurwarka,ai Naga take takenka dama Budurwa kayi sabuwa mene idan ka fada min zaka Kara aure,Zan hanaka ne? Na rigada nasan nayi maka kadan, inji na ni na machine ne ba shike Nan ba tunda ko Haihuwa banyi ba ka tafi Neman aure ai na sani.

Dariya ta Bawa Fuzail yace me yasa kike son kala min abinda banyi ba? Bana son shirme tashi mu tafi asibiti,bazan je ba da ka damu Dani ai da baka tafi wata Uwa duniya ka barni ba har in kiraka ka dinga kashe min waya Wai Kar na sake kiranka,Manal tana nuna kanta Tace ni...ni...kamar Ni? na girmi wulakanci wlh kayi kadan ka wulakantani, sai yanzu ma Naga dacewa da Farida ta kwala ma botiki,Ni harda wani taimakonka ba komai ba laifinka bane, dama sai da akace ba Yan goyo bane ku naki yarda harda dakko zani na goyaka a bayana, ba ruwanka da rayuwata,laifi fa kika min Sunshine,naji na maka laifi ai na baka Hakuri ko? To kiyi Hakuri bazan sake ba,bazan hakura ba ta furta Masa direct, Kamar Wasa Manal sai ta koma part dinta ta kulle ta barshi,ba yanda baiyi ba Taki kulashi.

Rasa inda zai Kansa yayi lallashin duniya da buga kofa Taki kulashi ma,a jikin Kofar ya tsaya tare da furta Manal Hospital fa please....Baby.....Sunshine......dan Allah kiyi Hakuri ki fito ko baza ki kulani ba muje Asibiti,Shuru ta Masa tana ji dole ya hakura zuciyarsa a cunkushe, Haka ya koma bangarensa ranar kwana yayi baiyi bacci ba ga rashin lafiyarta ta dameshi,gashi ya Mata laifi tana Fushi da shi ga sha'awarta ta dame shi,da safe 9am ya shigo bangarenta sai ji yayi ance ta tafi asibiti ma,Tsaki Yaja ya fili yace Wai me take nufi ne da wannan uban zuciyar tata,yarinya sai taurin kai zama yayi Yana jiran dawowarta tare da zuba Uban tagumi.
Chapter 84 · 0% Book details