← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 95

Sashe 41

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna mota Fuzail yace Annatu Tace ki shirya gobe gidan miji ko ba Taya,Manal Tace Amma Wasa kake? yace da gaske wallahi ko da kafar katako sai an kaiki Inshaallah jibi ma Kamar yanzu a cikin jinya kike kina ta kuka na Miki fata fata na hangoki Allah sarki ya fada da tausayi.

Manal tace ban yarda ba ko dangina ai Basu Zo ba,Fuzail yace muje gida kiga su Annatu wallahi sunzo da Yagwalgwal Dinku da Goggo mutum biyar nasa an dakko su,Dangin Malam Kuma mutum Uku harda Hajiya Sharifa,Manal Tace a Ina kasan wata Hajiya Sharifa Yar Uwar su Malam? Fuzail yace to a gidanta ma aka saukeni da naje,Allah kaje kauyen su Malam bayan na Annatu? Idan Yaya Yazed yazo ki tambayeshi Kuma su Malam ma sun dawo da Yazed yanzu suna gida idan Baki sani ba yarinya.

Manal sai Kuma ta fara kuka yanzu Dan Allah gobe za a kaini gidanku? Ko ba tayar mota ma cewar Fuzail,Manal jikinsa ta fada Wai ta Suma Tace na mutu kawai aje a fara Haka kabari na tawa ta Kare,Dariya Fuzail ya dinga Yi yace wallahi nasan sai kinji a jikinki Dole ne,Da kyar Abban Ameer fa ya shawo Kan Memartaba,a Haka ma Ummi Bata San za a kawoki gobe ba,Amma Ameer yau zai fada Mata da dare,Kuma Tace ko an kawo ki Ma'aikata zata zuba a part dinki da part Dina Bamu Isa munyi wani Abu ba za a sanar da ita,tsaro za a bamu sosai Wai baza mu kwana tare ba.

Manal Tace ga shawara,Ina jinki,Kawai ka koma ka Tara Family dinka kaf kace dama ba so na kakeyi ba Wani rashin mutunci na maka shi yasa ka aure ni Dan ka nuna min iyakata,ka tsarasu yanda kowa zai tabbatar ba son juna mukeyi ba kaga za a Dan rage Mana masu tsaron idan Muka hadu a boye muyi hirarmu,Idan da mutane a wajen tsakaninmu gaba ce Kawai ko ya kace? Idan anyi hakan zaiyi Kuwa? Manal tace sosai ma kuyi shawara da Ameer kaji.

Dan iskancin Manal sun Gama hirarsu Amma suna sauketa a gida da kuka ta shiga da uniform dinta,Da Yazed suka ci Karo yace ke Kuma lafiya? Wai gobe za a kaini? Sosai ma an Gama komai ma dazu ma Mijinki ya turo Driver da wasu Bayi sun tafi da duk wasu kayanki Annatu ta hada musu Wanda kika ware tun Ana biki kika Ce da su Zaki tafi,sauran idan kin shiga ku karasa da su,Kuma an kawo lefenki Maman Ameer da wasu matan Suka kawo ki je ki gani daki Guda abin yayi yawa,Ga su Farida can Kuma suna ta zage zage karki kulasu.

Manal iya lefenta data gani sai da ta tsorata akwatuna sun Kai talatin Banda wasu jakankuna,gaba Daya kayan Wanda ya shafi English wears,Inners,Arabian,Indian, cosmetics Dukkansu a turai Fuzail yayi Order,Kayanmu laces,Shadda,atamfofi da wasu materials kadan sune Kawai aka siya a Nan,mutane sai turuwar kallon lefen ake zuwa ana dauka a waya,ganin za ayi surutu Annatu ta kulle dakin a daren Tace Fuzail ya turo a kwashe kayan a kaisu gidan Manal,ai Kuwa Manal tana kuka tana Kara hada abin bukatunta aka tafi da su,Malam ma yayi gara ta gani ta fada.

Shukrah tana gaba da ita ake komai Kuma Amarya sai da aka sake gyarata komai anyishi Dake akwai kudi,kayan kamshi na musamman duk Shukrah ta karbi kudi Hannun Fuzail anyiwa Manal,washe Gari Kuma Haka taje school har Islamiyya Tanko ne shi Daya ya kaita ba Angon,Tana dawowa abinci Kawai taci sai wanka,Sabon Wani shegen White and Golden lace aka Bata ta Sanya Riga da zani irin na Amare dinkin Fuzail ne ya Aiko da shi na musamman,kyan da Manal tayi ya baci,Me makeup ce ta Mata sama sama me kyau har daurin tayi Mata me kyau,ta ko Ina Manal kamshi takeyi.

Takalmin da jaka tare da Mayafin Golden,Dama tayi Alwala nafila tayi tare da Adduointa sosai,Shukrah Kuwa wata Shadda ta Sha dark purple ta zuba kyau ta Sha makeup,su Annatu Kuwa gaba daya dangin uwa Dana uba daga karkara suke ko wacce a hargitse Kamar korarru a Haka Kuma sun Sha gayu,Hajiya Sharifa ce ma ta Dan fita daban cikinsu.

Malam ne ya shigo da kafafunsa sauki Yana ta samuwa sosai yayiwa Manal Nasiha,Haka Annatu da Dangi,Hajiya Kuwa lekowa tayi tace to dai Kar aje aga an shiga daula a dinga cin mutuncin Yan gida sakinki za ayi ato,Harara Malam ya galla mata ta juya ta tafi,Farida Kuwa sabo da bakin ciki barin gidan ma tayi gaba Daya Dan Kar Malam yace ta shirya a Kai amarya da ita.

Su Falaqi Kuwa da su Masatura Dukkansu Yazed ya musu dinki matan su Uku atamfarsu me tsada ta Sha dinki gasu dama da iyayi musamman Masatura data Fara Zama Budurwa 14yrs,Su da su za aje rakiyar Amarya.
Falaqi Dan yaro Tasha shaddarsa yayi kyau shi Yana da haske ma,Yace Allah yasa yanzu Malam Yana da kudi da Sanda bashi da kudi ne Allah Aunty Manal zanbi na koma gidanta a sa min gadona kusa da nata,Dariya aka dinga yi,Oga Yazed ma fadansa daban yayiwa Manal,Manal sai kuka akeyi Kamar zata mutu,Yazed yace kinji na fada Miki bana son kawo Kara,babu yaji,Banda Raina Iyayen Miji da Yan Uwan miji duk da nasan Baki da matsala,Banda kawaye barkatai a kwashe sirri Ana fada musu.

Kwata kwata mutanen da zasu raka Amarya ba Sufi mutum goma ba Amma sai da Fuzail yasa aka kawo mota Guda ashirin Kamar za a dauki Yar Shugaban kasa,kowa motarsa shi kadai ya shiga har Falaqi zaba yayi tasa Guda ya kame a baya,ga securities ga Dogarai da Kuma wasu suna binsu a dokuna Wai Dole sai an San Yarima ne yayi aure, Mutane sun Sha kallo yau,Duk abinda akeyi akan idon Yahaya Wanda ya cewa Fuzail shege ya zagi Babansa a Idonsa.

Yahaya yace shi yasa aka ce mutum ya kiyayi bakinsa baka San waye mutum ba,wasu ko a motar haya ne su saki Baki suyi ta gulma ko a dinga zagin wasu baza a Fadi Alkhairi ba,Yahaya yace yanzu da Dan mafiya nayiwa Haka sai dai cikin dare su biyo bayana su Gama Dani,duk inda Yahaya yasan zai iya ganin Fuzail ya daina zuwa wajen ko da yawo Bai rabar gidan su Farida Kar ma a samu matsala su hadu da Fuzail yaji kunya,shi Kuwa Fuzail Yana sane da Yahaya matsalar Aurensa ce tasa Bai Neme shi ba.

Kaf gidan sarki mamakin irin gangamin da Fuzail yayi suke Yi sai da kowa yazo kallo,wasu ta saman windows Suka leko,iyalan sarki sai tabe Baki sukayi ba Wanda ya sauraresu,Yan Mata da samari ne na gidan Yaran sarki Suka zo wajen suna ta Isa da gadara sai Suka ga Yan kawo Amarya Yan kadan kowa Kuma shi Daya a mota suna ta Fitowa,Duk Yan Kauye Shukrah da su Alhaqatu ne Kawai Yan gayu sune da an gansu an San sun kandami ruwan birni, Gaba Daya har su Shukrah sai da suka Raina kansu ganin irin tsaruwar gidan da suturun da suke jikin Yaran sarki Kai ma'aikatan gidan ma wasu sunfi su Haduwa sabo Yaran sarki Indai zaka Yi Aiki a karkashinsu to fa kaima sai ka Zama Dan gayu basa harka da kazami kidahumi,idan kaga wani gara to Yan aikin tsakar gida ne,Amma duk na bangaren iyalan sarki daban Duke na musamman ne sai ka rantse ma ba Yan Aiki bane, part dai gashi nan iya kallonka kala kala,Tanko ma Dan suna daga cikin Yan bakin gate ne shi yasa suke abinda suka ga dama.

Ameer Wanda Amarya ke motarsa tare da Dahara shi ya Nuna part din Amaryar Fuzail,a wajen dama Suka Yi parking, Hajiya Sharifa tace mun Higesu yau mu Hikenan yauhe ne za a tsaya Ana kallonmu Ana Mana wulakanci Ana tabe Mana Baki He kace anga wasu dabbobin daji, Dahara Kuma Yar Fulani kauyen Su Annatu Yan Fulani Basu cika yin Hi da Hya ba,Tace yau mun Boni Kam aradu Ina zamu duru,dakin kwanan Amarya ba a nuna Mana ba bore a Bamu ko funkasau ne mu shi,su Shukrah Yan kawo Amarya sune Suka sheke da dariya sun San tasu ta Kare Kawai,Masatura ta gallawa Hajiya Sharifa Harara Wai ta kwafsa musu gashi Taki daina magana sai surutu takeyi tana ta Maganar kauye.

Iyalan sarki Yan Mata Yan iyayi su Na'ima da samari matasa su a Dole Gadara basa Dariya anyhow ko murmushi Basu Yi ba,jira Kawai suke suga Kalar Amaryar Dake mota,Ameer ne ya musu magana yace Wai Ina ta nuna muku part din Amaryar Kun tsaya ga wajen Nan a bakin part dinta kuke.

Hajiya Sharifa tace ahayeeeeee Ayyiriririri Masatura tsagera ce harda rawa Ana Guda tana Murguda duwawu yeeeee Allah ya kawo mu Amarya Zama daram Ina Dangin Miji kuzo kuga Amarya wacce duk gidan Nan babu kamarta Fuzail yayi sa'a,ya Dace shi yayi Dace ya tsallake rijiya da baya wallahi yeeeeeeeeee Sa'iha itama ta fara shewa tabi Mastura suna Murguda duwawu, Falaqi kamar Babba yace Anty Sa'iha muyi rawarmu da Muka Saba ya juwa duwawunsa Sa'iha ma ta juyo nata Suka hada Suka yi gware da Duwawun juna,Falaqi yace Aunty Me Zamani ce wallahi Yeeeeeeeeee Wai Dan yaji Manal ta fadawa Farida ita me zamani ce.
Chapter 41 · 0% Book details