Sashe 17
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana Gama dressing Masa Farooq ya maida rigarsa sannan ya mike tare da daukan kayansa na gwanjo kala biyu da aka siyo musu Suka ce mutumin Nan ne ya Basu Sadaka, Manal tace muje ko? Kai ya daga da Izza,Suna Fitowa Manal tace tsaya,cak ya tsaya Tace masifa Zan maka to na fada maka ka daina wannan Izzar, murmushi yayi kadan idan baka kula ba baza ka Gane murmushi yayi ba,Oh ba Haka ake murmushi ba yaye bakinka zaka Yi sosai kalla Haka ta gwada Masa tare da washe bakinta Tace Haka fa,Yi na gani Dariya ce ta kamashi ai Kuwa ya washe Dan karamin bakin sa,Manal tace kaga Baki Kamar kurtun Limamin rugar mu da yake dura kakin majina a ciki,yaji abinda tace yace zagina ko?Da sauri Manal ta furta no Ina nufin bakin me kyau, kyau? Ya tambaya tace ae,Okay yace Suka tafi,Napep Suka shiga zuwa gida,Ana zuwa Ta biya kudin sannan Suka shiga gidan.
Suna shiga gidan Farida da Hajiya sun tanaji ruwa botiki Guda ai Kawai sai ruwan Suka juye shi a jikin Farooq gaba Daya,Hajiya tazo ta zuba Masa Rankwashi a Uwar sumarsa me yawa,sabo da tarin Sumar Bai ma San ta rankwashe shi ba,yaga dai gilmawar Hannunta ta saman Kansa, kunnensa Zaki murde Dan matsiyata kwarto cewar Farida,Hajiya ta Kama Kunnen Farooq ta murde da karfi ya saki kara,Manal ta fashe da kuka tayi kukan Kura ta Kama fatar gadon bayan Hajiya tare da gartsa Mata uban cizo,ai Hajiya ihu ta saki ba shiri ta saki Farooq,kunnensa yayi wani ja,Manal ta kalle su Tace wallahi wulakanta Dan Adam babu Dadi a rayuwa Ina ruwanku da shi? Farida ta kalli Farooq Ido da Ido ta shiga dura Masa ashar ta uwa ta uba,Dan Bur....Dan bura..gidan Ubanka ne? Ai na tsaneka tunda har kayi sanadin da na kasa ganin masoyina har yayi tafiya sai ka bar gidan Nan tsinannen banza,Hajiya tace wallahi yau bazai kwana a gidan Nan ba,idan wani kwarton Zaki kawo Manal ki kawo kuyi ta kwana wallahi mu zamu rufa Miki asiri Amma Banda wannan algungumin Yana yawo da shegiyar Suma ga kasumba Kamar liman,me ci da addini Kawai Allah ya tsine maka Albarka tunda ka Hana yarinya ta haduwa da arzikinta Dan Iska mazinacin banza.
Wallahi Manal bazai kwana a gidan Nan ba wannan in Banda wari ma me zaiyi ke ko kunya bakya ji kalleki kyakyawa ai kinfi karfin talaka Manal,ke matar manya ce,kina so ki jefa rayuwarki a wani sabon talaucin cewar Farida,Hajiya Tace in Banda masifa gamu talakawa ki kwaso wani talakan again.
Hajiya tabarya ta dakko tace gidan Nan ba asibiti bane ya bar gidan Nan ko na rushe Masa Kai ko Kuma wallahi yau na Tara muku mutane a watsaku a Internet,Manal tasan Hajiya zata iya aikata komai tace ba sai kinyi Haka ba zamu tafi Zan bishi sai Sanda Suka samu wajen Zama kullum zan dinga zuwa inda suke Ina kula da su,idan Yaya ya dawo ki fada Masa nasan abinda zaku ce Kenan,ai dai baza ku Hana nayi musu girki na Kai musu ba,taimako ne sai nayi,Hajiya tace munji Amma ba a gidan Nan ba,ya Gama cutar mu zaizo ya tare Mana a gida bazai yuwu ba,Manal tace muje Farooq.
Hajiya da Farida tare da su Sa'iha suka rike Baki da mamakin Manal su duk abinda suke Mata hange talaka ta kula,Masatura Tace tab ko asiri ya Mata ne? Suna kallo Manal ta fito da wata Leda Viva da kayan Fuzail da komai na bukata sai da ta dakko,Farooq Yana tsaye a jike sharkaf da ruwa yayi mutuwar tsaye,ransa Bai taba baci ba irin yau,wani zazzabi ma yake ji,Manal tana Fitowa da hawayenta sai kace Kanin ubanta ta Furta muje Suka juya da komai nasa har kayan gwanjo Dake Leda ta dauki musu komai suka fice.
Direct wani layi Suka nufa me nisa da layinsu Wanda shi layin ma sabuwar Unguwa ce babu gidaje da yawa,Wajen wani Dattijo Wanda take cefane a Wajensa ta karasa,Baba ya washe Baki Yana 'yata Ina zuwa Haka? Manal ta fashe da kuka tace Baba wannan Mijina ne yazo daga rugar mu,kasan Yan Fulani mu da wuri ake Mana aure,nazo birni wajen Yaya na,to yayi tafiya kishiyar Mamata ta Hana Mijina Zama kalli yanda ta kwara Masa ruwa,Kuma bashi da lafiya kalli bayansa Manal ta kwaye rigar Farooq Tace kalli Baba a hanyarsa ta tahowa sukayi hatsari,ka taimaka ka Bamu wajen Zama zuwa kwana Uku ko hudu zasu tafi kauye,Baba ganin Manal Bata da Wasa sai ya yarda da zancenta ya tausaya yace na yarda dake Yata,akwai gidan babban Dana Daya Gina sabo ne Amma ba a Gama ginin ba zaiyi aure amma baya Nan ya Yi tafiya sai watan gaba zai dawo ki Shiga Ciki ku zauna kafin ya dawo,Amma fa Kamar kango yake, sannan nayi alkawari kullum kizo gidana ki daukar masa abinci safe,rana da dare,Manal ta dinga godiya,Fuzail ma Haka harda Addua,Dattijon yace muje na nuna muku gidan,Yana gaba suna binsa.
Suna zuwa Suka ga gida an Gama komai har plasta an sa kofofi ma Amma duk ba a sa wasu abin ba babu paint,Baba yasa key tare da Bude musu gidan,Suka Shiga Ciki har tiles anyi ga pampo da ruwa toilet ma an Gama komai me kyau da ita,Baba yace har toilet gata Nan Ana amfani da ita,Fuzail yaji Dadi dama Bai kaunar ta gidan su Manal ko kadan suna ta godiya Baba yace da zuciya Daya na Baku da Kuma yakinin cewar mijinki ne,idan har ba mijinki bane wani Abu ya Shiga tsakaninku kin cuci kanki,kuji tsoron Allah mace da Namiji basa kebewa face na ukunsu Shedan ne,bazan tsananta Bincike ba amma aji tsoron Allah, karki biyewa zuciya, Manal tace Inshaallah ai ba kwana zanyi tare da shi ba abinci Kawai Zan dinga Kai Masa Ina Taya shi Hira amma kafin Magriba ma Ina gidanmu, to Madalla Me kayan Miya ya furta.
Baba Yana tafiya Manal ta fito da kayan gwanjo da sauri ta gansu da kyansu ba laifi kala Daya ta bashi dogon wando arsh da Riga me gajeren hannu red,Daya dakin ta koma Wanda ba komai a ciki sai tiles,Shima inda yake ba komai sai tiles,toilet din ya Shiga da Sabulun data dakko yayi wanka komai Yana Yi na toilet din gata sabuwa gal fes,yau sai da ya Dade kafin ya fito fes cikin sabon kayan gwanjonsa yayi kyau sosai,Abincin ya dauka ya fita dakinta zai kirata yaji itama a toilet dake room dinta tana wanka,mamaki yayi tana wanka Kuma ita da zata koma gida,Bai San Manal sabo da tana period tayi staining shi yasa tayi wankan Dole Kar ta fita a Haka.
Itama cikin shiri ta fito ta ganshi a dakin da ta shige bayinsa a tsaye gashinta ya kalla me uban tsayi Wanda yasha ruwa Bai bushe ba Amma ta tsane shi,sai tayi Masa kyau ya Shiga kallonta itama Kallonsa takeyi yayi kyau sosai,sai da suka dauki lokaci me tsawo a Haka sannan Ya dawo Hayyacinsa tare da Furta Abincin?Yana Nuna Mata ledojin hannunsa,Zama tayi a saman tiles Tace kayi Sallar la'asar? Yace ae nayi yanzu abincin ta Bude Masa Tace wanne zaka ci a ciki? Ya kalleta Kawai sannan ya nuna yace all duka, Tace to muci ta Mika Masa spoon na Roba itama da nata duk a take away din aka Sako Mata, pounded Yam Suka Fara cinyewa sannan Fried rice din,Nama daya ne ya rage a karshe ya dauka ya saka Rabi a tsakanin hakoransa Rabi Yana daga waje ya nunawa Manal Wai ta gutsira,Manal Bata san mene hakan ba,Tace cinye na barmaka tana kallonsa a kunyace,cinyewa yayi sannan yasha pure water tare da kuskure bakinsa.
Paracetamol ta bashi ya Sha da sauran Magungunansa sannan ya fara lumshe Ido zaiyi bacci,dakin da yake a matsayin nasa ta Shiga tare da shimfida Masa wani zaninta kasancewar babu ko Tabarma a ciki,Tace jeka kwanta,ba musu sabo da bacci yake ji Haka ya kwanta a saman zaninta ta lulluba Masa wani zaninta .
Itama Manal dakinta ta koma ba ko Shimfida ta kwanta sai bacci suka dinga bacci sai Magriba Suka tashi,Sallah ya Gabatar Manal Kuwa ta zauna tayi Shuru a dakinta tana ta mamakin kanta me yasa taji wannan bawan Allah ya kwanta Mata ne,me yasa Idan tana tare da shi take jinta ta Zama safe,me yasa Idan tana tare da shi ta Kan tsinci kanta cikin tsananin farin ciki marar misaltuwa bayan tasan bashi da komai Bai da kowa Bai da wajen ajiyeta,jinsa takeyi har jininta.
Har bayan Sallar Isha tana wannan tunani shi har yayi Sallah ma tuni,Fitowa Manal tayi tare da lekawa dakinsa Tace muje gidan Baba me kayan Miya Nan ne kusa na karbo abinci,Fuzail Wanda Manal ta sani da Farooq mikewa yayi suka fita tare Yana me murmushi,a Kofar gidan ya tsaya Yana jiranta Baba Yana gida Manal ta shiga Bayan sun gaisa da matar Baba da shi Baban,Baba yace laraba zubo Mata Tuwon ta tafi da shi,Laraba ta Mike ta dakko flasks shake da Tuwon shinkafa Miyar kubewa Danya da kifi ta bawa Manal,Manal tayi godiya ta tafi.
Can suka koma gidan Fuzail yace yunwa yake ji sannan Suka ci Tuwon tare a kwano Daya,suna Dan Hira Sama sama har Manal tare da Yi Masa Sallama tace Zan tafi gida to dare yanayi,Kamar zaiyi kuka shi Bai so ta tafi gashi Bai Saba ba tsoro ma yake ji shi,har Kofar gida ya rakota yace Good Night,Murmushi tayi tare da furta ka kulle ko Ina kaji gobe da wuri zanzo,da sauri yace karfe Nawa? Dariya ya Bata duk ya damu tace karfe Tara na safe,No 8am please, Kallonsa take Yi Kawai yace I mean Takwar,Dariya Manal tayi ba shiri tare da gyara Masa takwas ba takwar ba, Allah ya kaimu Kuma ta juya ta tafi gidansu.
Sharhi fans pls
AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭
MAFARKIN FARIDA IS DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA GP
21-25
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Hajiya Khausar
Uktee
Fulani gal ce
Bamalli ce
Jiddah
Hajiya Abou
Hafsat Bako Maibeza
Teema's collection
Mmn Waheeda
Aisha Fulani Gal
Hadiza Mukhtar
Meerah
Rahmatu Kunde
Rukayyatu
Bilkisu