← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 95

Sashe 72

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Mota Uche ya rakasu suka tafi suna dagawa juna Hannu,Belloti da Amaryar sa Ana bayan Mota,tafiya tayi tafiya Farida ta kwantar da kanta a kafadar Belloti tana ta bacci, sai da Suka shiga garin Bauchi Belloti ya fita ya siyo musu wani Naman rago gasashe da ruwa da yogurt har driver din nasa daban,Suka ci suka koshi a motar,a Haka har suka dauki Hanyar rugar me shegen nisa Kamar ba a duniya suke ba,Farida ta kalli Belloti Tace sannunku kunyi kokari kowa da inda Allah ya ajiye shi,Murmushi yayi kawai har Suka karasa garin Farida taga gidajen Basu fi Guda Hamsim ba,Tace Lallai Manal ta waye da wuri idan Haka ne to Kuwa ba karamar basira Allah ya Mata ba,kaima Haka my Husband,kalli ikon Allah Wai kana Nan garin a wannan nisan amma har Allah ya kawoka garinmu ka aure Ni,lallai Mijin Aure daban yake,wanda baka taba zato ba Ashe duk wannan haukar da nake kana Nan kauyen ma tuni,da ace a lokacin za a fada min bazan yarda ba Amma gashi ya faru,Belloti yayi Dariyarsa me kyau abinka da Dan Fulani me kyau ga Hanci,Yace Allah kenan ai Allah ba abin Wasa bane abinda ko a mafarki baka zata ba shike faruwa,Farida Tace ko a mafarkina na jaraba ban taba ganinka ba ko me Kama da kai,Suna karasawa kusa da gidan su Belloti Suka hango wasu lafiyayyun motoci Guda biyu da securities tare da Dogarai,Belloti yace ga kanwarki Nan Maybe Manal,Wannan da Alama da mijinta suka zo,Farida gabanta ya Fadi,Belloti yace ki daina damun kanki kina daukarwa kanki karya Farcy,ba a daka ta Dan Adam a rayuwa,idan ka biyewa Dan Adam to a rayuwa ba abinda zaka iya yi,Ki saki ranki,Farida tayi murmushi tare da Furta ba damuwa wancen ne kenan gidan Annatu? Yace yes shine Mana,kannen Belloti Yan Mata da maza ne Suka fito suna ihun murna da oyoyo,Nan take Belloti yasa suka kwashe kayan kaf tare da shigewa cikin gidan da su,gidan su Belloti na Bulon Siminti ne,su biyu ne gida na bulon Siminti kaf garin,Bayan Belloti ya sallami Me Golf ya tafi,Farida Tace to Manal dinfa ya kamata na ganta Kar na tafi Bamu hadu ba,Farida so take Kawai taga wani na gidansu ko zata ji sanyi a ranta,Yan kauyen sai kallonta sukeyi sunga Yar gayu,Ganin ta damu yace Kira Manal din a waya kiji ko da ita aka zo,Farida ta Kira Manal Wayar Bata shiga ba sabo da karancin network,Belloti yace Naga kin damu Jeki gidan Ina jiranki a gidanmu sai kin dawo,Farida da shagwaba Tace Kai da kake Dan gari muje tare,Haka Suka jera suka tafi gidan Annatu.

Farida ce ta gyara handbag dinta tare da shiga gidan da sallama Belloti yace Ina jiranki a waje,Sallama tayi a gidan tunda taga wani shegen chogen takalmi me tsada tasan Manal ce ma,shiga tayi kusa da dakin,can ciki taji dariyar Manal suna magana ko da waye oho sai lokacin ta tuna taga takalman Fuzail masu tsada,ga kamshinsa ya cika ko ina na gidan,Gadon Annatu Me Spring ne yake Lilo Yana Kara kiiii...kiii....Manal tana ta dariya tana cewa prince da zafi fa kaji yanda ka sake Ni a saman bed na fada ka manta da Babynka,Farida ce da masifa tace Wai su waye ne suke dariye dariye Ana Sallama baza su amsa ba sabo da soyayya Haba,Manal tana daga ciki Tace ya naji kamar Aunty Farida kaji muryar prince,Shigo cewar Fuzail Yana Rufewa Manal cikinta da rigarta da ya janye Yana Mata Chakulkuli,Farida ta shiga,Manal ta Mike tsaye Tace laaaaa Aunty Farida yaushe kika Zo? Me ya kawoki kauyen Nan? Farida ta kalli Manal Tace uhm su Manal Wato dai an Zama mayyar miji Allah ya shiryeki yanzu har bedroom din Annatu? Tana Ina? Bata Nan sai anjima zata dawo ita Muke jira Bamu Dade da zuwa ba da Yamma zamu tafi,Farida ta Furta Uhm I can see,to kin manta garin Nan surukai na suke? Manal tace na tuna fa kinzo gaisar da su,yaushe zaku koma? Zanzo gidanki? Farida Tace to munafuka ba yanzu Zan koma gida ba sai na Saba da surukai na sunji dumi na,Dariya ma ta bawa Fuzail,Farida tace Kanina ya gida ya aiki? Bata taba gaisar da shi ba sai yau,Wai kaninta ta ma,Fuzail yace Aunty Lafiya nake,Farida Tace na gani ai,ka daina biyewa Yarinyar Nan wlh tasa kana ta rashin ta Ido a gadon Suruka tam,Fuzail dai Bai ce komai ba,Farida tace Manal Zan tafi gidanmu Zan na zuwa ai Muna gaisawa da Annatu kafin mu tafi,Manal tace hakan yayi zanzo Nima muyi Sallama, Alright Farida ta juya zata tafi,Manal Tace Aunty kinyi kyau wallahi sai kiba kike Yi, to ya na iya komai zam zam ai ko ya kika ce? ,Manal ta Kama Dariya tace Aunty kina Jin Dadi,zanci uwarki nasan Gulmar da kike ta Yi kizo mu sa labile tunda kin matsu kiji in ba munafunci ba mace da mijinta kin damu da matar wani kije kema a Baki Mana ai gaki gashi Nan,Tashi Manal tayi ta biyo Farida har tsakar gida tana karewa Farida kallo tun daga sama har kasa tace Aunty ana harka...harka...harka.....Farida tayi Dariya tace zanyi maganinki ne kin San Halina wallahi kika sake agaban mijinki Zan Baki kunya,Zan fadi kalmar fitsara a gabansa kinga Zaki ji kunya yayarki tayi Maganar banza Gaban suruki kin San Halina Allah idan kina min irin wannan abin sai na Baki kunya,Manal Tace ance Miki kunyarsa nake ji yanzu Ni,Yaya Aunty Hope dai Bellotin akwai Aiki? Hand bag Farida ta kwadawa Manal suna dariya Farida tace Cucumber ai tayi ta fice abinta,Manal tana ta dariya Wai Cucumber.

Dawowa tayi wajen Fuzail Tace idan Annatu baza ta dawo ba mu tafi Dan Allah,akan me? Sai mu koma cikin garin Bauchi mu kwana a hotel gobe sai mu dawo, Fuzail yace sabo da me? Manal ta kwanta a jikinsa da shagwaba tace cucumber zaka bani,Fuzail yayi Dariya yace lallai Yarinyar nan to Ni tawa ba Cucumber bace Cassava ce,Manal ta fara Dariya harda rike ciki,yace karki kashe min yarona da dariyar masifarki,Jin sallamar Annatu sukayi da sauri Manal ta koma kasa saman Tabarma ta bar Fuzail a gefen bed sabo da daki Daya ne irin dakin kauye,Sannu da zuwa Annatu,Yawwa Ashe Kuna ta jirana cewar Annatu tana shigowa sai kunyar Surukinta take ji,a kasa ya zube tare da kwasar gaisuwa ta amsa da fara'a Nan take ta hada musu Fura lafiyayya Anna Ina su Khairan ne?Suna gidan Kakarsu tun jiya,Yaran Ni ban San ya za a saka su a school ba wannan ta kauyen ta Gomnati ce,ko Birni zamu koma da ku? Annatu ta Bude Baki tare da furta Allah ya kiyaye kin San dai ba zaman kaina nake ba,Mijin Annatu ne ya dawo daga Gona ya Iske Ana zancen yace na tafi na barwar wa duk tarin shanu na da sauran kadaronina,Fuzail ne yace to shike Nan Zan samu ayi sabon gidan a Nan din a canja ginin gida,Mijin Annatu ya washe Baki Yana godiya,Annatu ta kalle shi kawai ta tuna Sanda yake dukan Manal Bata Masa komai ba,tace Allah me iko yau Albarkacin Manal zaka ci Kuma,ba irin duka da zagin da baka Mata ba iya yaranka sune mutane to gashi yau arzikin Manal zaka fara ci Wanda ma ba a San iyakacinsa ba sai Allah,Mijin Annatu jikinsa yayi sanyi yace Manal ki yafe min,Kaga rayuwa shi yasa akace da na kowa ne baka San me Jin kanka ba Akan Mahaifiyarki na samu Yara ki yafe min.

Baki Annatu ta tabe Masa tace da Bata yafe ba ai da baza ta bar mijinta ya taimaka maka ba,Manal tace Saudiya Annatu Inshaallah Zaku Yi aikin Hajji Yarima ya biya,Murna Kan murna suka dinga Murna,Manal tafi so su Annatu su koma birni sabo da karatun su Khairan amma ubansu bazai yarda ba sai dai Nan gaba idan sun girma sai suyi karatun a wajenta.

Fuzail yace Gama mu wuce Ummi Inshaallah kafin ta koma Brazil zata Zo ta gaisar da ke Annatu cewar Fuzail,Annatu tana mamaki tace Allah ya kaimu,Ya Riga Manal fita ya barsu suna zance na sirri irin tsakanin Uwa da Yarta,Annatu Tace Ina Dan Uwan naki? Manal tace Yaya Yazed tab ya fada Miki? Baki ga gidan da Malam yake Gina Masa ba na Alfarma wlh sai dai Yaya Bai da matar aure,Allah zai kawo Masa ta gari ne,Shukrah fa an saka bikinta da wani me kudi babban Custome shima da farko wajen Farida yazo ta Masa wulakanci a Hanya ya hadu da Shukrah,Allah kenan Farida anyi banzar yarinya amma tunda kika ga Haka dama can ba rabonta bane Allah yayi duk ciki ba majinta, Allah ya Basu zaman Lafiya da Bellon,Manal ta Furta Ameen ai zaki ga tazo tana garin Nan tazo gaisar da surukanta, Mashaallah cewar Anna,Rumaisa kawarta itama an kusa bikinta Wai Uk mijinta zai tafi da ita can zasu zauna Kuma Anna shima Saurayin Farida ne,Dariya Annatu tayi tace Allah ya kyauta shi Kuma Tanko bawan Allah fa? Yana Nan an Kai kudin Aurensa da wata yarinya Islaha Bata fini ba Baki ganta ba wlh kyakyawa me haske Kuma suna da rufin asiri sosai ba talakawa bane ta kusa Yin candy ma final Exam suke Yi,tana karewa za a daura auren Fuzail ne zaiyi komai,Annatu make manal tayi tace ban hanaki fadar sunan miji gatsal ba,mantawa nayi fa Anna,to tashi ki tafi Yana jiranki,kudi ta ajiyewa Annatu masu yawa Tace gashi inji Shi yace a Baki kayan abincin Kuma Wai na Baban su Khairan ne,Anna Tace to angode Ana ta dawainiya Haka Allah ya Kara Budi,Manal tace Amin ta yafa mayafin Abayarta me kyau da tsada Wata dark green ta fita.
Chapter 72 · 0% Book details