Sashe 47
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manal Fitowa tayi tana tafiya a nutse kanta a kasa,ji tayi an finciko Rigarta tana Juyawa taga wata Kuyanga ta washe Mata Baki tace Balkisa kin dawo? ai sai yanzu kika dawo daga wajen Da'awar Taki ta Yan Izala? Balkisa Ina gargadinki wallahi ki rage sa Nikaf din Nan jibi yanzu abun naki ya girmama yayi tsamari harda safa bakake kike sawa wallahi ki kuka da kanki Balkisa Kar labari ya Kai kunnen su Jakadiya zasu iya sanarwa sarki Kin Fara tafiya cikin gari Da'awa kina mace,Manal ta gyara Yar muryarta tace wallahi Sabon Malami Muka samu me zafi? Kuyanga ta jinjina Kai tace da anyi magana kice kunyi sabon Malam wallahi Balkisa ki kiyayi kanki,ke kadaice me addini dalla muje part din Ta Brazil ta samu Aiki,Gaban Manal ya yanke ya Fadi Jin part din Ummi za a jata,Duka Kuyangar ta dadawa Manal a gadon baya me shegen zafi Tace dalla Kamar Baki Sanni ba kawarki ce fa Sailuba ya kike min wani Kamar Baki Sanni ba,Manal hayyacinta ta dawo tace muje Kawai,Sailuba tace Balkisa lafiya Kuwa yau Anya? Ko dai haddar Hadisin ce Baki Kai dai dai ba? Manal tsoron Kar a kamata yasa ta fashe da kuka sosai,Sailuba ta tsaya tare da sakin Baki Tace yau me Zan gani me ya faru? Ko Fyade aka Miki ne?Manal ta girgiza Kai Wai a'a,to ko zaneku aka Yi yau a makaranta? Manal tace ae kawai,Baki Sailuba ta Bude tare da cewa da girmanku? Manal tace Wai sabon tsari aka kawo,Sailuba ta dinga dariya Tace maganinku kenan da nacin karatun bala'i Kun girma ma baza ku hakura ba,karatun Nan Kun samu na Sallah Dana zaman rayuwa ku hakura kunki ai sai kuyi ta Yi muje ta fisgi Hannun Manal suka tafi.
Suna dosar part din Ummi sai ga Balkisa ta asali ta fito itama Kuwa da Nikaf Amma ba safa gata tana da haske itama,Allah yasa Balkisa ta asali aka kwala Mata Kira ta juya da gudu,Sailuba tace a'a ya nake hango Kamar Balkisa Kuma? Da sauri Manal tace ba ita bace Yar uwata ce,Sailuba tayi Dariya tace na manta fa kina da kanwa ai wallahi Kowa Yana fada Kuna Kama da Saddiqa kanwarki,Manal Gaba Daya ta hada zufa a ranta Tace Wato a gidan Sarki babu kwashe kwashen da babu sabo da yawan mutane kowa kace sai a samu a gidan.
Suna shiga part din Ummi Suka ga komai nata na Larabawa ne a ciki ka rantse gidan Larabawa ka shiga dake balarabiyar ce.
Tana zaune ta warware gashinta har kusan Mazaunanta tana yatsina tace Zo ku gyara min gashina,Tsoro ya Kama Manal,Ummi ko kallonsu Bata Yi ba Tace Daya tazo ta wanke min kafa Daya ta gyara gashin kuyi sauri Shopping Zan fita na samu time tunda Yar Iskan Yarinyar can ta tafi school Allah ma yasa sai Nan da 3days zata dawo mutum ya samu yayi bacci a nutse.
Gashin Ummi Manal ta Kama tana Dariya a ranta Suruka da gyara gashin surukarta abin kunya,gashi da Ummi tasan Manal ce zata taba Mata gashi da taci ubanta Amma Ummi har da mikawa Manal Mai wani color Tace Fara shafa wannan,Manal ta ta zare Safar Hannunta ta karba ta fara shafe Kan Ummi tana taje shi a hankali harda wani lailaye Mata gefen goshinta,Ummi Tace kin iya gyara gashi ba irin wasu ba Rannan Kamar zasu tsige min fatar Kai,wata shegiya ma Kamar tana cire min kwarkwata Haka ta dinga min sai da nasa aka Zane shegiya daga yau ke Zaki dinga gyara min gashi,Zan dinga sawa Ana kiranki,Manal tayi murmushi cikin Nikaf Tace ba damuwa,Ummi Ashe tana surutu idan jininta ya hadu Dana mutum tace sai naji kin shiga Raina ko Dan kinyi shigar irin tamu ne ta Larabawa oho,Kin birgeni Haka ake son mace ta dinga suturta jikinta,Manal a ranta Tace sai kace ita suturta nata takeyi duk uban kwalliyar da take sha.
Mu a kasar mu Can Arab site bafa Brazil ba,Brazil Latin ne Business ya kaimu Ina fada Miki a bangaren Arab irin su Sa'audiyya Ummi harda wani kalkala,kin gane? Manal Tace ae to mu duk Haka muke shiga ba irin Nan ba a fito da kirji waje ba,Haka Zaki ga Mata da damatsa a waje wasu ma damatsan nasu ba kyan gani kamar na maza wahala da daukan kayan nauyi yasa duk sun Zama irin na maza Chaiiii Ummi ta furta tana yatsina,Sailuba tana ji tana ta faman wankin kafar Ummi,Ummi tana cewa shi yasa bana son Dana ya auro min Yar Nan,musamman Wanda Basu da kudi Kai sai suzo suna Kai maka sunan yaro wajen Malam sabo da suci kudinsa,Dan Matsiyata ba abin a jawo shi jiki bane,Bai iya cin arziki ba,Manal tace wasu ba,Amma wasu Zaki gansu masu hankali,Banda surukata da Fuzail ya kwaso min gidansu ba tarbiyya,ban so ma Dana ya fiye son mace sabo da zata kwace min Dana Ni Dana Sha wahalarsa,Manal tace uhm ai na hangota dazu ta fita,Baki Ummi ta tabe tare da furta ai na tsaneta Yarinyar da ganinta idan Dana yana Muamula da ita zai so ta da yawa ne ta kwace min yaro na,shi yasa bana hutawa banso suna haduwa Kar ma ya sota,Allah yasa ma ba sonta yake ba,Nan gaba zai sake ta kowa ya huta,Yana sakinta Zan tafi Brazil,yanzu lallabashi nake Yi ya saketa kawai da wuri sai na tafi.
Sailuba sabo da Neman gindin Zama harda cewa Nima Bata min ba Sam,ta fiye ji da Kai munje ganinta part dinta sai wani basarwa take ita a Dole matar Fuzail,tana da kyau amma dai hmm ta wani tabe Baki,Ummi tace kyau ba shine aure ba ai,ka auri mutum Dan kyau ai ba birgewa bane Matukar mutum baida Hali na kirki,Ni Kam koma tana da halin kirki ba ruwana bazan so ta ba,Manal mamaki takeyi Wai dama Haka Ummi ke da labari har ta kula Bayi suyi surutu Ashe dai ita take wulakantawa sabo da Bata kaunarta.
Bayan sun Gama zasu tafi Ummi ko Sannu babu Haka ta Mike tare da haurawa sama,Sailuba ta kalli Manal Tace matar Nan fa kamar me Aljanu Haka take Watarana kirki Watarana rashin mutunci muje Kawai,Manal Tace bana Jin Dadi tafiya zanyi Zan dawo fit ta fice ta bar Sailuba,tana Fitowa Nan ma wata Dattijuwa tace yawwa Balkisa tayani kaiwa Yarima Fuzail abinci sashensa Umminsa ce ta damu mutane a Kai Masa abinci kin gansu sunfi kala biyar Wai duk shi zai ci yau,Manal tayi Dariya a ranta tasan sabo da ita aka ce a kawo.
Wani Basket ta dauka Suka tafi da Dattijuwar tiryan tiryan amma jaraba kafin Manal su karasa Ummi ta fito ta wuce su ko gajiya kafafunta basa Yi da sintiri zuwa part din Fuzail
Manal suna shiga taga Angon nata sanye da 3qtr silver da Riga Armless fara,yayi mugun kyau Yana Zaune a nutse cikin kujera,Suna Shiga ya Gane Manal sabo da Safar da ya gani wata Designers shi ya siyo su da hannunsa, ta cikin glass ta kalle shi ta kyafta Masa Ido,Dattijuwar tuni tayi waje da sauri sabo da aikin Dake gabanta,Ummi ce ta shigo tana cewa zaka rakani Shopping din ne? No Ummi bazan iya fita ba yanzu na gaji,dama kin fada min a waya Kawai ba sai kin Zo ba,ki dinga hutawa Ummi,Manal mikewa tayi Kamar zata tafi a tsawace yace ke Baki Yi Serving Dina ba Zaki tafi,Ummi Tace Allah sarki tana da kirki itace Nasa yanzu ta gyara min gashi,Fuzail ya zaro Ido tare da furta wannan kazamar Yana Nuna Manal,Manal murmushi tayi a boye Wanda shi kadai ya gani,Ummi Zama tayi a palon ta juyawa Kofar kitchen Dake palon baya,Manal ganin sai Bayan Ummi take gani Fuzail Yana cewa Shiga kitchen ki kawo plate da cups,Ganin Ummi Bata kallonta Allah yasa kujerun Dole sai dai ka Juyawa Kofar kitchen baya,Manal tana ganin Haka ta juya tana tafiya ta dage Hijab din sama tana wani juya Mazaunai,Fuzail ya manta ya wani washe Baki har da yin dogon wuya,Ya kafe saitin Manal dake tafiya Yana kallon Hips,a gabansa Kuma suna facing juna da Umminsa.
Ummi Tace Kai Kuma lafiya? Me kake kallo kana dariya? Da sauri ya Bata Rai yace Allah wancen ac din na kalla Kawai tana birgeni Ummi Ac tayi a rayuwa Allah yayi wata baiwa a can, na tuna wani bakauye da yaji sanyin ac shima yace Ras dani,Murmushi Ummi tayi Tace ai mutanen Kauye sai su, amma sai kace wani abin kirki wacce Kalar ac ce baka gani ba sai wannan ko matar taka ta fara koya maka kauyancinta ne? Fuzail ko Maganar Ummi baya saurara yace Uhmmm Kawai yana daga Kai sama Yana hango Manal.
Manal tana shiga kitchen sai ta tsaya a bakin Kofar ta juyo suna kallon juna da Fuzail girgiza tayi tana Dariya marar sauti yanda sai Wanda ya kalleta shi zai gani,Fuzail Yana kallo ya Sosa Kansa sai ya jawo wayarsa yasa ta a flymode sannan ya Kama Wayar karya yanda Manal zata ji yace barni Haka Dan Allah kar muyi kaca kaca da Kai anjima,Ummi Tace Hala Ameer ne? Fuzail yace ae ai kin San sai shi,Manal ta tsaya sai magana take yiwa Fuzail da yatsu da hannalaye da Baki,plate ta dakko da komai ta sake tsayawa a Kofar kitchen ta fara tsalle tsalle yanda ba Wanda zaiji sautun kafarta,Fuzail Yana ta kokarin danne dariyarsa,nutsuwa tayi sannan tazo tayi Serving dinsa sannan Ummi tace ke muje ki dakko min Kaya a Mall,Fuzail da sauri yace da aikenta zamuyi Ni da Ameer ki tafi da wata,Ummi tana son danta ba musu Tace to ta tafi abinta zuciyarta wasai Manal ta tafi ta huta na wani lokaci.