← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 95

Sashe 42

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yara masu sa mutum dariyar da Bai shirya ba duk bala'i sai da su Na'ima Suka Yi dariyar Yaran,Shukrah ce ta budewa Amarya mota wacce ta lullube fuskarta ba a gani duk Nacin su Na'ima Basu gani ba Amma sunga Hannunta da kafafu Fara tassssss ce har ta zarta Fuzail haske su da suke Gadara fari ne.
Falaqi ya Saba da Zama cikin Mata yace Uncle Fuzail ya tsallake rijiyoyi da baya,ba Rijiya Daya ya tsallake ba,Masatura tace Yarima yayi Dace Allah yasa itama Haka Amaryar ta dace,Fatima ta kalli Naja'atu tare da cewa Yaran Nan fa Kamar Habaici suke Mana,Na'ima tace zata ci ubanta ne ku kyalesu amma fa farace kwalli sunan wata Unguwa a Kano,Ummi tana can ta kulle kanta tana ta kirsar kuka duk da Fuzail ya tarasu ya fada musu ba sonta yake ba shi fansa zai dauka su Maimartaba duk sun yarda yanda ya musu zancen shi da Ameer ba wasa,Abban Ameer Kuma ya Kara gishiri yace ai da shi aka shirya komai ma shi yasa irin wulakancin da Manal tayiwa Fuzail shine dalilin da yasa ya jajirce akan ya aureta ayi Mata hukunci dai dai da abinda ta shuka.

Dan wulakanci ba Wanda yaje tarbar Amare sai Maman Ameer Hajiya Safiya da Danginta ta gayyato manyan Mata su Biyar,sune Suka tarbi Amarya,Memartaba baya ma gari ya tafi England sabo da Auren Fuzail baya gabansa sai Nan da sati Daya zai dawo,Maman Ameer su dai da fara'a da mutuntuwa Suka tarbi Amarya da danginta aka sauki Baki da Abinci iri iri,dukkansu Har su Shukrah sun Zama Yan Kauye sai kalle kalle sukeyi a part din Manal,Basu taba gani gida me irin kayan alatun rayuwa ba Haka,komai na daban ne Kuma Fuzail ne ya kashe wannan kudin,komai na ciki White and sky blue,Part din sama da kasa ne,Sama 3bed room Palo har biyu Haka ma kasan sai katon kitchen na gaske da store ga dining side, Furniture na alfarmar gaske komai an Shiryawa Manal Kuma duk Hajiya Safiyya Maman Ameer itace ta jajirce,har kayan Manal ita aka kaiwa Suka je Suka shirya abin sabo da su Annatu cewa sukayi ba ruwansu Kar a wulakantasu, Su Maman Ameer tafiya su ma Suka Yi Suka bar Dangin Amarya kafin a kwashe su,Sai ga Kannen Fuzail Mata gaba dayansu Yan Mata zagada zagada da masu kyau da Munana da Yan tsaka Tsaki duk sun shigo suna wani Taku dai dai suna Iyayi zasu ga Amarya Dole.

Manal ganin ita Suka zo gani sai ta sake dukunkunewa ta dunkele cikin mayafinta,Sai kamshi suke kamar me,Na'ima ta shiga fisgar Mayafin Manal, su Hajiya Sharifa suna kallon ikon Allah,kowa ciki Kuma an rasa me musu magana gaba Daya ganin Na'ima ta kasa Fisge gyalen Suka hadu Dukkansu zasu fisge ta karfi suna wani wulakanci.

Masatura ta sagale Hannu Daya da yanga tare da canja muryar Yan gayu Tace Heeeyyyy chill....relax....why kuke Abu kamar villagers,what's your problem? Ai Kuwa cak Suka tsaya sai ga Ameer
Ameer ne yace ku fito mu tafi,tsayawa sukayi sabo da sun San Ameer zai fadawa Fuzail sai da ya fita,su Kuma su Masatura Suka Mike da Shukrah Suka ce sai munzo ganin daki,Su Hajiya Sharifa ma Tace gobe kafin mu koma garinmu Ina Jin ai Dole He mun Zo da Annatu ta ga dakinki,sauran Suma Suka ce Hike Nan Manal He da safe He munzo goben,Masatura Tace Kun ba damu wallahi ace bayin Allah ga hausa me kyau me Dadi baza ku iya fada ba Kai Allah ya sawwake Kun jaja mana wallahi.

Hajiya Sharifa tace Yau mun Higesu kaji min yarinya Dan Allah dan annabi to Yasin Baku Isa ba yauhe Za'a kalle mu ace ba dai dai muke magana ba yo ko Ubanki yauhe zai fada Mana haka,ko Hi Malam din ai Bai Isa ya fada Mana Haka ba,Dahara Tace ke rabu da ita fitsararriya Suka fice gaba Daya har Falaqi a cikin mata yace Aunty ki dafa min kaza idan nazo,Manal kuka ya kwace mata Cikin mayafinta me karfi,Dukkansu yanda aka kawosu Haka aka maida su gida Lafiya.

Suna ta bawa su Annatu da Yazed labari,Annatu tace kaddara ta fadawa Manal Dita Allah ya tsare,Yazed hankalinsa ya tashi tunda yaji abinda aka fara gani Amma ba yanda ya iya sai Addua.
Hajiya da Farida su sai Murna.

Ummi Kuwa tana can ta tashi cikin Fushi Jin labarin irin mutanen da Suka kawo Amarya bayin gidan Sarki sunzo sun Bata labari daga cikin wasu munafukan,Tashi tayi zaune tace ai nasan ma da gaske Fuzail bazai so wannan ba na yarda Kawai dama Aurota yayi dan ya dau fansa,ai na taba karanta irin labarin a wasu novels ma irinsa zaiyi sai dai kafin ya Kai ga fadawa sonta Zansa ya saketa da wuri baza a Dade ba,sai taji sanyi a ranta ta Mike ta koma part din fuzail,shigowarsa kenan ya ganta tana jiransa ya Salam ya furta a ransa,Yana zuwa tace an kawo Amaryar taka,Fuzail ya Bata Rai yace Dan Allah Ummi ki daina min zancenta ba kaunarta nake ba,dama Kawai Dan nayi maganinta ne sai na Gama daukan fansa Zan fada muku irin abinda ta min,Ummi tayi murmushin Jin Dadi tace ai dama na San Ni Dana na daban ne,Fuzail yace ki zuba kuyangi ma su dinga kalle Miki abinda Zan dinga mata sabo da kiga zahiri,Ai ba sai ka fada ba tunda har yanzu ba yarda zanyi da Kai ba ko Ina a gidan Nan na saka cid na wallahi suna kalle min abinda zaka Yi,part dinta ma yanzu na tura wasu Kuma a Nan ma suna Nan,daga Nan kisa CCTV Mana Ummi,hauka nake ka Gama wayewa Zansa CCTV salon ka cireta ai gwara na zuba mutane Ina Nan a gidan Nan sai na ga kwal Uwar daka.

Daga Sanda Naga ka sake min karya Kawai Zan tsine ma ne, Dariya Fuzail yayi Yana Shan ruwan Roba yasan baza ta iya tsine masa ba ko me zaiyi a duniya kawai baya son bacin ran Iyayensa ne shi yasa yake binsu a Sannu Yana musu karya sabo da Kar hankalinsu ya tashi sanadiyarsa.
Wanka ya Shiga Yayinda Ummi duk ta baza mutanenta a dinga Sa mata Ido akan Fuzail da Manal,Ita tunaninta Farida ce Manal shi yasa ko ganinta Bata fatan yi,Dan Kawai Abban Ameer ya zuga sarki ne anfi karfinta ne gashi ba aurenta sarki yake ba bare ta samu power.
Su Na'ima ne Suka yiwa Manal taron dangi tare da fisge mayafinta Ido Suka zaro tare da Bude Baki gaba dayansu............

AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭

DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP.

51-55

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne masoyan asali

Miss Jalam
Hindu Moha
Maman Afrah
Aisha Usman
Mace ta gari
Sa'adatu A muhm(Hajiya)
Saulerwah
Mmn Teemah
Khaltum Zanna
Hauwa'u
Zainab Ali
Ummu Jafar
Mr Nazir
Maman Nusy
Mmn Waheeda
Alhamdulillah

Mamakin kyan da Allah ya Mata sukeyi yanda suka ganta Fara tassss Haka suka ga matsanancin kyanta ya zarta tunaninsu su a Haka ma a tunaninsu Basu taba ganin me kyan Manal ba sai dai ko a turai sun manta,Sai dai kowa ya ganta yaga yarinya Danya sharaf da ita,Manal mikewa tayi tsaye zata dakko Jakarta da Suka jefar Mata garin son kallonta,Tsayinta Suka gani da Kyawun Surarta ya Gama da su,Bata kulasu ba Suma Basu ce Mata kala ba Suka juya suka tafi cike da mamaki,Lokacin Kuma Cid na Ummi duk Suka zo part din Manal suna ta sintiri,Su Fatima suna fita labari Suka dinga watsawa na kyan amarya,aka dinga turuwar ganin Manal har ma'aikatan gidan,cikin Matan Sarki ma su ukun Suka shigo Ana take musu baya kuyangi,Suna shigowa da takama Manal ta zube a kasa tare da kwasar gaisuwa,suna ta kallonta Kamar mayu amma ba Wani Dan mutunci Suka fice Manal Baki ta bude tare da furta tab suna matan sarki ma baza su bada Umarni a Kai musu Amaryar har can ba sabo da gulma na Cinsu har da takowa da kansu, Manal Tace wannan gidan Sarautar nasu na daban ne ban San irin nasu Kalar ba.

Sai da kowa yazo na Mata sai maza Suka Fara Sallama Amma kanne Yan samarin,sunji Ana ta zancen kyan Amarya Suka zo ganewa idonsu,Mazan ma ba yabo ba fallasa gasu Nan dai amma gwara maza da matan a mutunci,itama Manal ganin kannen Fuzail ne duk da sun girmeta Taki gaishe su Kamar yanda tayiwa Yan matan su Na'ima,Ciki Daya yace ba gaisuwa? Manal Tace ai ku ya kamata ku kwashi gaisuwa wajen Auntynku, wani kallon Up and Down Suka yiwa Manal suna wani takama Suka fita abinsu,Hassan da Hussain ne Suka shigo karshe,wannan dama ba ruwansu Manal ta sansu da fara'a Suka ce Oyoyo Auntynmu,ita Manal mamaki ya kamata shigowa Kawai akeyi Abu ba sirri Haka,Su Hussain sun Dade suna Taya Manal Hira kafin su Mata Sallama tare da tafiya,Sai da kowa ya Gama zuwansa sannan ta huta da Baki su Kuma ma'aikatan suna waje da Cid na Ummi,Wasu kuyangi ne Suka shigo bayan sun gaisar da Manal suka ce ko akwai abinda Amarya take bukata? Manal tace Babu na gode kuje.
Bata Sa ran Fuzail zaizo ba yau tunda tasan halin da ake ciki Amma saman Bed ta koma ta zauna tana latsa wayarta,a Wayarta message ya shigo,Fuzail ne taga ya turo Mata Zan shigo fa karki Yi bacci.
Alright ta bashi amsa.

Ummi Taki barin part din Fuzail har ya sheko uban wanka tare da saka wata sabuwar jallabiyyarsa ruwan toka Yana kamshi ya fito,Yana son yayi gayu Amma yasan Ummi Dole ya fito Kamar ba Ango ba,Zama yayi tare da canja Chanel Ummi tace mu je wajen Amaryar tare tunda kace ba wancen bace Dana sani,Fuska ya Bata yace me Zan Mata ai ki Bari tayi sati Uku Bata ga ango ba ta fara Gane kurenta,Ni bana son ganinta ma,Ummi taji Dadi Tace muje dai Naga kiyayyar da Ido na.
Chapter 42 · 0% Book details