← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 95

Sashe 78

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bangaren Islaha Amarya kuwa yarinya ce shi yasa tunda aka Daura Auren take kukan rabuwa da gida,ta kasa sukuni Ana magana sai kuka,an kashe kudi Tasha makeup amma duk ta Bata kwalliyar da Hawaye,Koda angwaye suka zo da kyar Kawayenta Suka lallabata ta daina kukan,har Fuzail aka zo yaci Uwar gayu cikin Shadda ta Alfarma sai kace shine Angon ana ta kallonsa,Ameer ma Yana Nan gidan su Islaha,Islaha ana hoto Hawaye ya kwace Mata Ameer yayi Dariya yace lafiya? Tana shesheka Tace K...ka....ka...kakataaaaa....ta karasa da kuka,Tanko yace Haba an Isla Isla na....aka sheke da dariya, Suna Nan Maman Islaha tace ga Fried rice din angwaye a take away,Islaha tace how many times Zan na repeating wannan Maganar Mama tun kafin abin Nan nace Ni Jullof rice...Ni Jullof rice nake so ita Zan Basu sai kusa ayi min Fried rice sai kuka tana Allah Ni bana sonta bazan Basu ba baza suci ba,Angwaye suka Fara dariya Kamar me...

Fuzail yace tab wannan duk rikicin Manal gwara ita,a bamu Haka cewar Fuzail,Islaha tace Ni bazan Baku ba ai ba ita nayi Niyya ba sai dai ku koma gida haka,Tanko yace to idan anyi Alawar Madara a bamu mu raba,Harararsa tayi tace Ina Naga lokacin wata Alawar Madara Ni,sai dai idan an kawoni ka dinga auno Madara Ina Yi,Tanko harda biye Mata yace ko Dan Baki ma ai a dinga Yi su Sha,Islaha tace tab bazan samu riba ba sai dai nayiwa baki?
Mama ce Tace ku rabu da ita Bata ji,haka aka kawo musu take away dinsu Fried rice da Rabin kaza kowa ga ruwan Roba ga lemo,Islaha zuciya tayi an bawa Angwaye abinda ba shi take ra'ayin Basu ba ta juya ta shige daki taci gaba da kukanta Wai an tozartata, suna ji Kawayenta suna Dan Allah kiyi Hakuri sai kin Bamu kunya an Raina mu ance Mana yara yanda Muke ji da kanmu,Ki daina kukan Nan,Islaha Tace Jullof nace ayi min Ni Jullof Zan basu,to shike Nan sai muyi Jullof din da Rana a sake kai musu can ba shike Nan ba, sai lokacin ta daina kukan,Dariya ma ta basu anyi hotuna Suka tafi da take away din a mota,Na Ameer dama suna Abuja matan sai da Yamma za a kawota a jirgi.

Kawayen Islaha Jullof Suka Dora da kansu suka dinga Iyayi su a dole Yan mata garin Haka Suka cikawa girkin gishiri sai Almajirai ne Suka cinye.
Da Yamma Badiat Amaryar Ameer aka fara kawowa gidanta ita kadai a layin gidan Maimartaba, Ameer shima Bai son Zama cikin gidan yawa shi yasa Abbansa ya dankara Masa gidansa daban a layin.
Islaha Kuwa kazar Amare aka Kara Bata ta cinye da sauran Magunguna sannan tayi wanka tare da Sallar Nafeela tayi Adduointa,Gaf da Magriba aka kawo motoci da yawa,Islaha ta kalli Yan Uwa Yan biki tace ku tayani da Addua Dan Allahhh.....sai ta barke da kuka,Haka aka kawota sashenta me kyau su Manal suna wajenta har aka maida Yan Kai Amarya gidansu,Farida tace to Amarya sai hakuri da zaman aure,sannan Kuma yau wannan kukan zakiyi me dalili gwara ma ki daina anjima Zaki Yi babban kukan,Manal tace wallahi Kuwa yau Zaki ga Cucumber,Rahila Dariya tayi kawai,Manal ta dafa kafadar Rahila Tace karki damu Baki da matsala ke ta Yaya Banana ce baza ki Sha wahala ba,Farida tace wallahi Manal Baki da mutunci a Ina kika sani? ,Shukrah Tace a'uzu Manal wallahi Baki da mutunci Walida kawar Farida tace yo Nima sau nawa Ina ganin ta Yayana a wando wa yace su dinga yawo da gajerun wanduna a gida,suna ta dariya Rumaisa tace kunfi Karfina,Islaha tana jinsu Farida Harda cewa ko ta Angon naki mece oho.

Kin shiga Uku Yau Islaha Zaki Suma yau cewar Manal Haka suka dinga tsorata yarinya tana ta kuka,Suka koma gidan Badi'at Suka bar Islaha da Kawayenta mutum biyu,Badi'at ma Haka Suka dinga Mata badala,Manal tace ai Badi'at ke Biggi ce ke kin waye Yan Abuja Baku tsoron Cucumber sai harka,Badi'at Bata kuka ta kalli Manal Kawai tace Cucumber Ina Shanta a zobo Mana? Suka Fara dariya Farida tace wannan Kalar ai ta gagari Gwauruwa samunta,ai wacce kike nufi kowa na ci Gwauro da gwauruwa,Ameer dai ya Dade a kasa ba Mata kawai ki shirya Dan Allah Banda yanga, Badi'at tace ku dai kuka sani ke Manal Ina ganinki Shuru Shuru ta Allah Ashe ba Haka bane? Nasiha nake Miki Mene nayi Marar kyau? Fuzail ne ya Kira,Sai wurin 9pm Belloti yazo ya dauki Farida da Rahila,Shima a gidan su Farida aka Masa masauki,Suna dawowa ya shige masaukinsa ya gaji sosai,Yazed yana tsakar Gidan sanye da 3qtr da Riga t-shirt yayi kyau dama gashi Dan gayu,Farida ya kalla data shigo yace Sister Kun dawo? Mamaki ya kashe Farida Yazed Bai taba ce Mata wani Sister ba harda wani sa Mata sabon suna sabo da tazo Masa da Budurwa,Farida tace ae mun dawo Brother,ya sake cewa a gida kuka sauke kawar Taki? Farida tana Dariya a ranta tace ai a Nan zata kwana,Wani farin ciki ya Kama Yazed yace ai Kuwa gidan Nan Kamar lemo ya Kare Kuma su Afrah ne Suka Yi jagwalgwalonsu baza ki iya ci ba,Farida tace a ranta Yaya Ni za a yiwa wayo Wai baza ta iya ci ba yake nufi ba wata Farida ba.

Raheela ce ta shiga gidan a karshe tayi Sallama tace kin wani taho kin barni ga abinki kin manta to,Yazed sai satar kallonta yake yi,Raheela tace Sannu Yaya Yazed,Kallonta yayi kadan tare da Furta yawwa ya fara latsa wayarsa Wanda Bai ma San me yake dannawa ba,Raheela tace Aunty Farcy Bari nazo ki min massage na gaji ta furta tana shiga palon,Yazed a ransa yace Ina ma Ni zanyi tausar Dana girgije,fita yayi a motar Malam yaje ya samu kaza gashashiya Tasha hadi da su Ice cream tare da sauran kayan Sha ya dawo gida,Ko Belloti Bai bawa ba Kawai Farida ya kwalawa Kira ta fito sunyi Shirin bacci ya Mika Mata yace gashi Nan kici Kuma ke na siyawa yayi tafiyarsa,Raheela tana cikin Bedroom sunyi Shirin bacci taga nama, da sauri ta Mike zaune tace Kamar yasan yunwa nake ji Kai mun gode Dama bana sha'awar komai sai nama,Farida tace Nima haka amma kalli ya Mana yawa kaji har uku fa Bari mu dauki Daya mu bawa su Afrah Daya,sai Mijina Shima,Haka Suka Basu,Malam Kuwa ya Kai Masa tasa daban Yana kurmusu a dakinsa.

Da Sassafe Yazed harda zuwa kitchen da Kansa ya duba kayan tea komai akwai,kwai ne ya Kare ga su Afrah sun tafi school sai yaje da Kansa ya siyo da yawa,Raheela Kamar gidansu harda shigewa kitchen ta hada musu Breakfast,Yazed sai zirga zirga yake a wajen,tana gyara kitchen ya shigo ko kulata baiyi ba ya Bude fridge ya dauki ruwa zai fita tace Ina kwana Yaya,Lafiya Kawai yace yayi waje,ya sake dawowa ya dauki cup ya fice,Yana shigowa ya Iske Raheela ta zuba dankali a plate dinsa sabo da Yazed shi kayan cin Abincinsa ma na daban ne masu tsada yake siya,Ajiye min plate Dina yace tare da Mika Mata wani yace juye a Nan,Raheela tace Ni anan nake son ci,Gidanku ne to harda shigowa kitchen ki Mana girki Ina ruwanki,akan wannan plate din ta dauki wani ta juye Tace ga abinka nan tayi waje.

Suna karyawa Farida tace Yaya fa sonki yake yi ko Baki Fahimta ba? Raheela tace wannan masifaffen tunda nazo ya tsaneni Ni na fasa kwana biyun ma gida Zan tafi anjima,Farida tace ke wallahi sonki yakeyi sosai Yaya ko magana Bata hada shi da wasu,Shukrah ba irin son da Bata Nuna Masa ba amma kallo bata isheshi ba Haka Mata da yawa binsa suke kina ganinsa me Kama da Manal,Raheela a ranta Tace da Kuwa Na more a duniya Allah yasa ya kasance,a fili kuma tace dan Allah mu bar zancen Nan.
Da Yamma Yazed da Kansa yace Farida baza ki zaga gari bane kizo na kaiki a motar Malam ki Dana kiji,Farida tace zamuje gidan Manal sai ka kaimu, yawwa dama zanje wajenta ban taba zuwa gidan ba,Farida ta zaro Ido tace to Yaya.
Bangaren Amare Kuwa bayan kowa ya watse ya barsu Fuzail da masifa ya dawowa Manal tana kwance zata fara bacci yace Dan Iskanci Manal sai kuje ku zuga Amare,duk Kun tsorata su yanzu kinje kin jikawa Ameer Aiki Badi'at tana can tana kuka Tace kece Kika ce Mata da zafi zata Suma yau,Manal tace na shiga Uku Ni din yaushe? Karki sake Bata min rai ai gasu can ta kulle kofarta da key ta Hana Ameer shiga yanzu ya min waya.
Manal Tace da Dadi fa nace mata Prince,Tsaki Yaja yace sai ki tashi kije lallai duk yanda zaki Yi kisa ta Bude kofa muje Fuzail ya tasa keyar Manal a gaba da hijab Suka tafi tiryan tiryan.
Chapter 78 · 0% Book details