Sashe 8
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Pure water ta siya da ragowar kudin Dake Hannunta ta Sha tare da yin Alwala ta shimfida dankwalinta tare da Gabatar da Sallar Magriba da Isha Bata Saba da Addua ba ga matsala jimgim a kanta amma Bata iya tunawa ba ga inda ya kamata ta Kai kukanta wajen Allah Kawai tana Idarwa ta fada tunanin rayuwarta Wai cikin Bai fi wata Daya ba rayuwarta ta canja Haka,daga zuwa birni gidan mahaifinta wajen Kuma Dan uwanta,Sarkar Zoben Yazed ta shafa Hawaye ya zubo Mata wani zuciyarta ke zafi Kamar ta fashe bakin ciki yasa ta Mike a fusace tana cewa Wai Yaya Yazed da Annatu Basu Sanni ba Kai jama'a hodijam,yo idan ma Malam yace Bai Sanni ba ai bazan damu ba Amma kamar Annatu da Yaya Yazed Ni zasu manta? Aradu yaci ubansa ba Wani Yaya daga yau babu sauran mutunci tsakani na da su Kuma duniya Zan shiga Allah yasa wani yayi min Cikin shege kowa ya huta, Ghana must go dinta ta fisga ta Kara gaba garin sauri ta masge wata Dattijuwa me abincin siyarwa ta tashi da kwanikanta zata koma gida amma sabo da karfi irin na Manal tayi gaba da Dattijuwar Nan tare da kayanta gaba Daya Kuma ko kallonta Bata Yi ba bare ta Bata hakuri,Ran Me abinci ya baci ta Shiga durawa Manal Ashar da tsinuwa,Kaga tsinanniyar yarinya,baza kiyi albarka a duniya ba Shegiya gantalalliya,Manal tsayawa tayi tace yo na nawa kuma ko ance Miki dama Albarka na fito Nema?Ni da Zaki taimaka ma ki nuna min gidan karuwai shi nake Nema Dan Allah ki nuna min,Mutunci na ya isheni so nake naje inda Zan watsa shi,Dan Allah Naga kinyi Kalar Yan bariki nuna min Hanya zanyi amfani da damata ne wajen dai dai ta Kima ta da daraja ta wacce take ta ya mace,me abinci ta karewa Manal kallo yanda ta ganta wata muguwar kyakyawa ajin karshe tasan za a samu kudi da ita Tace yarinya Ni Kuwa nasan Gidan karuwai ai duk garin Nan babu bariki sama da gidana idan kika shiga to darajarki ta dagu,kin shiga wani kundin tarihi a rayuwarki,Manal tace bana bukatar dogon turanci muje gidan,Me abinci ta tattara kwanikanta tare da furta Sunana Hajiya Amaratu,Manal Fuska ba Rahma Tace Manal Bariki nake suna na kenan, Hajiya Amaratu ta dinga dariyar Sunan Tace Manal Bariki? Manal harda guntun turancinta data tsinta a birni Yassss...(Yes)
Hajiya Amaratu Tace bini muje to,Tiryan tiryan suke Tafiya har zuwa Wata kazamar kasuwa wacce Sam Bata da kyau,wani gida na bulon Siminti me Dan kyau Suka shiga,gidan karami ne Amma duk wani Abu na gidan na Yan gayu akwai shi a gidan,Gidan ya kayatu gaba Daya sai Manal ta koma Kamar yanzu ma ta shigo birni,Suna shiga Manal taga Yan Mata wajen su takwas duk sun girmeta da shekaru sama da biyar ko shida ita kadai ce yarinya,Kuma gaba dayansu daga Kauye suke Yan Kauye ne futuk.
Manal kallonsu tayi tace wallah Ashe ma na gida ne,Yan Uwa na sannunku bayin Allah mutanen karkara Yan Uwana,Cikin Yan Mata da su a tunaninsu sun fa fara wayewa,Wata aciki Jamila Tace kaji banzar yarinya ke da yanzu kika shugo birni to mu Nan satin mu Daya a birni,Manal dake Dan kulla hausarta da kyar wata a Gane wata ba a Gane ba Tace Yo Allah na tuba Ni Kin San tun yaushe nake a birni to nafi wata Daya yara Kuma Yasin ki min Shuru ko na Miki laga laga a gidan bani da kirki a cikin Fushi nake,ba Wasa ne ya kawo Ni ba,Fitowa nayi neman Wanda zai lalata ni,Su Jamila suka saki Dariya Harda tafi wata ciki tace karya kike Yi yarinya,Manal Tace Uwarki ce dai take karya Ni Kinga na Miki Kama da makaryaciya wallahi badan ta rayuwa ba Yar gidan Annatu Kanwar Yaya Yazed na rantse da girman Allah, wallahi,Ke Alqur'an kinji rantsuwar Yaron Musulunci Ni nafi karfin na Miki karya sai wacce baza a rasa ba,Hajiya Amaratu tana jiyo Muryar Manal tunda ta shigo ake bala'i da ita,a ranta Tace wannan kwai jarabar yarinya.
Jamila Tace ke da Alama masifaffiya ce Amma? Manal Tace ai Bala'i ne ya yaye Ni Sanda Ina karama,wurin Zama zata Nema a palon sai da ta samu kujera wacce Jamila ta zauna a Kai Tace matsa a Nan Zan zauna,Manal dagewa tayi sai ta zauna itama Jamila Tace wallahi Baki Isa ba baza kizo ki sameni a waje ba Sannan kice sai na tashi kin zauna Haifa ta kika Yi,Manal tace Allah sai kin tashi Ni Haka nake ko a Kauye duk inda na shiga sai nayi mulki sai dai a bini bana bin mutum ni,kokawa suka fara Yi tasa karfi tare da janye Jamila Kamar tsinke tayi jifa da ita kasa ta zauna a wajen tare da lumshe Ido Tace loyi (Laushi) wallahi Allah,Suka sheke da dariya Wai Loyi.
Hajiya Amaratu ce ta fito da Tsawa tace Enough is Enough,Manal ta washe Baki ta shiga tafawa Hajiya Amaratu tace kin birgeni tsohuwa dake Amma Haka kika iya turanci? ah wallahi Ni Kam sago wararas dani ko banza naji turanci inof is inof Yayi Alhmdllh cewar Manal, Hajiya Amaratu me aikinta ta umarta tare da zubo musu abinci a katon tire suka hadu gaba Daya Suka ci Jullof din taliya suka Sha ruwa sannan Hajiya Amaratu Tace to ke Manal kece sabuwa a gidan Nan dokata itace aiki zaku dinga tayani kullum Kama daga gyaran gidan Nan zuwa Girka abincin siyarwa ta,Manal tace Ni fa ba Bauta nazo yiwa wata katuwa ba Hanyar lalacewa nace a nuna min,Hajiya Amaratu itama Kamar yarinya Tace to ai a hankali ake lalacewar tunda kin matsu Naga sauri kike Yi idan muka Gama aikin sai muje wajen siyar da abincin dake a Haka Zaki samu dai dai dake ya Gama da ke,Manal Tace yanzu naji zance,a farko ma nayi tunanin Uwar karuwai ce Ashe aikin banza ma kema duk abin naki kame kame ne,idonki Bai Bude ba,Hajiya Amaratu ta jinjina Kai tace ke yarinya ki San Maganar da Zaki dinga fadawa mutane ba karamar Yar Iska bace Ni,karuwanci ba irin Wanda banyi ba,sutura ba wacce ban San ba,shinkafa ba Kalar da ban ci ba idan kika Yi Wasa har bindiga ce dani,Dariya Manal tayi Kawai sabo da Bata da tsoro.
Yo Ni yanzu Yan birni wani birgeni kukeyi abinda na gano Ashe duk karya ce abin,na dauka ci kukeyi Kuna koshi ashe duk yunwa ce a jikinki,Shuru sukayi Manal ta tsigale Hajiya Amaratu tas.
Washe gari Dukkansu suka hadu tare da gyara gidan Manal Kuwa tana bangaren girkin abincin Hajiya Amaratu Wanda zata Kai shagon siyar da abincinta,Manal tana soya Naman ta tuno da Yayanta Yazed tare da Annatunta Hawaye ne ya Shiga gangaro Mata ba tare data shirya ba,Hajiya Amaratu ko a jikinta sabo da ita babu ruwanta da wani me ya fito Dake daga gidan ubanki,sai da Manal ta Gama kukanta ta hakura,bayan sun Gama girkin sannan tayi wanka tare da saka wani katon skert dinta Dan kanti peach Amma irin na masu siyar da manja ga wata t-shirt dark blue me gajeren hannu,Dan gyale Baki ta daura a kanta tare da daukan wasu kayan Suka shirya a Napep sannan Hajiya Amaratu tace Da Manal to muje,Takawa tayi Suka fita tare abinsu.
Tare Suke siyar da abincin kowa ya kalli Manal sai ya kyasa,wasu maza da Suka zo gaba daya sun kasa komai sai kallon Manal sukeyi duk motsin da tayi,kunya ce take Kama Manal duk ta kasa sakewa sai soshe soshe take Yi,Hajiya Amaratu tana kallonta Tace Yar banza kika ce bariki kika fito,Manal ai sai Hannayenta biyu ta sa tare da rufe fuskarta tace na fasa.
Hajiya Amaratu a ranta ba Haka ta so ba taso ace Manal ta fara bariki ko banza zata samu kudi sannan zata Kara samun customers,sai Kawai ta fara Jin haushin Manal,fitarta da Manal sau Uku ta daina fita da ita sai dai suyi Mata aikin abinci Kawai Kamar jakai tukwicinsu a Basu su ci su koshi,satin Manal biyu kacal da Hajiya Amaratu Yau Hajiya Kasuwa ta Aiki Manal ta siyo Mata kayan abincinta da Sassafe Napep ya sauke ta a kasuwa tana tafiya tana siyayyarta sai da ta Gama kaf aka zuba Mata a taxi zata shiga kenan Kamar ance ta juyo Suka Yi Ido Hudu da Yaya Yazed dinta shima hannunsa da ledar kayan Miya da Alama cefane yayi shima,Kallon juna sukeyi ba Wanda ya iya janye Idonsa,kowa ya gansu yasan jinin juna nane sabo da yanda suke Matukar kama da juna,a hankali ya Bude Baki tare da Kiran sunanta Manal.....mamaki ya kashe Manal,Yatsa ta zura a kunnenta tare da karkade kunnenta ko ba dai dai taji ba,idonta ta Shiga murzawa tana kallonsa da Mamaki,Muryarsa ta sake ji ya furta Manal me kike Yi a Nan? Muje gida,kinje school Kuwa?
Manal Hawaye ne ya zubo Mata muryarta tana rawa Tace Ya...ya...ka Gane Ni ne? Da sauri ya daga Kai shima kamar zaiyi kukan tare da furta na ganeki Manal bayan barin ki gida da sati daya Muka dawo hayaccinmu Ni da Annatu,Bamu San dalili ba,Allah yasa Baki Yi nisa ba,babu irin Neman da Bamu Yi Miki ba,Malam fa? Shima ya dawo normal ya Gane wace ke Manal mu Bamu San dalili ba wlh,Kalli yanda kika rame Amma duk inda kike wahala kike Sha Manal? Manal tayi Dariya Tace Kai Yaya Ina ci ina koshi Kawai rashinku yasa na rame,Hannunsa ta rike Tace shiga Taxi muje na kai Mata kayan sai mu koma gida ko? Kayi Mata godiya Manal ta furta tana bashi labarin Hajiya Amaratu.