← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 95

Sashe 81

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen Raheela ta koma tace Dan Allah kaiwa Yaya Cumb din Nan kice nasa ne ya manta shi a Nan,Wayo Farida ta hada,Raheela ta Bata Rai Nifa bana son wannan Dan girman Kan Kar ya min wulakanci wlh,Idan baza ki Kai Masa ba bani Kawai kin tsani bawan Allah,Raheela ficewa tayi ta duba baya nan tace baya Nan fa,Ki duba dakinsa,Ido ta zaro da sauri Farida ta Bata Rai Tace bani idan baza ki Kai ba, dakinsa ta nufa Yana jikin mirror Yana ta fesa turaruka Yana ganinta ya hade Rai a ransa Kuma sai murna yake Yana Jin Dadi,lafiya? Ya tambayeta Yana Mata wani kallon raini,Raheela tace Aunty Farida ce tace na kawo maka Cumb dinka,Kuma sai kin biyo Ni dakina? a ransa Kuma Yana Weldone Farida Weldone Halina dake wayewa, Raheel Tace gashi tana Mika masa,yace ki shigo ki ajiye idan Kuma gashinki kika taje min da Cumb ki tafi dashi na bar Miki,Bani da Dundrub fa Cewar Raheela,wa ya sani Abu a duhu a Nan ya nuna Mata Saman mirror, tazo zata ajiye hucinta Kawai da yaji kusa da shi sai da tsigar jikinsa ta tashi ya rumtse ido tare da dafe Kai da sauri,ganin zata tarfa shi yace Dan Allah kiyi sauri ki fita turaren jikinki kauri zai sa min ciwon kai.

Hararsa tayi zata fice yace dawo duba kasan pillow ki dakko min paracetamol sauri,Tsaki ta ja a ranta taje duban duniya Bata gani ba ta juya baya Yana ta kallonta ya murmushi Yana Jin Dadi idan ya fahimci zata juyo sai ya s
dafe Kansa da sauri ya Bata Rai,ta gaji tace ban gani ba yace duba Dayan zata zagaya yace kibi ta saman bed din Mana Haba kiyi sauri,ta haura saman Bed tana dubawa,Yazed a ransa yace yau zanyi bacci me Dadi ta hau bed din nan,ta Gama dubawa babu yace Dan Allah fita na duba da kaina,Raheela ta dire a kasa Tace kayi kyau yau,yace mashaallah kurwata tafi karfinki,Dariya ya Bata ma,tana ficewa ya dinga Murna ta yaba.

Yana Fitowa yace Farida Zo na kaiki,Wai bazai ce kuzo na kaiku ba,suka fito lokacin Belloti ya tafi wajen Yayan Uche sai gobe zai tafi,Suna Fitowa Suka ga motar Malam ta Sha uban wanki tana kyalli,yace ya Naga ku biyu? Farida Tace ai tare zamu tafi,nayi zaton yau zata tafi gidansu,Farida Tace ka ganta Yaya nayi nayi ta sake kwana Wai da Magriba zata tafi gida,Yazed yaji wani dukul yace ai Kuwa maybe anjima a sa dokar kulle yau da safe Gomna ya sanar,Farida taje gano Tace Kar dai kace labaran Dana ji dazu Yan bindiga Dadi sunyi harbe harbe a gidan Gomanti shi ya jawo,ae shi fa da yuwuwar ma suce har jibi ba shiga ba fita.

Yaushe ya faru Raheela ta tambaya tana dafe kirji ke Baki gani ba a social media? Cewar Farida,Raheela Tace shike Nan ai dama a gida bance Zan dawo yau ba sai na Bari sai gobe ko jibi,Farida Tace sai mu tafi tare Nima naje na kwana ko Daya ne a gidan Uncle din naku,Yazed yaji Dadi ya tabe Baki yace da aurenki ki dinga kwashe kwashe ku Shiga mu tafi,Raheela da sauri ta tafi zata Shiga baya,Farida Tace ke koma gaba Mana,Haka ta koma gaba tana tsoron Yazed,tunda yazo driving yake tafiya a hankali Kamar bazai tafi ba,Haka Yana biyo wani layi yasan mutane a wajen sai ya sauke glass ya dinga tsayawa Suna gaisawa ta glass, Farida tana ta dariya kasa kasa,sai da Suka Yi Dan nisa dai dai wani kanti Farida tace tsaya Yaya Zan siyo Abu a nan ki jirani Raheela tace to,tana fita Yazed sai wani basarwa yake yace ki gyara kujeraki ta Mike da yawa tana bani matsala,Ina ruwan kujerar mota da tukinka,Tsaki Yaja tare da sa Hannu da Kansa ya taso sosai Kamar zai kwanta a jikin Raheela ya dinga ta gyara kujera yayi baya da ita ya Danna ta koma gaba Wai saitawa yake.

Wayar Raheela ce tayi Kara ta daga tare da furta ranka ya Dade,Yana Jin Namiji ne ya fake da gyara kujera ya tankade Wayar Hannunta ta Fadi kasa a ransa sai kishi yakeyi har Farida ta dawo Suka tafi gidan Manal,Lokacin Manal Alawa ta sake ta baccin ma tashinta kenan ta Iske Fuzail yayi wanka ya shirya cikin Jallabiya Fara har yaje Sallar la'asar ya dawo,a gurguje itama tayi wanka da Brush tare da Sallah,tunawa tayi zata Yi Baki a gurguje ta shirya,Fuzail ya shigo tace Sannu da zuwa ya jikin? Murmushi yayi yace naji Dan sauki,Bari na dafa ma wani abin,ki huta naci abinci wurin Ummi jibi zata tafi ma,Allah ya kaimu zamu missing Ummi.

Su Farida ne Suka shigo har Yazed Manal Jin Muryar Yazed ta fito da sauri tana Dariya zata Rungume shi Fuzail ya riketa da sauri harda wayancewa Baki da lafiya kibi a hankali ya zaunar da ita a kujera,duk da Haka sai da Manal ta koma kusa da Yazed ta zauna tana Masa Sannu da zuwa Suka gaisa Tace Yaya sai yau yanzu ka kyauta kenan? Harda kwalla ta kwantar da kanta a kafadarsa,Fuzail kishin jaraba ne da shi kasa Hakuri yayi yazo Gaban Yazed yace Bamu gaisa ba ya Mika Masa Hannu tare da cewa da manal matsa Mana tana Dan Matsawa ya zauna a tsakiyarsu ya shiga tsakaninsu ya zauna daram,Manal Tace Yaya kayi kyau,Aunty Farcy Ina Mijin naki? Fuzail Yana jin haushi da sai lallai Manal kullum sai ta tambayi lafiyar Belloti,Raheela ta kalla tace Amaryar mu sannu,Prince ga Budurwar Yaya Nan ita Muke so a tayamu Addua,Da fatan Raheela Zaki karbi Yayan Nawa Muna ciki,mun fada da yawa,Raheela taji kunya,Yazed ma Haka Manal ta tona Masa asiri lokaci Guda,yace ke dai baza ki waye ba yacewa Manal,Manal ta Mika Hannu ta tsalle ta saman Fuzail zata rike Yazed Dinta Fuzail ya bige Hannunta yace ke kin fiye kiriniya bakya Zama lafiya ki kyale shi ya huta Mana,Sawa tayi aka kawo musu kayan motsa Baki Suka Fara Hira,Raheela sai ta kalli Manal ta kalli Yazed kamarsu Daya.

Fuzail ya kalli jakar Farida yace ki dinga Adana hand bag dinki ki daina barinta Galala,Farida ta Gane Kar ta bari Manal ta taba,Farida tace to,Yazed ya Mike yace idan Kun Gama ku kirani ya tafi,Manal Tace kuzo mu leka gidan Amare,Fuzail yace sai dai suje amma Banda ke,hakura tayi tana kallo su Farida Suka tafi can,wajen ta Tanko Suka Fara zuwa Suka ji kamshin girki me Dadi tun kafin su shiga,Amarya bakya laifi cewar Farida ta leka kitchen sai taga Tanko ne a ciki da jallabiya brown Yana ta soye soye,kamar Bai taba ganin Farida ba Haka ya nuna Suka gaisa yace tana cikin daya palon,suna zuwa tana kwance a doguwar kujera ta Sha Shadda tana kallo da remote a Hannunta,Islaha ta dinga murna.

Farida tace ya Jajjagen? Islaha tana Jin kunya Tace ya daku lukwi,Haka ake so Suka gaisa da Yar Hira sai ga Tanko da tire Yana wakarsa kasa kasa Kamar wani me girki a Resturant Yana la...la.la..la,Islaha tana daga zaune Tace sweety a kawo musu ruwa,Farida sai kallon Tanko takeyi yanda ya Zama wani Dan gayu kyakyawa,gashi dogo,Tace a ranta Wai dama duk Haka yake ban sani ba, istingifari tayi dai ta zauna ya kawo musu lemo da snacks sannan ya zauna Suka gaisa,Farida kunyar abinda tayiwa Tanko yasa ta kasa Zama Tace su tafi ta musu sallama.
Basu je wajen Ameer ba Suka koma tare da Kiran Yazed Suka tafi.

Tunda Manal ta fadawa Raheela Yazed Yana Sonta Sai ta fara Jin kunyarsa Kuma,Shi Kam sai Dadi yake ji,Yana kallo ta tafi gida Bai iya karbar number dinta ba sai Farida ce ta bashi tace Yaya ka fada Mata wallahi tana da samari masu sonta,gabansa ya Fadi yace dole yau da dare ya kirata ya fada Mata ya gaji.
Ko da Daren yayi kasa Kiranta yayi sai text ya tura mata kamar Haka
Hello
Yazed ne,Maganar da Manal ta fada Miki gaskiya ne,ya kika gani?
Itama tace
Hmm Ina godiya amma ka Dan bani time.

Washe gari Belloti cewa yayi ya fasa barin Farida ta zauna har Nan da sati wani biki Kawai zasu dawo Ganin dakin Amare,ba yanda Bata Yi ba yace shi bazai iya Zama shi Daya ba,Haka ya kwashi Farida Suka tafi sai hakuri ta Basu,suna tafiya a mota Belloti Yana driving yace 3days babu Injin Dap Ina lafiya,Kamar nayi tsuntsu Haka nake ji na yau ba bacci huce gajiya zamuyi Kara'i cucumber zata yi,Belloti idan yayi maganganunsa sai ya juyo Farida ta manna Masa kiss a Baki da sauri ,Belloti sai wuta yake a Hanya Kawai Faridansa yake hangowa suna zuba love.

Malam ranar da aka Daura Masa aure ranar Amarya ta tare,washe Gari aka sake daura Masa aure da Hajiya itama ta dawo,Hajiya harda zuwa gidan make up bayan gyaran jiki data Yi ba'a magana.
Bangaren Yazed Kuwa tunda ya fada tace zata Yi tunani Bai sake Kiranta ko text ba bare yaji amsa,gashi kullum tunaninta ya hanashi sakewa,Farida ya Kira a waya,tana dagawa bayan sun gaisa yace ki tambayi kawarki ta Gama tunanin idan Bata so tayiwa kanta sai na fada safgata,Farida tayi Dariya a ranta Tace zaka sani Bari muga karyar Ji da Kai,a fili tace Zan nemeta,yace better idan Kuma tayiwa kanta ne to shike Nan, ki Gama jin me yace bata yi ba ya kashe wayarsa.

AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭

DEDICATED TO DUNIYATA AAMNA FANS GP

106-110

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

H Umar
Rukey Muaz
Munie Bash
Ummu Abba
~-
Chapter 81 · 0% Book details