← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 95

Sashe 30

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar tana ta Kara ya kalla yace baza a daga ba kin Sa mutum sai wahala yake Sha Ana ta dukana tunda na fara sonki dai dai ranar da bazanci zagi da duka ba,abin haushi yau Dogarai yarana Yan aikina da Hannunsu suka zaneni a gefen Titi Gaban mutane,ai na ganeku su Tanko ne zaku Gane kurenku wallahi bari komai yayi settling zaku San kun Zane Prince.
Manal ce ta sake Kira ya kalli Wayar yace baza a daga ba aikin banza ya juyawa Wayar baya,har 1am Manal ta kasa bacci ta Hana Fuzail bacci da nacin Kiran masifa sai taji ko lafiya,Gajiya yayi ya daga tare da kumbura Baki Wai Fushi yake Yi Kamar Yaron yaye yace Hello....Manal Ajiyar zuciya ta sauke tace wallahi hankali na ya tashi kaje gida lafiya? Fuzail Direct yace a'a ba lafiya naje gida ba,Ido ta zaro me ya faru?yace Yaran sarki ne akan sarki zai Shiga motarsa suka Hadar min da zanewa, Manal ranta ya baci tace Allah ya tsine musu tsinannu Shegu har Sarkin Azzalumi,in Banda zalunci Kawai sai yasa a zaneka me ka musu aikin banza aikin wofi Ni wallahi shi yasa ko me Unguwa bana so wani Nawa yayi sabo da zaluncinsu,Fuzail yace idan kika samu Dan sarki fa zai aureki nasan guduna Zaki Yi? Manal da sauri Tace Dan Allah rufa min asiri Dan Sarkin banza ina da Kai wa yake ta wani Dan sarki,Kai Nifa irin wannan biyayyar ta gidan sarakai bazan iya ba,Ni Allah ma ya taimakeni Mijina Bai da hadi da azzalumai,Ni wallahi kasa Sarkin Nan ya Gama sire min ko motarsa na gani sai na zagesu.

Fuzail yaji za a zagi babansa yace karki zagesu ba ruwanki ko so kike ki zama Farida kema? Ba Haka na sanki ba,Manal Tace to Kawai sai su zane min Kai,Kar dai ki zage su na fada miki,to shike Nan tunda kace a kyalesu,Hira Suka ci gaba da Yi har 2am Yazed ya fito zaije fitsari yaji Manal tana ta waya,Kai ya girgiza yace sai da safe zanyi maganinki Manal Naga canji Zaki amsa tambayoyinki idan da Rabon kinci duka ne to.

Sai bayan sun Gama Wayar sannan Fuzail yace Sarki ba ruwana Kai ka jawowa kanka gashi Nan surukarka ta zageka baka sani ba,Ni Kuma bazan hanata ba tunda Kai ka jawo,Haka da safe Ameer Yana zuwa wajen Fuzail ai ya bashi labarin dukan da yaci da komai ma har abinda Farida da Yahaya Suka yi,Ameer ya dinga dariya kamar mahaukaci.

Fuzail Kuwa wanka ya dauka na karshe cikin kana Nan kayansa Brown and white ya zuba kyau gashinsa na asali Yana uban sheki yasha wani Aski na gagara,cikin Fushi Ya wuce part din Maimartaba Yana zuwa ba ko gaisuwa ya dinga masifa Taya za a dinga zubar da mutuncin sarauta yanzu na gani a media yanda Dogarai suke Zane bayin Allah Haka Kawai,Ya kamata ka tsawatar musu ai mulki ba Haka ake Yi ba,ba dama ance mutum ya tsaya kusa da ku da glass a Fuska ko kuma idan Kun tsaya Dole sai dai mutane su bar wajen ko su durkusa wannan ba dai dai bane.
Sai da Fuzail ya Gama masifarsa Sarki yace to Ubana Sannu Mahaifina,Shuru Fuzail yayi ya zauna a kujera,Sarki yace kayi hankali Zansa a kulle min Kai wlh, duk sauran yarana ba Wanda nake magana da da shi direct sai Kai ka kiyayeni,Sarki ya kalleshi yaga ransa a bace, sai yace Naga wani yaro jiya Kuna Kama naso Yaron yazo da na hadaku.
Shuru Fuzail yayi Yana ta Fushi sai da sarki ya lallashe yace za a kiyaye zai yiwa Dogarai magana su daina hakan sannan Fuzail ya daina fushin.

Washe gari Yazed dakinsa ya Kira Manal bayan ya tanadi Bulalu masu kauri jira yake yaji Abu ba dai dai ba taci ubanta a gidan,ita Kuma ta kulle a ranta Matukar Yazed yace baza a Mata aure ba to wajen su Malam Salahu yayan Babansu zata tafi ta Kai kararsu Dole sai an Mata aure Kuma tasan Annatu dama tana so Yarta tayi aure Bata da matsala Yazed ne uban Iyayin karatu.

Dole nasan aci dariyar dukan Fuzail,nayi Dariya Kamar me wallahi.

Masu Sharhi Ina godiya musamman
Hajiya Khausar
Ummi Deejat
Hauwancy cool life
Etc

AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭

IS DEDICATED TO

DUNIYA TA AAMNA FANS GP.

36-40

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne Yan Albarka

TAMORMIE
AYNAH
AISHA UMAR
MAMAN AMAL
ABIDA ALI
HINDU MOHA
CWT FAUXAH

Da Sallama ta shiga dakin tare da Zama a gefen katifarsa ta Furta Yaya gani,Kayan jikinta na Jiya su ta maida yau kallo ya Kare Mata yace Ina kika samu wannan kayan? Duk Naga kin canja tafiyar sati biyu me ya faru ne Haka?bana so fa naji abinda ba dai dai ba Manal fada min a Ina kika samu kayan Nan Naga kin canja ma gaba Daya ban Gane ba,sannan wannan saurayinfa daga Ina Naga kin bashi matsayi da yawa.
Zama Manal ta gyara tun bayan tafiyarsa duk har haduwarta da su Fuzail sai da ta kwashe ta bashi labarin komai ba abinda ta boye masa karyarta Daya Bata ce ya taba kwana a dakinta ba,sannan Bata ce ta taba kwana a gidan da ta Nema musu su zauna ba Tace ai a waje take tsayawa su fito su karbi abinci ta juya gida,sai labarin kayan da Shukrah ta bata da kawancensu da karatun da take koya mata,har abinda su Hajiya sukayi Mata sai da ta fada masa.

Sai da ya Gama ji sannan hankalinsa ya kwanta yasan Manal Bata karya komai zata fada idan har ta boye abu to tasan fadarsa zai iya jawo matsala,To Yanzu dai Shukrah ta kyauta na gode data Dan koya Miki karatu,shima Saurayin naki yayi kokari Daya koya Miki wasu abubuwan,Manal ta fara dariyar murna Tace Yaya Kuma nafi Gane karatunsa ma,Ae ai dama Dole ki Gane Nasa cewar Yazed,da ace naji abin tsiya wallahi yau sai kinci duka a gidan Nan,ka tambaya kaji idan karya nake Allah Yaya gaskiya na fada maka,Na yarda ai yanzu su Hajiya Haka Suka Miki?Manal tace kyalesu Ni wallahi Farida da Allah zai kawo Mata Prince din nata ma a Mana auren tare kowa ya huta da jaraba.

Yazed ya kalli Manal yace Wai ke ban Gane ba karatunfa? Ni wallahi Yaya ka bar zancen Nan,
Tab Aiki Babba taso mu tafi ayi zancen Nan a Gaban Malam,Manal ta Mike tare da cewa ae aje...aje.
Suna zuwa Malam da Yazed Suka Fara lallaba Manal akan Kar ta Yi aure sai tayi karatu,Malam yace Manal mu maza ne gaskiya muke fada miki gwara ki zauna kiyi Ilimi ki fara Aiki kina samun na kanki mijinki ma Sai yafi rikeki da amana,Mazan yanzu kana da ilimin ma ya aka cika bare wannan Saurayin naki wlh da gani ba kunya ce da shi ba,Yazed yace ai Ina Kallonsa Naga a waye yake Kar,Kuma bako ma Wanda ba a sansu ba haba Manal auren bako fa hatsari ne a rayuwar nan,na rasa jarabar da yasa ma daga taimako ta manne masa,Su Malam suna ta Yi har Suka Gama.

Manal tace Nima a bani dama nayi magana,Muna jinki cewar Yazed Manal tace da kuka Ce sai nayi karatu ai yace zai sani a school,Kuma Bayan Haka ko nayi makaranta Ni bazanyi Aiki ba bana so,Aiki ko wahala Indai mijin zai min komai ba matsala Balle ma Yana da zuciya,Nawa ne basa Aikin Kuma sunfi masu aikin komai da komai na Jin dadin rayuwa sabo da mazajensu suna da rufin asiri,idan yayi kudi ba kasar da bazan jeba,ba motar da bazan hau ba Indai Allah ya azurta shi Ilimi Kuma zai saka Ni yace,sannan Malam Kai ma fa ba Bokon kayi ba Kuma gashi kayi aure gamu,sannan shi duk da bako ne to na kirki ne ayi Bincike Nan gaba Ni Ina da tabbaci Inshaallah baida matsala,Yazed yace Malam Yaron ya hure Mata kunne ya samu dama Bama gari ya Gama hure Mata kunne wallahi ko me zamu ce baza ta yarda ba,Dan Ubanki za a miki auren Amma ki sani Bamu da kudi sai dai Annatu ta siyar da shanunki a Miki Nima Nawa shanun Fili Zan siya sabo da Haka tunda bakya Jin shawara ayi Miki da ragowar shanunki Malam Baida kudi.

Manal tace ba komai ai na fadawa Annatu ma munyi magana a waya,Yazed ya girgiza Kai yace Wato itace ta Baki goyon baya ko? To Wai dama da a Kauye aka barni da tuni yanzu ba a min aure da Belloti Allah ya taimakeni na samu Wanda nake so sai ace sai nayi karatu wallahi Allah idan baza ku yarda ba Kara zan kaiku wajen Kawu Salahu wallahi ai ba laifi nayi ba.

Haushi ya Kama Yazed yace je ki Kai karar mana yaro yazo ya hure Miki kunne ya yaudareki da kudi kalli Wayar hannunki fa,karya kike wannan kayan duk shi ya Siya Miki,Manal Tace naji ai Ina Kauye kasa sai na dawo wajenka na maka biyayya na dawo kace duk abinda nake so zaka min shine yanzu ka canja sai na koma wajen Annatu gaba Daya,ki koma mana ai Kinga dai yanda mijinta yake Miki Jeki tunda Baki da hankali.

Kuka Manal ta fashe da shi baza a Mata aure ba,Malam tsoro yaji ko sha'awa ce take damun Manal Kar ya jawo ta lalace,Bai San Manal ita babu ma Wannan a ranta Kawai soyayya ce ta kwashe ta da Kuma kuruciya,Malam yace tashi kije zanyi tunani,Kafin ta fita Ashe Hajiya tana labe ita da Farida suna Jin komai ai wuf Hajiya ta Fado dakin Tace wallahi bazai yuwu ayiwa Manal aure ba sai an fara yiwa Farida sabo da itace Babba Dole Manal tabi layi ehe,Manal tana Hawaye tace layi Zan bi? Ah Kawai a makarantar kwana nake naje karben abinci,ko banki naje Karbar kudi? Hajiya tace Baki Isa ba yarinya kinyi kadan
Malam Yace idan kika sake sa min Baki a Maganar auren Manal a bakin aurenki na gaji da halinki,Mukus Hajiya tayi tare da ficewa Kamar Iska.
Chapter 30 · 0% Book details