← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 95

Sashe 63

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yar Hira sukayi sannan Farida ta dawo Belloti ya fisgota a mota kamar zai tashi gari faaaaaa duk Wanda ya ganshi da gudu yake kaucewa wuta Kawai yake shararawa shi ga me Amarya, ya kalli Farida yace akwai chasu a Kano idan Muka koma,Farida ta saki murmushi tana kallon Uwar Sumar Belloti daya Tara ta Yan Fulani me kyau baka me santsi,Kida Belloti ya ware a motarsa duk inda Suka wuce Ana Jin kidan sosai wakar Amarya da ango tana tashi,Belloti har sitiyari yake saki ya Dan Yi rawa da kirji yaci gaba da tuki, Belloti an waye yace muje Asibiti ayi Mana test sabo da tsaro,Haka ya kaisu wani lab aka musu gwajin aure Allah yasa komai lafiya kowa lafiya yake,Belloti yace yawwa dai dai kenan.
Gobe zamu ware da ke tunda ba a shirya bikin ba daga Ni sai ke sai uban gidana zamu wuce Kano,Farida Tace kano ta dabo tumbin giwa tana rausaya Kai.

AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭

DEDICATED TO DUNIYATA AAMNA FANS GP

76-80

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne ta wajena

HABEEBATULKHAEER

Jinjina ga
GIDAN HAUSA NOVELS

Belloti Yana sauke ta ya bada kudin Dj yace matsalar Ni bana saka manyan Kaya yanzu duk da kana Nan Kaya na shigo garin Nan,a Kira me Dj na cashe Iya rabona zanje na dawo da Yamma,Farida tana Murmushi tace a dawo lafiya ta Balle murfin mota ta fice shima ya Fisgi mota ya Kara gaba,Tana shiga ciki ta Iske Kawayenta da yawa su Rumaisa,Walida gasu Nan da yawa sunfi su Goma Sha biyar wasu ma suna Kan Hanya,ita dai Manal Shukrah Kawai ta gayyato sauran Yan makarantar tasu Bata gayyaci kowa ba,su Walida ne Suka ja Amarya saloon aka gyara Mata gashinta sosai, Yan Magungunan Mata Suka siyo Mata da wasu abubuwan na gyaran jiki Wanda zata tafi da su Yan kadan kasancewar Basu shirya komai ba sakamakon Tanko ne Angon,Amma yanzu tunda Belloti ne yafi Dama dama zasu shirya ko Yaya ne.

Zuwa 2pm Suka dawo tare da sake sabon wanka Ana Jiran Masu Dj zasu Fara,suna ta daukan wanka wasu suna shigowa kuma sun Sha gayu,Su Annatu ne Suka Yi shinkafa da Miya sai Abincin da Yazed ya bada a wani Restaurant Ayo,aka kawo Fried rice lafiyayya da Pepper chicken ga lemuka Nan da ruwa sai ka gaji,Manal wanka ta sake Yi tare da Shafa lotion dinta me kamshi,Walida ta daga lotion din Jin matsiyacin kamshinsa Tace Nawa kika siyi wannan? Manal Wai Prince Charming ne ya siya ba Ni ba,Baki su Walida Suka tabe sabo da dama Mata Haka suke sun tsani a fisu,duk wacce kaji Mata suna Zaginta ko Ana tabe Mata Baki to tafisu ba yanda zasu Yi sai a dinga Mata gani gani,Rumaisa ce Tace naganshi ana talla dubu ashirin da biyar, Farida yatsina Fuska tayi tana taje gashinta Walida tace Farida ya Naga gashin naki Yana ta Kara tsayi ne? Tace sai ma yaji sinadarin jikin Muhammad,Wai harda canja Masa suna baza ace Bello ba.

Dariya Manal tayi da sigar wasa Tace Zaki fada musu ne sai Daren farko Allah ya kaimu,Farida da masifa tace Wai Ina ruwana da harkarki? Ina magana da Kawayena kina tsoma min Baki ni kina nufin Ni yarinya ce Kenan fuuuu Farida tayi waje tare da Kiran Yazed Tace ka rabani da Manal wallahi a Gaban Kawayena zata dinga ce min Yarinya tana fada min Maganar data ga dama Ni sa'arta ce, Manal Bata Saka kayanta ba Tana kwance tana tunanin mijinta me yasa ya tafiyarsa dazu oho Bata sani ba,ta Kira wayarsa yaki dagawa,Muryar Yazed taji ya kwala Mata kira,Kasancewar ba Kaya a jikinta Hijab ta saka ta fita kawayen Farida suna wani tabe Baki Walida tace wlh Yarinyar Nan iyayinta ya baci Yar Dakikiya Wai Dan tana auren Prince Wai Charming Prince ko Prince Charming jaka,Rumaisa tace Banga laifinta ba ai abin Alfahari ne wlh ko nice abinda yafi Haka ma zanyi waye Bai son Harkar Hutu,Zugar Yan Rawar Solo ne Suka zo Mata suna da yawa Shegu ne wajen taka rawa,a Haka Kamar na kirki,Dj dinma nasu ne da abinsu Suka zo.

Yazed Kuwa Hararar Manal yayi yace kin San Allah yanzu sai na sa a maida ki gida so kike Ana zaune lafiya ki jawo rigima bana son Iskanci fa,Sa'arki ce a mutane Zaki dinga kunyatata,Manal tace Ni wallahi ba abinda nace Wasa nayi Mata ma Allah Yaya,Wasan dole ne? Tunda Bata so ta fada Miki ki hakura Mana,Ko Wasa kayi da mutum kaga baya so ai sai ka hakura,ki shiga hankalinki ai ba Sa'arki bace,Farida ta Mata gwalo tace Wai Dan ta rigani Aure shine take ganin Kamar kanmu Daya Ni zata gayawa duniya matar da yaushe ma ta waye yaushe ma ta shigo birni Kawai Dan ta auri Prince sai ta rainani,Yazed yace kiyi Hakuri to ke Kuma kika sake Mata abinda Bata so wlh kin Gama bikin nan,Manal tace shike Nan ya wuce Indai nice baza a sake ba,Farida Tace sai kije ki zubawa Kawayena abinci Kuma Banda waccen girkin na mutan Kauye Wanda Yaya ya kawo shi za a basu,Manal Tace Ni fa wallahi ba dadin jikina nake ji ba,Kuma ma Ni akwai abinda ke damuna kina kallo Fuzail yayi Fushi yayi tafiyarsa na rasa dalili,Farida tace Wai ke Baki da Aiki sai zancen Fuzail...Fuzail...Yarima...prince haba uban waye yace ki tsaya da Mijin wata ba naki ba,Dariya Manal tayi Tace Kai Aunty Farida Ko Kara babu,Ke wallahi ki kiyayi tsayawa da Bello yawwa karki jawo min,kije ki Basu abinci ni ba ruwana da wani mijinki Yana Fushi,ya shekara Yana Yi,Manal tace karki jawo naki zubawa,da Kuwa Na Kai karar ki wajen Yaya Yazed wlh yaci Ubanki.

Manal Cooler Kawai tasa aka ajiye musu da komai har ruwa da lemuka Suka ce sai an fara cashewa zasu ci a barshi,ita Manal Pepper chicken din ta zuba a plate Kawai tana ci da lemonta,Farida Tace kiyi sauri rawa za ayi fa,Manal Tace Rufa min asiri ni yanzu Fuzail ya kamani Ina rawa Gaban karti ai Naga ta kaina....ke dalla Yar Kauye ki zauna ki tsufa akan kinyi aure,Shukrah da shigowarta kenan itama taci gayu tace Manal dole fa muyi rawa,Gane min Hanya Yar gari.
Manal Dakin su Annatu ta koma zata shirya ta sake kwanciya kusa da Annatu,Hajiya Sharifa tace ke Yar Nan ko ciki ne da ita ne Alqur'an,Naga tunda tazo sai kwanciya ta kwanta can Hyaraf ta tahi can Ni ko gidan Hutu ne ya lalata ki an Saba da Hawa gado kullum? Dole ta koyi bacci ai wannan ac Haka ko Ina sai sanyin Dadi ga gado
Sabin by Sabin (Seven)
Annatu tana jinsu suna ta tsokanar Manal ta musu shuru.

Mikewa Manal tayi ta zauna Tace Annatu Ina Saniya ta? Ke karki dameni da jarabar Saniya bakya mantawa da ita tana can ta Haifi Yan biyu,Manal ta dinga Murna Tace Tinkiyata fa? Tsohon ciki ne da ita,Kaza ta fa? Idan Yaran sun girma ki dinga kamawa kina yanka su kici kinji Anna,to naji tashi ki koma wajen Yan matan ku can,Shiryawa Manal tayi ta saka wani Sabon lace dark green and Golden tayi kyau sosai Ana ganinta an San akwai Naira,Hajiya Sharifa da Bata gani tayi Shuru tace Uhmm matan manya a saka wannan a fita a saka wancen wannan kyau Haka dole Angon naki ya zauce to anga Jar fata jiki Kamar jini ya fito ba dole ba,hi yasa duk Rawar jikin Nan da yake akanmu nasan ba banza ba,kafarki kafarsa kullum nanai nanai da ke Yana Rawar jiki Unguwar ma baza a barki ki sake ba,Dahara tace Banga laifinsa ba,Yaran zamanin Nan dama Yaya bare Kuma an samu dama,Allah Ni kunya ma yake bani cewar Wata Hindatu tace Yana gaihe mu amma Idonsa Yana kanta Kai wannan Surukin namu,Wani kallo da yake mata Ni ban taba ganin irinsa ba a duniya sai yau hyu'umin kuma ya iya cewar Hajiya Sharifa,Tace yo aike Hindatu Baki hya kallo ba sai ranar da aka Daura Masa aure da Manal Munga bidiri ni Hyarifatu nace cab.
Chapter 63 · 0% Book details