← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 95

Sashe 28

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Driver ne ya shigo motar ya bar Farida a gefen kwalta tana tsala ihu wasu da Basu San me ya faru ba suna ta Bata hakuri aka sa ta a mota,a ranta tace wallahi akan Manal Zan Rama zaka gani yau Indai can zakaje wallahi Nima yau sai na Bata maka Rai shege da shaddarsa Yar Dubu biyar talakan banza.
Driver Kuwa passengers suka cika a motar aka matse Fuzail Dan sarki Guda a lungu yana manne da Jikin Kofar mota numfashinsa Kamar zai dauke ya Saba idan a turai ne duk inda zaka je a taxi to Kai kadai za a dauka komai nisa,a Nan dinma Farida ce ta jawo masa wajen Kiran sauran mutane suzo ga mota.

Ga goslow kafin azo ma ya Gama jigata a mota Shaddar tasa duk ta yamutse,Ana zuwa ya mikawa driver 1k zai bashi canji yace barshi Kawai,Driver ya dinga godiya ya wuce,da bakar ledarsa ya karaso Kofar gidan su Manal wacce lokacin ta Gama shirinta tsaf,Falaqi Yana waje ya Gane Farooq da gudu ya shiga gidansu Yana kwalawa Manal Kira ga Wannan mutumin Nan da kika taimakawa me gashi da yawa,Manal a fili Tace baiyi Aski ba kenan,Mayafinta ta yafa tare da lekowa ta hango shi Kuwa a gefe yayi wata tsaiwa ta manyan Yara a tsaye an harde kafa,Manal ita dai wankan Nan ya Gama tafiya da Imaninta Allah sarki Bata Raina ba ai ita gani tayi ma ya Gama kure karshen wanka a duniya,sai da ta Kare Masa kallo sannan ta fito gaba Daya tana takawa inda yake da kyar take tafiya sabo da Bata Saba da sa Kaya damammu ba,bayan Haka ma sun so suyi Mata kadan,Fuzail sai kallonta yake yanda ta zuba kyau Kamar a sace ta a fece,Shi Bai ma San ta Kai Haka ba sai yau,har kunya taji yanda yake Kare Mata kallo a ranta taji Dadi tasan ta Gama haduwa tayi kyau tunda ta Zama abar kallo a Wajensa da duk Wanda ya kalleta.

Tana zuwa gabansa yace Sannu da zuwa Kareena Kapoor Yaya su Salman Khan suna lafiya dai ko? Dariya Manal ta dinga Yi tana boye Fuska Tace wannan ai tsokana ce.
Daga soron gidan nasu ta shimfida musu Tabarma ya zauna shi dai Yana kallo ta kawo Masa kayan ciye ciye yayi mamaki dama ta iya irin wannan snacks haka,ta kasa magana sabo da kunya sai Dariya takeyi ita kadai ta rasa inda zata saka kanta,Yace ya akayi ne wannan murmushin fa? Manal ta sa Yatsa a bakinta tana ta faman gwigwiya,Hannu yasa tare da zare Mata Hannun yace sai kin cinye min yatsan Kuma? Dariya ta sake Yi tana daga zaune tayi kasa da kanta,Yace Ikon Allah,Ina kwana au Ina yini ta furta,I'm Good and you? Tace Alhmdllh,Kinyi kyau fa yarinyar nan,idan Baki aureni ba kika yaudareni sai mun koma makiya da ke,Manal ta kyalkyale da dariya tace Haba dai ai bazan yaudareka ba,Idan Malam yace bazai bani ba fa? Manal tace karma ka Fara Malam bazai hanaka Ni ba Indai Ina so,to a gidanku basa kaunata da wa Zan Kama kafa? Manal ta nuna kanta da yatsa Tace ai Kai ka Riga ka Kama dahir ba ruwanka da wani kamun kafa.

Yace Farida fa Wai me na Mata ne? Karfa ta kawo cikas a aure na dake? Manal tayi yanda Yan tauri keyi ta Kai wani Suka gefe Tace akanka Zan iya sara Suka,Dariya ta bawa Fuzail Suka dinga dariya,a ransa yace kallo ya bar Ameer yau.
Ledar hannunsa ya Mika mata,Tace Mene? Bude ki gani mana,tana budewa taka wata sabuwar Wayar Tecno spark 5 wacce ta ninka waccen tsada da komai,Baki ta Bude tare da tambaya Ina ka samu kudin? Na siyar da gonar gadon ai an tura min kudin shine naji Wayar Taki ta lalace na canja Miki wacce ta fita tsada,Manal tace to Kai Kuma fa? Shi Kuma ya nuna Mata wata Vivo karama yace ta isheni nafi damuwa da ke nafi so Naga matata ta fito,Manal Taji wani kaunarsa sabuwa, ta shiga jero Masa godiya da adduoi,wacce ta lalace ta Mike zata dakko Masa ya bi Bayanta da kallo yanda ta dame komai ya fito,Fuzail a ransa yace wow Zan huta,Amma wannan Shukrah ta dame min Baby da yawa za a rabawa maza a titi su gani Ina bazai yuwu ba Dole a Kara Size din Ashe katuwa ce haka.

Wayar ta kawo Masa yace me zanyi da ita ki siyar da ita idan za a siya ki kashe kudin,Fafur Manal Taki yarda Wai sai dai ya tafi da ita Dole ya karba,Lemon ta Bude Masa ya karba ya Sha Yana cin snacks din yaji Dadi yace ke kika Yi? a Ina kika koya? Manal tace ai kawata ce Shukrah da Mamanta suka koya min,Kai ya jinjina yace wow yayi Dadi kina da brain,kaci da yawa Kai nayiwa akwai wani ma da yawa nayi zaka tafi da shi kaga sai Ameer ma ya ci da Dan uwanku,Thanks My love,Murmushi tayi Kawai yace Haka Zaki ce You are welcome,idan ance kinyi kyau kice Thanks,Manal ta amsa da to,Karar Napep taji a Kofar gidansu Tace Ga su Yaya Yazed Nan ma na sani...kafin ta rufe Baki taga keken Guragu Yazed ya turo Malam a kai,Manal Tace ba a Dace ba kenan,magani baiyi ba,suna shugowa sai taga Malam Yana sarrafa Hannunsa yanda yaga dama ba irin a baya ba,Manal mikewa tayi da sauri cike da kunya Wai tana zance da saurayi an ganta.

Yazed ganin bako tare da Manal yayi mamaki ko a waya Bata taba bashi labari ba duk surutunta,Sallama Malam Yayi Fuzail da sauri ya zube gwiwoyinsa a kasa ya Shiga gaisar da Malam Yana Masa ya jiki,Malam ya amsa da fara'a da sakin fuska yaji Hausar Kuma ta saurayin Bata fita da kyar ma yaji wani abin,Fuzail Mikewa yayi tsaye tare da mikawa Yazed Hannu,Yazed ya karba da fara'a Suka gaisa ya Masa ya Mai jiki ya amsa da sauki,Manal tana ta murna Fuzail ma Haka ya samu Shiga.

Manal ce tace Yaya Yazed yau baka rike min ko Hannu ba ka daina so na ta furta da shagwaba,Murmushi yayi kawai,Malam shi tuni su Falaqi Suka fito da gudu Suka gungura kekensa cikin gidan,Manal Hannun Yazed ta rike Tace Yaya kayi kyau Kamar ba Kauye kaje ba kalli yanda kayi Dan kumatu ta Kai Hannu zata taba da wasa yace Zan mareki,Uhmm Yaya baka min fada ba kaga Ina zance,Ya zanyi Dake Manal idan na hanaki zance Ni Zan aureki? Ciki ya shige ta bi bayansa zata tafi,Fuzail ya sa Hannayensa a hips dinta tare da jawo ta baya da sauri,Sai ga Farida ta shigo da kayanta fuskarta ta kumbura,taga shigowar Su Malam shi yasa Bata saurari su Manal ba ita ta tsaraba takeyi tukun Amma ta tabbata kafin Farooq ya tafi yau sai ta Kona Masa Rai.

Tana shiga gidan Malam Kawai ta gaisar a tsaye tace babu Yar Ayabar Hanya ne? Ko Dan Orange,Sa'iha Tace Aunty Kinga Malam Hannunsa yanzu Yana komai Yaya Yazed ma yace Yana Dan takawa da kafafunsa kadan kadan,Farida tace Good Haka ake so Ina tsarabar? Harara Malam ta gasa mata tayi Shuru.

Hajiya Kuwa ta rasa inda zata sa kanta sabo da Murna Dama ita kullum Sha'awa ce ta dameta gashi Malam baya nan shi yasa take murna tunda ya dawo zai biya Mata bukatarta ba Wai lafiyarsa ce ta dameta ba, Manal tasan yau ta Gama tafiya da Imanin Fuzail yanda yake nacin kallonta, yace je ku gaisa da su Malam sai ki dawo,Kida sukaji ta cikin gidan Farida ta kunna Blootooth speaker a dakinta ta cika gidan,Malam yasan ko yace ta rage baza ta rage ba,Yazed ma ko ta kanta baibi yasan Bata Jin magana Manal ta Mike tare da juya baya zata shiga gida abinka da karamin gida sai kidan ya cika ko Ina har waje Kamar kayi rawa,Manal kidan taji me Dadi gashi yau a cikin murna take step daya tayi tare da juya hips dinta a Gaban Fuzail tayi cikin gida ko juyowa Bata Yi ba,Fuzail Kansa ya Kama kaikayi sabo da yanda Manal ta tafi da Imaninsa ya nutsa a hannunsa a cikin sumarsa me uban yawa ya Sosa sai yaji Kamar Bai Sosa ba ya sake sosawa Karo na biyu sai lokacin ya tuna Ashe hular gashi ce a kansa,Murmushi yayi tare da daukan ruwansa me sanyi ya kwankwada ji yake kamar Kar ya tafi ya bar Manal.

Dakin Malam ta shiga tare da durkusawa ta sake sabuwar gaisuwa Tace Malam ya jikin? Malam da fara'a yace Alhmdllh ai Hannuna yanzu Ina sarrafa su sosai sannan tafiya ma Ina Dan takawa kadan me maganin yace a hankali Zan dawo dai dai,Manal ta dinga Murna,Baba yace Manal Ina kika samo wannan me gashin Haka? Bai Jin Hausar ma tamu fatan ba Arne bane? Dariya Manal tayi a kunyace tace ba Arne bane Malam Dan Niger ne yazo Nan na Dan taimake su ne lokacin da sukayi hatsari shine muke mutunci,Malam Yayi murmushi yace Uhmmmm a Haka sai na ganshi Kamar Yana da nutsuwa da sauri Manal tace sosai ma Sai ka zauna da shi ma,ai kasan Malam wallahi Hankali ne da shi,Ni Indai bana kirki bane ma ai bazan kula shi ba,Malam yace gashin nasa ne yayi yawa,Manal tace yo ai liman ne a unguwarsu Malam,Dariya ta bawa Malam yace a Ina kika sani? Kuma Liman ne zai hada Suma a Kansa haka? Yo Malam ai koyi yake da Larabawan Madina,Malam yace Hakane dake a Madina aka haife shi ko? Kunne Manal ta Sosa tace idan an tashi auren ba sai ayi Bincike ba kuji,Baki Malam ya bude yace au kika ce mutunci kukeyi, Malam Allah mutumin kirki ne ko a addini ka kirashi kaji sai Kun tafka mahawara da shi nasan ma shi zai lashe Mahawarar, Ma'ana dai kina sonsa Ko? Karatun fa? Nayi ko secondary ce a dakinsa bayan aure sauran jami'ar na karasa abata a kitchen,Malam yace dama na lakanci bakya son Ilimi Manal mazan yanzu wallahi idan Suka lallaba Suka kaiki shike Nan kin Zama nama,Mikewa Manal tayi Tace Malam ka huta kayi wanka kunyarka nake ji ni ta fice fit Dan Kar ma ace ta hakura da Aure.
Chapter 28 · 0% Book details