← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 95

Sashe 69

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fuskar Farida ya leka yace gaskiya kinyi Zaki da yawa Allah ya saka,ai ban San Haka kike ba na daina takura Miki kinji,Farida Harda shagwaba Belloti yace sai abinda kike so Me Engine Daf,Gashinta yake shafawa yace Haka nake son matata ta kasance Dan uban ko wacce mace taje da Kyawun fuskarta Dana jiki mu mun Kama babban Ogan.
Farida Dadi ya lullube ta tace Har Manal din? Wa yake ta wata Manal fata kamar Jan kosai ai su irinsu baiwarsu a iya skin ta tsaya ciki kamas suke cewar Belloti,Farida Taji tafi kowacce Mace Dace ma,sai da Belloti ya Gama zuba santinsa sannan ya dauki Farida Kamar jaririya Suka Yi wanka tare da tsarkake jikinsu,Farida ta gasa kanta sosai,Belloti yace muyi Nafeelar yanzu a Haka Suka Yi abarsu sannan Suka kwanta sai bacci Belloti ya Hana kwanciya da ko pant Haka suka shige bargo abinsu.

Shukrah Kuwa Custome dinta ya dawo har gida wajenta ba tare da Bata lokaci ba Soyayya me zurfi ta shiga tsakaninsu,Rumaisa Kuwa da Fahad sunyi nisa tuni har Ana tunanin turo manya.
Ameer cikin wata Shadda ya fito Gezna airport ya nufa da Niyyar dakko Mamansa ta dawo daga Abuja,Yana zuwa ya fito Yana jiranta waya ya daga Yana magana da Fuzail,Mama ce ta sakko da Jakarta tana ja Haka ga wata budurwa a Bayanta zata Kai 23yrs kyakyawa Yar gayu baza ace Mata Fara ba Haka baza ace baka bace,Ameer gaba Daya Budurwar ta tafi da Imaninsa wata Yar doguwa,Ameer yace Mama Barka da zuwa,Yawwa muje please Ina da abinda zanyi sauri ta furta tare da Bude mota ta Shiga baya tace Badi'at shiga muje,Da Yar muryarta Tace Yaya Ameer Ina yini? Lfy Kawai yace,Wai baka ganeta ba ne? Badi'at ce fa Yar gidan kawunka Alhaji Yusuf,Ameer yace oh Naga ta girma ne da yawa,Badi'at motar ta shiga tana satar Kallon Ameer ta Dade tana son Ameer sabo da shi ma tace zata Zo tayi Hutu wajen Mama Suka taho tare.

Washe Gari Fuzail a part dinsa dama baya barin kowa ciki musamman yanzu da yayi Aure, bangaren shuke shukensa Suka je da Manal sun shimfida katon Carpet suna wata game a wayoyinsu sunyi connecting suna Yi tare,Sai cinye Manal yakeyi tace gaskiya na daina Allah sai cinyeni kake Yi,Dariya yayi yace to an daina Zo ki min massage naji kin iya,Manal Tace to da Murna ya gyara kwanciyarsa ta Shiga Masa Massage me dadi,Yana lumshe ido Yana playing musu sweet music a wayarsa,Manal sabo da zuwa school tana haduwa da mutane daban daban duk ta sake Zama tantiriya a wajen Fuzail Amma,Duk wasu wakoki da ake yayi ta sansu sababbin rawa ma ta sansu har ta iya wasu ciki,sabo da kullum a school sai Yan ajinsu sun cashe sakamakon yanzu makarantu musamman private sun Zama wasu iri,har rawa ake koyawa su Manal duk karshen Term,shi yasa basa kunyar mutane yanzu Yan primary ma a Gaban kowa rawa sukeyi sabo da yanda ake girke musu ganguna.
Duk da Haka Manal sai taga Dama takeyi Amma ta iya shi Fuzail ma Bai San anayi ba a school din,sai yaga Manal tana rawa iri iri ya rasa inda take koya.

Sai da ta Gama Masa massage yace Saura rawa,Kunya ta rufe Manal tace Ni Allah kunya nake ji da ka rabu Dani sai da kaga Watarana nayi da kaina idan naji dadin kida,Alright kawo min lemo,Yau fa Fatima tana Birthday a gidan Nan gasu can a part dinsu ana ta rakashewa,Baki Fuzail ya tabe yace Ni birthday baya tsarina kwanan mutum Yana karewa amma Yana murna Wai,shekarun mutum suna ta tafiya Kuma Wai Ana murna,Nidai zanje na kalli Yan Mata,Murmushi Fuzail ya saki yace ke fa ba Yan matan bace?wuce Nan ,Nasan dadinka fa ai Ni ba Yan Mata ba ce,Ameer ne ya Kira Fuzail a waya,ya Mike yace muje na shirya Zan fita,Okay Nima zanje wajen party na kalla,sai kin dawo ya Mike tare da rike hannunta Suka koma ciki,ya dauki wanka zai fita Manal ta hade Rai tace Indai ka wuce 9pm a waje Kawai ka tafi wani bangaren ka kwana kofa Zan rufe,da wuri Zan dawo Karfe nawa kike so? Karka wuce 8pm gaskiya Ni ta Furta da shagwaba tana gyara Masa agogon hannunsa,an gama Ranki ya dade Inshaallah ya Mata kiss ya fice,ita Kuwa gayu taci cikin English gown readymade Brown and White ta wuce wajen Masu party,sai wani kula manal sukeyi har wajen Zama na musamman aka bata,Maza da Mata sun taru suna ta rakashewa.
Sai dare Maimartaba ya Kira Fuzail da Manal sannan ya Kira Ummi da sauran Iyalansa kaf,cikin Fushi ya kalli Yaron Nasa tare da furta Fuzail abinda naji na gani gaskiya ne? Fuzail babu Bata lokaci yace Haka ne amma ai duk kune kuka jawo har na fada wannan halin,zaiyi magana Sarki ransa a bace yace bana son Jin komai kanka kayiwa,ka dinga karya karya ba abinda zaka fada Mana mu yarda Ni tunda ka dawo in Banda bacin Rai ba abinda kake jawo min,yanzu Kai a kanka hakan ya Dace? Shine dai dai ai Maimartaba cewar Fuzail, Baki kowa ya Bude yace to wallahi idan bincikena ya tabbata sai na daureka karkace ban fada maka ba,Dan Iskan yaro duk abinda ake baka gani tunda kazo baka Jin magana sai Takaici kake sa mu.

Abban Ameer yace Babu laifin Fuzail fa me yayi a nan? Duk laifin na Ummi ne ke ba aurenki akeyi ba kinzo kin tare a gidan mutane ko kunya bakya ji,kin Hana yaro sakewa kullum kin Wajensa Kamar kece matar tasa,Maimartaba Ummi itace ta Hana Fuzail shiga bangaren matarsa ta zuba Matakan tsaro,nasan da wannan ai abinda yasa na kyalesu shi Fuzail laifinsa ne akan me zai wani yarda da bukatarta tun farko mahaukacin inane shi,a'a Allah ya bada yawan Rai kaima fa ba son abin Nan kakeyi ba da goyon bayanka sai data kwabe kowa zai Fara zamewa cewar Hajiya Babba,To shike Nan sai ya shirya sabon aure,mace Zan zaba na aura Masa tunda ga matarsa amma Bata da amfani,Fuzail yace Wallahi bazan Kara aure ba,Sarki yace to ba a gidana ba kuwa Ni wallahi da wannan abin kunyar gwara da barinka nayi acan Brazil,Ina Zamana lafiya nace ka dawo,Yanzu Ni a barni Mana na koma,baka Isa ba ka Gama zaman waje sai dai da yawo,tunda Kai baka da mutunci Nan naji ance ka zuga Tanko ka koya Masa karya zai yaudari Yayar matarka shi da Bai iya karyar ba kwabarsa tayi ruwa,Kai Fuzail Wallahi ka kiyayeni daga Kai har Tankon naso daukan mataki a kanku,Fuzail yace Ni da kasa aka zaneni fa a Kan Titi,a gidan Ubanwa? Nima karyar zaka min inji Maimartaba yace wuyanka ya Isa yanka lallai aure za a Kara maka dole tunda matan kake so,Manal ta fashe da kuka ta Fadi a kasa ta fara Rusa kuka tana wutsul wutsul da kafafu,Baki kowa ya Bude aka koma kallon Manal,Hannu biyu ta daura aka na shiga Uku, Sarki Dariya ma ta bashi yasan kuruciya ce,Sarki yace kiyi Hakuri sarauta mu mun gaji aure aure,Bamu gaji Zama da mace Daya ba,Manal ta Mike Tace Ni ba'a kaunata dama tayi waje da gudu,su Na'ima Suka dinga dariya Sarki zata maidawa matarni shine ta fada ta fece.

Fuzail Yana tsaye yace Ni to a barni na koma Abuja da Zama is better bazan iya abin Nan naku ba,Sarki yace da Kai mutumin kirki ne sai na barka tunda dama Mene amfaninka in Banda jawo magana,an baka sarauta kaki karba ba yanda ba ayi da Kai ba,bana so ni Ina da kudina cewar Fuzail,Sannu Billoniare idan kana da gaskiya ka Kira wannan me shigar Kuyanga kowa ya ganta Ni Kuma na yarda a cikin kasar Nan ka zauna a duk inda kake so da Matarka,Fuzail ya saki Murmushi tare da furta Bari a kirata,Manal ya Kira a waya tana ta kuka har tayi shigarta ta Kuyanga taji za a Mata kishiya zata je ta tons asiri sai ga Kiran Fuzail yace ki fito a Kuyanga kizo,Manal da masifa tace ai ba sai ka fada ba ta kashe Wayarta ta fito da sauri ta shigo,Manal a Gaban kowa ta tsaya,kafin Tayi magana Su Tanko sun Fara cewa ita ce wallahi,Tanko harda zakalkalewa Yana ke dai ba Yar arziki bace,bakar tantiriya......Manal ta Bude Fuska ta cire Nikaf Ummi da sauri ta hangame Baki,Fuzail Yana dariya yace to Manal ce kowa ya sheda sabo da Ummi Muka Yi Haka,kullum muna tare,Watarana ma Ummi kina part Dina a Palo Manal tana kitchen,Watarana kina Bedroom tana Palo,Kuma Nima Ina zuwa har shigar Dogarai nakeyi,lokacin da su Tanko suke ganina suna ce min Nadabo ai nine,Tanko ya dafa abokinsa Sani sabo da tsoro ga irin zagin daya antayawa Nadabo,Fuzail yace Ni ka zaga to ba Nadabo ba lokacin Nadabo ma baya gari,su Sale ma Ina Nan da ku sai nayi maganinku akwai ranar da Zan Tara kowa na bada labarin asalin haduwata da Manal da komai ma Amma ba yanzu ba bani da time.
Chapter 69 · 0% Book details