Sashe 32
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameer shi ya samu tiryan tiryan ya kwashe labarin komai ya Bawa Yazed da Malam sabo da mamaki kasa magana sukayi sai da ya cire gashin ma suka tabbatar,Nan take Malam da Yazed murna ta kamasu Kuma Manal ta birgesu, hankalinsu ne ya kwanta da Auren,karshe Suka ce a sirrinta auren,Yazed da Malam Suka Fara tunanin mafarkin Farida da yanda abin ya faru Wato Farida Akan Manal take mafarkin,gashi ita ta fara haduwa da shi Amma ta wulakantashi ta samu dama,Malam a ransa yace iko sai Allah Farida tayiwa kanta Ashe da gaske ne mafarkin nata amma ta gudu ta bar ladanta ita da uwarta mafarki ya Kare Kam,Yazed zai Basu labarin mafarkin Farida Malam Yayi sauri ya canja zancen ya Hana a fada musu,Fuzail yace sisi baza ku kashe ba a bikin,Sannan kafin bikin Inshaallah za a canja ginin gidan nan,Yazed Ma Idan ka karbi takardunka ka sanar min,Yazed shi dai mamaki yakeyi wata azurtawa ta Allah dare daya,a wajen Yazed dare daya ne mana,Malam sai murna da farin ciki yakeyi ,Su Fuzail suna gamawa Suka fito Har Yazed Sai Manal taga Yazed Yana ta murna,Sai taji wani sanyi,Amma gogan Fuzail ko magana baiyiwa Manal ba shi a Dole ya Gama hayewa,Yazed ne yace baza ki raka su ba?Manal Tace to ya kulani ne? Kee Yazed ya daka mata tsawa...mikewa tayi tare da tafiya rakiya,Shukrah ta zauna sai faman satar kallon Yazed takeyi ita dai akwai son me kyau,gaba Daya tunda taga Yazed ta nacewa zuwa gidan tana fakewa da Manal.
Manal tana fita soro inda su Ameer suke Ameer ta yiwa magana itama Suka gaisa ta share Fuzail,ruwa Pure water ta kawo Amma sai ta mikawa Ameer Ruwan Tace Ameer gashi,Ameer Yana dauka yace Ina jiranka a waje ya fice,Yana fita Fuzail ya kalleta Kawai yaki magana sarauta ta motsa Manal Bata sani ba ita,Tace Maimartaba sannu Ina kwana tana cin magani,murmushi yayi yace ki barni naji da abinda yake damuna Manal kika sake bazan sake zuwa ba sai anyi biki,Ka ma Isa ta Furta,lallai Ni kike cewa ban Isa ba,to da ka Isan ne?idan ka Isa ka nuna min isar Mana,Kinci abinci duk Sanda na fito Miki a mutum baza ki iya min magana ba,Shine yanzu kika rainani,Manal Taji bawan Allah da son girman masifa Tace Dan kana ganina karama shi yasa ka rainani Farooq baka Sanni bane Yaro,Dariya yayi yace Shikenan Zan wuce na kiraki yau? Sanda kake kirana tambayeta kakeyi sai yau? Fuzail yace to wannan masifarfa? Kafi kowa saninta ai, sai na kiraki a waya Mayi magana akwai abinda
Yake damuna ki min Addua kawai,to ta Furta tare da Shiga gida,Ameer masifa ya fara Dan Allah muje yadin Nan kaikayi yake min a jiki Nima an jona min masifa,Dariya Suka Yi,Malam da Yazed kwana sukayi suna mamakin ikon Allah.
Maimartaba Suka samu tare da sanar Masa sun fadawa Abba zasu Kai kudin Aure,Memartaba Allah ya haneshi Bincike da Kansa sai yace zanyi magana da Dan Uwana yayi Bincike sosai,Ameer yace tun yaushe yayi Bincike ai ya Gama komai zaizo ya ma bayani,Sarki harda murna,Ana gobe za a Kai kudi Abban Ameer yazo ya samu sarki yace nayi duk Binciken da zanyi Yarinyar Yar malamaice Basu gaji sarauta ba Amma dai suna da asali da rufin asiri,Nan take sarki Ya Bata Rai yace what? Nufinka talaka na ce? Abban Ameer shima yayi tasa karyar yace a'a Babanta dai Dan Kasuwa ne na gaske ma Kuwa ya shahara,Sarki ya tabe Baki yace na rasa irin Yaron Nan me kwashe kwashen masifa ga Yara an Kawo Masa na mutunci yaki ya Kare a talaka,bana murna da wannan auren nasa,tunda Naga Yana nuku nuku nasan ba abin arziki a ciki,Abba yace tunda Yana Sonta ka kyale shi,Sarki yace ba ruwana wallahi shi da Mahaifiyarsa nasan baza su Kare lafiya ba,Kuma ba ruwana ko Baki tayi masa.
Allah ya gani nayi abinda Zan iya,kuma kasan Yan Uwansa na gidan Nan da Mata na ko? Idan ta shigo ta Zama Allah sarki babu me Shiga lamarinta Ni kuma bazan tsawatarba tunda shi ya jawa Kansa,Abba yace wannan fa ba tsari bane Yaya,babu Wanda aka Haifa da arziki ko wani mulki,Sarki yace ai Danka ne kaje kuyi abinku Allah Sanya Alkairi Amma idan matsala ta faru ba ruwana,Abba yace tunda ka Amince ba damuwa,sai ka fadawa uwarsa taji,Abba yace ba yanzu ba sai an daura za a fada Mata,Hmmm Kawai sarki ya furta ransa a jagule tun Bai ga Budurwar da iyayenta ba baya ma marmarin ganinsu.
Washe gari Abba da wasu Yan Uwan nasu aka Kai kudin auren Manal Itama su Kawu Salahu ne Suka karba,Annatu sai murna take yi,Yarta zata Yi aure,dubu dari biyar aka kawo kudin aure amma sai Yazed yace dubu sittin ne, su Farida Suka dinga yiwa Manal dariya,Lefen Ma Yazed yace ko an hada Kar a kawo sai bayan an daura Aure.
Babu Bata lokaci Fuzail yasa aka fara tsara gidan Malam da gini me kyau sabo kar azo aga gidan matarsa a Haka a halin Kuma Yana da kudi ace ya bar Iyayen matarsa a lalataccen gida suna Shan wahala abin a zage shi ne, ,kullum Ana Aiki ba dare ba Rana,Malam yace shine ya samu wasu kudi yake ginawa abinsa Yaran Basu Sani ba,Su Farida sai iyayi akeyi harda cewa Manal za a tafi gidan Talauci a bar Mana gidanmu na Yan gayu,Yazed Dariya Kawai yayi.
Haka Fuzail Yana zuwa zance akan lokaci,yayinda Suke Bawa Shukrah kudi tana tallafar Manal ta ko ina yanda baza ta Gane ba,Haka Yazed da Malam Kakarsu ta yanke sake ta accnt Fuzail yake tura musu kudi akan lokaci ai tuni Gidan Malam ya canja da yaransa,Yazed wani kyau ya Kara da haske kullum dinkuna yake sawa masu kyau Yana fesa gayu abinsa.
Hajiya ganin Basu da wata matsala komai a gidan Shar za a ci a koshi ga makaranta Yara suna zuwa ba matsala ga sutura yanzu sosai Malam Yana ta gyara halayensa wajen kyautata musu Haka jikinsa Yana ta sauki Yana takawa kadan kadan har masallaci Yana zuwa yanzu,Ga gida ya dauki kyau dagwas,Manal tayi Niyyar Shan shagalin biki Yazed yace babu bikin aure kawai za a daura a kaita,Farida Suka dinga dariya ana Mata habaici Manal harda kuka.
Tunda Belloti ya samu labarin Auren Manal yace lallai Ja'e yayi gaskiya wahala ta saka Riga da wando Kai har da Singleti Amma ba komai Bari nayi kudi wallahi ko waye Bai Isa ba sai na kaishi Kara Nan gaba,Annatu Kuwa kayan gyara ta hadawa Manal aka Kai mata kafin taje, Manal Bata sani ba Yazed ya dauki Su Fuzail har wajen Annatu Suka je suka gaisar da ita itama Yazed ya Mata bayanin komai a sirrri,Annatu harda kukan Murna Ashe arziki ne ya Kira Manal Birni,ai Kuwa ta Sha kyauta a boye sabo da can ma da shigar Talaucinsu Suka je Kuma a motar haya.
Fuzail ne yace da Maimartaba Manal zata Zo ta gaisar da su yace Kar ta sake tazo ta Bari idan an daura shike nan,Fuzail yaji Haushi yace nifa idan aka takura min Barin kasar Nan zanyi wallahi Kuma bazan sake zuwa ba ko da yawo,Sarki yayi banza da shi har ya tafi,Abban Ameer ganin Abubuwa zasu iya kwabewa ko yaushe yace da Ameer suyi shiri a saka ranar aure Kawai tun kafin gulma taje kunnen Maman Fuzail,Sati biyu aka tsaida magana,Manal tayi mamaki amma Malam yace Haka yaga dama,Dama anyi sa'a Manal a birni Bata da kowa na kawaye sai Shukrah,Haka Fuzail Ameer ne sai Danginsa
Yau Farida taje gidan Sarki taji Ana labarin Yarima Fuzail zaiyi aure Nan da sati daya,Kuma Yarinyar Yar talaka ce a Nan garin take,ai Farida da kuka ta dawo gida ta bawa Hajiya labari, duk ta haukace Yarima zaiyi aure,Hajiya Kamar zata Yi hauka Haka take cewa sai naci uban Dan Haru Haru,ko Malam din ma an daina Fada, makaryacin banza ba abinda ya iya sai karya cewar Farida,Wasa Wasa Farida kwana tayi tana zubar da hawaye,Manal Taji tausayinta ta dinga kwantar Mata da hankali Tace Inshaallah Fuzail naki ne Yar Uwa zaizo ya aureki karki damu daula da kudin Nan sai kin ci,Sai kin hau jirgi,sai munje makka,Farida ta Bata Rai Tace kije Makkah? Lallai kece ma kike auren Dan Sarkin Ashe? lallai to ki cire Rai wallahi ko airport baza kije ba,Manal ta zaro Ido Tace tab Allah ya sawwake Miki Farida wannan wacce bakar zuciya ce dake? Takalmi me tsini ta dauka ta bugawa Manal a goshi,Goshin Manal ya fashe tare da kumbura sabo da bakin ciki za ayi bikin Manal shine ta fasa Mata goshi Dan aga Amarya da fashashen goshi,Yazed Yana shigowa yaga Manal tana danne goshinta da tsumma ransa ya baci yace mene ya faru,Manal Tace Farida ce ta fasa min goshi Amma ai Dan kadan ya fashe Yaya Kyale zancen,Ai Yazed yace wallahi tayi karya Bulala ya samo ya Kama Farida sai da ya Mata laga laga sannan ya kyaleta Yana masifa Dan Iskanci za ayi bikinta ki fasa Mata goshi Yar Iska Yar bakin ciki.
Chemist ya kaita aka Mata treating suna dawowa Fuzail yazo sanye da Shadda Fara me Araha yayi kyau matuka da gashinsa dai,Fuskar Manal dinsa ya kalla yasa yatsa a habarta tare da dago da Kanta yace me ya samu goshin Kuma? Manal ranta a bace tace ba komai,Ya Zaki ce ba komai waye ya miki wannan raunin? Farida ta Furta tare da yin shuru,Tsaki Yaja kawai tare da furta kiyi Hakuri Bata da hankali Naga alama, Manal tana kumbura Baki irin na Yan tabara ta furta Amma dai tasan kullum Shukrah ke kaini wajen gyaran jiki yanzu ta dawo da gyaran Baya,Dariya Fuzail yayi yace gyaran yaushe zai dawo baya Kuma Kai Baby ai yayi min haka,Manal tace ai dai an cuceni kafin ya warke fa?Amarya da kulu a goshi.