Sashe 45
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sabo da Manal ba a dauke ta komai ba shi yasa aka Bata Bayi Guda biyu kacal Bayan wasu nasu bayin barkatai ake Basu.
Kanta a kasa tana tafiya a hankali cikin Part din na Iyalan sarki, Yan gidan Mata da maza suna ta wucewa Ana kallonta kamar watan ramadan sabo da Kyawun Manal,Gashi tayi kyau tayi shiga ta Alfarma babu raini,part ne Dan ubansu Suka shiga cikin wani kantamemen palo na Alfarma sanyi da kamshi ne ke tashi babu kujeru a ciki Wani carpet ne me tsadar gaske ga abubuwan ado da wasu manyan Pillows na fata,yasha ado da golden abubuwa,Manal ta hango Iyalai wasu manyan mazan yayyen Fuzail da matansu da yaransu sun Sha rawani,Wasu matasa sun Sha wanka,sai Iyaye Mata ga Yan mata Nan Yan karya, Gefe Ummi ce tana Jan carbi sai hamma take Wai Bata samu bacci ba jiya,Tasha kayansu na larabawa,Gaba Daya idon kowa Kan Manal ya koma,Duk yanda Suka Kai da son kin kallonta abin ya fassakara,duk Manal ta diririce,jikinta sai rawa yake Haka ta Dan fuske,Hajiya Babba Uwar gida kuyanginta ta kalla da izza,Suka ce Samu guri ki zauna Hajiya Babba ta Baki dama,Manal ta samu a nutse ta zauna sannan ta kalli mazan manyan yayyen Fuzail tace Ina kwananku? Barka da Asuba ake cewa cewar wata Jakadiya,Manal tace Barka da Asuba da fatan an tashi lafiya? Ko amsawa basuyi ba sai Jakadiyace ta bada amsa Wai sun amsa,Manal a ranta Tace cab Dole Fuzail ya tsani gidan Nan wallahi ko Ni bana so Kawai ya canja min gida a wata Unguwar Ni wallahi bazan iya ba,Kamar zatayi kuka kanta a kasa Suma matan ta musu Barka da Asuba Suma dai Basu Suka amsa ba,Fuzail ne ya shigo da kamshinsa ya Sha gayu,ko kallon inda Manal take Baiyi ba wajen Ummi ya wuce tare da Zama kusa da ita ya nuna Kamar Bai San ma Manal ba,Yan Uwa Suka ji dadinsu Wai Dan Kawai Manal ba jinin sarauta bace duk sun tsaneta,Ummi ta gaisar gaisuwa ta Mata ta musamman,Fuzail ya harari Manal da kyar ta danne Dariyarta shima haka.
Ummi Tsaki ta ja ma Bata amsa ba Kuma tace Kar wasu kuyangi su Mata shishigi su amsa.
Abinci Yan aikin Suka zubawa kowa abinda yake so,anzo Kan Manal Fuzail sai inkiya yake Mata da Ido Wai ta zabi irin nasa,Ummi Saura kadan ta kamasu ta kalli Fuzail da sauri ya daga Kansa Sama ya fara wakar karya la...la..la,kowa sai da ya kalle shi sabo da sun San bashi da wasa Maganar arziki ma ba yiwa mutane yake ba,Manal duk Ido na kanta kasa cin abinci tayi,Amaryar sarki me kallon Gabas ta Gaza gani tace ke idan baza kici ba ki tashi ki tafi kin samu ma Hajiya Babba tana kaunarki tasa a kiraki kin shigo family Zaki Mana Iyayi abinda ma Bai dace ki shigo Nan ba,Fuzail haushin Amaryar sarki yaji ya galla Mata harara Ido da Ido,Amarya ta rike Baki tace Fuzail Ni kake Harara akan matarka? Jin Asirinsu zai tonu da sauri yace Ni Kuma? Na harareki akan wannan abin? Wai kun manta me nace ne? Ummi tana cin abinci tana murmushi ta Furta ai Watarana son yana da wannan kallon karki damu nature dinsa ne,ai ko Fuzail yace matsalar Ido gareni idan ya motsa sai nayi wata guda Ina irin wannan kallon,Dariya Kawai Fardan babban Dan sarki yayi,mazan Nan Shuru sukayi Kawai Amma Basu yarda da karyar Fuzail ba,ai Kuwa Fuzail yabi ya tsani Amaryar sarki daga ta yiwa matarsa masifa,tana yin magana sai ya dinga gallawa Amaryar Sarki Harara Wai duk a ciwon idonsa ne ya motsa.
Manal tana kallo kamar tayi Dariya Amma ba dama,Bata Rai yayi ya kalli Manal Fuska ba Rahma yace ke Miko min abincin Nan naki ki zuba wani da kanki Amma Baki Isa kinci irin Wanda zanci ba ya kwace plate din Gaban Manal da tea dinta da komai ya fara cinye nata ya ajiye nasa duk Dan yaci bakin Manal ne,Wai spoon din da ya shiga bakinta yake so yaci da shi sabo da so,cup din ma saitin inda yaga jambakinta ya kafa a bakinsa ya cinye komai ya shanye,Manal tasa Hannu zata janye na Fuzail Daya fasa ci Ummi ta bige Hannunta Dan Ubanki Bai Isa ya fada Miki kiji ba,yace baza kici irin nasa ba ya karbe naki shine Dan rashin kunya Zaki sake daukan nasa? Da kudin Ubanki a ciki,Jin an ambaci uban Manal babban Dan sarki Fardan cike da takama ya daga Hannu yace Bama son ana wannan a masarauta baza mu lamunci cin mutuncin wani ba,ta Zama Surukar mu ko ba komai Kar a sake Bama so,Mukus Suka Yi sabo da suna Jin Tsoronsa Babba ne gashi ba Wasa Bai son Kuma wulakanta mutum ko kuyangi Wajensa suke Kai Kara idan an samu matsala,Fardan me jiran gado yafi sarki Adalci da sanin ya kamata.
Manal tashi tayi zata tafi jin za a fara zagar Mata Uba,da Sauri Hassan da Hussain suka Mike Aunty Bari mu taho Miki da abincin can,Yan matan su Fatima Baki Suka tabe suna ciye ciyensu masu latsa waya suna yi,Hassan Maid ya bawa abincin Manal Suka daukar Mata Suka rankaya gaba Daya Suka bita,Zasu Fita kenan Fuzail ya taso Wai zai fita Yana sani ya bangaji Manal Saura kadan ta Fadi Fuska ba Rahma,Manal itama tasa takalminta tare da take Masa kafa Daya ta murza da karfi ya kwalla kara,Yana dingishi ya kalli Manal Suka hada Ido da wayo ya Mata magana da Ido Wai naji zafi fa da zafi,Manal ma tace da Ido jiya marina kayi Nima,Da wayo tayi magana a hankali Tace afwan Dan Allah ka yafe min,Ummi Bata sani ba ta taso fuuuu tare da daga hannu zata Mari Manal da sauri Fuzail ya rike Hannun Ummi tare da furta kyaleta zanyi maganinta yau sai tasan da Fuzail tayi,tayi da Dan halak,dukkan Iyalan Sarki da Masu Aiki Baki Suka Bude yanda Manal ta samu power harda dukan Dan masu gida.
Alright Ummi ta furta ka tabbatar ka dauki mataki a kanta bazan lamunci wannan abin tazo ta Raina mu ba,Fatima da Na'ima tare da su Naja'atu Suka ce Yayan Zaki taka?lallai wuyanki ya Isa yanka wallahi sai munsa Kuyangu sunyi maganinki,Manal ta kalli Na'ima da tayi Maganar tace dalla kalleki ai bakinki ne kuyangar ai ke da kuyangin ma kika Yi Kama Baki Dace da Sarautar ba,Matan Sarki Suka Bude baki,Manal Tace ku Yara ne Ni Auntynku ce daga yau wallahi kusan Maganar da zaku fada min bazan dauki raini ba,ba ruwana da sarautarku inci mutuncinku ba komai bane a wajena, idan manya zasu min ku kyalesu suyi min wannan Iyayena ne Zan dauki Hakuri amma ku Kam nafi karfinku,Shuru kowa yayi ana mamakin Amarya daga zuwa jiya,Ummi murmushin Takaici tayi tace nasan daga gidan da kika fito abinda yafi Haka Zaki aikata,Fuzail ya kalli Manal tare da kyafta Mata Ido Wai ta birge shi Good,a fili kuma ya Bata Rai tare da Murdewa Manal Hannu Kuma taji zafi yace Dangin Nawa Zaki ciwa mutunci tun yanzu? Tun ba aje ko Ina ba? a hankali yanda baza aji ba ya furta kiyi Hakuri Dan Allah nasan kinji zafi bazan sake ba,Kuma Yana murde da Hannun nata Bai saki ba,Manal ta samu kafarta ta daki kaurinsa da zafi itama ba shiri ya saketa,ta fice da sauri,Hajiya Babba Tace tab wannan Amaryar Yar Yi ce baza ta kyale kowa ba.
Ummi Tace kayi dai dai ,Yace Ummi muje part dinki na huta muyi Hira Dan Baki San ma abinda nake Mata bane idan naje Muka hadu a Nan Watarana Zaki ji labarin na ballata a gidan Nan.
A waya Kuma Fuzail text na ban Hakuri ya turawa Manal,Itama ta bashi Hakuri irin dukan da ta Masa a kafa.
Tuni Fuzail ya janye Ummi zuwa dakinta ya dinga janta da Hira bayan Kuma yasa Wasu Kuyangi a boye na sirri Wanda a bangaren su Ameer suke Aiki sune Suka raka Manal part dinsa ta kalli ko Ina a part din mijinta,komai fari ne na part din,da taga part din Fuzail sai da ta Raina part dinta duk kyansa,Sauran part na gidan aka nuna Mata gaba daya sun mugun dadewa suna zagawa ta kalli iya inda ta iya ta koma part dinta yau da dare wata basaja zasu yiwa Ummi Manal ce zata je part din mijinta,bangaren Fuzail Kuma ya Gama shiryawa yanda yau zai angwance ya kwashi zakin Amarya komai sun tanada shi da Ameer,Amma ya yiwa Manal wayo, sabo da taje yace ai Romancing zasu Yi Kawai sai bacci ita Kuma ta yarda.
Su Annatu Kuwa Fuzail Yana part din Ummi yayi waya da Ameer aka dakko su zuwa gidan Sarki zasu Yi Sallama da Amarya sannan za a rakasu wajen matan sarki da Baban Ameer a madadin sarki su gaisa ayi magana irin ta manya tunda zumunci Dole ya kullu,Wajen Abba aka fara kaisu Suka gaisa ya musu kyauta ta girma tare da godiya na Basu 'ya da sukayi,Matan Sarki aka Tara Suma su Uku harda Ummi tazo tana yatsina,Hajiya Babba ce kadai tayi godiya Kawai suna ta wani yatsina musamman Ummi da Amaryar Sarki,Hajiya Babba ta kalli Hajiya Sharifa tace ya sunanki ke? harda gyara Zama sannan Tace Hajiya Hyarifatu Amarya da ta tsakiya Suka wani kwashe da dariya,Hajiya Babba tace Mene Haka Dan Allah? Shuru sukayi Tace Mashaallah Ina Uwar Amarya aka nuna Annatu Tace ai Naga Kama da Amaryar Dan namu,Wata Yar yarinya ta gani tace ke ya sunanki? Hajiya Sharifa da Shishigi tace sunanta Hemsiyya, Tace shamsiyya ko? Hajiya Babba ta tambaya Suka ce ae,sunzo tafiya Wata Shatu Tace to He Watarana idan Allah yasa Muna da nisan kwana.