Sashe 15
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni a Ina Zan kwanta kenan Manal ta tambayi kanta a ranta tana kallo ya fara bacci hankali kwance,Tace yau Dole dakin su Farida Zan koma na kwana ai bai Dace na kwana da Namiji a daki Daya ba amma Bari na jira baccinsa yayi nisa sai na tafi, Haka ta zauna a gefen katifar tana jira baccinsa yayi nisa Wutar dakinta ta kashe dakin ya dauki duhu,Gyangyadi ta fara har ta fara bacci Bata sani ba itama sabo da gajiya bacci ne yayi awon gaba da ita a Haka a zaune, har ta kwanta a kasa kusa da katifar Bata sani ba ta manta da wani bako ma.
12am sanyi sanyin da ake Yi yasa tana bacci Bata San ma ta koma jikinsa tana furta Annatu na,kanta ta daura a saman kirjinsa tare da Rungume shi sosai ta kankame shi,shi dai cikin bacci yaji wani dumi me Dadi da jiki me laushi a jikinsa sabo da Haka baccin ya Masa mugun Dadi,a Haka suka ci gaba da bacci abinsu Manal kwance a jikinsa wani kamshi na Fitowa daga jikinsa na musamman me Dadi kasa kasa.
Basu farka ba sai da Rana ta fito sannan bugun Kofar Manal da ake faman yi ya tashe su a bacci,Da sauri Manal ta janye jikinta Dake cikin nasa a kunyace duk ta rasa inda zata sa kanta sabo da kunya tana mamaki ya akayi ta zo saman katifar ma,Da sauri ta bude Kofar tare da leka iya kanta waje taga Farida ce,Dariya Farida tayi Tace kwartuwa oh Manal an San kwana da gardi a daki,ko kunya Baki ji ba ki rasa Wanda ma Zaki kula sai wannan talakan marar asali Wanda ba'a San asalinsa ba,Mahaukaciya a rayuwar yanzu masu kudin ma ya suka Kare to wallahi duniyace take so ta tashi Nan gaba ance Kafin kiyama ta tsaya sai an shiga tsananin Talauci kasa zata daina yin noma da yawa za a rasa abinci Kinga mu da muke Yan karshen zamani ai idan Muka auri masu kudi mun tsira daga wannan ko da lokacin ya riske mu.
Amma ki duba Malam yanda yake Talaka duk danginmu babu Wanda zai dauke Mana matsalar dubu goma,Rance ma babu Wanda zai bamu bare ya iya daukan nauyinmu,Kalli Manal Malam da mu yaransa yanda muke karbar Cable ta ko Ina Talauci yana ta zanemu da cable ta ko Ina,Dariya abin ya bawa Manal,Manal tace Farida Idan da cable yake dukan mu ai da sauki Ai dankon injin Nika Talauci yasa yake faman ragargazar mu,gwara ma ku a Dangin Mamanku akwai masu Dan rufin asiri Kuma suna taimaka mu,mu Kuwa ai da muje Dangin Annatu Neman taimako gwara mu shiga duniya Baital Mali yafi sauki amma babu Wanda Allah ya Halitta da arziki a Nan duniya ya samu,Kuma mu godewa Allah duk da Haka munfi wasu,Ki Gane Anty Jirani Wada babu kyau wulakanta Dan Adam tunda baza ki iya taimako ba ki kyaleni,Da talaka da me kudi Allah ne yaga dama ya bawa kowa Kuma zai iya azurta kowa lokacin da yaga dama,babu dabara da wayon Dan Adam da zai bashi Abu sai Allah yaso.
Baki Farida ta tabe tare da furta to ckin talauci Zaki kare,Hajiya ce ta karaso wajen tare da shigewa Gaba Daya dakin Manal tana tafa Hannu tana Salati ganin Fuzail kwance Yana ta baccinsa Amma a zahiri Yana jinsu Kuma ya fahimci masifa suke yiwa Manal a kansa,Suna ta zaginsa,Hajiya ashar ta dinga dura masa,Manal ta juyo da masifa tace Hajiya Ina ganin mutuncinki karki sake zaginsa bako na ne bana wani ba,sannan Nan gidan ubana nane ko Malam ya rasu Ina da gado a gidan, ba ruwana da ku kuyi rayuwarku nayi tawa ko Yaya Yana Nan na tabbata bazai hanani taimakon bayin Allah ba Wanda Basu San garinsu ba,Basu da gidan Zama ga hatsari sunyi bazan iya sallamarsu ba wallahi sabo da Haka babu Ni ba ku kowa yayi harkarsa naji kwarto na kawo idan ya min ciki kunga dama kuzo suna ko barka taja Tsaki,Hajiya da Farida Suka tafi suna zagin Fuzail Wanda yace sunansa Farooq.
Bayan sun tafi Manal ta kalle shi ya Bata tausayi ya zauna a gefen katifar tare da zuba tagumi,Manal Tace kayi Hakuri sorry Bari na kawo maka sabon Brush,Hijab ta zurma ta fice da gudu da Naira dari taje ta siyo Masa sabon Brush,Kayansa data wanke ta Shanya su ta Iske Farida da Hajiya sun dauka sun kone su sai ganinsu tayi suna cin wuta falfal,Fuzail Murmushi Kawai yayi tare da karbar Brush da Toothpaste din da ta kawo Masa ruwa a buta can jikin pampo yayi Brush a Nan lokacin ta Kai Masa ruwan wanka me dumi toilet,a ransa Kamar zaiyi kuka Manal tace kayi wanka sai muje Asibiti anjima kaga halin da Dan uwanka yake ciki,Haka ya shiga da kayansa da Sabulun data bashi yayi sauri yayi wanka a ciki ya maida kayan jikinsa ya fito fit da sauri,yanda Manal taga ya fito da sauri tayi mamaki sabo da ita dai tasan kafin ya Shiga ma Sai da ta wanke Masa toilet din.
Itama wanka tayi sabo da shi a toilet ta shirya ta canja wata Yar doguwar rigarta ta gwanjo me gajeren hannu pink duk ta ji jiki sai dai tana Mata kyau,da wani kofin Silver ta shigo da Dan karamin flask a Hannunta da spoon da sugar,a gabansa ta Ajiye ta bude Koko fari tas da kosai manya,yasan Kosai Amma Bai taba ganin Koko ba,Yace sunan this? Yana Nuna kokon da yatsa,tunawa yayi ai da sauri yace No..no I knew,na sani ya wayance,Manal Tace Wai Kai da baka iya hausa ba a Ina asalinka ka taso? Kawai yace Wani Kauye ne a Niger mana, French na iya,Manal Tace Oh Allah sarki,a Haka ta zuba sugar a kokon itama ta sa spoon dinta ta fara Sha,shima Haka da nasa Spoon din da kyar yake Sha yafi cin kosan, har Suka Gama sannan Tace an kone maka kayan sai dai ka zauna da wannan na jikinka kafin Nan gaba,Bai Gane ba yace meaning what? Manal Baki ta turo tare da furta Kai Farooq Ni na gaji da halinka na rashin iya hausarka kasan dai ba Jin turanci nake Yi ba,a Niger din a wanne yankin kake da har zaka kasa Jin hausa,Nima daka ganni Hausar Nan ba Isa ta tayi ba da kyar nake yinta tashi muje Asibiti wajen Dan uwanka Ni ai cin Fuska kake min Dan kaga ban iya turanci ba ta karasa da shagwaba,Dariya ta bashi yayi ta a ransa kawai.
Wannan Maganar da tayi ya fahimta sai ya Mike da tarin sumarsa da gemu da saje me uban yawa,mayafinta wani tsoho tukuf Baki ta yafa tare da saka slifas dinta local, kallon takalmin nata yayi a ransa shi ko a toilet bazai iya amfani da wannan local takalmin ba,Fitowa sukayi a tare da Takalminsa flat me Dan kyau Wanda da abinsa yazo dama,Suna Fitowa Hajiya da Farida suna tsakar gida Farida Ta kalle shi ta fetsar da Yawu gefe Yana kallonta a ransa Yana mamakin me ya Mata ta tsane shi haka Bai San Farida ita Bata kaunar talaka ba ita da uwarta tanadin shiga daula suke Yi, gashi Kuma ya Mata laifi sunyi sanadin da Bata ga masoyinta ba Fuzail Dan sarki.
Farida tana yatsina Fuska tace dama ance Yan Fulani ba abinda Suka sani sai sex always sex..sex...a daji ma babu komai sai sex,ance Haka ma kuke bin yan uwa da sex da juna wannan tabi Mijin wannan,har Yan uwanku binsu kuke Yi,to wallahi Bari Yaya Yazed ya dawo sai mun fada Masa kin kawo katon gardi Kuna Sex kullum Baku da Aiki sai Zina,Manal kalleki 17yrs kin San Namiji,kin San bin maza,Fuzail ya Gane duk abinda take nufi sabo da Farida tana hadawa da turanci,Yaji Haushi a ransa sosai shi a rayuwa ma in Banda Manal babu wata mace a duniya da ya taba yiwa kallon kwaf.
Shuru ya musu,Manal tace muje Farooq Haka Suka fice tare suna tafiya zuwa gefen Titi,Manal sai surutu take Masa shi Kuma wani ya Gane wani baya ganewa,Tace a gidanku kuwa Kun taba kwana da yunwa Baku ci ba? What? Ya sake tambaya tace babu abinci har kwana Daya ta Masa zancen tana nuna Masa da hannu,Ohhh ya furta Yana murmushi yace Yes Uku kwana,Dariya ta dinga Yi Tace Dan Niger Kawai kwana Uku ake cewa ba Uku kwana ba,No Uku kwana,Kwana Uku Haka yes,murmushi yayi suna tafiya sun jera yace na gani,Na Gane zaka ce fa, alright na gane ya furta da kyar ,Manal tace Zan koya maka hausa Kai Kuma ka koya min yaren faransanci da turanci,Okay ya furta yasan Bai iya french ba Amma zai mata yaren Brazil Kawai ya barta a French,Tace Ina jinka har kwana Uku Kuna Yi ba abinci? Kai ya daga Mata kawai,Manal Tace Ni fa ban Gane ba sai kace wani Dan sarauta kayi ta yanga gaka da Izza da Gadara Naga Alama talaucin da kuke ciki Bai koya maka darasi ba,ita duniya a Sannu ake binta,kana Dan talaka futuk ka dinga wannan Gadara wallahi ka canja hali,gaba Daya ka faffake Hanya sabo da Izza Haka ake lamarin duniya ga Gadara ga rashin kudi to wallahi Dole ka daina wannan halin ba tsabiyar kirki bace,kace zaka zauna Dani har sati Daya kafin ku samu wajen Zama to Dole ka daina wannan mummunar Dabi'ar taka,shi dai abinda ya tsinta ya gane Yana ji kuma,da kyar yace Haka nikai,Haka nake zaka ce,Okay Haka nake ya furta Yana dariya.