← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 95

Sashe 52

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya da jimami Tace ta kaimu kasa wallahi Malam,Malam yace karya ne wane mutum inji mutuwa Surukarta Bata kaunarta har yau,fada min sunan Surukar a sa ta Kara tsanarta da Alama ta fara son Yarinyar Malam ya furta Yana kallon wata Yar tukunyarsa ta tsafi da take gabansa,Hajiya Tace yawwa tunda Bamu samu ya auri Yata ba Itama Kar a Bari taji Dadi a gidan,a sa Surukar ta Kara Mata tsananin yanda zata Sha azaba da bakar wahala karatun ma Kar a Bari tayi a Hana a cireta daga school Malam,Mijin ma ya tsaneta,Malam ya sake leka tukunyarsa na wani lokaci yace tab Aiki ja,Sai dai ita Suruka ayi Mata ta Kara tsanarta amma Wannan Yarinyar takadara ce makaranta sai tayi ta Dole,asirin Nan bazai ci ba wallahi Kar ma mu Bata lokacin mu,Haka Mijin Nan kaunar Yarinyar tayi Masa yawa asiri Yana Aiki ne da karfin zuciyar mutum.

Idan mutum Yana da taurin zuciya to kafin asirin yayi Aiki Kansa akwai wahala sabo da ba adddua bace Aljanu zamu tura magana ta Allah idan mutum mugun kafaffe ne me masifar taurin Kai Aljanu suna Shan wahala a Kansa,shi yasa asiri yafi saurin Kama Mata sabo da raunin su na zuciya,Wannan Mijin nata zuciyarsa kyam take wallahi ko Uwarsa da yafi kauna Bata Isa ba akan wannan Yarinyar Kam sai dai a kashe shi,kirji Hajiya ta dafe tare da furta shege da gani dama zuciyarsa Bata rawa,Malam yace ke wannan Yaron Me martaba ya Gama da su,Addua yasa ake musu duk sati sai anwa kowanne Dansa sauka ayi yanka da sadaka,duk Makkah da kika ji Yana yawan tafiya duk akan yaransa yake zuwa Yana musu dawafi Yana musu Addua Allah ya Kare su,Baya bacci kin dai ganshi Kamar Bai da Imani to malamansa suna Nan a fada waresu akayi musamman Kawai akan Iyalansa suke Addua Kuma yafi dagewa akan Fuzail sabo da Yana wata kasa inda ba tamu ba,sabo da Haka wallahi ko ba a guna ba Karki sake ki kiyayi taba wannan Yaron Billahillazi gidanki zai Kama da wuta Zaki Yi muguwar asara ko ki rasa ranki ko na wani naki,ke kin San sarauta ba Wasa ba ke kin San Haka Kawai ma tsafe tsafe suke bare an taba su.

Ba shiri Hajiya Tace a tsaya iya Uwarsa Kawai ta sake tsanar Manal,Malam yace ya fiye miki,yarki Kuma nata Mijin ya kusa Yana Nan tafe da manyan motoci,Kuma tuni ya ganta Yana Sonta itace Bata sani ba kuje ku jira shim mijinta ya kusa zuwa kusan yanda Manal ta samu nata shima a Haka zai zo banbancin kadan ne.
Hajiya dubu goma ta ajiyewa Malam sabo da farin ciki,har zata tafi ta dawo tare da Kara Masa dubu biyar Tace a siyawa uwargida Omo ace Ina miko gaisuwa Malam yace zata ji sai na jiki Tace to.

Tana komawa gida taga Malam ya dawo Yana Neman Farida Hajiya bala'i ta Bude da masifa an takurawa yarinyarta ba dama ta fita Kar a sake takurawa Yarta yawwa,Jin Haka Malam ya kyaleta tare da furta gaki Nan ga Farida Nan Hajiya idan gata muke Mata Zaki gani na barki da Farida, Inshaallah bazan sake magana ba,ae yafiye maka aikin banza an bi an sa Mana Ido shegen Yazed din Nan ai na gano duk shi yake zugaka.
Ficewa Malam Yayi ya bar Hajiya tana ta bala'i.
Farida Kuwa a gidan Babbar kawarta Walida sukayi wanka Suka cakare cikin matsatsun Kaya sun Sha kyau Kam wani siririn mayafin Suka rataya a kafada me Napep din Walida yazo ya dauke su sai gidan Solo,Dake Walida ita ta gagara wani Chairman ne na local Government ya Kama Mata gidan haya farkarsa ce taci Uwar su Farida a Iskanci.

Yau Su Tanko an saki Salary karshen wata yayi,Tanko a bakin gate tare da abokan aikinsa ya zauna Yana irga kudinsa casss....Yana washe Baki yace yau akwai kara'i wasu kudin ya ware yace wannan na Gyatumata ce,wannan kudin kashewa kafin wani watan,ragowar ya irga yace yau da Yamma akwai kallo a gidan Solo na Gaza,yau Ingallo zata cashe a can Zan yayyafa Mata liki,Sani Abokin aikin Tanko ya kwashe da dariya tare da furta shegiya Ingallo tana birgeni Kaga in tana kada kugun Nan tana tafiya da Ni,Tanko yace ai shi yasa Ni sai lokacin da take tsaka da kada shi nake zuwa Ina Fara like Mata kudin a duwawunta Ina wayo Ina shafawa ai fakewa nake da liki,Suka sheke da dariya tare da tafawa,Sani Yace ba abinda nafi so irin in shiga layin karuwai daki Nan masu Zama Tsirara me bukata yaje kasan fa Ni ba kudin bin Mata gareni ba Haka nake zuwa Ina zagawa Ina kallonsu Ina rage zafi ko wacce sai na leka dakinta na kashe kwarkwatar idona da kallo.
Tanko yace Ni ba ruwana da wani kallo Rawar Nan tafi birgeni sabo da ita nake zuwa zanyi Hakuri har na samu me rangwamen gata na aureta,Allah yasan manufar jaki da bashi kaho ba,da wasu mutanen Allah ya Basu kudi da irin barnan da zasuyi Allah ne ya sani Amma sai ya sa musu Talauci kaga Allah ya taimake su cewar wani Shehu shima,Wai Tanko Ina budurwar Nan taka Farida ne? Tanko yace tana can ban San Ina ta shiga ba kasan fa Ina son Yarinyar Nan Kawai wallahi Dan baza ta aure Ni bane,Yayar Matar Yarima Fuzail ce fa,tafi karfinka Tanko cewar Shehu,Tanko yace ai Ni ya Dace nace nafi karfinta Kuma ko yanzu kasuwa ta watse Dan koli yaci riba sabo da ba abinda ban taba ba a jikinta kyauta.

Kai mufa muke kaskantar da kanmu Amma mu ya kamata ace muna yanga ma kamar mu masu Aiki a gidan Sarki Guda muma fa masu kudin ne kana Aiki a gidan Sarki Haba Haba ai wallahi kamata ma yayi ace Yan Mata ne suke bin mu ba mune muke binsu ba cewar Tanko harda cewa kwana Nan Zan fara daukan wanka Nima tsaftar Nan ai ba gagarata tayi ba,ba yabon Kai ba Dan Kawai Baki ne Ni Amma jibi hanci,Bille a Fuska ba kowa yake wa kyau ba Amma Ni kyau yake min sabo da baiwata,Dariya su Shehu suke ta Sha yanda Tanko yake yabon Kansa,Sani yace ai Kai Tanko wallahi Yarima Fuzail Watarana yana tafiya da Kai Unguwa Matukar baka Fara tsafta ba wallahi sai ya dauki mataki a kanka bar ganin kamar baya gani ko baya sa Ido kasan Yana da Yar Kara ne shi yasa ba irin sauran bane,Duk Ma'aikatan gidan Sarki na bangaren Iyalinsa sai yarima ya barsu yazo ya fita da Kai Tanko mene sirrin ne?
Tanko yayi murmushin Jin Dadi yace Hali me kyau da iya sirri,da wasu ya fita da su na tabbata da yanzu zancen Yana yawo a garin Nan Amma kaga Dake nine kamar an Haka Rami an binne shi yasa Kuma Ina Shan kudi a Wajensa duk fita,so nake idan na fara gayu naje na Kama kafa da Matarsa ko Zan samu shiga ko yaronta Dan aike na koma,ko ya mai Dani Driver dinta me kaita makaranta kullum,Dariya sukayi Sani yace Ina goyon baya.

Yamma na Yi Tanko ya samu shi da sani Suka bada sanarwa sun je gida,Kuma gidan Nasu a gidan Sarki yake bangaren bayi,asalinsu Bayi ne su Tanko,duk a gidan Sarki aka haifesu tun daga Kan kakanninsu gaba Daya tsatson su tanko Bayi ne na kirki,Wanka sukayi da Sani Suka Sha manyan Kaya Shadda harda wata babbar Riga katuwa dinkin wani barmeme sai gidan Solo,Tanko Yana Shiga ya hango su Farida ta Kara haske ko ganeta baiyi ba yace ga wasu Babys can Sani muje mu zauna kusa da su ko ma sake daraja a idon Yan gidan nan,Gidan Solo an San Tanko sosai Yana liki,akwai Kuma wakar da Tanko yafi so Wato wakar Baba Ayi mini aure,dama kana ji a gidan Solo na Gaza an canja kida an sa Baba Ayi mini aure to Tanko ya shigo gidan,Ai Kuwa Kawai kida Suka ji an canja,Tanko ya samu guri ya zauna shi da sani kusa da Farida,Sai lokacin Farida ta juyo ai zumbur Tanko ya Mike tare da daga hannaye sama ya kwala ihun Nepaaaaaaaaaa......kowa ya maida hankali Kan Tanko Ana baza ido,me kida ya kashe gidan yayi tsit,Tanko yace Farida me Zan gani kece kika koma baturiya Haka kin tashi daga Yar baka Sari daddawa,ai tsabar hasken wannan yasa nace Nepaa ai kinfi Nepa haske ma,kece Lantarki Farida Kan uba wanne Mai ne Haka? Kumatun Farida ya shafa da hannunsa me kaushi yace Tangaran,Wannan ai kece Talliyar sunan wata kakarmu,kunya ta Kama Farida yanda kowa yake sheka Dariya ana kallonsu Ana Jin abinda Tanko ke Mata,Kida aka saki Baba ayi mini aure,Tanko Ya fisgi Hannun Farida yace sai sun hau sama sun cashe, Farida tana Jin kunya za a ganta da Tanko kamarta ita Farida a ganta da Tanko,Walida cewa take Dan Uwarki kuyi Rawar mu samu rabonmu,sauran kawayen su biyu Shahida da Jamila Jamcy Suka ce Dan Allah ki cashe karki kwafsa Mana,Farida Kuwa sai bala'i take ma Tanko tana harararsa,Ga Mutane Ana tafi,Tanko yace duk inda aka je sai an dawo an same mu,ko Ina Muna Nan,mu din dai mu din ne,Tanko yasa aka canja Waka me kidan sauri sauri Remix,Ya fara baza babbar riga,Dj yace Tanko wakar Kumurci zaka Mana ta da wacce ake katangar kauna,Wuri ya dauki tafi Dama an San Tanko ya iya bin wakar Nan ka rantse Dan dabar gaske ne,ai Kuwa aka sa wakar katangar Kaunaaaaa.....
Tanko ya fara ciccijewa a Gaban Farida Yana bin Waka Kamar shi ya rera yanda aka Yi Haka Tanko yayi da Waka ta dau zafi sai Kuwa ya Fisgi Farida ya jata a kasan wajen suuuuuuu ya wani murde Mata wuya shi a Dole shege,waje ya dauki sowa da tafi Nan fa Alhazawa Suka dinga ruwan kudi Ana yayyafin Naira ba karamin kudi Suka Tara da Tanko ba.
Chapter 52 · 0% Book details