← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 95

Sashe 61

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Kwana biyu Fuzail Tanko ya Nemo yace ya janye Neman auren Farida da yake Yi,Tanko Bai da ikon yiwa Fuzail musu Amma Kuma asiri yasa bazai iya Jin Maganar kowa ba akan wannan,Tanko rasa me zaiyi yayi sai Kawai Idonsa ya cika da Hawaye ya fara kuka sabo da bala'in da yake ji a ransa idan Matukar aka ce ya bar Farida shi Kam bazai iya ba,Mamaki ya Kama Fuzail da Manal,Yanzu har son Faridan ya Kai Haka? Tanko Kamar yaro ya daga Kai Wai ae,Tausayin Tanko ya Kama Fuzail sai kace tsafi Namiji da kuka Haka Kuma akan soyayya,Manal Itama sai taji Tanko ya Bata tausayi Yana tsugune a kasa Gaban Fuzail,ganin Haka duk sai suka kasa sake Yiwa Tanko zance Fuzail yace wannan wacce Jarabta ce Tanko,Tanko da Hawayensa yace Nima ban sani ba wlh ban San dalili ba,kana Addua Kuwa? Tanko yace Sosai ai ni kasan dama bana Wasa da Ibada,Azkhar kullum baya wuce Ni,jeka Kawai Fuzail ya furta,Tashi yayi ya fita da sauri,Manal ta kalli Fuzail tace Ni Kuwa baka min irin son nan sai dai in mutuwa nayi kayi kuka,Dariya ta bawa Fuzail ya gimtse ya fada jikinta ya fara Mata kukan karya,Ummi ce ta shigo ba zato ta Kama Fuzail dumu dumu ai Fuzail sai ya zarce da kukan gaske Kamar na gaske ya koma yi harda shesheka,Manal ta Bata Rai tare da tureshi Ni daga Ni baza kazo ka ci min mutunci ba sannan da masifa ta samu tace ka isheni,Ni Nace ka sa Hannun Jarin a can,Ummi tace Kai...Kai..wallahi ku kiyayeni Hannun Jarin ubanku tun kafin na karaso naji dariyar ku shine Zaku raina min hankali,Wannan shigar da kika Yi uban wa kika yiwa idan bakwa tare? Na Dade Ina zarginku dama Ana fada min Kuna tare kullum Amma ban taba Kamaku ba sai yau shi yasa na Kyaleku,Yau sai ka sake ta tunda baka da mutunci,Fuzail yace saki Kuma? Manal tana ji tace Ni magana ta Allah zuwa yayi ya fada min tsautsayi yasa yayiwa Yar Aiki ciki shine nace sai na fada muku shike Nan fa ya Kama kuka ba Dariya kika ji ba Ummi.

Tsoro ya Kama Ummi ke karki min karya wallahi Zansa a daure ki,Manal Tace ki bincika a gidan Nan kiji ta Mike tare da saka Hijab ta fice daga part dinsa Yana cewa kiyi Hakuri karki fada Dan Allah,au da gaske ne Fuzail? Ummi ta tambayeshi Mukus yayi Yana alamar rashin gaskiya,fita Ummi tayi zuciyarta fal da damuwa tana rokon Allah yasa ba Haka bane,a ranta Dariya tayi Tace so suke su Raina Mata hankali ta kwantar da hankalinta ta koma sashenta.
Ganin Farida ta dage baza ta auri Tanko ba Malam ya Kira Tanko cikin gaggawa yace idan ya shirya a sa Rana,Tanko gidan Sarki ya sanar inda za a sanarwa Maimartaba,Umarni sarki ya bayar a wucewa Tanko gaba ko yaushe a sa Rana a shirye suke,Yan Uwan Tanko da wakilan Sarki Suka je Malam ya matsa shi Nan da Sati biyu za a sa Rana,Haka aka tsaida ranar aure,Farida ta haukace ihun kuka take Kamar Mahaukaciya ta Kira Manal a waya ta zazzageta Wai duk itace ta hada Mata mugunta gashi Nan za a aura Mata Tanko,duk wani shiri Malam Yayi shi Dake akwai kudin ya Gama komai,Farida ba Wanda ta fadawa Haka ba Shirin da ta Yi,Farida Bata San Iyaye suna da power Haka ba sai yau,Kawarta Walida Tace ta gudu ta bar gida Farida Tace ba inda zanje Kuma ba Wanda ya Isa ya kaini gidan Tanko wallahi sai in gawata za a Kai,da a aura min Tanko gwara a bani ko waye a duniya,Walida duk da Yar bariki ce sai da Tace ke Farida ki daina cewa kowa,Farida Tace na ce Haka.

Belloti Allah ya kawo su Nasarawa Lafiya gidan Emeka yayan Uche suka sauka gida hadadden gaske daki Guda aka bawa Belloti,girki dama ya Saba da cin abinsu shi yasa ko Uwar me Suka dafa Belloti ci yake,Abinci ya Sha Snail aka kawowa Belloti ya kwashi gara,sai da yayi kwana biyu a garin Yana yawo Yana shakatawa sannan ya nemi gidan su Manal,Ai Kuwa har gidan aka Nuna Masa yazo a Galleliyar Motar Uban gidansa Uche,Yasha kana Nan Kaya yayi kyau Belloti akwai kyan diri,Yaci sa'a ya samu Yazed,Yana Fitowa ya Gane Belloti amma ya waye yayi kyau ya kile ya zama Dan gayu,Yazed yace ba Kai naji ance ka bace ba,Dariya Belloti yayi Suka tafa irin shegen Nan yace wlh Neman kudi kawai Kano nake neman arziki kasan bazai yuwu a rayuwa ka zauna kana kallo a fika kudi Kuma a fika nishadi ba, Ina karka sake idan baka da kudi ka nemawa kanka nishadi,Yazed yayi Dariya yace Haka yake dama Yazed baifi Mate din su Belloti ba,dakinsa ya sauke shi tare da kwalawa Farida Kira ta kawo Masa abinci,tana Fushi ta kawo sabo da tana Jin haushin Yazed an hada Baki da shi za a Mata auren dole,Belloti yaga Farida Yar gayu Malam irin wacce suke mafarkin samu wayayya, Farida ganin Belloti ya dau wanka Dan matashi sai ya birgeta Tace dama shi aka aura min da yafi,Belloti Dan Karya harda cewa af na manta ban kulle motata ba,Jin da mota yazo sai ta Kara Jin kaunarsa,Fita yayi Yana bin Farida da kallo,Yana dawowa yaji Yazed Yana zancen auren Farida,Belloti yace Nima na shigo sahun Yan takara,Saura kwana shida fa bikinta kace ka shiga ciki kaima ai ba Nema cikin Nema,Belloti yace na yarda da kaina Allah Yana so na Yana bani abinda nake so ni Haka nake da sana'a ta, aiki nake a babban Super market inji karyar Belloti yace da gidana a Kano Rufin asiri Ina da shi,Yazed yace baka da hankali,Belloti yace wallahi na shiga cikin Yan takara babban Yaya,Fuzail yace to maji ma gani ci abinci,Belloti shi sai yaji girkin ba Dadi sabo da ya Saba cin na Igbo akwai su Snail da su kwari kala Kala.

Tun daga ranar Belloti Bai sake zancen Manal ba kusan kullum sai yaje gidan su Farida sabo da ya ganta su danyi Hira,Ana Haka har biki ya rage Saura kwana biyu,duk abinda ake na aure anyiwa Farida shi dai dai gwargwado Kuwa Akwati biyar Fuzail ya hadawa Tanko komai anyi a mutunce,Ana gobe daurin aure Dangin Malam da Dangin Hajiya da su Annatu Suka cika gida Ana Shan shagali Banda Amarya da Mamanta,Farida kwana take kuka,Hajiya ta rasa inda zata sa kanta ta rasa me zata Yi a fasa auren gashi tasan abinda tayi,a ranar Ana gobe aure cikin mutane lokacin Malam da Yan Uwansa maza sun shigo Yazed suna ta Hira da Annatu da Dangi Hajiya ta fito tana Kururuwa Haka Kawai,Farida dama tana daki kukan take Hajiya ta cakumi Malam wallahi baka Isa ba kayiwa yata auren dole ba,dama ai ba sonsa take ba yazo da abin arziki ne nayi Masa asiri,asiri na muku wallahi wajen Malam naje azo aje Wajensa kuji Ni Nace ayiwa Tanko asiri lokacin munyi zaton me kudi ne Ashe Dan karya ne,kaima Baki na rufe maka nace a saka lallai ka daura auren wallahi Duk nice na jawo Hajiya ta zube kasa tana kuka,Malam ya bita ya kwada Mata Mari yafi biyar,ya rufeta da duka Yana Allah ya Isa tsakanina dake,Yan Uwansa ne Suka rikeshi mutane dangi Suka fito kowa Yana tofa albarkacin bakinsa Ana tsinewa Hajiya,Malam tunani ya fada yace wallahi duk abinda kayi sai an maka Nima nayiwa wasu gashi Ashe Ana ta Yi min ban sani ba,an cutar Dani an cutar da yarana kamar yanda na cutar Dana wasu,Allah na tuba Bai kamata ma naji haushi ba Amma wannan malamin sai an tona Masa asiri.

Malam murmushin bacin Rai yayi bayan ya Gama zancen zucinsa yace muje ki kaini wajen malamin,Keyar Hajiya aka tasa da yayyen Malam su Uku aka tafi da Yan Sanda tare da Yan jarida,Malam Dan Haru aka Iske a dakinsa Yana kwance Yana Jan carbi Kamar mutumin kirki,Hajiya ta Shiga tare da cewa munafuki tashi duk Kaine ka jawo dubunka ta cika.
Malam Dan Haru mikewa yayi yace wlh sai dai dubunmu ta cika da ke,Yan Sanda Tsawa Suka daka Masa Nan take Malam Dan Haru yace zanyi bayani,Yan jarida suna dauka ya bada labarin duk irin asirin da Hajiya tayi da mutanen da tayiwa da tun lokacin da Malam shima Yana malaminsa,Malam sai kuka yasan duk abinda yayi ne ake masa,Jin yanda Manal ma ba a kyaleta ba Yazed Ashe duk su Suka hanashi Rawar Gaban hantsi,suka Kori Annatu sannan shima aka Yi Masa,Bai damu da wannan ba sabo da idan ya tuna shima ya cutar da wasu da yawan gaske,a ransa yace dole ya fara Neman Wanda ya sani su yafe Masa, Kallon Hajiya yayi yasan shi ya jama Kansa shi yasa aka jarabce shi,Kuma tun farko laifinsa ne shi ya dinga wulakanta su Hajiya shi yasa har ta koyi zuwa gidan Malam,Dan ya koya Mata darasi yace idan an wuce da Malam kurkuku kema kiyi gidanku na sakeki saki Daya.
Hajiya ta Fadi kasa tana Malam kayi min Rai Malam na tuba Hajiya tana kururuwa,Malam yace aure Kuma da Farida da Tanko ba fashi sai in Tanko ne ya fasa.
Chapter 61 · 0% Book details