← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 95

Sashe 86

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yazed Yafi kowa Murna Jin ta Haihu lafiya,su Annatu da Farida duk sai gasu sunzo Suka ga Manal ras da ita,an gyarata an gyara Jariri tsaf,Hajiya Sharifa ta kalli likitar tare da furta ai he ku sallamemu ko? Likita tace ai mu Nan ba a gaggawa Baki ga wasu sai an sallamesu ba Kawai a dawo dasu jini ya balle ko wata matsala,Sai da Manal tayi wanka ma tare da canja Kaya,Farida tana zuwa ebo Mata tarkace gidan Sarki ta fada musu Manal ta Haihu,Kafin kace me sai turuwar zuwa sukeyi Ana nunawa Manal gata.

Yazed ta tambaya ka fadawa Prince kuwa na bar wayata a gida,Yazed Ango yace na manta wlh kukanki ne ya dinga daga min hankali,Nan take ya Kira Fuzail lokacin Yana jirgi wayarsa Bata shiga sai hakura yayi,sai yamma wurin Magriba aka sallami Manal Suka koma gidan Malam,Yan biki sai turuwar ganin jaririya akeyi Yar ficika da ita sai Kyawun masifa Hanci dodar.

Ai Kafin kace me su Hajiya Sharifatu an Dora tukunyar ruwan zafi katuwa,tana tafasa ta Kira Manal Suka shige toilet,Manal taga ganyen Dalbejiya Yan kauyensu sun samo sun wani gyarashi fes,Hajiya Sharifa ta sa Mata kujera tare da furta zauna ki Bude kafafun ga towel ma harda shi Zan gashe Miki wajen,Sai kace wata kaza Wai so kuke ki maidani baka da ruwan zafi Ni gaskiya bazan yarda ba,Wallahi ko ki tsaya ko na fadawa Annatu,Manal dai Taki yarda,Hajiya Sharifa ta fito tace Annatu Taki yarda fatarta Wai zata lalace,ita din banza wa zai barta ta lalace ai yanzu danya ce,Annatu lekawa tayi tace idan Baki tsaya ba wallahi sai naci mutuncinki wannan wankan mu shi zamuyi Miki,Manal Tace Ina da hawan jini fa na haihuwa, a asibiti sunce Banda ruwa me zafi da yawa Babu wankan jego ku tambayi Prince kuji,Annatu Tace da mu da aka Mana mutuwa Muka Yi wa yasan wani hawan jini,Hajiya ce Tace karfa ku kashe yarinya da ruwan zafi yanzu an waye mu a Nan birni ba a wannan Dan Allah karku Yi Mata babu wani danya Matukar zata samu abinci me kyau ba wata matsala,Hajiya Sharifa Hannu ta dagawa Hajiya baza ki koya Mana saka a mugun zare ba wanka Dole ayi mata..

Farida tazo zatayi magana Suka ce kema Muna jiranki nice Zan zauna a can gidan Alhaji Belloti Cewar Dahara,Allah sarki Manal Haka Hajiya Sharifa ta Mata wanka da ganyen Dalbejiya da tafasheshen ruwa,bayan Haka ta gasata da towel,Manal Nan Ana jiyo ihunta a tsakar gida,mutanen Kauye suna Kai wannan yarinya Bata da juriya yanzu wankan ma Sai an Masa Kuka,Manal Nan take ta fara Jin jiri jiri a Haka aka Gama suka fito Idonta yayi jajir na bala'in ruwan zafi Haka fatarta ma duk tayi ja dau,ta kalli Annatu ta fashe da kuka tana Dan Allah ku barni Haka karku lalata min fata,Annatu tace yo ai dole sai an daki nono da ganyen ruwan zafi sannan nono zaizo da yawa,Ni a barshi ko Madara na Bata,Baki Suka bude ga Nonon Uwarsa,Hajiya tace a ranta Aiki sai mutanen karkara.

Hajiya Sharifa ta dakko zanin atamfa aka yafawa Manal ki dinga rufe jikinki sabo da Aljanu me jego Bata Fitowa Haka Kawai he da dalili maza Higa ciki,Manal ta fashe da kuka taki Shiga ta tsaya tana shagwaba,Su Dahara Suka saki Salati kin Haihu ma baza ki daina iskancin Nan ba,to ki sani yanzu dai kin tsufa,Manal Tace walli ban tsufa ba ehe,Fuzail Bai San ta Haihu ba Yana dawo daga airport ko gida Bai je ba ya taho gidan hankalinsa Yana kanta yanda ya barta tana kuka,ba ruwansa da ayi Masa iso sai ganinsa sukayi ya shigo duk anyi zaton yasan an Haihu sai Barka ake Masa,Hajiya ma tace an samu karuwa Allah ya raya nayi Yar kawata Yar ficika,mamaki ya Kama Fuzail shi dai yayi Shuru Farida Tace yanzu ta Gama kuka an Mata wanka tana ciki shiga,Shiga yayi kawai Manal tana shafa Mai me kamshi,Hajiya Sharifa tana yiwa Jaririya wanka yace ban Gane ba wai,Manal kukan ta daina ta fara murmushi suna wani kallon juna Tace na Haihu fa dazu kana tafiya na fara nakuda.

Fuzail ya kalli Yar jaririyarsa yace Kan uba duk cin Nan da kike yi? Kaima ka fada cewar Hajiya Sharifa,Zama yayi a gefenta yace Mene ya samu fatar ko duk wahalar ce? Idonki sunyi ja,Hajiya Sharifa tunaninta birge Fuzail zata Yi ta fara bashi labari tun daga Fara nakudar Manal har haihuwarta da wankan da aka Mata na jego,sai taga ya juya Yana lallashinta,Hajiya Sharifa taga yanda suke magana cikin rada kunya ta kamata,Harda taya Manal Shiryawa,taji yace panties din fa Wanda na siya na jego? Manal Tace suna gida sai na koma,Hajiya Sharifa ta zaro Ido a boye kunya ta isheta tana Gama wanke jaririya ta dakko set din mayukanta zata shafa mata,Fuzail yace waccen blue din Zaki Fara shafa Mata sabo skin dinta waccen ya Mata karfi sai tayi 1year za a fara shafa Mata shi,Hajiya Sharifa a ranta Tace to Dan Iya,Wanda yace shi ta shafa Mata,Kayan ma da shishigin Fuzail duba kayan da aka kwaso yayi ya zabo wasu farare yace zata Fi kyau a wannan a sa Mata su,Manal Tace Baby Kamar pink din zasu fi,no a sa Mata white din,Hajiya Sharifa da harara tace idan Kun Gama zabin ku bani wacce Zan saka Mata ko na bar muku abarku ku sa Mata Ana muku Abu baza ku gode ba.

Mika Mata white din yayi tare da furta Thanks,Manal da shagwaba ta nuna Masa wuyanta Tace duba min Nan Kamar na kone ko? Kaiiiii wajen yayi ja baza a sake wannan wankan ba,tsaya na Miki Addua a wajen har da karanta fatiha kafa bakwai Yana tofawa Manal a wajen da Tace ya kone,Hajiya Sharifa kunya ta isheta da sauri ta karasa shirya jaririya ta sheka kyau,Tana kallo Fuzail harda kissing Manal a saman goshi babu kunya,Babu ko kunya,Sharifa da sauri Tace Kai karbi yarku ga ruwan da za a Bata Nan ta Mika musu ruwa Faro,Fuzail yace Bata bukatar ruwa, Nonon uwa zalla ya isheta, mu da aka sirka Mana da ruwa gashi Nan shi yasa kika ga Muna yawan mantuwa Bamu da wata basira Cewar Fuzail,Hajiya Sharifa tace yayi tsari man ai da ka sani Ungozoma ka karanta kaga sai ka dinga Bawa Mata shawara a asibiti,karyar banza maji ma gani ta Mike ta fice bayan ta dauke ruwan wankan ta goge room din.

Shi Kuwa Fuzail tuni yarsa yake yiwa Addua yanda sunna ta koyar,Manal tana Daure da towel yace a Bata nono Kinga tana cin hannunta,Manal tana kallon fuskarta a karamin mudubi Tace gashi Nan ai kana gani ka Bata,ya kuwa janye towel kasa,Sai ya kasa bawa Jaririya ya tsaya tare da kafe Boobs din me jego da kallo Yana hadiyar Yawu,Yace Kinga yanda Suka Yi kyau Suka Kara girma sai sheki sukeyi yanzu Kuma ba nine Zan Sha ba? Ya tambayi Manal,ba tare da ta kalleshi ba tana kallon Mudubi tace ka Bata Mana to ta Sha ko sai yunwa ta karasa ta kana ganinta dama karama,Fuzail yace na taba Nima? Dariya ya bawa Manal Tace idan ka tashi Cassava wa zai baka abin sakata ciki? Ba komai Zan jure ya furta Manal tace taba to ka tashi ka tafi tun kafin a fara min surutu,da Kansa ya Kama Nonon Yana cusawa jaririya a Baki Hajiya Sharifa da Dahara Suka shigo da kwanon kunun kanwarsu me zafi,Salati suka saki Manal Tace lafiya Wai? Shima Fuzail Bai kalle su ba ya maida hankali sai jaririya ta Kama nono,Dan Ubanki Manal Haka ake shayar da Jariri Ashe ku idan aka barku ku Daya kasheta zakuyi to wlh Zan fadawa Annatu dole a tafi Dake Kauye,Manal Tace me nayi Dan Allah tunda na Haihu kuke cewa a Bata ta Sha Kuma gashi Ana Bata kunce ba Haka ba Ni na gaji ne idan zai Bata ya Bata ai ba hanawa nayi ba gashi Nan,Fuzail yace yes....yes.....yeahhhh......Good girl.....ta fara Sha yace kin gani ta sani Allah me iko Kinga Allah ya Bata basira ta Gane abincinta,Manal Tace tana ja naji a jikina zuuuut.....Kai Amma da zafi cireta zafi....no....zai daina a hankali tsaya ta koshi....Hajiya Sharifa ta rike Baki tare da cewa yau mun higai me Zan gani Dahara kin gani,Dahara tuni kunya tasa tayi waje, Itama Sharifa ta fice da sauri,Fuzail ko a jikinsa sai ma Daya nonon da ya canja Mata Manal tana Gyara Mata sosai,yace to na Sha Dayan? akan me da girmanka banci komai ba fa so kuke ku ramar Dani Kai da jaririya,Kadan fa please zuka daya zanyi Ina Sha kadan Zan tafi,Fuzail harda Bismillah yasa Baki yana zuka Farida ta shigo,mamaki ya kamata ta koma da sauri,Manal taga shigowar Farida ta kwace abinta Tace kaje pls gobe ka dawo,gobe zamu tafi gida ko? Sai abinda Annatu Tace kana ji suna zancen tafiya Dani,Haba bazan Bari ba wlh Kima fada musu,Ummi fa an maida Aurenta da Maimartaba week din Nan zata dawo da Zama gaba Daya Nan gidanmu,Manal tana murna yace amma naji Dadi abin yayi wlh,Bari naje a kawo Miki kayan ci ko? Manal tace ae da fruits da nama,Karki damu ya Mike ya fita Yana ta kallon yarsa kyakyawa.

Sai da ya fita Annatu da su Hajiya Sharifa Suka Fado dakin Suka dinga yiwa Manal fada Akan shayar da jaririya suna koya Mata yadda akeyi,Sai da suka Gama suka fita Jaririya tana cikin Showel Farida ta shigo tana Dariya Tace Manal wallahi kunga ta kanku,Ina ganin Sweetheart Dina Maye Ashe naki Ogan ya ninka Nawa maita,yau fa kika Haihu ko kyankyami Bai Yi,Manal tace to kema Indai Belloti ne zamu gani Allah ya kaimu,ai wlh gwara Sweetheart da prince dinki.
Chapter 86 · 0% Book details