Sashe 18
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da Manal ta koma gida su Hajiya ko kallonta basuyi ba Itama Bata kulasu ba ta shige dakinta tayi kwanciyarta da Niyyar bacci Amma ya gagareta Kamar yanda ya gagari Fuzail,ga kwanciya a kasa ga Kuma tunanin Manal.
Gaba dayansu kasa bacci suka Yi sai dai Juyi kawai,Manal baccinsu na Jiya take tunani da yanda suke Muamula cikin Dan lokaci ya shiga ranta Bata son kasancewa sai kusa da shi,Shima bangarensa saman shimfidar zaninta yayi juyi tare da Jan Tsaki Yana mamakin Kansa daga Fitowa ganin rayuwar talakawa ko zai tsinci wani darasi a rayuwa Kawai ya hadu da yarinya mistakenly yarinya karama wacce Bata ma da ilmi,Yar Kauye amma gaba Daya tunda ya daura ido a kanta yaji duk duniya ba wacce yake so kamarta,Ji yake bazai iya rayuwa ba sai da Manal,Yana wannan tunanin ya Mike zaune abinsa gashi wayarsa Saura kadan ta mutu ba charge.
Kasancewar gidan yayi wajen Unguwa sosai ba gidaje kusa sai kukan wasu tsuntsu yake ji da wani jifa tassss a saman kwano,Tsoro ya Kama Fuzail ya Mike tsaye da sauri,kunne ya kasa yaji Shuru sannan ya koma ya kwanta,da kyar bacci ya kwashe shi.
Itama Manal Haka baccin tayi sabo da gajiya,Washe gari Sassafe ta farka,ai da sauri tayi wanka dama Bata sallah,Yau Harda saka wata Atamfarta me kyau Riga da skert sun kamata sosai sabo da ta Kara girma sun janye,Hijab ta saka Kawai yau Harda Shafa powder da lipgloss,Fitowa tayi tsakar gidansu duk su Sa'iha sun lalata shi,Farida da Hajiya tare da sauran Yaran sun zuba tagumi sunyi jungum jungum sabo da Basu da ko sisi yau ko na Koko Basu da kudin Siya,Hajiya a hankali ta furta tashin hankali baka da shi me baka ma babu, Farida ta zumbura baki tace Manal Sanda tana sana'a duk tsiya Muna ci yanzu ta rasa mun rasa.
Manal tana kallonsu sabo da suji haushi ta zaro dubu Daya da dari biyar ta karkade su tare da dagasu sama tare da furta Allah yasa ku isheni yau madarar gongoni Uku Zan juye a cikina yau Ni da Bawan Allah na bako na, Ta kalli Farida tare da furta Yar kurkura karfe nawa? Farida tana so a Basu ko dari biyu ce su karya da sauri Tace 7:30am,Manal ta kalli Yaran su Falaqi sunyi malaho sai Suka Bata tausayi ta zare dari biyar a ciki Tace Falaqi Zo ka karba ka siyo muku kayan shayi Allah bazai hana bawa abin kaiwa Baki ba,Allah sarki Masatura ta Mike tare da Furta an gode Manal Kai Falaqi tsaya na rakaka karka Yi shirme,Hajiya Kuwa da Farida tsabar ki Fadi ganin an Basu sai ma tabe Baki da sukayi Farida Tace mu Muna da kudin karyawarmu,ai ba ku na bawa ba kunji nace Hajiya ko Farida? Kanne na na bawa idan kune ai ko takardar littafi bazan Baku ba bare kudi na,ta juya tayi tafiyarta ta barsu Nan suna hassada.
Direct Gidan da Farooq yake ta karasa tana ta sauri,a lokacin Fuzail ya fito Kofar gida yafi sau goma Yana jiran ganin ta inda zata bullo sabo da Haka Manal ta samu Kofar gidan a bude ya gaji da jira ya koma dakinsa ya kwanta,a hankali Manal ta lallaba ta shigo gidan tare da wucewa dakin data Yi wanka a toilet din ciki, Lallabawa tayi zata fito
Itama wajen Farooq sai ya rigata shigowa dakinta da zanin shimfidar a hannunsa gaba daya.
Sai da ya tsorata da farko Bai San ta shigo ba,Karfa kaji tsoro nice yanzu nazo,Murmushi ya saki tare da Mata wani kallo,Manal ta Kare Masa kallo taga yayi wanka ya Sa Daya kayan nasa na gwanjo,Shuru tayi sannan ta gaisar da shi tare da furta Ina zuwa,da sauri ya furta no Ina Zaki tafi Kuma? Minti Biyar Zan dawo,Okay ya furta tayi waje ta bar gidan sai wajen me shayi ta siyo cup biyu Hadi me kauri sai Bread harda kwai Bata je gidan Baba Me kayan Miya karba ba, tana dawowa ya karbi kayan Hannunta Yana murmushi,Farooq yace wow kin San a Kauye na taso ban Saba da Zama da yunwa ba,Manal ta kyalkyale da dariya Tace Nima wallahi haka ai bakwai na safe tuni na karya,Farooq ya furta me too Yana Bude tea din, yace to Ina karamin cup? Manal tace Sha ka rage min sai na Sha,Yana kallonta da mamaki Haka ya Sha ya rage Mata komai itama ta Sha ta koshi sannan Suka zauna basa wata Hira sosai.
Yace bani labarin kauyenku,Manal kanta a kasa tace Ni me zance to sai dai in kana son labarin tinkiyata da Sanuwa ta da kaji na,Ina so bani labarinsu ya furta,Manal tace Tinkiyata ce dai-Tinkiyata ce dai Watarana tana da ciki cin abincinta ya karu ta dameni sai na Bata abinci,Rannan Ina bacci ban sani ba tazo garin Neman abinci ta taka min bakina da kafarta kallo ka gani inda ya fashe ya Zama tabo,Fuzail Ya kalli inda take nuna Masa kusa da lips dinta babu Wanda zaice wani tabo ne ma,Fuzail yace Very Bad wannan akuya ba kyau,Manal da sauri Tace Kai kyakyawa ce Dan baka taba ganinta bane.
Dariya ta sake Yi Tace baka San Sanuwa ta ba ko? Fuzail ya fara Dariya shi Ina zai San wani Saniyarta yace no ban sani ba,Manal Tace Kallo ya barka ai baka gani ba da aka Mata ciki Manal ta rufe Ido da kunya tana ta dariya Tace Allah sabo da Yan Iskan Shanayen bana zuwa garkensu kunya suke bani,Saurayin Saniyata na Uku yaga Saurayinta na farko yaje wajen Budurwarsa ai Kuwa kishinsa ya tashi naje Zan tatsi Madara akan kishinsa na jaraba ya samu ya min Wata Masga sai Dana fadi,Fuzail ya Kama Dariya yace Saniyoyi suna Yin Budurwa Suma? Manal tana ta faman Dariya da nishadi Ana zancen Saniyarta sabo da Murna ta manta ma Fuzail Namiji ne tayi zaton kawarta ce Khaltum ta dage ta dada Masa duka a cinya tana Dariyarta Tace nayi Mafarki Jiya Tinkiyata ta Haifi Yan Biyar, Fuzail ya saki Kara sabo da iya karfinta ta dake shi,cinyarsa ya duba da sauri ya janye Wandonsa yaga wajen yayi ja,Manal Baki ta rufe tare da tsayawa cak da dariyar kunya ta lullubeta tayi Shuru kamar ruwa ya cinye su,Fuzail Murmushin me tsada ya saki tare da Matsawa can nesa da ita yace Ina jinki daga Nan kar dadin Tinkiyarki ya kwashe ki kizo kina Balla min cinya Nan gaba.
Manal tayi murmushi sannan ta dinga bashi labari wani abin baya ganewa sam,Sun Dade a Haka sai da Rana Manal ta karbo Masa Wake da shinkafa gidan Baba me kayan Miya,kasa ci yayi yace yaji. Haka ta Masa Sallama ta koma gida sai Yamma likis ta taho Masa da doya da kwai da yawa a leda.
Zata tafi ya hanata tafiya tare da kulle gidan yanda baza ta iya budewa ba,ta dinga rokonsa amma yace sai anjima zata tafi Dole ta hakura ta zauna har bayan Sallar Isha yaki Bari ta tafi karshe ma yace sai dai ta kwana a Daya dakin.
Manal tayi kawaici duk da cewa tana tsoro amma ta yarda da shi ta Kuma yarda da kanta,Zama tayi har yayi shimfidarsa a dakin da take ya kwanta,zata tashi ta bar Masa dakin yace tsaya na fada Miki gaskiya I'm serious tsoro nake ji jiya da kyar na iya kwana Ni Daya,ya kamata a sallami Ameer Haka ya dawo Ni tsoro nake ji ya karasa da shagwaba,Manal tace Ah ta fara sheka Dariya tace Namiji da shagwaba sai kace wata ni lallai Ina shagwabaka Dole kayi min shagwaba.
Ita Bata da zanin lulluba bare na shimfida ma ga uban sanyin tiles shimfida Mata nasa yayi yace kwanta ke yarinya,dama I knew kin tsorata to babu komai calm down and Relax okay? Manal dai ita Bata San ya fita Jin tsoro ba Amma ta Gane nufinsa sai tace to tare da kwanciya saman zanin,Dayan ya shimfida shima can nesa da ita ya kwanta abinsa.
Manal Dadi ya kumeta sai taji ta samu nutsuwa,Shima Haka yaji,babu wuta a gidan bare ya saka charge sai uban duhu da kyar yake haska wuri da wayarsa,Kowa ya kwanta yayi Shuru can taji Muryarsa me Dadi,muryar Dake sata nutsuwa ya furta Baki da phone waya?
Manal da tausayi tace Dan Uwa tayani jaje mutumin namu ya hana Ni mallakar ko ta dubu biyu ce,Farooq yayi Murmushi tare da tambaya waye mutumin mu? Talauci Mana cewar Manal,yanda ka bani labarin talaucin da kake ciki,gaka Maraya baka da kowa sai Yan tsirarin dangi a Kauye,gashi Dan kudin daka Nema da guminka ka Tara ka taho Nigeria zaka Yi Business ka nemi kudi Wannan marasa kirkin Suka cuceka Suka maku fashi da makami ai wallahi kaga rayuwa ka fini ganin ta duniya shi yasa Idan na kalle ka sai naji masifar tausayinka,sai naji Hawaye Yana Neman zubo min,Haka Kawai nake Jin tausayinka a rayuwa,ai gaba Daya kayi a rayuwa wallahi Dole ma na tsaya na taimakeka sai ka samu wajen Zama.
Farooq Yana Jin Manal Yana ta dariya a duhu yanda take da surutu Wai,Zafi ne ya dameshi sai zufa ya hada sabo da ba ac,wayarsa ya haska dakin da ita Manal ita sanyi ma take ji harda dukunkunewa a cikin Hijab,Fuzail ya dinga ta mamaki Yana kallonta,tana kallonsa taga yanda ya jike da gumi Tace Kai Kai a wannan sanyi sai kace Wanda kayi rayuwa a iskimo,Dariya yayi ta dakko Plate din Robar da Suka ci doya a ciki dama ta wanke shi tas gabansa ta koma ta fara Masa fifita da plate din Robar Yana ta Jin Dadi tana Masa tana wani Waka Fi.... Fi.... fi....a hankali ya kalleta cikin hasken yace Manalll.....wani Dadi sunan ya Mata dake shi ya fada,ta washe Baki Tace Dan Kara fada naji Yasin baka taba Kiran Sunana ba sai yau Fadi naji,Yana murmushi sosai ya sake cewa Manalll....Plate din ta ajiye gefe tace wayyo Allah ka iya fada,duk Hausar da Manal takeyi a Gaban Fuzail ya Gama haddacewa shi Bai ma San ta mutanen Kauye bace Hausar duk kalolin rantsuwar da Manal ke Yi ya iya tas.