← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 95

Sashe 88

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bangaren Farida Kuwa sai washegari wurin 12 Belloti yace suzo ya Gaida su Hajiya sai su tafi Kano,Haka Kuwa akayi ba Wanda ma ya tambayi Ina taje tunda aka ganta tare da mijinta,Sai da Belloti ya gaisar da kowa har da bawa Annatu dubu goma,Ita ma Hajiya 10k,Kishiya 5k,Farida tattara kayanta tayi Suka musu Sallama zuwa gidan Manal Suka sake ganin Jaririya Suka tafi abinsu sai Kano ta dabo.
Tanko da Amaryarsa Islaha suna ta cakaki su biyu rak Amma Kamar mutane da yawa ne a gidan,Islaha tace Yeeee Wasa ya Kare tare da kashe tv game din da suke Yi tana cewa yanzu nice Yar jarida na Zama Yar jarida zanyi Hira da Kai a gidan Tv, Tace ko zamu iya Jin ta bakin Alhaji T&k Wanda aka Fi sani da Tanko wanne irin gwagwarmaya ya Sha a rayuwa?
Tanko harda gyaran Murya tare da furta ehem gaskiya ba karamin gwagwarmaya na Sha ba sabo da har kanzo naci Suka kwashe da dariya,yace an taba kulleni na Sha Bulala dari sabo da Rashin ji na,Islaha sai Dariya take Tanko Yana ta Mata soki burutsu,Tace ko zamu iya Jin wacce Nasara ka samu a rayuwa? Tanko yace babbar Nasara ta itace na taba Zane Dan sarki Guda da hannuna sakamakon Bamu San shi bane wannan ma wata Nasara ce suna ta dariya sabo da munafuki Ameer ne ya fadawa Tanko a boye sun Zane Fuzail Basu Sani ba,Islaha Tace ya akayi ka hadu da Matarka? Ko zamu iya Jin irin yanda Alhaji T&K ke son matarsa?

Tanko yace Yo a Napep Mana na tafi Neman auren wata wacce nake sa ran Zan aura sai Kuna cikin ikon Allah a hanyar na hadu da wacce tafi waccen komai,Ina sonta da yawan da yafi gashin tinkiya musamman sabo da kyawawan halayenta gata Pepper soup me dadi idan Ina ci bana so Gari ya waye,Islaha ta rufe Ido tana Dariya, Tanko yace shima Yau muna dauke da babbar bakuwa Wato Hajiya Islaha Me farfesun Dadi wacce ake wa lakabi da an Isle Isle suna ta uban dariya da Hayaniya Islaha tace sunkuya kayi min doki doki,Tanko ya duka ta Haye sama Yana tafiya da rarrafe a saman carpet, Badi'at Amaryar Ameer ta shigo tana cewa Baki kuka Yi ne Haka,Islaha an matse cikin kana Nan Kaya wando legins da rigarta me dogon Hannu Fara gashin Nan ya Sha gyara,Sannu da Zuwa Aunty cewar Islaha Kamar babbar mace mamakin da Badi'at take kenan Yara kanana Wanda Kannenta ne na wajen Uku sun fita iya sakin jiki da Miji,ita har mamaki suke Bata Basu kunya,ita me yasa ta kasa ne har yanzu sai tayi ta Jin kunya da tsoro,gaisawa sukayi da Tanko Islaha ta kawo Mata lemo da snacks,Badi'at tace kwashe snacks Ni Abu me yaji nake so me zanyi da snacks,Islaha tace ganin ku Yan Abuja ne ai shi yasa Naga sai Zaki da maiko,Tanko yace Nima nayi tunanin hakan,aka kawowa Badi'at wani potatoe balls yaji nama da kwai,Badi'at tace a ranta Yara da iya abun duniya Ni yaushe ma na iya wannan abin dole na tashi tsaye

Tana kallo Islaha ta zauna daram a Cinyar Tanko Tanko rada ya Mata tana kallonmu fa,Islaha ba sirri tace ai itama tana Yi Aunty ai itama ta fimu su da suke Yan Abuja,Badi'at tayi Dariya tana cin abinta Tace kin dameni da Abujan Nan sai kace kasar waje,ke da Manal Haka kuke ce min wlh Zan Rama ne Komai nayi kuce Yar Abuja,Manal fa sun dawo kije ki gano jaririya me kyau wlh,Islaha Tace suna dawowa muka je ai da shi mun gano Baby,Badi'at tace Nima naje ai Ameer tun suna asibiti yake sintiri,Suna ta Hira Tanko ya tashi ya fice ya bar Islaha da Badi'at suna Hira.
Abokan aikin Tanko duk inda Tanko ya gilma sai sun Masa tsiya yayi kiba da haske,har ya gaji ya daina ma maida musu martani.

Manal Kuwa tunda Suka dawo Yan Uwa da abokan arziki suke sintirin zuwa ganin Baby,kaf Yan Uwan Fuzail ba Wanda bai je part din prince ba dama tunda Suka dakko Manal Part din Fuzail aka kaita tare da Hajiya Sharifa, sunyi Niyyar komawa part din Manal Prince yace su zauna Kawai a Nan ga rooms Nan barkatai,Maimartaba ma da kafarsa ya taka yaje ya gano jikarsa Yana murna,Gab da Magriba sai lokacin mutane Suka tafi ba kowa sai Hajiya Babba,Hajiya Sharifa da Kuma Wasu kuyangin Suma Manal sallamarsu tayi kasancewar Prince Bai son taron masu Aiki,suna Gama Mata abinda zasuyi tace su tafi,dakin Fuzail ne kadai da kanta tayi kokarin gyarawa,Hajiya Babba murmushi tayi Kawai tace kinyi kokari Manal Haka ake son mace da karfafa jiki jiya Kika Haihu yau gashi harda gyara dakin miji Haka ake so kin birgeni wlh bana son mace me son jiki,Manal ta dakko room freshner da turarukan wuta masu shegen kamshi ta haura sama har toilet din Me gida sai da ko Ina ya dauki uban kamshi a saman prince.

Hajiya Babba da kanta tayiwa Baby wanka aka shafe ta da mayukan jarirai,Kayan da za a saka Mata Manal ta dakko wata pink rigar Mata da wando masu Dan kauri Tace a saka Mata wannan,Hajiya Sharifa ta watsa Mata Harara tace ke Wai Allah da yayoki Baki da kunya Yar fari ce fa, Hajiya Babba tana Dariya tace ai yanzu an daina wannan Hajiya Sharifa,sai da ta shirya jaririya tsab kayan ma Sai da Manal ta shafesu da turaruka,Sallah tayi sannan ta yiwa su Manal Sallama ta tafi,Hajiya Sharifa har da godewa Hajiya Babba,bayan Manal tayi wankan towel tunanin Hajiya Sharifa ai ta Gama wanka Haka zata kwanta ganin Manal da shigarta me kyau cass da ita,Ana yin Sallar Isha sai taga ta Shiga wani sabon wanka ta fito tana kamshi daure da towel har gashin an sake wanke shi,Hajiya Sharifa tace Sannu kwaduwa sarkin ruwa,Manal tace kawota na Bata nono Kar tayi bacci ta dameni cikin dare,Gashinta ta daure da towel ta zauna harda saka Hijab Kar a kallar Mata Nono a ciki ta saka Baby tare da Bata ta Sha ta ko shi,sannan ta mikawa Hajiya Sharifa ita,ta karbeta tana cewa tun safe Banga prince Chami na ki ya dawo ba,Manal tayi Dariya tace prince Charming fa Ni kadai nake fada Masa Anty,Kuma ba Chami ake cewa ba, Nan da 15mnt Zaki ganshi ai munyi waya.
Hajiya Sharifa nama ta jawo taci ta koshi ga nama Nan kala kala ake kawowa,su fruits, abinci lafiyayyu duk Manal ba Wani ci take ba amma Hajiya Sharifa komai ci take da maganin zawonta kusa idan taci taji alamar cikinta zai rude sai ta Kora maganinta.

Tana kallo Manal ta busar da gashinta da handdrier ta gyara shi Yana sheki da kamshi harda Hairspray ta fesa ma gashin bayan ta shafa body lotion, English gown ta zabo Wata doguwa fitted me gajeren hannu Yellow and Red,Hajiya Sharifa tana kallon rigar yanda ta fito da shape din Manal ta ko ina,ta sheka kyau,Hajiya Sharifa Tace yau Nahi he kace ba ke Kika Haihu ba,karfa kisa ya kasa Hakuri wlh kije ki jefa shi a sha'awa bayan kina jego yaje ya hadu da wata budurwa ta lalata Miki shi,Manal Tace ba Wani Abu sai dai dama can Idan Dan Iskan Ne amma ai akwai hanyoyin da zai gamsu ba tare da anyi komai ba,Hajiya Sharifa harda shewa eheheheeee Ahayye lallai Yarinya Manal....Yar hekara hya bakwai zuwa hya takwas auren bara ke kike fadar Haka lallai duniya tazo karhe ayi mugani.

Manal tana Dariya ta Gama tsara kwalliyarta a Gaban mirror ta Mike tsaye tana kallon kanta Tace wa zai ce na Haihu wa ma zai kalle Ni yace Ina da aure? Alhmdllh,Hajiya Sharifa tace to wani kokari Kika yi akan kin Haifo wannan Yar ficikar? a nakudar me kika Yi he kuka da abin kunya an Gama zagin Miji za a koma wallahi ki kiyaye Wato har kin manta wahalar da kika hya ko?

Suna Haka Fuzail ya shigo da Sallama ko Ina an kalkale shi tas,dakin da suke ya shiga tare da gaisar da Hajiya Sharifa,tace an dawo kenan yace ae Sannu da gida ya dawainiya? Alhmdllh ai mu Kam sai godiya tunda nazo nake ta cin kaji nake ta cin nama daban daban daga wannan sai wancan Kai gaskiya gidanku yayi,Haka nake son gida Inga girki Yana sauka Akan lokaci,kaga Yarima nifa Dan Tani Alqur'an idan naje gida to Indai za a kawo min girki to wallahi Kar ma matar gidan ta kulani,Kawai ta kawo girkin ta koma dakinta ta barni yafi ta hanani abinci ta zauna muyi ta surutu Ina hamma, ai kafin na koma Kauye inaga sai dai nayiwa Alhaji sa'idu waya kafin na koma a Sara min kofa a sake fadada min ita Kar tayi min kadan,Dariya Fuzail yayi yace to kiyi ta ci da yawa,yo ai ba he ka fada ba Dan Nan.
Chapter 88 · 0% Book details