Sashe 55
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bangaren Tanko Kuwa Izni ya Nema na ganin Fuzail,Bayan ya same shi a palonsa Yana latsa waya time din Manal tana sashen da shigarta ta Kuyanga tana kitchen tana sheka girki a matsayin Yar aiki ce,Murya Fuzail ya daga tare da cewa kawo min Juice,Alright Prince Charming,Manal Bata San Tanko ya shigo ba,Baki Tanko ya Bude a boye Jin ta Kira Fuzail da wani suna na soyayya,a ransa yace Yar aiki fa ce,sai ga Manal shima Tanko yace Ashe Balkisa ce ba ke na gani dazu ba kince kin tafi taron Da'awa? Manal tace na dawo to tare da canja muryar, Fuzail yace Tanku Zauna sabo da Bai iya fadan Tanko ba sai dai yace Tanku,Tanko ya zauna tare da baza babbar riga,daidai lokacin Manal ta Miko Juice Fuzail yazo karbar Juice ya hada da Hannun Manal ya damki cup gaba Daya,Tanko yana kallo a Idonsa a ransa yace kut Haka abin yake dama Balkisa ba Wajen wa'azi take tafiya ba,Allah sarki Manal an hanashi kula matarsa ta sunna gashi sha'awa tasa Yana bin Yan Aiki kuyangi,Wayyo Yarima Guda Yana bin kuyanga,Allah sarki Manal Ina ma Ni ba me boye sirri bane da naje na fada Miki ki kula Kar ya shafa Miki kanjamau,Fuzail ne ya katse Masa tunani da cewa Ya akayi?Yana rike yatsun Manal Yana cewa lallen ya goge a canja min wani,Ido Tanko ya zaro yace wannan tsohon Hannu ne da Alama sun Dade wallahi bazan iya ba sai na fadawa Manal Ana ta zalintarta,Manal ta gyara Nikaf dinta tare da kwantar da kanta a saman kafadar Fuzail ta sarkafe yatsunta cikin nasa,Tanko ya diririce,Amarya da ango suna ta dariya a boye.
Tanko wayarsa ya zaro tsabar munafunci yayi Kamar Yana dannawa ya dauki Fuzail da Manal pics sannan yace Yarima dama fada maka zanyi nayi matar aure,Fuzail yace to Mene Nawa ciki ai can zaka fada inda ake kula da aurenku,Ba Haka bane ranka ya Dade mun Dade tare da Farida Yayar Manal,to Ina sonta Amma Bata so na Kuma Ni da gaske nake Yi Aurenta zanyi Dan Allah ka taimaka min ka sa min hannu ba tare da Matarka Manal ta sani ba,so nake ka daure min Gindi a kasar Nan inyi karya in aure ta idan ta shigo daga ciki ta Gane gaskiya,Nan Tanko ya dinga rokon Fuzail yana bashi labarin irin lalacewar da Farida tayi yanzu da yanda mahaifinta ke kuka da ita,Manal tana ji tasan komai ita tafi so ma Farida tayi auren ko ta nutsu amma ba irin Tanko ba sai ta kalli Fuzail Tace a boye karka taimaka Masa wannan ba aikin Allah za ayi ba tunda karya ce,Tanko ya gallawa Balkisa Harara sabo da tana kulawa Manal mijinta,ya kalli Manal wacce ta fito a suffar Balkisa ya ja kwafa a boye da Ido ya nunawa Balkisa Wai sai ya fadawa Manal,abin Dariya ya Bawa Su Fuzail Suka Fuske.
Fuzail yace yanzu ya kake so ayi? Tanko yace irin yanda kayi ka auri Manal,ita kaje Mata a talaka ta aureka karshe taga kai me kudi ne,ni Kuma ka dafa min inje a me kudi nasan dole zata so ni sai tazo taga Idonta,Fuzail yace wannan yayi Tanko maybe ma ko taga talakan ne kai ta koma sonka a Haka,Tanko yace wannan jihadi za ayi a ceto ta Yarima sannan Ni ko a gidan karuwai take Ina sonta a tallafa min.
Fuzail yace yaushe zaka je? Tanko yace ai Maganar taka ce tunda kudi zaka kashe min,sai ka min dinkuna ko ka karbo min Aron riguna manya da rawani na Alfarma,sannan dai....Fuzail ne ya daga Masa Hannu yace na Gane jeka Zan nemeka,Tanko a ransa yace shege Yarima dama ya kware a iya karya,Watarana karya tayi a rayuwa Watarana Kuma Bata Yi ba,Fuzail ya yarda da Tanko akan taimakon Farida zaiyi, Tanko Yana son Farida Amma badan sonta zai aure ta ba sabo da ya Rama bakin cikin da ta haddasa Masa iri iri sanadiyar wulakantashi da ta dinga Yi tana Gaya Masa magana yanda taga Dama.
Tanko ya Gama tsara komai a ransa tallafin Fuzail Kawai yake jira.
Salo Manal da Fuzail Suka canja yanzu Manal a Gaban Yan aikin gidan take zuwa ta shige part din Fuzail sanye da kayan Yan aikin Mata,tun ba'a Fara munafunci ba har zancen ya fara yawo a tsakanin Yan aikin gidan Yarima Fuzail yanzu Kuyangi yake lalatawa,Duk matan Yan aikin sai Suka shiga tsoron Fuzail,idan Fuzail ya Kira wata da Niyyar sata aiki sai yaga jikinsu na kyarma suna Tsoronsa suna ja da baya da kyar suke shahada suje,hakan Yana Bawa su Manal dariya,Yau ma Manal tana Gama Sallah Isha Fuzail ya Mata waya kizo Ummi Bata Nan tana gidan kawarta Ina jiranki,ai Manal sai tayi shigarta ta Yan Aiki ta fice tana tafiya tana Sanda tana waige waige a dole marar gaskiya,Yan Aiki maza da Mata sun buya sai leke suke suna munafuncin abin,suna kallo Fuzail ya Bude kofa da Kansa sai da ya fito har wajen part din sabo da aji dadin Kallonsa ya Fisgi Hannun Manal ya shige ciki da ita tare da banko Glass Door,Wanda abin ya faru a idonsu Salati Suka saki sai munafunci tsakanin ma'aikatan gidan,Yayin da gefe Daya Kuma ake Murna Maimartaba ya dawo daga Uk Lafiya.
Washe gari Dukkan Iyalan Mai Martaba taruwa sukayi har Fuzail, Manal ce ta shigo a karshe sanye cikin wata Arabian Gown Black and white tayi rolling da mayafinta,me kyau ce ta lefenta,gabanta Yana faduwa Haka ta shigo itama palon da ake taruwa an saka Sarki a tsakiya Yana zuba mulki,tunda ta shigo Angon nata yake Binta da mayen kallo sabo da Basu hadu ba,waje ta samu ita Daya can nesa ta samu tare da tsugunawa yanzu Kam ta koyi gaisuwar sarauta Haka ta Gaida sarki,Kallon yaransa yayi yace wace wannan? Da sauri Na'ima ta Riga kowa magana tana tabe Baki Wai Matar Yaya Fuzail ce,Sarki yace wannan Yarinyar ta Isa aure? Ai Bata Isa aure ba wannan zalunci ne,Iyayenta sun zalinceta,irinsu ke haduwa da Yoyon Fitsari,yarinya karama duk da kace laifi ta maka ai bai kamata ma ka kula wannan ba ai Bata da Hankalin da za a saurareta ma bare a dau fansa a kanta,Dariya suka kece da ita musanman Na'ima da Fatima dama Manal tafi tsanarsu sune suka Fi Mata wulakanci.
Sabo da yanda zuciyar Fuzail ke azalzalarsa ji yayi Kamar ya Mike ya Fadi gaskiya Yana son matarsa a daina takura Mata amma yasan Yana magana Bangaren Ummi ya samu matsala,Hajiya Babba ce tayi magana a nutse Tace Ranka ya Dade Maimartaba ai Sanda ko mu aka Mana aure ban fi 11 to 12yrs ba,wannan Kuwa gata katuwa zata Kai 17yrs kace yarinya ce,wlh abinda kukeyi Bai Dace ba,Bai kamata ba zubar da girma ne wannan,dole surukai su dinga Raina Iyaye,Maimartaba Yana son Uwar gidansa yace wani Abu na fada? Daga nace tayi yarinta,kina dai ji Gomnati yanzu yanda ake yaki da irin wannan auren na wuri,kuma lokacin da na aureki ai Nima yaro ne yanda kike yarinya,amma Fuzail 32yrs ita 17yrs,Hajiya Babba tace ai sai kuyi nasan dai dalilin da ake Mata Haka sabo da Bata gaji sarauta ba,Daga Mata Hannu Maimartaba yayi tare da ci gaba da cin Abincinsa,Fuzail ya kalli Manal zata Yi kuka.
Ido ya kyafta Mata Wai karta damu,Da Yatsansa yayi Rubutu a Iska a Gaban kowa ya zanawa Manal Hakuri.....Hakuri....Hakuri har sau Uku,sannan ya zana I love you,Mana ta bada hankalinta sosai tana karantawa,Duk Mazan suna kallo suna dariya a ransu,Amma sarki Bai kula ba Yana ta cin Abincinsa,matan ma Basu Gane ba,Amarya wacce Fuzail yake Jin haushi sabo da ta zagi matarsa itace tace Wai me kake zanawa ne a Iska? Sarki yace taimaka min ki tambayeshi,Fuzail yace Ni calculation nakeyi na wasu kudi bana so na manta,Hajiya Babba ce Tace Manal abinci fa? karya tayi tace naci a part Dina nasa an kawo min,Maimartaba ne ya kalleta Jin bakinta Yana Hardewa sabo da Fulatancin da take ji,Maimartaba Ya zauna a yankin Fulani Yana Jin fulatanci,sai Kuwa ya komawa Manal da Fulatanci ya juya Harshe,Manal taga Dan uwanta sai Suka koma Fulatanci da sarki Yana tambayarta da Kansa a Ina take da asalinsu da inda ta zauna,duka palon sai Suka koma Yan kallo,Manal mayya an tabo yarenta gaba daya sai surutu,Basu San me suke cewa ba,Fuzail sai Dadi yake ji yanda yaga Manal tana washe Baki yasan Hirar kirki sukeyi.
Maimartaba ne Suka ga yana dariya sosai suna magana da Manal,Baki Suka bude Ana binsu da kallo,sai da suka dauki lokaci sannan ya koma hausa yace wannan har Rigar mansu na sani,na San ma Mijin mamanta Ashe,tun lokacin Ina Aiki a ma'aikatar noma an turani kauyen shekarata biyar a Rigar Ina koya musu kiwo na zamani da Noma,Maimartaba yace Kin San gidan Ardon Iro? Manal Tace sosai ma Yana da Yaya Alhaji Manu Me shanu dari? Mai martaba yace kwarai Kuwa to a Nan gidan na zauna a Nan aka bani daki,lokacin Ina matashi Allahu Akbar,Manal Tace ai kasan Yafendon su ko? Sarki yace Yafendo me Furar tsafi ai tayi tashen Fura,Manal tace ai ta rasu wata Uku kenan,Allahu Akbar Allah sarki Allah yaji kanta,Ina Liman Anlalo Kuwa? Manal Tace ya tsufa tukuf yanzu ma Shanya shi akeyi a Kofar gida,Allah sarki rayuwa cewar Maimartaba,Fuzail murna ta Gama cika Masa zuciya shike Nan an Gama da sarki,Sarki sabo da Fillancinsa Yana son Dan Fulani Matukar kana Jin fulatanci ka Zama nasa Kawai.