← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 95

Sashe 5

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal ta Gama shirinta tsaf yau asabar yau zata taho Birni tun daga kauyen Bauchi,Yazed Yana Shirin zuwa Tasha ya taho da ita Yayin da Annatu da kanta ta kaita Tasha da kullin kayanta a daure cikin dankwalin atamfa,sabuwar Atamfarta ta saka ta salla wata ja da yellow dankwali Kuma irin Dan kanti ta daura tare da zamge kanta,goshinta Yana kyalli abinka ga fara sai goshin Nan yayi dau,Gaba Daya a firgice take yaune Karo na farko a rayuwarta da wayonta zata Yi tafiya me nisa zata bar Kauye,dara daran idanuwanta ta zazzago su Kamar zaka ce kyar ta zura da gudu,Manal zata Yi kuka tana Kallon Annatunta ta Glass din mota ta leka da kanta cikin yaren Hausar da baya fita sosai Tace Annatu ki dinga yin furarki kina kaiwa tallan da kanki ko Sabulun wanki sai ki dinga siye,idan naje Birni sana'a nikai Ina akko minki kuddin(Aiko Miki kudin)
Annatu tayi Dariya tace to Manal Dita Allah yasa Ameen ta furta tana murmushi Tace karki Yi kuka kinji Annata?Anna ta daga Mata Kai,Kaddara ce ta rabamu Annata shi yasa kike a ruga Ni Zan koma Burni wajen Yaya,Kinga yace karatu zanyi Nima Zan dinga Jin turanci karki damu Anna ga su Khairan Nan ko?Anna tace tabbas Haka ne Manal ki kiyaye kinji dai fadan da nayi Miki kina sauka ki sa Yazed ya bugo min waya,To Anna zak rakado Miki waya cewar Manal,Haka Annatu ta hau machine ta koma rugarsu ita Kuma Manal ta fashe da kuka ganin Bata San kowa ba ita Daya a mota sai passengers.

Hakuri Yan motar Suka dinga Bata Ana gaki katuwa Dake Amma kina kuka yarinya gari Daya fa zamuje Tasha Daya zamu sauka,Manal tana kuka Tace yo ai ban sanku ba Kawai na saki Raina Ina ruwana da ku dan zamu sauka gari Daya to Alqur'an bazan daina kukan ba,Mutane Suka dinga dariya taci gaba da kukanta a mota a Tasha,Me tallan gurasa ne yazo da tirensa Yana gurasa a sai gurasa yar Kano,a zo a siyi Yar Kano me Dadi ga sugar,Manal hawayenta ta share Tace Kai da gaske ta Kano ce? Yace kwarai kuwa,kudi ta zaro naira Hamsim Tace bani ta Hamsim naci ko ban taba zuwa Kano ba naci gurarsu wallahi,ba Wanda ya Isa ya min gorin Kano Nan gaba,Ana cewa Kano zance yo Ni Naga karshen Kano tunda naci gurasarsu,Wani Dan fillo da sandarsa yace Nima a bani ta dari Gurasar Kano Dadi gareta Yar Nan,Manal tace to Yasin Ni kadai zanci a motar Nan Baku Isa ba,Kai wallahi me gurasa ka siyarwa wani sai na fito munyi ta da Kai,Baki me gurasa ya Bude yace akan ta Hamsim Sai na fasa ciniki ke Yar uban waye? Manal tace Dan kaga dazu Ina kuka ance maka Ni saliha ce to aradu Ni ba kyaleka zanyi ba,Me gurasa ya Shareta ya Mika Mata ta Hamsim dinta yaci gaba da bawa mutane a motar masu siya sai kuwa Manal Tace Kai Karen mota daga min kujera na fita daga motarka dama ban biya kudi ba Matukar ba Ni kadai zanci gurasar Nan a motar Nan ba to bazan zauna a motar Nan ba,Ni ba a kwaikwayona Dan wulakanci daga na siya sai kowa yace zai siya ai ba ayi min Adalci ba,aka Bude Baki Ana kallon Manal ta dage sai ta bar mota,Driver wayo ya Mata yace zauna idan mun tashi duk Zan karbe gurasarsu babu me ci min gurasa a mota sai ke Daya Yar Anna,Manal ta washe Baki Tace laaaa kasan Annata? Me mota Yana ji da suna magana da Anna tana ta cewa Annanta sai yace ae mana na taba siyen nono a garken su,Tafi Manal tayi Tana Dariya Tace wallahi ka San Anna na yarda ai shanunmu kaga farar wata Saniya me katon kunne? Driver ya zaro Ido Yana dariya a ransa yace ai sai da na shafa Mata kanta ma, Lailahaillallahu aradu Sanuwa Tace to,Anna ce ta siya min ita idan na Isa aure za siyar ayi min kayan daki,wancan satin ma sabuwar tawa ta Haifi Yan biyu,Driver yace ai na sansu Yan biyun,Manal sai ta gyara zama Tace kowa yaci gurasarsa wallahi Driver yasan Sanuwa ta,Ana dariya Dake duk kusan Yan fulani ne a motar sai cin gurasa wasu fanke,wasu awara.

Manal tana ci Tace Shegu Yan Kano an Iya gurasa Allah yasa ba gumin gardi muke cinyewa ba,kasan idan suna kwabawa sai kaga gumin garada sharrrrrr Yana shiga cikin kwabin ,Wasu gaba Daya sai kyankyami ya kamasu masu tsamtsami Suka kasa karasa ci,Manal Tace kazantar da bangani ba tsafta gareta ta cinye a barta tas sannan Tace Driver kasan tinkiyata? Driver yace na ganta sau Daya ta fito Daga gidanku da katon cikinta wata Fara Yar budurwar tinkiya,Manal ta sake kwashewa da dariya Tace Allah ka santa Aradu itace Ina Bata dusar dawa kullum da ruwan Danwake,Driver yace ai ance kajinki ma cinye su kike Yi,Manal ta rike haba tana mamakin yanda Driver ya santa Haka Tace duk sati sai na Kama zakara ko kaza an yanka min na cinye abata kajina sunfi ashirin Amma duk na cinye su Saura Uku Yan kanana yanzu,Har mota ta tashi Manal Hirar Sanuwa da kaji takeyi da Driver wani ya amsa wani yayi Shuru Bai Santa ba,bacci ne ya fara kwashe Manal Tace Dan Allah idan anzo tashar ku tashe Ni Kar na bace,Ana ta dariya daga Fara tafiya,tafiyar da sai sun kwashe wajen 9hrs a mota.

Manal tayi bacci ta tashi ta koma bacci dare yayi suna mota,Basu sauka a Nasarawa ba sai 1am,Kuma sabo da gudun Matsala Yazed Yana irga time tun 11pm yazo tashar Yana jira shima a tashar sai da yayi bacci ya tashi sai 1am sannan wata mota ta shigo tashar itace wacce Manal ke ciki,lokacin ta gaji da bacci,Ana zuwa ta fara duba Yayanta rabon da ta ganshi ta manta sai waya,Yana kusa da motar Amma Bata ganeshi ba har Suka Gama Fitowa da kullin kayanta, Yana ganinta ya dinga Murna kasancewar tashar ko Ina haske ne,Hannunta ya rike ta firgita sosai sai da ta kalleshi sosai sannan Kuma ta saki ihu da tsalle ta cikwikwiye shi tana Yaya Kaine? Wallahi Kuwa Yaya Yazed ne cab Yaya Haka ka girma? Yazed Yana dariyar yanda yaga Manal gaba Daya muguwar Yar Kauye ta gaske shigarta kadai abin Dariya ne,Amma ta girma sosai ta Zama Yan Mata,yace Manal wannan girman fa Ina Zaki da shi 16yrs kin wani girma Haka,Manal ta washe Baki kyawawan hakoranta Suka Bayyan Yazed yaga Kanwar tasa ta Kara kyau na azaba sai rashin wayewa,dare yayi da yawa duniya ba yarda yanzu bana son tafiyar dare gwara mu kwana a tashar Kinga duk matafiya gasu Nan zasu kwana da Sassafe sai mu tafi,to Tace kawai,Gaban me gasa nama yaje ya Siya musu tsire me zafi,ya Siya musu pure water da yawa a Leda sai lemo Guda biyu ya jata inda yake safe tare da karbo Tabarma wajen wata me abinci a tashar tare da shimfida musu ya zauna,Manal Tace Yaya na gaji da Zama Allah kwanciya nake so Amma bana Jin bacci,yace kwanta to sai kisa kanki a cinyata,Haka Kuwa akayi Manal ta kwanta ta Mike sosai a Tabarmar tare da dora kanta a Cinyar Yazed,sai da ta huta yace to tashi muci naman sai kiyi Sallar da ake binki ki kwanta.

Ta Mike Kuwa tana cewa Yaya amma Kuna Jin Dadi a duniya ku godewa Allah iya hasken Wutar Nan ya isheni Ni nishadi ma,Tana cin Naman Tace shegiya karya Aradu harda kabeji da Albasa a cikin naman,Dariya ta bawa Yazed yace to bana son surutunki Manal kiyi Shuru mu Gama ci,sai da ta koshi ta Sha lemo da ruwa sannan tayi Alwala tare da Gabatar da sallolin da ake Binta,Yana kallon yanda takeyin ibadar duk kusan da gyara Amma baiyi magana ba,tana Idarwa ta kwanta a cinyarsa sai bacci shi Kuwa jingina yayi da jikin bangon Yana ta baccin shima har gari ya waye sukayi Sallar Asuba sai da gari ya waye Rana ta fito sosai sannan Yazed yace su tashi su tafi gida,Tunda Suka fito daga tashar Manal take kalle kalle tana kallon motoci Iri iri Tace wayyo Yaya Dole kuyi ja kalli garin ba gona sai motoci tana ta nune nune da yatsa har suka shiga Taxi zuwa gidansu.

Suna zuwa Kofar gidan duk taga an wuce gidaje na Alfarma amma su nasu gidan shine ma mafi kaskanci a layin Manal tun anan ta Bata Rai tare da cewa yanzu dama duk Wayar Nan da mukeyi Yaya Yazed a Nan gidan kake? Fuska ya Bata tare da furta wallahi zamu Bata zanci Ubanki Nan ba gidan Ubanki bane,Manal tace Kan uba tana nuna wani katon gida Tace dama can ne gidanmu ai da sauki,a waya idan muna waya Watarana kace abinci nake ci,Watarana wanka nakeyi Sisto,Watarana kace karatu,Watarana kace kana kwance hutawa kakeyi ashe duk a Nan gidan kake, Ni Ina ta hango ka a Aljannar duniya Ashe ina,Allah Ashe akwai Yan Muna birni,idan kana birni baka da kudi gwara na Kauye da Kai, Amma da Ko Malam ya dinga Hawa irin waccan motar ta nuna wata mota,Yazed yace shiga ciki muje ransa a bace,Manal Kamar Amarya tace kafin na Shiga gidan Yaya Bari nayi Addua zanyiwa kaina fatan Alheri, kafar damanta ta zura a cikin Kofar ta daga hannu sama Allah yasa Watarana na ganni irin waccan gidan me kyau,Allah yasa Watarana a dinga tukani a irin Arniyar motar can ko me gindin kwado ce Ina so,Allah yasa Watarana na ganni a jirgi,Sannan Yaya Allah yasa Watarana Dani da Kai mu dauki shatar jirgi mu kadai daga Ni sai Kai da Annatu da Malam.

Watarana mu kwana a hotel mu ajiye motar mu a ciki a rufe Mana ita da Tempol, Yazed ya rike Baki yace kema Irin Farida ce Sis? Manal tace a'a Nifa fatan Alheri nake yiwa kaina,shike Nan bazan yiwa kaina fatan Alheri ba Ni wallahi a wajen Allah nake Nema idan zaka roke shi ka roka da Babban masaki,Ina laifi ko motar Dubu dari hudu na siya maka ko ka siya min,Yazed yayi Dariya Kawai yace Ameen to muje,Ciki Suka shiga Farida ta fara gani.
Chapter 5 · 0% Book details