← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 95

Sashe 53

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida Ita ba rawa taje Yi ba Kallo sukeyi dankwalinta ya tuge Tanko ya daura Mata abinta Ana tafi raf raf,Takaici da bakin ciki yasa Farida ta fashe da kuka tayi fuuuu wajen su Walida ta fisge mayafinta zata fita,Mc ya tsaida ita taga an irgo kudi sunfi dubu goma an Bata nata kason,a Haka ma cutarta akayi Dan Lada aka San Mata, Nan take ta washe Baki sai Kuma ta daina fushin,Tace Ashe Haka ake samun kudi lallai Mata Dole su watse a Nan, Nima Watarana Zan Dan dinga Shiga.

Amma idan ta kalli Tanko wani tsanar kanta take ji gashi Tanko sai Signa yake Mata da Ido ,tashi tayi ta bar gidan gaba Daya,Tana Fitowa Tanko da Sani Suka biyota zai Bata hakuri yaga taji haushi ai Farida Sai ta kwashe Tanko da Mari har biyu tana dura Masa ashar,Tanko ya tsaya sororo Yana kallonta da mamaki,yace kin San ba Kya so a tabaki kike zuwa bariki,duk Wanda kika gani a Nan zuciyarsa babu tsoron Allah a ciki,bariki fa kika fito,ke in ba Ni ba ma waye zai saurareki,wallahi Kinga Marin Nan da kika min karshenki yazo,sai kin San kin mareni,sai nayi Miki abinda har ki koma ga Allah kina nadamarsa,Farida tace me ka Isa ka min banza gaja irinka,dakiki kazami irinka,in ka cika Dan Halak kayi duk abinda zaka Yi, kinyi da Dan halak cewar Tanko ya juya zai tafi sai ga Yazed Da Malam an saukesu a Napep,Malam ya rike Farida Ram Yazed ya ebo bulalansa ya dinga zanar Farida har gida kafin suje ma sun farfasa Mata jiki,Tanko yana kallonsu suna Kallonsa Kuma sun sanshi sun ganeshi har gaisawa sukayi ma ya tsaya Yana kallo Ana Zane Farida ya kyalkyala Dariya yace yanzun Nan akan na fito da ita Ina Mata Nasiha Nan ba wajen zuwanta bane shine harda marina,Malam yace ai Bata da mutunci Bata da tarbiyya na gode Tanko Allah ya saka da Alkhairi daka tayani tarbiyarta,Tanko yace ai da na kowa ne Suka tafi da Sani abinsu.

Washe Gari da safe wata Mahaukaciyar makara Suka Yi a bacci yanda Fuzail yayi bacci me shegen Dadi Wanda Bai taba yin irinsa ba tsawon rayuwarsa ba,Manal kuwa baccin wahala tayi Kawai gajiya da ciwon da jikinta ke Mata shi ya hanata farkawa har 11am suna uban bacci ba Sallah,Fuzail ne ya fara farkawa yaga bargon ma sun jefar dashi kasa gaba daya,tunawa yayi cikin dare yaji tana zazzabi jikinta yayi zafi ,lokacin da zazzabin ya sauka shine ta fara hada zufa ya tube Mata kayan jikinta gaba Daya shima ya zare nasa Haka Suka shige Blanket Amma yanzu sabo da bacci Bargon ma ya Fado Basu Sani ba Kuma jikinsu ba Kaya gwara ma shi Yana da boxers.

Murmushi ya saki ya shiga karewa Surar manal kallo a Sadaka Ido na ganin Ido,Yana ta Jin Dadi shi Kam ya Gama dacewa,ji yake kamar ya tashi ya taka rawa,Tunawa yayi da Medical Glass dinsa Wanda yake sawa idan zaiyi Aiki da Computer, wardrobe ta jikin bed ya jawo a hankali tare da dakko glass din me kyau fari tas me tsada ya saka a Idonsa yanda zaifi kallon Manal sosai duk na Idonsa Bai ishe shi ba sai da ya Kara da glass,Kansa ya sunkayar da shi Kamar Yana leka microscope Haka ya dinga kallon Boobs din Manal,Ya taho ta cikinta zuwa cibinta,Manal Ana ta bacci Yana ta dariya a ransa duk uban ac din bata Jin tana Shiga jikinta Kawai bacci take yi,A hankali yanda baza ta farka ba Yana tsoro Kar ta kamashi ya Dan Buda tsakanin kafafunta tare da gyara glass dinsa Yana murmushi yace Uhmmmm Allah ya Kara lafiya Jogodo,Yana Kiran Jogodo Manal ta farka a hankali ta Bude idonta ta ganta ba Kaya Bata San ya cire Mata ba,gashi yanzu har da Glass Yana ta kalle kalle,Kafa Manal ta sa zata kwada Masa ta saki Kara sabo da zafin da taji,Dariya Fuzail yayi kadan yace Sannu kin manta ne? Famu kika Yi? Dariya ma ya Bata harda Glass Amma ta danne,Glass din ya Adana Yana kallon jaraba har 11:30am da sauri yaje da Niyyar daukan Manal Tace karka taba Ni bana so tunda Kai cinnaka ne baka San na gida ba,Dariya yayi cike da Nishadi yace Haba Ambaby na,Kin yarda tayi Dole yaje yayi brush tare da wanka sannan ya daura Alwala ya fito tare da tada Sallah,A hankali ta jawo rigarta tare da sakawa tana dingishi taje itama tayi brush sosai tare da wanka ta fito,lokacin Yana jikin Mirror yaci Dan Karen gayu cikin wata sabuwar Shadda Milk,sai sheki da kamshi yake zubawa,Fuskarsa dauke da Annuri yake taje sumarsa wacce taci kudi,Manal Sallah tayi sannan tazo inda yake tare da sa hannaye ta hankadeshi daga jikin mirror din ita ta tsaya a wajen.

Sai da ta Gama shafa lotion dinsa ta gyara gashinta, rigarsa me dogon Hannu ta zabo ta zurma a jikinta ta Mata yawa sosai har cinya ta kawo mata,Tana kallonsa Yana ta gyara dakin da Kansa sai da komai ya dawo normal fes,Toilet zai shiga ya wanke tana kumbura Baki Tace na wanke Nan kafin na fito, Saman bed din ta haura yace taso muje naki room din Kar Ummi ta Zo,Ba musu ta Mike ya dauketa kamar jariyaya Yana cewa I'm Sorry nace,Indai Baki daina Fushi Dani ba sai na Kara Yi anjima kadan,Gwara ma ki daina fushin Nan sannan ki dawo Normal irin yanda Muke a baya Matukar bakya fara'a wallahi kinji na rantse sai na Kara Yi anjima kadan,Tsoro ya Kama Manal Taji ya rantse ta tsorata da halinsa,ba shiri ta washe Baki harda tafi Wai ya gani ta dawo Normal,Dariya yayi tare da kwantar da ita a saman bed din duk ya kwaso kayanta ya boye su a dakinta sannan ya Bude ya fito kenan sai ga Ummi.

Ummi fa taci gayu iya gayu wani lace ta zuba Malam fari Kal tana kamshi sai kace itace Queen din,Katon basket ne a Hannunta da kayan abinci yasan shi ta kawowa,Da girmamawa ya gaisar da ita tana murmushi Tace lafiya Fuzail? Wannan farin cikin fa? Ko wani Abu ya faru ne me Dadi bani labari Ina ji,gashinsa ya Sosa tare da Furta company na ne dama na mota na samu riba me tsoka,Wow cewar Ummi, mashaallah Son Ina tayaka Murna,Fuzail yana tuno dadin da yaji ya karbi basket din Dake hannun Ummi ya rungumeta yace Ummi ki tayani Murna da Allah abin Nan ba na Wasa bane Ni kadai nasan dadin da naji,Ummi Tace Hala kudin Nan dai suna da yawa Ni ban taba ganinka kana murna Haka ba,Fuzail yaki sakin Ummi ya Rungume ta Kam Kam Yana tuno Daren jiya,Ummi Bata San dawar garin ba sai ta Kama murna itama ganin danta Yana cikin farin ciki,Tunowa yayi Manal tana Jin yunwa fa,Abincin ya dauka yace wannan girkin special ne nasan Ummi ce ta min da hannunta Bari na boye abina a wancen room din yau shi Zan yini Ina ci,Ummi wani murna taji tace Kamar kasan Ni na zauna na tsara maka,Ina zuwa ya furta ya shige dakin da Manal take zaune a tsakiyar Bed a saman bed din ya daura Mata cikin sauri yace pls Baby Serve your self Ummi tazo ya fita da sauri tare da Jan Ummi palon kasa.

Manal taga su pepper chicken,ga wasu girke girke daban daban ai Kuwa taci duk abinda take so ta cika cikinta,Ummi suna cikin Hira sai Fuzail ya Mike zumbur yace Ina zuwa sai ya haura sama ya gano lafiyar Manal sai ya dawo,Ta rasa uban me yake a sama,ya Mike zai koma Tace Wai me kakeyi ne? Murmushi yayi yace Electric kettle na jona banso ya tafasa ban sani ba,Okay cewar Ummi,Amma me zaka Yi da wani Electric kettle yanzu? Fuzail yace hmm ai tunda nazo kasar Nan yawan jarabar cin shinkafa ya jawo Basir ya kamani kullum sai nayi gashi nake Jin Dadi Kamar mejego,Ummi tace Eyyaa Sorry my Son,kaga Doctor? Yace ya bani magunguna ma na fara warkewa,Good jeka ka duba Kar ya tafasa da yawa,da sauri ya tafi,Manal ta ganshi ya dawo tana ta Masa dariya saman Bed din ya hau yace tana kasa Yi min kiss na tafi,Manal ta Masa kiss ya sauka ya koma Yana cewa ki zuba min abincin kafin nazo nima Tace to.

Yana komawa ta Gama hada Masa abinda zaici a saman Dan wani tire ta fito daga dakin a hankali Sadaf Sadaf ta leka kasan daga sama,ta hango su a Palo suna Hira Ummi ta juya baya yau saitin kitchen take kallo kuma,Dan karfen steps Dan buga kadan da zoben Yatsanta,Fuzail ne yaji karar ya dago Yana kallon saman,Manal ta fito daga jikin bangon data buya ta daga Masa plate din sama ya gani,Da yatsa take nuna Masa bakinta Wai yazo yaci,Da Ido yace gashi Nan,a jikin bangon ta manne tana jiransa tana Yi tana lekowa suna kallon juna da Fuzail tana cewa ya taho da Hannu,kiss yayi Mata a boye tare da buso Mata shi,Ummi karaf ta kamashi Amma Bata Gane Mene ba,Tace Kai Fuzail Wai kwana biyu meke damunka ne? Kai kadai ka dinga abubuwa Wai Mene Haka,Kai Ummi me nayi? Gashi Nan kana Busa Abu da bakinka sama, No wani gashi ne fa na kujera zai hau min jiki shine na hure,Yana magana Yana kallon Manal Dake lekowa tana kiransa.
Chapter 53 · 0% Book details