← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 95

Sashe 2

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin Malam yayi Sallah Yazed ya fito ya kalli Farida Dake zaune tana Shan kunu yace me aka dafa yau? Sai da tayi minti biyu kafin tayi magana Sabo da ta rigada tayi mafarki ta Zama matar Dan sarki prince,tana yanga tace shinkafa da wake ce tana kitchen,Amma Dan wulakanci shine kuka bar Malam da yunwa tun safe da ya Sha Kunu da kosai har 5pm Bai ci komai ba,uban waye yake siyo abincin gidan idan ba Malam ba da dukiyarsa yake ciyar damu Yana tufatar damu da komai ma Amma shine za a dafa abinci baza a bashi ba? Hajiya ce ta fito Tace to jarababbe me hakkewa kannai baka da Aiki sai masifa idan Yana Jin yunwar uban waye yace Kar yayi magana a bashi abincin aikin banza,Tsaki Yazed ya ja Kawai ya Shiga Rubabben Kitchen din da Kansa ya zubowa Malam abinci a plate ya Iske Hajiya ta yanka harda salat da tumatur ya zuba,shima ya zubawa Kansa ya shige dakin Malam.

Malam Wanda Kansa Bai daguwa sosai da kyar yake iya ciyar da Kansa abinci sai Yazed ya hutar da shi ya dinga bashi a Baki Kamar kullum yanda ya Saba har Malam ya koshi sosai ya Sha ruwa Yana ta sawa Yazed Albarka,Shima Yazed yaci Abincinsa sannan ya tura Malam Suka fito ya kaishi Kofar gida gindin bishiyarsu ta Dattijai da suke Zama suna Hira Nan ya kaishi sabo da ya shakata,ai Kuwa suna ta Hira da abokai.

Shi Kuwa Yazed Toilet din ya wanke da Omo harda Detergent da yake siyowa na wanke farin kaya kullum shi yake wanke Toilet sannan ya gyara dakinsa Dana Malam,Bayan ya Gama yayi wanka ya shirya cikin wani Dan yadinsa dinkin matasa me kyau ya fita gab da Magrib ya dawo da Malam yayi Alwala zaiyi Sallah Shi Kuma ya wuce Masallaci abinsa.
Haka washe gari Yazed kafin ya tafi school shi ya zaro dari biyar kudin cefane ya bawa Hajiya ya fice abinsa ya barsu da bakin halinsu.

Yazed Yana fita Wata Yar wayarsa Tekno ya dakko wacce zata Kai dubu Arba'in da wani Abu irin dai ta matasa da suke Dan rage zafi da ita,Kira ya Danna bugu biyu aka daga Hello Yaya Yazed Manal ce Annatu tana Bayi yanzu zata fito,Yaya Ina yini? Murmushi yayi tare da amsawa yace lafiya lau sister ya kauyen naku? Allah Yaya mu ka daina ce Mana Kauye kana gani ma ginin Bulon Siminti har biyu ne fa a garin mu ai Billahillazi mun Faso gari muma,Dariya Yazed ya saki yace yaushe Zaki dawo gida ne zanzo har kauyen Nan na tattakaki yarinya ba ilimin Boko babu na Arabic itama laifin Annatu ne wlh da tun kina jaririya ta tafi Dake sai da nace ta bani ke na raineki Taki yarda da yanzu a Nan Nasarawa Lafiya kina Jin turanci sis sannan Ilimin addinin ma Sai kinfi samu haba Manal gaki kyakyawa ajin farko na tabbata kika dawo garin Nan ko Miji sai kinfi samun Wanda zai rike ki,gashi karatuna ya dau zafi da ace kina Nan Zaki taimaka min wajen kula da Malam,Kinga mu biyu Annatu ta Haifa da Malam ko ba komai Zaki samu lada,sai na saka ki a makaranta,Manal tace Allah Yaya? Sai nake ganin Kamar tallan furar Nan da nake taimakawa Annatu da ita yafi Lada,inji uban wa? Annatu ga kanwarki Nan Khausar da Khairan ai sun ishi Annatu dama tace kece bakya son zuwa birni.

Manal tace Yaya Annatu tace Allah wani satin zata hado min kayana na taho wajenka Wai nazo na zauna cikin Yan Uwana a gidan Ubana Kawai tunda kaga Mijin Annatu Yayansa su Khausar da Khairan yake kauna Kawai Ni Kuwa baya so na sabo da Ni agola ce jiya ma Sai da ya min duka akan na zubar da nono Manal ta rushe da kuka,Kuma Wai wani Belloti Dan Uwansa zai aura min har an kawo kudin auren ma shine Annatu Tace Kawai wani satin na gudo wajenka, Yazed da masifa yace wani Dan kauyen za a Baki? Wallahi kanwata Uwa Daya uba Daya ko an daura sai nazo an ware auren Nan gwara ki taho dama ke ba Wani hankali ne dake ba,kwata kwata 16years din za a Miki aure? Manal tana Dariya Tace Yaya na girma fa Allah baka ganni ba na Zama zankaleliya,Yazed yace to Ni dai ki taho birni Zan rike ki,idan kika Zo Nan Kinga dama Muna fama da talauci wallahi da kyar muke kaiwa badan ma Yan Uwan Malam Ana kawo Mana Yan kayan masarufi daga gonakinsa na Kauye ba da munci ubanmu,Ni Kuma ranar da ba makaranta sai naje kasuwa wajen uban gidana da nake Masa yaro Yana siyar da shaddoji,Manal tace Allah bazan dawo ba Haka Kawai Ashe wahala kuke Sha a birni,Ni bazanzo na dinga yini da yunwa ba sai dai kayi ta bani Hakuri a Nan Kuwa rigarmu ko banza na Sha Nonon Saniya na koshi,ko garken su Khaltum kawata naje na Sha nono na cika tumbi na,ga kayan marmari shine kake so nazo yunwa ta kasheni,Ni fa Yaya Allah ya gani ban San babu ba,bana Zama da yunwa,inyi talla na kaga a kasuwa inshi Burodi,kuli kuli,Gyada marau marau,in shi kosai na in shi fanke ranar Juma'a Annatu tayi Mana Tuwon shinkafa Miyar Taushe da manshanu ga nama ga tantakwashi in samu in Dibgawa ciki na Taushe Allah aradu Yaya bani dawowa Wani gari naku,Gwara in Auri Belloti na ko banza shayi Nika Sha kullum aradu sabo da Babansa me kuddi ne.

Yazed Yana ta dariyar Hausar Manal Sam Manal hausarta abin dariya wata ma kadan ake ganewa idan baka Santa sosai Bama baza ka fahimci komai ba sabo da fillanci take ji da shi ta taso a Haka ma Dan Annatu tana Mata hausa ne amma wata kalmar ma Sai tayi minti biyu Bata tuno me zata ce da hausa ba,Yazed yace kizo sisto na kullum abinda kike so Zan Baki Baki da matsala kina da Ni kinji,Manal tace yo Yaya kana Iya kashe min kuddi Naira dari kullum? Yazed ya dinga dariya Naira dari har kudi ce,Yace Dari Uku ma Ina Iya kashe Miki kullum,Manal ta washe Baki Tace Yaya Wai Annatu tace Sunana na farko da Malam ya sa min wai Wa'qia? Yazed Yana dariya yace kwarai Kuwa Ni Kuma Wai Falaqi,Manal tace to ya akayi? Yazed yace Ni Nawa sunan da girmana na yanka rago na canja suna,shine da aka haifi kaninmu Malam ya mayar da sunan a Kansa Wai Falaqi,Ke ma Wa'qia Ni na canja Miki na yanka Miki rago na zabar Miki suna me ma'ana kika koma Manal tun kina jaririya sanadin Haka Malam Me Almajirai Mahaifinmu ya tsane Ni,da tuni ma sunanki Masatura,Manal Tace Yaya Masatura Kuma da Naga ta kaina Allah yasa Ina da Kai Yaya,Ai kin San fa Malam Wai shi Dan Babban malami ne me Almajirai shine ya dinga wannan irin abun na malaman gargajiya to gashi yanzu Almajiran ma babu Allah ya jarabce shi da lalura Allah ya yaye masa,Annatu Tace Malam Wai yayi tsiya kala kala shi yasa watakil Allah ya jarabce shi,Yazed yace Uhm ai shi yasa mutane Basu ganin kimarsa tunda kowa yasan abubuwan da ya dinga aikatawa Amma Mahaifin mune mu ba ruwanmu Dole muyi Masa biyayya,Manal tace hakane Yaya ga Annatu ta fito bari na Bata Wayar Ni talla Zan tafi,Yazed yace ki dai Iya Furar Nan in kinzo Zaki dinga Yi Mana Muna Sha,Manal tana Dariya tace to Yaya ta mikawa Annatu Yar kwakurar Wayar wacce ta Sha manni.

Annatu Bayan sun gaisa Tace ja'ira ta tafi tallan yanzu ta dameka da surutu ai tunda me gidan Nan Bai son rike Dan wani Yazed nace Mata Dole ta shirya ta dawo gidan ubanta,wallahi kullum tsangwama,Harara daga tayi Abu zai Mata dukan tsiya,Rannan ma Sai Dana kaita gyara ya sata a gaba sunje gona Wai Bata Yi aikin kirki ba wallahi Haka ya Mata duka sai da ya tsaga Mata kashin hannu Kuma Dan zalunci ya korata tabi shanunsa kiwo ranar ita tayi kiwon shanun ga Hannu ya kumbura a Kan haka nayi yaji na tafi gidanmu Nima da kyar na dawo,gashi yanzu Wai ya kakaba Mata Miji sabo da Yana aikin noma a gonar Baban Belloti kyauta Bai so a hanashi noma kyauta shine ya karbi kudin auren Manal,Yanzu ba kudin ba mota Amma gobe Zan Kai tinkiyata kasuwa na siyar sai na hada Mata kudi ta taho Dan Allah ka kula da Manal Yazed Bata da hankali kasan dai a dajin Ruga ta taso ba Hankali ne da ita ba,Dan ma Ina Dan koya Mata karatun Addini da yanzu ko fatiha Bata iya ba,Yazed yace to Zan turo Miki katin MTN na dubu Uku sai ku siyar da katin a Kara Mata kudin mota sannan idan motar ta taso ku sanar min a waya sai naje Tasha na dauketa,ki fada min a tashar da zata sauka sannan Dan Allah ki sata a mota da kanki Annatu, Inshaallahu cewar Annatu,yace a gaisar min da Khausar da Khairan sannan Suka Gama Wayar ya karasa makaranta abinsa.

Kamar Yanda Hajiya ta furta da dare Suka tafi wajen Malam Haru Haru domin ya fassara musu mafarkin Farida da take yawan Yi kusan kullum,Malamin ko Kuma bokan ya kallesu Bayan ya Gama Jin bayaninsu ya sheke da dariya sannan ya Bata rai tare kallonsu ya Furta tabbas mafarkinki gaskiya ne, Miko min Hannunki,Farida ta mikawa Malam tafin Hannunta ya rike tare da kafe zanen tafin Hannunta da Ido Yana kallo sai da ya dauki lokaci me tsawo sannan yace Allah ya taimakeki,Saura baifi satikai ba wannan bawan Allah yazo har garin Nan gidanku,Kina da sa'a a rayuwa,mutum ne na kirki,mutum ne na kwarai me hankali me zuciya me kyau,Tabbas Dan sarki ne na gaske Amma Sam Bai Zama a kasar nan sai da yawo yake zuwa, sai yanzu Mahaifinsa yace Dole ya dawo gabansa da Zama.
Chapter 2 · 0% Book details