Sashe 9
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Godiya yayiwa Allah da kanwarsa Bata Shiga wata Hanya ta banza ba,Kafin ya Gama godewa Allah Manal tace Saura kadan Yaya na koma gidan karuwai Allah Bai sa ba,babu rabo da tuni kanwarka ta shiga duniya,Dariya Yayi yace Allah baya sa ba,suna zuwa Hajiya Amaratu tana ganin Yazed babu tambaya tasan Dan Uwan Manal sannan ita Manal Bata fada Mata dalilin barin gidansu ba Itama Dake ba wata ta kirki bace Bata tambaya ba,godiya Yazed ya mata sannan Manal ta musu Sallama tare da dakko kayanta zata tafi gefe ta ja su Jamila tace karku biyewa duniya ku koma gidan iyayenku yafi muku shawara ce,Da masifa Suka yo Kan Manal tace yo Ina ruwana kuyi ta Zama Nima Allah ya Kara min jarabar surutuna,Hajiya Amaratu ta galla Mata Harara tace dalla kuje,Yazed ya Kama Hannun Kanwarsa Suka tafi zuwa gida.
Farida sabo da naci sai da ta kwakulo gidan su Fuzail Jin labarin ance ai yazo gari ya dawo da Zama Nan Nigeria,tunda ta ji labarin kullum tana Kan hanyar zuwa gidan Sarki,gidane na mutane har wani part din zaka iya Shiga sabo da gidan sarauta ne gidan talakawan sarki me Adalci,Cikin fadawa masu tsaron gidan Sarki Farida ta samu sai da ta Zama Budurwar wani bafade sabo da Kawai yayi Mata hanyar ganin Fuzail,Duk ranar da take zuwa Kuma sabani sukeyi da Fuzail ko ya fita ko kafin ta karaso ya shige part dinsa.
Bafaden me suna Tanko Yana bakin aikinsa Farida ta shigo ta Sha uban wanka cikin lace dinta pink na Sallah,Tanko ya kalleta yaji ta birge shi a rayuwa,tana zuwa ya ja ta can lungun wani part inda suka Saba haduwa Wanda ba kowa a wajen,Cikin Rada Tanko yace na gaji da aikin banza ya kamata Nima tunda kince na Zama saurayinki kafin kiga Dan sarki Fuzail ya Dace Nima a dinga Dan bani Ina Dan runguma ko Yaya ne,Farida tana kallonsa Tace amma ka tabbatar zaka shigar Dani har part dinsa Nan gaba? Tanko da sauri yace sosai ma ya fara kokarin rungumeta,Farida Bata son Tanko wani mugun wari ma yake yi Amma Haka tana gani Tanko ya rungumeta sosai,bakinsa Yana feso wani wari marar Dadi ya Miko Mata bakinsa Yana Ehemmm.....muje....muje....Yana magana Yana cinno bakinsa gaba,Farida tana kautar da Fuska gefe tana yatsina tace wannan sai ranar daka shigar Dani part dinsa,Tanko ya sake Kankameta tare da daura hannayensa a saman Kirjinta Yana shafa Manyan Boobs dinta Yana lumshe Ido,Farida tana gani sai da Tanko ya Dade Yana Shan Dadi sannan ya sake ta Jin Kamar motsin mutum na tahowa,ko yaushe Farida na zuwa ba a San me take aikatawa ba Kuma da Sanin Mahaifiyarta Hajiya komai tana Bata labari idan ta dawo,Haka jiki ba kwari ta dawo gida Bata samu ganin Dan sarki ba.
Kamar kullum yau ma tana Bata labari tare da kwanciya a Cinyar Hajiya Tace mafarki na ya kusa tabbata,Hajiya tayi murmushin Jin Dadi tare da cewa ai nasan idan ya Kalli jikin Nan naki bazai iya dauke Ido a kanki ba,Allah ya bani ya sankaceciya,Farida ta kyalkyale da dariya tana Jin Dadi tace yama Isa yaga hadaddiya kamata ya tsalle ke Ni sannan ya kasa cewa Yana so na ai karya ne nasan bazai taba faruwa ba,idan ya ganki ma bazai iya daina kallonki ba Faridata cewar Hajiya,suna dariya kenan sai ga Yazed rike da hannun Manal sun shigo dauke da Sallama,Kirji Hajiya ta dafe da Matukar mamaki a ranta,Haka Farida ma gaba Daya sai Suka gigice,Hajiya tace ko nisa ba ayi ba? Maganin Malam Haru Hatu sai kace kumfar Omo fuuuu Abu kamar gaske Kinga har ya karye.
Farida Tace kiyi kasa da Murya Kar suji mu Amma Ni kaina na Dade da ganewa maganin Nan ya Kai sati Daya da karyewa sabo da yanda Yaya Yazed yake yawan fita da Alama duba Manal yake Yi,Kuma na taba ji suna waya da Annatunsu itama ta warware Haka Malam da Ido na naga Yana kuka Yana tambaya Ina Manal ta shige.
Dundu Hajiya ta dirkawa Farida tana masifa Dan Ubanki Amma Baki fada min ba ai da komawa zamuyi baza mu Bari ta dawo gidan Nan ba Sam Amma gashi yanzu ta dawo Allah ya tsare Amma yanzu zamu barta tunda kin kusa haduwa da Dan sarki ma nasan Kuma Zaki ganshi Kuma zai so ki,Farida tayi dariyar Jin Dadi tace Dan Allah Hajiya kyale banza na gaba yayi gaba na Baya sai labari Yarinyar da har yanzu Dariya ake Mata a layi ta kasa Dan canjawa ma bare a sa Rai zata waye me Fuzail zaiyi da ita.
Manal Bata San me akeyi ba da sauri ta karasa tana washe Baki Tace Anty Farida na dawo,Baki Farida ta tabe tare da Furta to Sannu,Hajiya Kuwa Tsaki ta ja Tace banza karuwa kin dai tafi karuwanci Kawai dalla malama tafi ki bawa mutane waje,Manal ranta ya baci tace idan ban Kifar dake ba a Nan shegiya Uwata ta haifeni,ba ruwana da wani girmanki tunda bakya Jan girmanki wallahi ba abinda ya dameni sai na Daki gyatuma ba ruwana,Hajiya Ido ta zaro tare da dafe kirji tace Ni din? Manal tayi fari da Ido tare da furta Annatu ce ke da Zan daga Miki kafa? Kin haife Ni ne? Ko Malam ce ke? Hajiya Tace a'a,Ko Yaya Yazed ce ke? Manal ta tambaya,Hajiya ta sake furta ko daya,Kai Manal ta girgiza da karfi Tace to tunda Kuwa babu Daya a cikinsu wallahi kinji na rantse dama sabo da Malam nake daga Miki kafa,Karfi gareni sai nayi kasa kasa da ke in tatsile Miki wuya,Ni Jariri ma idan ya Bata min Rai ba tausayinsa Zan ji ba,Kuma Aiki sai Naga dama zanyi daga yau ai ba tsoronku nake ji ba,sai abinda Yaya Yazed yace ko Malam yawwa ku Gane,ba ruwana da wani mafarkin banzar ku Zaki auri Dan sarki Ko Sarkin Zaki aura ba abinda ya dameni dake da Sarkin Zan hada inci uba ba tarbiyya ce Dani ba.
Yazed Yana ji Manal ta birge shi Hannunta Yaja yace muje dakinki Sister bana son Rashin kunya bana son zuciyar Nan Taki da masifa Wai a Ina kika iya masifa Haka? Tafi Manal tayi da shewa Ahayye Ayyiriririri wallahi Yaya kaga Yasin Ina Jin dadin kaina,rashin mutuncin Nan nawa Yana birgeni,Ina birge kaina da kaina,idan Ina cin mutuncin wani har wani nishadi nake ji a raina,musamman Idan babban mutum ya zubar da girmansa na hau saman girman nayi dere dere na take shi woooo Allah Hodijam ai idan kasan Ina Jin wata Waka me shegen Dadi Haka nake ji a raina.
Ni Yaya nafi so kullum Inga Ana fada shi yasa ma nake zuwa kallon masu Shadi a Kauye ko wajen kokawa,Yazed Yana ta dariya Yace Sister akwai fa Wanda Zaki gani a birni ko tari baza ki iya a gabansu ba,Manal Tace Allah kiyaye wallahi ba ayi su ba babu su Kuwa,Sai dai idan mutum Bai min rashin mutunci ba,Matukar zai zubar da girmansa wallahi ko Sarkin Garin Nan ne sai zage shi,Yazed kallonta Kawai yayi Yana dariya yasan Dan Bata ga masu kudin bane da mulki, Shiga ki gyara room Dinki ko ki koma dakin su Farida ku dinga kwana tare,Da sauri Manal ta Furta Allah kiyaye naje dakinsu aradu gwara na koma Kauye Akan naje wannan Dan akurkin dakin yo Yaya idan ma naje ai ba wajen da Zan kwanta na sakata na Wala,sai dai idan kwanciyar kifi Sadine kake so muyi kifi na kankara Wanda ake zubowa a kwali,Dariya Yazed yayi yace to Kinga maza kizo kiyi Mana girki tunda kika bar gidan Nan Rabon da mu samu girkin rana,Manal ta karba kayan miyar ta shige dakinta.
Tana zuwa dakin da ba komai sai katifa shi ta gyara fes sannan ta fito ta fara aikin girki da gyaran gida,tunda Manal ta dawo shike Nan Aiki ya dawo gashi ba kudin ma da zata dinga zuwa school duk kokarin Yazed ya Gaza ta cikinsu ma sukeyi,tunaninsu Yaya zasu ci su koshi,ganin Sabulun wanki ma Yana gagararsu sai ta samu Yaya Yazed a dakinsa Yana karatu.
Da Sallama ta shiga yace Manal bana hanaki saka wannan shegen kayan sakin na Fulani ba,Nan fa ba a daji muke ba,yanzu kalli cibinki a waje ga wasu Yan iskan kayan ado kin daura a jikinki so kike sai Aljanu sun shafe ki,gashinki ba dankwali,yanzu wannan kayan sakin wa Zaki birge da shi? Manal a gefensa ta zauna tare da turo Dan karamin bakinta tare da furta Yaya nifa Banga amfanin karatun Nan naka ba,gwara ma ka daina yafi kullum sai kashe kudi Amma baka samun komai ta hanyarsa Allah Yaya asarar lokacinka kakeyi,wani katon banza ya zauna ya kirkiro muku littafi Kuna ta fama da shi Ni ba gwara ma ayi min aure ba,Ido Yazed ya zaro yace Ina tunanin sakaki a makaranta kiyi Ilimi ki Zama Yan Mata masu aji Amma shine Zaki ce a Miki aure kina yarinya Haka Manal har aure kike so?
Ido ta rufe da tafukan hannayenta tana Dariya Tace Ni dai Allah bana son karatun Nan Kawai gwara aure na,Ni Banga wani ci gaba da kuka samu ba ta hanyar Boko gashi kana ta karatu Yaya Kudin Sabulu ya Gagara ai wallahi bature macuci ne kamata yayi Littafan nan manya manya na Boko su dinga yo kashin kudi Amma sai dai a karanta a banza kullum,Yazed ya murza kyawawan Idanuwansa yace to wa Zaki aura? Manal Tace me Rabo Mana,murmushi Kawai yayi yace Alright yanzu Mene ya kawoki? Tace dama so nake idan ka saka Kati ka latso min Annatu mu gaisa,sannan Kuma ka samo min jarin Gyada ko kwano Daya ce Zan na soyawa Ina siyarwa ko na Sabulu sai mu samu,Kin iya Soya gyadar ne? Sosai ma Yaya na iya, shike nan wannan ma dabara ce ki fara kafin a saki a school.