Sashe 31
Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa zaune suka Yi suka kasa tsaye Farida Tace ko wajen Malam zamu koma a Kori Saurayin Nan mu wargatsa zancen auren? Hajiya Tace Baki da hankali ai gwara mu kyaleta ta auri talakanta taje tayi ta Shan wahalarta,idan Muka watsa abin kika sani tazo ta samo wani me kudin gashi ke har yanzu Prince yaki zuwa wannan Mafarki naki fa na fara gajiya da shi gaskiya wallahi tallahi kwana Nan Zan fara dirka Miki duka cikin dare mun gaji da Jin sunan Fuzail Cikin mafarki yaki zuwa,Abu yaki ci yaki cinyewa gashi Dan kudin zuwa wajen malamin ma ya gagaremu komai babu.
Farida Tace zaizo ne Hajiya Haba zaizo ne karki damu daula ta kusa zuwa Kuma ai yanzu ma na daina mafarkin nasa gaba Daya na rasa dalili,tunda Farooq Dan Iskan Saurayin Manal ya bige Ni da tsuran machine dinsa ban sake mafarkin Fuzail ba ko da Wasa ,Hajiya Tace Allah yasa dai yazo Amma gaskiya na fara tsorata da lamarin Nan gata mayayyar Yarinyar asiri baya cinta,mu barta ta auri talakanta su karata ta fara zube Yara bala'i ya musu yawa,rabu da su mu koma gefe mu Sha kallo Ana Yi Muna kyalkyala Dariya.
Yazed da Bai yarda da Auren Manal ba Amma Jin hassadar su Hajiya karara sai yace a ransa za ayiwa Manal auren mu bita da Addua mu gani,idan ya kasa riketa ya sakar min kanwata Kawai,Manal kuwa dakinta ta koma ta kulle da key take ta Rusa kuka baza a Mata aure ba,tana kuka tana zagin karatun Boko.
Su Falaqi ne suka taho da gudu suna fadawa Malam Aunty Manal fa tana ta kuka tana zagin karatun boko,Malam hantar cikinsa ta kada gwara ayi Mata auren kawai,Da Kansa sukayi shawara da Yazed.
Yau da dare Farida so take ma ko a mafarki ta sake ganin Fuzail Amma abin ya gagara,ta daina mafarkin Sam,Farooq ta dinga tsinewa duk shi ya jawo Mata,Kwanciya tayi saman katifarta tare da danne fuskarta da pillow tana cewa Fuzail yau kazo Dan Allah,Zo Nayi mafarkinka Fuzail,Zo Mana kaji ta sake rumtse idanunta tana wutsil wutsil da kafafunta saman katifarta tana Yeewwww.......Zo......Fuzaillllllll.......Zo nan Nayi Mafarkinka, Hajiya ce ta leko Jin Surutun Farida,Tace da tausayi na cire Rai ba lallai yazo ba ko a mafarkin,Ina tsoro kar arzikin Nan ya wuce Ni,Farida Tace ai Kuwa da Bola Zan koma da Zama na haukace Kawai,Hajiya ta bude Baki tace karfa Muna Nan muji zaiyi aure? hmm ai Kuwa kabari ne yake kiran ko wace Amaryar wallahi da wata ta aure shi gwara ayi min daurin Rai da Rai a gidan yari yafi,ko Kawai ku Haka Ramin Kurege ku binne ni Haka a ciki,Hajiya Baki Bude Tace kina da hankali Kuwa? Idan kin mutu Ni fa? Farida Tace ga su Sa'iha ne,kuka Hajiya ta saki yau Ni na shiga Uku nasan da gaske kike Farida ta juya tayi cikin dakinta,Farida Dariya tayi ta sake yin Mika tana cewa Wayyo Fuzail ka rungumeni ko a mafarki ne Haka Farida tayi bacci Bata Yi ko mafarkin Tanko ba bare Fuzail.
Washe gari Manal kwana tayi tana kuka a dakinta ta kashe Wayarta gaba Daya, Yazed ya buga Mata kofa ta Bude Ido jage jage da Hawaye,Tsaki Yaja yace ke yanzu Baki ji kunya ba?Manal ta daga Kai Wai ae Bata ji ba,ai shike Nan kice idan da gaske yakeyi Malam yace ya turo manyansa bayan sunzo zamuyi Bincike muma,Manal sai kuka ya tsaya cak Nan take ta washe bakinta tare da Furta to Allah ya bar zumunci Yaya,Allah ya Kara Mana son junanmu,shi yasa Nake ji da Kai, ko kulata baiyi ba yayi tafiyarsa.
Tsalle tayi tare da fadawa saman katifarta sabo da Murna, Wayarta ta jawo ta Kira Fuzail,Lokacin Suna tare da Ameer a part din su Ameer, Yana dagawa yace ranki ya Dade,Dariya tayi tare da furta tare da naka,ka tashi lafiya? Nayi Fushi sai yanzu Zaki kirani tun safe Ina kiranki Baki picking ba,Kayi Hakuri Muna meeting da Yan uwa ne, Alright Yaya Yazed din me yace a kaina? Manal Tace ka lashe zabe nawan,Allah? ya tambaya, Tace sun dangwala maka Yaya Yazed ya maka Signing,Malam Ma Ya manna maka stamp a Office dinsa,Dariya Fuzail yake tare da furta Good My love, ai in fada maka shi da Malam sunce idan da gaske kake Yi ka turo manya,Kawai kice na Zama Ango, Ameer ya kalleshi tare da tabe Baki a hankali ya Furta sai kace wata Babbar Budurwa ji yanda yake murna kamar me,Fuzail yace kice gobe za a kawo kudin aure,Manal Tace Ina laifin ma Jibi ko Nan da kwana uku,Ameer yace ka nuna fa da gaske kakeyi ka fitar da yarinya kunya Kawai a barshi jibi za a zo,Fuzail yace Ameer yace Jibi yayi kice Jibi za a zo,Manal Tace to tare da kashe wayar ta fita domin sanarwa Yazed.
Yazed yace to ba damuwa,Fuzail ya sake Kira yace ta tura Masa number Yaya Yazed Bata San Mene ba ta tura Masa dai,Fuzail ya kalli Ameer yace yanzu ya za ayi kenan? Ameer yace karya ta Kare a aure dai kasan ba karya babu Wasa sabo da Haka yanzu yakin zamu tunkara Kawai ayi ta Kare,mu samu a sirri a fadawa Yazed komai,ita Kuma Manal Kar ta sani sai an daura muku aure wallahi idan ta sani zaku Yi fada ne kasan karya ba Dadi Kuma mun Raina Mata hankali,to ai munyi ne da kyakyawar manufa Banga abin damuwa ba,kasan fa Manal da sauran Mata ma yanda ta ganka tana so a Haka take sonka ba ruwanta da kudi,Ni na fada maka Manal sai an Kai ruwa Rana da ita Amma duk bala'i idan an Riga an daura shike Nan Igiya na hannunka sai yanda kaga dama,kaga Umminka da Sarki tare da Yan uwa Dole su kyaleta idan an daura yanzu Target dinmu Yazed da Malam su zasu sani a sirri farko kenan sai masu Kai kudin Aure kaga Abba na baida matsala Waziri Kanin sarki kasan duk aure idan ya taso shi ne akan komai Kuma an wuce wajen nayi Masa bayanin komai a nutse ya fahimta yanzu dama ai ba da Memartaba za a Kai kudin ba,manya ne maza,Abba nasan zaiji da komai tunda mun Gama komai,Fuzail ya kalli Ameer Yana Kora lemo yace kana so na da yawa Dan Uwa,anything for you Bro shima Ameer yace.
Washe gari Fuzail waya sukayi da Yazed yace zaizo gidan zasuyi magana shi da Malam,Yazed yace sai kunzo,washe gari Manal Bata sani ba ma Bai fada Mata ba, Shukrah tazo wajenta suna tsakar gida a zaune Manal,Sai sallamar maza ta ji,tana daga kanta suka Yi Ido hudu da Fuzail tare da Ameer Dukkansu Yardi Suka sa Ishurunka Maraya,Ameer nasa fari,Fuzail Kuma Sky,duk da Haka sunyi kyau,Shukrah ta kallesu Sam Bata Gane Ammar ba Wanda ta gani da gashin Bob merly wannan gashi ne Kawai normal,A ranta tace shi dai wannan Ameer abokansa duk masu uban gashi,Manal ta kalli Shukrah Tace shine fa saurayina me gashin,Shukrah dai tunda taga yadin jikinsa tasan Manal cikin wahala zata jefa kanta kawai Amma sai tayi Shuru da bakinta.
Anci Sa'a Hajiya Bata gidan sun tafi yawon Maula wajen danginta tare da Yarta Kuma kawarta Farida,Manal tashi tayi ta dakko sabon Hijab dinta data Siya me hannu maroon ta saka,duk tunaninta akan kawo kudin aure ake wannan meeting.
Shukrah Tace ko duk akan kudin Auren ake wannan shawarar? Me kika gani? Manal ta tambaya,No ba komai nasan dai idan mutum Bai da Hali sai kiga akan dubu goma Ana ta shawara a kanta,Fuska Manal ta bata tace Wai ku Yan birni meke damunku ne Haka? Kowacce kudi -kudi shi yasa aurenku baya karko,je Kauye ki gani wallahi yarinya tana mugun Shan wahala Amma ko yaji Bata taba Yi ba,Kuma yanda takewa miji biyayya sai ki rantse duniya yake Bata gaba Daya,ta dauki aure Ibada ne,ta hakura da Jin dadinta,wasu mazan ma zaluntarsu suke Yi Kawai Amma kiga tayi zamanta ta hakura,wasu ma su ke ci da kansu duk sun fice a hayyacinsu amma babu bazawara matashiya,Indai Kinga bazawara matashiya to mutuwa mijinta yayi ko kuma wata babbar kaddara Amma badai akan abin duniya ta fito ba.
Kije ki gani yanda butar me gida daban,kwanon abinci,ba a Isa ko Dansa yaci abinci a kwanonsa ko cokalin megida daban ne sabo da ganin darajarsa da mutuntuwa,Ana bashi girmansa komai sai da izininsa akeyi, Kawai kice Farooq talaka ne zasuyi shawara Bai da kudin kawowa Zaki min wani kwane kwane to a Haka nake sonsa ai ba ke Zaki zauna min ba,Shukrah ta zaro Ido tare da Furta Allah ya Baki Hakuri daga Wasa,Ameen wannan ba Wasa bane cin Fuska kika min ku dama Haka kuke Baku iya magana ba sai Kawai ku kwabowa mutum magana,shi yasa Wasu idan Suka Yi aure suke fada da mazajensu sabo da Rashin iya sarrafa harshe, a koma baya a duba rayuwar Iyayenmu ai ba Haka Suka Yi ba,ko a Bayan Ido mace ta zagi mijinta gani akeyi kamar ma Allah ta taba,Mukus Shukrah tayi.
Rannan Ina jinku kawayenki Yan wajen akinku sunzo kuka hadu Kuna ta zagin Mijin Yusrah,Kuma itama wawiya harda ita tana tsinewa mijinta tana zaginsa akan zai Mata kishiya Kuna tayata ita Kuma ta saki Baki tana ta tonawa kanta asiri wallahi ku gyara halinku barikin Nan da Iya shege muma fa mun iyata,kudin Nan mun San dadinsa hakura mukeyi Kawai Zaki fada min magana Ina ganinki Babba da hankalinki Ashe kema gososuwa ce? Shukrah tace to jaraba naji Haba wannan masifa Haka akan Farooq,Murmushi Manal tayi tace ai kece Ni Ina da zafi gaskiya,to Afwan cewar Shukrah.