← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 95

Sashe 25

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doya da kwai ta siyo da lemonta,Ta gaji da Halin su Hajiya Bata siyo da su ba ta kyalesu ta dawo gida da nata,tana zuwa ta zauna a tsakar gida ta baje abinci da maltina,Farida yunwa ta fito da ita ko za a tausaya Mata,Itama Hajiya ta dinga zaga tsakar Gidan ko za ace gashi Amma Shuru sai taje daki ta fito ta shiga kitchen ta fito,ta wuce ta Gaban Manal ta zabga Mata Harara ta wuce,ta sake dawowa Tace Allah sawwake abinda za a ce wani ne zai baka,me zaka Yi da kayan wani,Nima maganina kenan Dana ke karba,Farida tayi Mukus ita dai tana so a San Mata,Hajiya ta kalli Farida Tace Yar Iska marar zuciya sai kwalalo Ido kikeyi ke da kike shiga har gidan Sarki ki zaga inda kike so ko a gidan Sarki baza kici ki koshi ba muma ki taho Mana da shi banza lusara,doya da Kwan ce Baki sani ba kinyi asara wlh.

Farida tayi Shuru Kar ta fusata Manal ta hanata,Manal Bata kulasu ba sai ma kafa data harde kafa Daya Kan Daya ta daga gongonin Maltina ta tiltilawa bakinta tayi gyatsa me karfi Wai Dan suji tafa koshi,Wakar barmani coge ta fara Yi... sai dai tatashi nokai nokai sakarai Bata da wayo....muryarta ta Karo da karfi tana wakar sai dai ta tashi Nokai Nokai....Farida taja kwafa a ranta Tace Zaki sani Duk Randa na Zama Gimbiya Farida wallahi sai na tozartaki a duniya,Wayar Manal ce tayi Kara,Farida ta zaro Ido ita da Hajiya sai yanzu Suka kula da Wayar Manal,Farida ta taba ganin Wayar a Hannun Farooq ba shakka shine ya bawa Manal ita,wani bakin ciki ya Kama Farida Taya Manal zata rike Pop 3 ita tana fama da Vivo karama.

Manal Wayar ta daga tana kwankadar Maltina,Farida ta bayan Manal ta koma Dan taga waye ya Kira sai taga an sa (Maganin kuka na)Dariya ta Kama Farida Manal tana cewa Hello Farooq ita Kuma Farida da karfi Wai Dan Farooq din yaji ta sunkuyo da kanta saitin Wayar tare da cewa Yar Kauye Kawai Haka ake sawa Masoyi suna Wai wani maganin Kuka na banza doluwa Ana My love,Honey, Sweetheart ke Kuma kina wani maganin Kuka na kinji kunya kinyi asara wallahi,Fuzail Yana ji radau a wayarsa yaji duk Maganar Farida,wani Sanyi da murna ta kamashi shine ma maganin kukan Manal wayyo shi Kam ya haye Ashe tana sonsa haka,ya dinga Murna da nishadi Farida tana ji Yana ta dariya ta waya Yana tambaya da gaske Haka kika sa? Manal tana tsoron zai kalleta Yar Kauye ta daure a kunyace Tace ae,Wow ya Furta I'm such a lucky Man,Baki Farida ta tabe tare da furta Jaki ta Kara gaba,shi baiji me Tace ba yanzu ma bare.

Me kike ci ne Haka? Manal tana Dariya tace ai yau Allah ne ya jefo min kudi daga sama Ina gyaran dakina in fada maka na tsinci dubu uku a kasan pillow,Yan dubu dubu sababbi baka gansu ba Kamar Kar na kashe su,sabon kudi da kyau suke a Ido Amma Haka na fara kashe su,Jiyama nayi sabuwar kawa anjima Zan baka labarinta sunanta Shukrah jiya tazo,Fuzail yasan sakonsa ya fara zuwa yaji Dadi Shukrah ta fara Aiki,Yace to dubun ukun ya kika Yi da ita?

Gashi Ina cin dadina da ita Bata fada Masa har kannenta da su Suka ci abinci ba sabo da Kar ya rainata da yawa ko taje tayi Abu Dan Allah ta zobe ladanta sai Tace ita kadai taci abin Dadi bayan ta karya,Yace Uhm Good kinji dadinki,Manal ta Mike ta bar ragowar abincinta ta saka Hijab suna waya tayi waje,Farida ba jira ta dauke ragowar ta lashe aka bar Hajiya sai hanji a ciki.

Manal tana fita katin MTN ta siya na dari biyar a cikin kudin Tace da Fuzail Ina zuwa Kawai ta copying Numbers din katin a kasa ta rubuta Ina sonka ta tura Masa ta text,Sai ganin Kati yayi ya shigo, ya dinga dariya Allah sarki tausayinsa take ji talaka ne shima bashi da kudi.

Sending back ya Mata abinta ya kirata Yana Mata fada shi baya so zai Fara sana'a Kuma Dan uwansu Yana Basu kudi,Manal Tace to Ni me zanyi da Kati tunda kana kirana,Nifa bana so na gode ban tura miki ba sai kece kina mace Zaki bani kudi karki sake turo min,Manal Tace to Dan Allah naji bazan sake ba Amma ka saka wannan Dana turo,Fuzail yaki yarda Ameer Yana jinsu yace Ni dalla bani na saka Nima naci irin kudin Prince,Fuzail ya kyafta Masa Ido Wai Kar ta ji,Ai Kuwa Manal Tace to bawa Ameer ya saka shi tunda na maka kyauta baka so ka watsa min kasa a Ido ai ya maka kyau Kuma Kar ka sake kirana munyi fada, idanba munyi fada ba ta kashe wayar tana cewa a bar katin ya gaji ya bushe a waya wallahi bazan saka ba.
Dole sai Ameer ne yasa katin Yana dariya Yana tsokanar Fuzail kaga na me tausayi inyee Dan gata har Kati ake sa maka,Fuzail ya share shi kawai.

Zuwa dare 10pm Manal tana dakinta suna waya da Fuzail da gwarancin hausarta tace Wai hadin gwiwa akayi da larabawa aka haife ka? Fuzail shima yace a'a mutum da mace Daya ne Suka haife Ni Zaki ce Wani Hadin gwiwa sai kace wani Business,Dariya Suka Yi gaba Daya tace kayi Hakuri ba nufina mutum da mutum ba Ina nufin Kai ruwa biyu ne Mamanka ko babanka ciki akwai Balarabe? Fuzail yayi Dariya yace ko Daya Haka Kawai Allah ya halicceni,Labarin Shukrah ta dinga bashi,yace kinyi Friend amma Banda fadar sirrinki ki kiyaye wasu matan Basu da hankali karki saurin yarda da mutum,to ai dama bazan saki jiki ba babu ruwana cewar Manal,Yace Good suna ta Hira a Haka suka Yi bacci ba tare da sun shirya ba.

Bayan Kwana biyu Shukrah Bata Zo ba sai a kwana na Uku taci kwalliya ta sake zuwa da Yamma,Manal sanye take da wani tsohon lace dinta pink,ta ja Shukrah Suka shige dakinta,Shukrah ta dinga Jan Manal da Hira har ta Dan saki jiki sannan Tace Manal a rugar da kika Bari kinyi makaranta? Manal Tace a'a Amma na fara iya karatun hausa da Dan wani turancin ma,Shukrah tace to ba damuwa ki tanaji littafi da biro daga yanzu kullum na samu time Zan dinga shigowa Ina Dan koya Miki wasu abubuwan,Manal tace Kai Amma na gode Allah ya bada Lada,Tace Ameen,Shukrah tace akwai wasu Kaya Kala hudu Dana dinka,Amma telan ya min shirme yayi min Dinki karami gaba Daya baifi size dinki ba,telan Nan ya cuceni Zan kawo Miki su ki dinga sawa naga kina da karancin sutura gaki Budurwa ya kamata kema ki canja,Manal ta dinga Murna tana godiya harda Rungume Shukrah sabo da ta tuno Farooq zai zo zance zata Masa kwalliya sosai shi yasa take ta faman murna,Shukrah Tace harda takalmi da mayafi Zan hado Miki,Manal tace wayyo muje ki nuna min gidanku kawancen Nan naki Naga da gaske kikeyi,Shukrah ta dinga dariyar Manal duk ta haukace akan kayan sawa,Shukrah tace gashi an Mana Albashi harda kayan kwalliya Zan siyo Miki,Manal ta Bude Baki harda Hawaye Tace Dole muzo gidanku da Farooq Dina ya Miki godiya ta musamman,Shukrah tace au har saurayi ne dake? Laaaa ai na kusa aure jira nake Yaya da Babanmu su dawo za a kawo kudi,Shukrah Tace mashaallah na tayaki murna Yar uwata yanzu dai kawo min ruwa na sha,Manal ta Mike da sauri ta fice lokacin Shukrah ta sake Bude kayan sawar Manal Wanda ta wanke ta linke,cikin ninkin zanin atamfa ta sawa Manal dubu biyu.

Bayan Shukrah ta tafi Manal tana gyara kayanta kudin suka Fado Amma wannan karon tsofaffin kudi ne tukuf,Manal tsoro ya kamata Nan take ta Kira Fuzail a waya tana kuka,tsoro ne ya kamashi duk ya rude Yana tambayarta lafiya? Tace kaga wani kudin na sake tsinta a cikin kayana dubu biyu,Fuzail ya sauke Ajiyar zuciya tare da furta kin bani tsoro wlh nayi zaton ko Baki da lafiya ne,Allah ne ya Baki karki ji komai ki kashe abinki,Zuciyarki ce me kyau Allah yake dafa Miki,Manal tana shesheka Tace nidai Kar nazo ko Aljani ne yake biyan Sadaki na,sai na ci kudinsa da yawa yace ya aure ni,Dariya ta Kama Fuzail da kyar ya Mata wayo hankalinta ya kwanta.

Hajiya ta kwana da yunwa ta yini Nan fa Ulcer ta shigeta me karfi ta fara ciwon ciki da ciwon baya tare da zafin kirji,kwana tayi tana murkususu,Farida Suma ta cikinsu sukeyi da kyar Tace ki tashi muje wajen Kawu Sani a kaiki asibiti,Hajiya tana rike ciki da kirji tace Manal ce tayi min asiri na sani a samu a kaini wajen Malam Dan Haru shi zai min magani wayyo gadon bayana,Farida Tace Ni wallahi wajen Ruma zanje ta bani dari biyar nazo naci abinci sai dai ki jira tukun tayi ficewarta ta bar Hajiya su Falaqi suna jinya, sai da Rana sosai Farida ta dawo cikinta a cike ko wajen Hajiya Bata kalla ba Ganin Manal ta tafi raka Shukrah sai ta shiga dakin taga irin kayan da Shukrah ta kawowa Manal sababbi na sawa Takaici ya Kama Farida,Wayar Manal ta hango saman katifa,da sauri ta dauki Wayar ta dauki ragowar pure water ta samu ta dura ruwa a ko Ina na kafafen Wayar sai da ta tabbatar ruwa ya ratsa Wayar sannan ta goge jikin Wayar yanda baza a Gane ba ta fice.
Chapter 25 · 0% Book details